Mijin Malama Book 1 Page 39
MIJIN MALAMA na kuɗi ne, don Allah ki biya ki karanta da ƙyar nayi typing sbd masifaffen zazzaɓi ga wani nataccen ciwon kai…….. More especially chat me via WhatsApp 08119237616Zame hannunsa ya yi da ɗan sauri yana jin kamar ya yi abinda take buƙata ɗin, but he can’t do that. Ya dubeta yaga gabaɗaya a hargitse take gashi ya rufe mata fuska, a nutse cike da kalama ya miƙa hannunsa da yake fidda wani ƙamshi ya fara ƙoƙarin tattare gashin fuskarta, baya da abinda yake burin gani sama da fuskar a yanzu. Kafin ya ƙarasa daga bayansa an ce”Oh hello!” Cak! Ya tsayar da hannunsa yana mai dungule su, gently ya miƙe tsaye tare da goya hannunsa a baya as asual kamar yadda ya saba. Ya juya sukai idanu biyu da Abraham, kamar yadda shi ma Abraham ɗin ke kallon Mutumin, Bad boy ya janye fararen Idanunsa cikin sigar tuhuma ya ce “Who are you? And why are you here?” Ya tambaya a ɗan gajarce cikin nutsuwar murya ganin wanda ke gabansa kamar yana da bala’in nutsuwa. Mai martaba Ajlaal Sultaan ya basar yana mai da idanunsa ga haɗaɗɗan agogon wrist ɗin sa. “Am talking to you?” Ajlaal ya ɗan rufe ido ya buɗe kamar ya zame face mars ɗinsa sai kuma ya nuna masa inda Majeederh ke kwance kamar numfashinta ya ɗauke ya ce”Ur Mom” Abraham bai jira jin waye wannan mutumin ba ya nufi kan Majeederh yana durƙosawa, da wannan opportunity ɗin Mai martaba Ajlaal Sultaan ya samu dama ya fice daga office ɗin, yana jin duniyar kanta na juya masa. Abraham kansa ya kulle ya rasa wanne kalar taimako zaiwa Majeederh, a hankali ya ɗora kanta a cinyarsa yana shafa sumar kanta slowly kamar bai tsoran taɓawa tashin hankalin Abraham ɗaya kada Majeederh ta mutu ta barsa, ya shiga bubbuga kumatunta a hankali ta buɗe idanu tana jan numfashi da ƙyar, idanunta ya sauka akan fuskarsa, ta marairaice fuska sosai kamar yarinyar goye ta ce “Little my son, mutuwa zan yi cikina” Kallonta shi dai kawai yake ta kama hannunsa da kyau za ta yi magana ya girgiza mata kai alamar ta yi shiru, sunkuyawa ya yi gabaɗaya tare da sunkutar ta bakiɗaya ya nufi duguwar kujera ya kwantar da ita, Majeederh azaba ta sanya ko idanu ta kasa buɗewa, ƙirjinta na yin sama da ƙasa ta jima ba ta yi ciwon ciki kamar haka ba. “Ina ke maki ciwo?” Abraham ya faɗa a takaice kuma a ɗan rarrabe, ba zata iya cewa komai ba sai hannunsa data kama ta riƙe ita ba abin ta ce masa ya yi mata addu’a ba, gashi bata ma gama yarda shi likita bane, ga tsoron kada ya sake yi mata wata allurar sai kawai ta nuna masa ya danna mata cikinta. Ɗaga kanta ya yi ya mayar kan cinyarsa a hankali ya ɗora hannunsa ta saman rigarta ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da ta ji saukar hannunsa daidai inda yake mata ciwo, slowly ya shiga danna mata yana shafa kanta cike da kulawa kana ganinsa kasan bai wani iya ba, idanunsa sun yi jajur yana mamakin yadda tsigar jikinsa ke tashi kamar waya na jan shi sometimes, a haka har ya ji