Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 34

Sponsored Links

XXXIV….
(34)

MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya FIRST bank,
Shaidar biya ta 07082281566
Masu son karantawa privately kuma yana arewabooks, username@NoorEemaan

Maleek ya yi tangal tangal kamar zai fadi, ya dafa bango domin har yanzu karfin sa bai dawo duka ba.

Maleek ya ƙara matsowa yana cewa “dan Allah Daddy hear me out, ka sau….”

Fushin Alhaji Dawood ya bayyana, ya kifa wa Maleek mari jikin sa na tsuma yace “me zaka ce min bayan bakin ganin da idanuna suka nuna min a zahiri, ni ni ni Maleek? Ni zaku yi wa haka, Ni zaku ci wa amana, ku wulakanta ni da wulakanci Mafi muni, ka rasa mace sai matata, itama ta rasa namiji sai kai dana, toh ga halin da kuka jefa min d’a a ciki, hankalin ku ya kwanta ko? Toh maza ka fice daga asibitin nan kafin na maka abinda baka taba zato ba, domin na tsani ganin ka, daga Yau ba Ni, ba kai, fita nace kafin securitys su fidda kai” Alhaji Dawood ya karasa cikin daga Murya, sosai Muryar sa ke rawa, ya koma kujerar dake wajen ya zauna, ya tsunkuyar da kansa, hawayen sa ya gani yana diga a kasan tiles din, rabon sa da zubar da hawaye tun lokacin da bilkeesu ta rasu, all his life bai taba ganin bakin rana irin ta Yau ba, da a ce abinda zai tarar kenan da yayi zaman sa a airport har sanda jirgin zai tashi, Domin anyi cancelling wanda yayi booking a farko, dama ya sani ya shiga motar haya zuwa Kanon taron da aka gayyace shi, daya fiye masa wanna baƙin ganin da yayi, ji yake kamar ba’a gaske abin ya faru ba sabar yanda abun ya girmama dattijon kwakwalwar sa, sai yanzu komai da Sa’adah ke yi ke dawo masa kenan wanna dalilin ne ya saka tafi nuna so ga Maleek? Shi ne Dalilin daya saka idan suna tarayya ta aure da shi take kiran sunan Maleek din? Wa’iyazubillah! Ya fada yana dago kansa sama, kaduwar da yayi bai gama tsakin sa ba, bai Kuma san ranar da zai sake sa din ba, ya shiga girgiza kafar sa, wanna tamkar al’adar sa matukar yana cikin ɓacin rai ko damuwa yayi ta girgiza kafa kenan.

Yana zaune a wanna halin ya doctor ya fito, ya zabura cikin sauri ya mike, yana fadin “doctor, doctor how’s my son? a wani hali dana ke ciki?”

MALEEK dake tsaye nesa da Alhaji Dawood ya matso cikin sauri, zai wa doctor’n magana kenan Cikin kakkausar murya Alhaji Dawood yace “doctor tell this young man here to leave this premisses idan ba haka ba Ni zan ɗauki dana na sauya masa asibiti!”

Doctor ya kalli Maleek ya kuma kalli Alhaji Dawood kamar yadda suke kama haka damuwa mabayyane ke rubuce a fuskar sa, kallo daya mutum zai musu ya gane suna da alaka ta jini Amma bai san abinda ya shiga tsakanin su ba, dan haka yace “young man please go”

“Doc.. doctor he’s my blood brother, idan nine a wanna halin Shakur will never go and leave me, zai kasance tare da ni, dan Allah allow me stay, ka barni tare da shi doctor” ya furta kalaman da busassun labbansa da tsabar tashin hankali ya saka suka koma haka.

Hakan nan likitan yaji tausayin sa, ya ja shi gefe yace “na tabbata Wanna Alhajin mahaifin ka ne, ban kuma san dalilin sa na cewa ka tafi ba, amma Kaji shawarar da zan baka, just go, kila idan ya sauko sai ka dawo, amma zaman ka yanxu zai iya janyo ɓacin rai”

MALEEK ya hadiye wani abu mai daci yace “zan tafi, amma ya jikin kanina yaji sauki ko?”

Likita ya jinjina masa kai domin ya kwantar masa da hankali.

Ya kara da cewa “idan ya tashi kace masa na zo, amma Daddy ya hana Ni zama, amma zan dawo”

“TOH shikenan” likitan yace kamar yayi wa Maleek kuka domin tausayi ya bashi, Maleek ma ya juya cike da sanyin jiki ya fita.

