Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 5

Sponsored Links

Page 5*

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Ɓambare jikinta tayi daga nasa ta ɗago manyan idanunta suka shiga cikin nasa hawayen da batasan sun taho ba suka gangaro kan kuncinta, gabadaya ilahirin jikinta rawa yakeyi saboda tsoro da tashin hankali.
Juyawa tayi tana kokarin kwasa da gudu tare da toshe bakinta da kukan yake kokarin fin karfinta, riƙe hannunta yayi da himmarsa cikin tashin hankali yace “ya Allah Habeebah me nayi Miki meye yasaki kukan ko bakiyi murna da ganina ba?”
Durƙushewa tayi ta turmutsa hannunta cikin ƙasa ta rushe da kuka me ban tausayi da ɗaga hankali, zama yayi da sauri yakai hannunsa don ɗago fuskarta ta tureshi da ƙarfi tace “ni nace ka daina taɓani ɗan birni na shiga uku so kakeyi sai an kasheni a garin mu yanzu idan wani yaga yanda ka kwaƙumani da jikinka zuwa za’ayi a faɗawa Jimo Ciwake kuma na tabbata kasheni zaiyi nima da wannan abin kunyar gara ya kasheni na huta kowa ya huta, duk jikina nasan yanzun warin maza yake….”

 

Rufe mata bakin yayi da hannunsa yace “Ke bafa haka bane tsoratar daku sukeyi amma babu wani warin maza da ake ji a jikin mace don namiji ya taɓata amma tunda bakiso shikenan yi hƙr nayi alƙawarin bazan ƙara taɓaki ba amma fah inada sharaɗina nima in kin yarda”
Da sauri ta ɗago tace “Wanne?” Lumshe idanunsa yayi ya ɗora habarsa kan tafin hannunsa ya buɗesu akanta ya motsa ƙaramin bakinsa a hankali yace “Wannan shigar zaki daina ki rinƙa killace jikinki kinga ita wannan shigar idan wani namijin yaganki da ita sako zai ɗarsu a zuciyarsa idan ya ɗarsu kuma zaiyi ƙoƙarin ya aiwatar aiwatarwar kuwa itace babban tashin hankali don zai rabaki da ƙimarki” sake kallonsa tayi tace “kamar ya?”
Miƙewa yayi zaune yace “Zaiyi yunkurin keta alfarmarki ta hanyar sanin ki ɗiya mace ma’ana a gwari² zaiyi Miki fyade…..” Miƙewa tayi a kiɗime ta dafe ƙirji tace “na shiga uku fyade irin wanda aka yiwa Tani ta mutu?” Jinjina mata kai yayi cikin jin daɗin yanda ya samu nasara cikin sauki yace “Wace Tani?”

 

Hawaye ta goge ta kama hannunsa suka nufi wani kurutturen ice suka zauna ta sake goge hawayenta ta ɗago ta dubeshi shima ita yake kallo tayi ƙasa da kanta tace.
“Tani yayace a gurina ƴa ce a wajen wan babana wato Baba Uda, ta girmeni amma soyayyar da take min tasa muka zama kamar ƙawaye komi namu tare mukeyi karshe ma Ni kusan a gdansu Tani na girma saboda gidansu akwai wadar yara abokan wasa nikuma gidanmu Ni kaɗai Jumme da Jimo suka haifa.
Tare muke zuwa gona tare muke zuwa tallen kunun zaƙi baban Tani Uda yana dafa Burkutu tare muke ɗauka mukai gurin bauta mu siyar, wata rana da bana mantawa ana bikin kamun kifi baƙi daga gari² sunzo domin ganin wannan bikin gwaninta da akeyi duk shekara domin kaf yankin nan a garin nan ne kawai akeyi kuma shi dama wannan ruwan na bayan gari da muke kira ruwan tsarkakewa tun tale² baa kamun kifi a cikinsa sai shekara shekara wannan tasa duk kifin da aka kamo zaka sameshi narkeke to wanda yafi kowa gwanintar kamun kifi a wannan shekara shine zai auri sarauniyar ƴammata ta wannan shekara.