saukar numfashinta damtsen hannunsa data ƙanƙame, abubuwa biyu suke yawo a kan Abraham, idanunsa kuma kafe a kan fuskar Majeederh dake bacci lokaci zuwa lokaci take yatsuna fuska.Ta ɗauki almost 45 minutes tana baccin wahala sbd lafawar ciwon, idanunta ta shiga buɗewa da ƙyar bakinta ɗauke da addu’a, ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious dake tashi a hankali yana ratsa cikin hancinta ya sanya ta juya ga mmkinta sai ta jita kwance male male a cinyarta mutum ta runtse Idanunta da ƙarfi, ƙirjinta na bugawa ta shiga furta “Asstagafirullah” Yau ita Majeederh ke kwance jikin wani? Ta shiga uku “Sorry” Ta ji husky voice ɗinsa mai tasiri a zuciyar duk wanda ya ji, wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke jin muryar wanda take kan cinyarsa sai a lokacin ta lura gabaɗaya ta ƙanƙamesa ta yi bacci sosai duk da na wahala ne, ta miƙe zaune cikin sauri ta tashi tsaye tana riƙe kanta da kyau ta ɗauki vail ɗinta ta yi rolling ƙoƙarin kawai take bayan ta yi baya ta zauna to others sofa ta kallesa taga gabaɗaya ba ita yake kallo ba, kansa a kife yake hannu ɗaya a tsakiyar kansa ya hargitsa sumarsa. “Are you okay?” Gently ya ɗaga kansa ya kalleta da idanunsa da sukai jajur kamar gauta ta ƙara cewa “Are you okay?”
“How can i be okay kina jikina Maa?” Ya bata amsa, ta ce “Me?”
“You scared me” A hankali ta ce “Sorry” Ya shafa kai yana danne laps ɗinsa kamar mai mata raɗa ya ce “How do you feel now?”
“Allahamdulillah!” Ta ce masa tana nuna masa hand bag ɗinta da phone da car key ɗinta ta ce “Miƙo mini” Ya dubi kayan ya ce “Home? Ok I’ll drop you” Ta haɗe fuska nan da nan duk da yanayin da take jin kanta bai hanata cewa “Khalil”
Yaƙi amsawa don baya son sunan ta ce “How many times do I have to tell you sai ka ƙara girma, before you start driving me? Ko so ka ke na shiga ka watsar dani a titi kafin naga aurenka?” Ya yi shiru sai kallonta yake ta ɗauke tana kallon wayarsa dake kawo haske tun ɗazo ta ce “Zuwa nan da shekaru 10 idan na gama rainonka sai na sallama maka Matsayin driver, Under age like you kamata ya yi a hanaku driving, ka kawo mini all bunch of keys ɗinka na mota” Speaking calmly ya ce “Ohk” Ta ce “Pick your call” Ya taɓe fuska kawai kalmar yaro na yi masa yawo a brain ɗinsa. Majeederh ta ce “Oh Allah, ba Grandpa bane?” A hankali ya miƙe yana cewa “Why do you want me to pick up the call?” Tana miƙe tsaye itama ganin ya tattaro mata kayanta ta ce “Masu kiranka sun damu, fatana kawai ba wannan yaran bane ku haɗu ku dinga nuna ƙuruciya” Ta faɗi haka tana nufar waje sai a lokacin ya ɗan yi murmushi ya ce “Haka zaki fita?” Ta tsaya tana duba jikinta ta ce “Akwai matsala ne?” Ya girgiza mata kai kawai kafin ta nufi ƙofa ya ƙarasa wajan ƙofar da sauri yana tsaya a bayanta ya cire rigar jininsa ta sama ya ce “Ki rufe jinin” Majeederh ta yi sai, sai kuma ta kai hannunta ta shafa ta jita duk a jiƙe ji tayi kamar ta nutse a wajan da kunya