Ɗan ya rika yayi wa Shakur alkawarin bazai ƙara shan giya ba da babu abin da zai hana shi sha a yau domin ya samu sauƙin abinda yake ji a ƙwaƙwalwa, zuciya da ma jikin sa, har yanzu mamakin abin yake, domin abu ne wanda bai taba hango faruwar hakan ba, taya ma zai hango hakan, bayan kallon uwa yake mata all this life, ba zai yi karya ba, lokuta da dama yana manta cewa ba ita bace mahaifiyar sa ta Asali ba, yanxu da ace Allah bai
kawo Alhaji Dawood ba da tuni ta samu galaba a kansa, domin a yanayin nan da yake dazu gaba-daya gangar jikin sa ji yake kamar ya daina aiki saboda wata muguwar kasala da yake ji, ga kuma bala’in da yake ji a Kasan marar sa, tabbas data far masa, ya runtse idanun sa yayin tafiya domin baya ma so ya hango abinda zai faru a gaba saboda tashin hankalin da yake Cikin sa wanda zai fi wanna da a ce Hajiya Sa’adah ta kusance shi, tuntuben da yayi da wani Dutse ya sanya shi Saurin buɗe idanun sa, ya tsaya yana bin ko ina da kallo domin bai san ina zai nufa ba, ba kuma yaso ya koma gida yanzu saboda yanda ya tsani gidan.

Company din sa ya fado masa a rai nan zashi, keke ya kara tara, ya shiga har bakin gate din Companyn, ya kwankwasa gate din, Nura mai gadi ya leko, mamaki ya kashe sa a tsaye domin ganin Maleek a kafa bakon abu ne ga kowa na Companyn nan, Maleek ya karasa ture kofar da kansa ya shiga fuskar nan ya fi koyaushe hadewa ko kallon Nuran bai ba, hakan ya saka Nura shakkar gaida shi, Maleek kuwa kai tsaye wurin sakatariyar sa yaje da kansa wanda ita ma tayi mamaki, domin baya zuwa kiran kowa sai dai yayi sanarwa ta pager. ya sanar mata baya bukatar ganin kowa kada wanda yazo office ɗin.

Direct dakin hutawar sa ya nufa, ya kashe hasken office ɗin gaba-daya ya kwanta kan sofa, yayi matashi da hannun sa, idanunsa na kallon sama.

***

“Doctor tun dazu nake tambayar ka, halin da yarona ke ciki, kaki min wata gamshashiyar magana?” Alhaji Dawood ya fada fuskar sa dauke da matsananciyar damuwa, domin ko dazun bayan tafiyar Maleek bai masa wata magana da ya gamsu dashi ba.

Likitan yace “Alhaji kwantar da hankalin ka, let’s go to my office”

Bayan sun shiga, Alhaji Dawood ya zauna, likita ya sauke numfashi, sannan yace “Alhaji ka kara kwantar da hankalin ka, in sha Allah he will be fine, dazun ma muna ƙoƙarin ceto rayuwar sa ne, fadan da kake wa dayan yaron ne ya sanya na fito domin ba’a son hayaniya…”

Alhaji Dawood da gabansa ke faduwa ya katse doctor da cewa “doctor what’s exactly wrong with my son?” yace cikin katse likita domin shi wanna dogon bayanin na sa bata ransa yake.

“zuciyar sa sa ce tayi mummunan bugawa sakamakon shock daya shiga ko kuma ya ga wani abu daya tayar masa da hankali, hakan ne ya sanya jinin sa hawa sosai fiye da kima, a takaice yanxu ya kamu da heart disease or i should said heart attack, wanda dole yanzu ana kiyaye abinda zai kara daga hankalin sa domin zai iya kamuwa da stroke, haka zalika yanxu iya balance diet zai dawo ci with less salt…”

“Innalillahi wa inna ilaihi raju’un, Innalillahi wa inna ilaihi raju’un, Innalillahi wa inna ilaihi raju’un” Alhaji Dawood ke ta maimaitawa cikin rawar murya.

Ya kara da cewa “ina ma nine a wanna halin ba Shakur ba? Tunda Ni na riga na tsufa zan iya jurewa, amma karamin yaro kamar Shakur ke Cikin wanna halin, ina zai iya jure zafin ciwo irin nan doctor?”

“Alhaji kar kace haka, kai fa Muslimi ne, Allah baya taba daurawa bawa abinda bazai iya ɗauka ba, Allah kuma ba ruwan sa da yaro ko babba idan zai jarrabi mutum, yanxu fatan mu shine Allah ya bashi lafiya, mu ma zamu yi dukkanin iyawar mu wurin bashi duk wani taimako”

Alhaji Dawood yayi kasa da kansa yana jinjina kai, domin kalaman likitan ya saka shi fahimtar cewa lallai yayi kuskure a furucin sa.

Hajiya Sa’adah kuwa tun lokacin data fita daga dakin Maleek ta fada na ta ta rasa nutsuwar zuci, sai zaga dakin take hannuwan ta biyu aka Kamar mai jin bahaya amma Kuma da mutum a banɗaki misalin abinda take yi kenan, hankalin ta yayi dubu ya tashi, gumi sharkaf a jikin ta, a yau ac din dakin ya daina yiwa jikin ta aiki saboda tsabar tashin hankali da sam bata hango zuwan sa ba ɓalle ta shirya masa, ta kalli kayan jikin ta da yake kamar Babu sai kuma ta nufi drawer dinta ta dauko zanin atamfar ta ta daura, ta samu bakin gado ta zauna, ina mafita yanxu? Wazai bai Bata shawarar yanda zata yi, Hajiya maimoona zuciyar ta ta raya mata, ta jinjina kanta kamar wata zararriya, tabbas bata da kowa da zai fidda ta a wanna halin sai kawar ta, ta janyo wayar ta babu bata lokaci ta danna mata kira.