 

Za’a ɗaukeshi a kaishi gdan Sarki aje a ɗauko sarauniyar matan shekara a kawo ta a daura musu aure kuma babu ruwan wannan bikin da cewa baƙone kai ko ɗan gari haka za’a bawa me Sa’a matarsa ya tafi da ita.
Kasan meye ya jawa Tani faɗawar azal?” Numfashi yaja ya girgiza kai ta sunkuyar da kanta tace “Kyau ɗan birni mu kininmu muna da wani irin kyawu da bansan ta ina muka sameshi ba bawai zallar kyawun fuska ba a’a direwar halitta ga kuma wani farin jini da kakanninmu suka roka mana abar dogaro ta bamu, Tani kyakkyawa ce ta wucce misali don duk kyawun nan nawa da ake faɗa ni banfi rabinta ba saidai fatar mu iri ɗaya ce wankan tarwaɗa, hakan yaja mata cincirindon masoya daga cikin garinmu da makota harma da ƴan birninku da suke zuwa kallon ajabin da aka halitta a wannan ƙauye namu, amma taƙi tsaida gwaninta.
Kwatsam sai Wannan shekara abar dogaro ta nunata matsayin sarauniyar ƴammatan shekara aikuwa maza suka rinƙa murna domin kowanne jarumi gani yake nasarar samun Tani tasace.

 

Haka muka dukufa shirye-shiryen wannan biki mukayi alibidi yafi kala goma Baba Uda da mahaifina Jimo har awaki da toron agwagi suka yanka mana dake haka al’adar take a gidan su sarauniyar ƴammata za’ayi girkin bawa gwarzon shekara.
Munata kaiwa da komowa munata hidima ranmu fes karma ni naji labari don ko hutawa banayi nakai na kawo ina tsokanar yaya Tani, abin dana fahimta saidai tayimin murmushi kawai idan na matsa mata sai ta kama hawaye inna tambayeta dalilin kukanta sai tacemin kawai tanajin tsoron a dauketa daga gari a kaita wani garin itadai tafiso mu kasance tare.
Idan ta fadi haka nima sai jikina yayi sanyi naji zuciyata ta karye mu hadu muyita kuka har sai Lamunde uwar Tani ta fatattakemu, ranar Wannan babban biki na al’ada daya zame mana idinmu mukayi kwalliya ta bam mamaki muka zauna a gda sai yamma muka nufi bakin kogi don mu ganewa idanunmu gwarzon mu muna tafe muna rera ƴan wakokin yabo ga abar dogaro domin gareta muke neman sa’ar wannan aure na ƴar’uwata Tani.

 

Tun a hanyarmu ta zuwa naji gabana yana faɗuwa nadai dake ban faɗawa kowa ba bayan mun isa mun zauna gurin da aka tanada domin mu ina riƙe da hannun yaya Tani ina mammatsa matashi naji taja ajiyar zuciya tace “Habibah” na ɗago da sauri don tunda nake da ita bata taɓa kiran sunana ba saidai tace dani Ƙanwa.
Idanunta naga yana zubar hawaye nayi saurin kai hannuna ina share mata ina girgiza mata kai ta riƙe hannu na tace “gabana yanata faɗuwa Habibah inajin kamar wani abu zai faru a gurin nan saboda jiya Liti ya rako Jamilu wannan ɗan birnin shine Jamilu yake cemin bai iya su ba domin bai gada ba kuma har yanzu yananan akan bakansa na aurena babu ruwansa da kafirci na indai zan aureshi domin shima ba ibadar ya damu da itaba, yace naje na faɗawa su Baba Uda kada su bari a fara wasan nan tun a daren jiya su ɗaura mana aure idan kuwa sukaƙi to shakka babu zaiyi kiran abokansa ƴan daba na Birni su ƙaddamar min ya rantse da Allansu abin dogaronsu indai ba’a bashi niba saiya barwa Tsaunin gawo tabon da har abada bazai goge ba”
Sosai kalaman sun girgiza duniyata amma saboda son kwantar mata da hankali sai nace “kayya yaya Tani kinada sanya abu a ranki kada kibar wannan soki burutsun haukan nasa ya dameki babu abinda ya isa yayi Saida sahalewar abar dogaro kuma inada yaƙinin bazata wulaƙantamu ba”

 