me ya sa wannan abin zai zo mata yanzu? Daman shi ne kenan shi yasa take ta ciwon ciki amma yaushe rabon da tayi ciwon ciki dan za ta yi al’ada, ta gefenta ya shige yana ɗan cije baki. Majeederh ji ta yi kamar ta dauwama a wajan, Abraham bayan ya kunna motar ya ɗan ɗaga murya cikin gurɓatacciyar Hausar shi ya ce “Na zo na ɗauke ka Jee?” Ta yi masa shiru gani ta yi ya buɗe mota hakan yasa tayi saurin sakin liƙab ɗinta ta nufi motar tata, front seat ta buɗe ta shiga, ya kunna motar tare da yin reverse cikin nutsuwa ya shiga murza kan motar lokaci zuwa lokaci yake ɗan kallonta ta mirror yana girgiza kai, Majeederh addu’a take Allah dai ya kai su gida lafiya har sukai nisa bata yarda ta kallesa ba haka kawai yau take jin nauyin ɗan nata yana tsaka da driving ya ji ta ce “Ina motar taka?” Sosai ya jita sai ya yi ƙasa da waƙar da yake ji ta crisdanial ya ce “What?” Ta ce “Banga motarka ba tana ina?” Ya ce “Ohk” Ta ce “Me?” Ya saki kan motar gabaɗaya ya zuba mata gajiyayyun idanunsa ya ce “I can’t drive, kina mgn” Yana faɗin hakan ya riƙe kan motar ya ci gaba da driving da mugun gudu tun a lokacin bata kuma cewa komai ba, wani irin mahaukacin gudu yake kamar zai tashi sama baya taɓa tsayawa danja, sun zo daidai roundabout suka samu ana faɗa tsakanin wani ɗan karota da wani me napep, Abraham ji ya yi jikinsa ya ɗauki rawa da ɓari ganin abinda yake shirin yi ya sa Majeederh cewa “Kada ka fita” Bai kalleta ba, domin yana kallonta dole ya bi umarninta a hankali ya ce “Zan amshi ruwa” Yana faɗin hakan ya buɗe motar tare da saka mata key kai tsaye ya nufi tsakiyar inda ake faɗan. Majeederh ta shiga bugun ƙofar hankali tashe domin tasan idan Abraham ya isa wajan ba sa a haifar da ɗa mai ido ba, cikin sa a ƙofar ta buɗe garin saurin yaje wajan faɗan ƙofar bai rufe ba, ta riga data mance rigarsa a jikinta saman abaya ɗinta ta shiga takawa zuwa wajan da ƙyar kanta na juyawa. Abraham ya kalli ɗan karota ɗin da yake cewa “Daman idan ana duba yanayin society to Gwamnati babu uban da zata iya ta ɓukawa, duk ƙoƙarinta wajan ganin komai ya yi daidai amma al’umma bata taɓa bata goyan baya, kuma sune kan gaba wajan tsinewa gwamnatin dake ci, kuna tsine musu suna ƙara lalacewa dole kuga abubuwa suna ta faruwa, yadda suka dama haka za a sha” Mai napep ɗin ya ce “Ok daga maganar hakƙina sai ya zama laifi? Akan miliyan ɗaya da rabi ake bamu napep ɗin nan, kafin mu biya kuɗin mu yi batun riba ta kwararraɓe tuni, amma baku gani abu kaɗan ƴan adaidaita za su yi aci su tara kenan mu ba mutane bane, bamu da ƴancin yin magana ko?” Ɗan karota na ƙoƙarin yin magana ya ji an kifa masa mari an kuma kifa masa, ya buɗe baki zai magana ya ji an sakar masa naushi a bakin.
Ihu ya kurma na azaba, yana kallon Abraham dake huci kamar zaki ya ce “Me na yi maka, wanne irin zalunci ne wannan?” Abraham ya shiga dukan ɗan karotan kamar an aiko shi.
“Fouk You!,
How dare you insulate him, like that, Eh?”