Numfasawa tayi ta girgiza kanta tace “Hakane amma fa nikam na tsorata” da haka na rinƙa kwantar mata da hankali har zuwa wani lkc da aka buga tambarin nasara guri ya bushe da iface iface da kaɗe kaɗe da bushe bushe.
Kwatsam saijin ihun mutane muka rinƙayi ƙura ta tashi muna ganin yanda mutane suke runtumawa da gudu su kuma makasan suna ihu suna ina Amaryar yau sai sun kasheta… Ai bangama jin hakan ba na mike na kama hannun yaya Tani itama ta rikeni muka runtuma da gudu muka nitsa cikin daji ashe dama Mun san abinda muka tunkara da munyi tsaiwarmu a can kilan abar dogaro ta bamu kariya.
Muna gudu muna haki duk mun sassoke da kaya jikinmu ya kakkarce muka iso wata sarƙaƙiyar duhuwa muka tsaya muna mayar da numfashi, can mukaji motsi ta bayanmu yaya Tani ta rikoni don na sake ta na nufi wata magudanar ruwa zan ɗebo mata kasancewar nasan bata jurewa ƙishirwa, naji tace “Habibah da mutum anan mu gudu….” Bata ƙarasa ba suka bazar da ita a gurin ta saki ƙara nima na saki Jami ya diro daga kan wata itaceyar mangwaro muna ganinsa muka zaro idanu Tani harda ajiyar zuciya tayi tunanin me cetonmu ne nayi saurin kwacewa daga hannun wanda ya riƙeni na nufesa ina sauke numfashi nace “Yawwa Jami kayi mana rai kada su kashemu mun……”

 

Wata mahangurɓa ya sakarmin a baki yace “Shegiya kin ɗauka cetonku nazo kafiran banza kafiran wofi uwarme zan ceta a icen jahannama kalidina fiha abada Nima rabona nazo ɗiba na rama cin amanar da kuka yimin kuma agabanki zanyi komai kije ki faɗawa manyan kafiran nine Jamilun Alh Kabirun Auta muga wanda karansa yakai tsaikon da zaija damu a fadin ƙauyen nan….”
Yana faɗin haka ya dakawa wasu samari uku tsawa yace me kuke jirane kuyi aikinku” kafin na Ankara sun kamani sun ɗaure sun sanya wani tsumma sun rufemin baki sun watsar dani a karkashin bishiyar kusa da yaya Tani.
Yaya Tani ta fara yunkurin tashi Jami yasa ƙafarsa ya taka ƙirjinta ta saki wata kara da nima bansan sanda na saki ba duk da bakina a daure yake don nasan ta azaba ce”
Zamewa tayi ƙasa daga kan icen ta rushe da kuka shima ya sauko idanunsa sun kaɗa sunyi jawur jikinsa har rawa yakeyi yakai hannu zai taɓata sai kuma ya tuna ya janye yace “So….sorry please inajinki Habibah kinga dare ya fara” ɗagowa tayi ta sanya hannu ta riƙo hannunsa tace “A gabana akan idanuna ɗan birni suka ketawa yar’uwata haddi suka keta alfarmarta sukayi mata kaca² su biyar ƙarata akanta ita kaɗai tana kuka tana Nishi tana gunjin azaba amma roƙonsu takeyi kada su taɓani kada su cutar dani, nima kuka nakeyi inata kokarin kwance kaina amma na kasa Saida suka gama abinda zasuyi lkcn ta gama galabaita sannan suka kwanceni na angajesu da ƙarfin da bansan ina dashi ba na isa gareta ina kiran sunanta ina jijjigata suka tsallake mu sukayi tafiyarsu sunata ƙyaƙyala mana dariya.

 

Na jima ina jijjigata sannan dabara ta fadomin na cire kallabina na nufi wannan gulbin dana nufa dazu na jikoshi nazo ina danna mata a jikinta sai kuwa taja ajiyar zuciya ta fara buɗe idanunta daidai lokacin da samarin garinmu suka shigo jejin suna nemanmu ashe wani manomi yaga duk abinda ya faru ya bazama gdan sarki ya faɗa, hannunta ta ɗaga ta kamo nawa ta ɗora a saman ƙirjinta ta sake buɗe idanunta akaina taja wata ajiyar zuciya me ƙarfi shikenan jikinta ya saki ashe tafiyar kenan.
Tafiyar kenan ɗan birni tafiyar da ba’a dawowa tun daga wannan lokaci na kamu da wata irin jinya da Saida na cinye wata bakwai ina kwance ba uhm ba uhm² saidai a kwantar a tayar haka akayita Shari’a akan wannan abin da ya faru amma babu nasara saboda baban Jamilu ya tsaya masa kasancewar shi kaɗai ya haifa kuma me kuɗin birni wannan dalilin yasa kwata² a cikin danginmu Bama ƙaunar mutanen birni ko kaɗan wlh ba ƙaramar wahala nasha ba da akace da Baba Uda anganni da ɗan birni cewa yayi ma da a ƙara bar musu mugun tabon da mutuwarsu ce zata rabasu dashi gara su su kasheni suji a ransu sune suka barranta kansu dani”…………..
[4/5, 9:11 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma.
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button