Har ya juya ya tafi yaga dukan bai masa ba, ya dawo da sauri tare da kama hannun ɗan karotan zai karya. A gigice ta ce
“Ibrahim-Khalil!” Bai kula ba sbd bai yi tunanin da shi yake ba, cak kuma ya tsaya dalilin muryarta da ya ji. Ya ɗago jiki a sanyaye sbd shi bai ba san yaushe ne ya shiga dukan mutumin ba, kallonta ya yi ya ce
“Sorry Mami” A fusace ta ce “Sorry for yourself Khalil” Ta kalli mutumin ta ce “Don Allah ka yi haƙuri, yaro ne ina mai baka haƙuri” Ta juya ta kalli Abraham da ransa ya yi masifar ɓaci jin ta ce wai shi yaro ne? Ta ce
“Say sorry to him, ka bashi haƙuri” Ya ɗauke kai tare da yin shiru.
Tun da aka fara faɗan yana zaune cikin mota, sanye da wata dakakkiyar shadda gezner sai ɗaukan idanu take, komai na jikinsa da mugun kuɗi aka siye shi. Uncle Isma’il dake ɗaya side ɗin ya ce “Majeederh’s disappointed me, na kasa yarda ita ce cikin tsakiyar mutanen nan” Abbu ya runtse idanunsa,wai ƴar cikinsa ce a nan wajan? Idanunsa ya sauka akan rigar Abraham dake jikinta, a hankali ya dinga binta da kallo, frm head to toe ganin jini kwance a bayanta ya sanya Abbu fara tari yana girgiza kai, Uncle Isma’il ya ce.
“Take heart Abdul’aziz,
Ka bi komai a sannu dan Allah, Please!” Shi kansa Uncle Isma’il idan ransa ya yi dubu to ya ɓaci, he can’t believe cewa Majeederh yake gani, akan idanunsu ta saka hannu ta jawo hannun Abraham har zuwa cikin mota. Shi kowa Abbu tari ne ya sarƙe shi idanunsa ya yi jajur sosai, da ƙyar yana jan numfashi ya amshi bottle water ɗin da Uncle Isma’il ke bashi ya shiga ja yana komai ya fice masa a rai.
Misalin 5 na yamma wata ƙatuwar mota, Mercedes-Benz EQS Black colour ta yi parking a compound na gidan Uncle Isma’il, Driver ya ce “We’re here, Sir”
Abraham dake bayan mota, ya shiga buɗe idanunsa da suke always sleeping sbd ƙwayoyin da yake sha, tar ya buɗe ganinsa akan harabar gidan, har ranshi ya ɗauka gidan zai ninka tunaninsa sai ya ga ko kwatan na Grandpa bai kama ba, balle kuma nasa gidan da bai fiya zana cikinsa ba. Sanye yake da Brown ɗin Armani suit, wacce ta kama jikinsa sosai dark black skin ɗin ta fito sai sheƙi take, hannunsa maƙale da agogon wrist na Patek Philippe, ga wani takalmi Half Cover Leather Shoe, komai na jikinsa designer ne. Fitowa ya yi daga cikin motar yana rufe idanu tare da zuba hannu a aljihu, a hankali yake bin komai na harabar gidan Uncle Isma’il, yana tsaye Uncle Isma’il ɗin ya fito cikin nagartacciyyar shigarsa tun daga nesa yake kallon Abraham har ya ƙarasu ya ce “Oh har ka iso?” Abraham ya nufi wajan Uncle I zai rungumesa alamar gaisuwa Uncle Isma’il ya miƙa masa hannu alamar musabaha bai musa ba ya amsa a hankali ya furta “Good day Sir” Uncle Isma’il ya ce “Come in, bismillah” Suka shiga har Parlourn baƙi. Uncle I ya gyara zama cikin turanci ya ce “Sunana Isma’il mahaifi ne ga Majeederh uwar riƙon ka, Ban yi wahalar gane ka ba, a wancan lokaci Little ake ce maka, sbd yadda kake baƙi ƙyakƙyawan mai ɗaukan hankali, ga saurin fushi da zafin zuciya,na lura har yanzu akwai ta kuma” Abraham dai kallon Uncle Isma’il yake bai ce komai ba.
“Kana da shekaru 3 a duniya Majeederh ta tsince ka, ta raineka da hannunta, ta ciyar da kai da albashinta tana hana cikinta ta baka, bata faɗa amma akan ka tana yi kamar wacce akaiwa asiri da jininka, a haka har kayi shekaru biyar bi ma’ana kayi 2 years a wajanta, Tayi kuka sosai lokacin daka sake ɓata a hannunta sai gashi yanzu ka bayyana a bayyanar da ban ji daɗi ba, ka bayyana a wani addinin da ba namu ba” Uncle Isma’il ya gyara zama ya ce “Tambayoyi nake son yi maka, ina fatan zaka bani amsa?”
Abraham ya jinjina kansa alamar yana jinsa.
“What’s your real name?
And who are you?
Meme aikinka? Matakin karatu? Ina familynka suke, Father, mother, e.t.c” Abraham ya sauke numfashi a ɓoye ya daɗe yana kallon Uncle Isma’il kafin a hankali ya ce “Abraham Daniel David, that’s my name, Who is me?” Ya yi shiru for a second kana ya ce “Bani da uba, but i have a mother” Uncle Isma’il ya ce “Mene sunan mahaifiyar taka?” Abraham ya ɗauke shi fa duk ya gaji da tambayoyin nan, kawai don Uncle ɗinsa ne ya ce “Ohk, Jee Malumana, i can’t I can’t pronounce the name” Ya faɗa yana ɗan yatsuna fuska.
Uncle Isma’il ya ce “Ok, Ina son faɗa maka abinda baka sani ba, Majeederh uwar riƙo ce ba uwar asali ba, ina nufin akwai aure tsakaninka da ita ba kamar yadda ba zaka taɓa auren wacce ta tsuguna ta haifeka ba, yadda kake zuwa kana rungumeta itama tana biye maka is prohibited in Islam. Ka saka a ranka duk sanda ka fara feelings na Majeederh to zaka iya aurenta, kasan Developing feelings towards opposite sex shike kawo So ka ji kana son mutum ko kasancewa da shi ko aurensa zama na dindin wani kuma sha’awa ce kawai take jan mutum ga abinda yake gani, kasan mata komai nasu mai kyau ne Zasu iya attacking opposite sex ɗin su, su ja ra’ayin namiji ya kwaɗaitu da su, Abraham I am telling you this as your Uncle, not as my guest” Tunda Uncle Isma’il ya fara maganar Abraham ke sauraren shi cike da fahimta, nan take ya ji komai na zuciyarsa na sauyawa. Uncle I ya ce “Think, U can marry Majeederh, but u can’t marry your real mother, maybe a duk sanda kke rungumeta kana jin wani abu a ranka baka saki jikinka ka fahimci mene ba sbd tunanin Majeederh is ur mother amma yaudarar kanka kawai kake, itama Majeederh takai matakin da zata iya haifar ɗa kamar ka shi ya sa ta manta cewa abin da take kuskure ne, ina fatan ka fahimta za ku ka yi nesa da jikinta” Abraham was speckless da ƙyar ya jinjina kai tare da miƙewa suka fito waje anan ya ci karo da Sona kamar ta san shi ta ce “Uncle” Ya ɗan yi murmushi domin yana ana bashi girma ya ce “Sorry gashi bana yawo da kuɗi?” Sona ta ce “Ba komai, kai ne mijin Anti Jeederh?” Bai gane ba sbd da Hausa ta faɗa ya yi al’ƙawarin zai dawo mata da gift…
Majeederh ta share hawayenta kwana biyu duk ta zama raguwa mai saurin kuka ta kalli Latifa ta ce “I’m tried Latifa na ga ji da rayuwar nan, tun ina son aure har ya fita akai na, yanzu wa nake da shi wa zai aureni da za a ce mini na kawo miji nan da 2weeks wlh bana da kowa” Katifa ta yi murmushi ta ce “Kina da wanda zai aureki mana Majeederh” Majeederh ta ce “Wallahi babu, ko zance ban taɓa yi ba” Latifa ta ce “C’mon ni na amince Mijina Aliyu ya aureki ko gobe ne…