Hajiya maimoona na daga wa ta fara yi wa Hajiya Sa’adah shekiyanci da cewa an kashe boss.

Kukan da Hajiya Sa’adah bata samu ya zo ba tun dazu saboda tashin hankalin ta fasa yanxu, daga can bangaren Hajiya maimoona tayi saurin cire wayar daga kunnen ta cikin zaro idanun ta, ta kara kallon wayar ta kalli sunan data yi saving number’n da kyau kana ta mayar tace “Hajiya Sa’adah! Lafiya menene?”

“Maimoona na kade har ganye na, Alhaji da Shakur sun Kama mu, ina daf da cika burina akan Maleek ya bugo kofar da karfi, ina cikin tashin hankali, maimoona ya zanyi?”.

“Sa’adah Meya kai ki barin kofa baki murza key ba? ke matsala ta dake zalama, da’a ce kin danna key a kofar da kin samu kalaman kare kanki tunda ba ganin ku yayi ba”

“Yanzu mu bar Maganar kofar nan, domin nayi matukar nadamar hakan, yanzu ya zan yi, menene mafita?”

Daga can bangaren Hajiya maimoona ta harari wayar hadi da tabe baki, Hajiya Sa’adah ta bata haushi, a ganin ta she’s not smart, da a ce ta iya takun ta babu yanda xa’a yi a kamata, ita baga shi shekaru masu yawa tana tare da wasu mazan ba, amma mijin ta bai taba sani ba, ita gani take zalama da rawar jiki ya janyo asirin Haj. Sa’adah tonuwa.

“Sa’adah ina zuwa zan kira ki” Hajiya maimoona ta fada tana katse wayar.

Hajiya Sa’adah ta cire wayar daga kunnen ta cikin mutuwar jiki, ita abinda ke kara daga mata hankali shine shirun da Alhaji Dawood yayi, gaba-daya gidan sai ya dawo mata wani iri har tsoron fita take.

Ɓangaren Maleek kuwa a Companyn sa cikin office dinsa ya kwana ba tare da ma’aikatan sa sun san da cewa yana nan ba, domin a tunanin su ya riga ya tafi, yanda yaga rana haka ya ga dare, this this the worst day in his life, tunanin halin da Shakur yake ciki ya tsaya masa a rai, jira yake gari ya waye kawai ya ganshi a hospital din nan, sai misalin ƙarfe biyar na asuba ya mike ya daura alwala yayi Sallah, yana iddar wa wani mugun bacci ya tsure shi.

Kusan a firgice ya farka da tunanin Shakur a ransa, domin bai son baccin ya dauke shi ba, ya kai idanun sa kan agoga ya fa ƙarfe tara da mintuna arba’in da tara, mamakin irin barci da yayi yake, ya mike ya fita, ya bude kofar toilet din shi ya shige.
Mouthwash da yake kuskure baki da shi ya dauka ya kuskure bakin sa hadi da wanko fuskar sa, ya sauko kasan Companyn, kai tsaye wajen masu siyar da motocin sa ya nufi, ya ce su bashi mukullin mota ko wacce, suka bashi na wata BMW blue color.

Sosai ya sharara gudu har ya isa hospital ɗin. Tun daga nesa ya hango Alhaji Dawood din a zaune kamar yanda kayan jiya ne a jikin sa, shima Alhaji Dawood din hakan ne da alama shima ba’a gida ya kwana ba, ya karasa wajen yana fadin a hankali yace “Daddy good morning”

Alhaji Dawood bai kalle shi ba bare ya amsa.
Ya kara gaida shi a karo na uku Alhaji Dawood yace “riƙe gaisuwar ka, ka kuma fice min daga nan kafin na yi munanan sa6a maka”

Maleek yayi kasa da kansa, tabbas ance mai hakuri bai iya fushi ba, bai taba tunanin Alhaji Dawood dana zafi haka ba, bai kuma ga laifin sa ba, yanzu da yake tsaye a gaban sa kunyar sa yake ji, amma bazai iya barin asibitin nan ba ba tare da ya ga halin da dan’uwan sa ke ciki ba.

“Ko baka ji abinda nace bane!” Alhaji Dawood ya fada a kausashe.

“I’m sorry Dad, amma bazan iya barin nan ba, i want see my brother, please allow me” ya fada gwanin ban tausayi, kwalla suka cika idanun Alhaji Dawood, wato daya ga halin da Shakur ke ciki hankalin sa yayi mugun tashi, hakan Kuma ya saka yake jin tsana da haushin Sa’adah dama Maleek din, domin idan ba Allah ya nufa yana da sauran shan iska a duniya ba da babu abinda zai hana shi mutuwa saboda bakin ganin da yayi ba.
Ya yi ƙasa da kansa bai kara cewa komai ba, ya shiga girgiza kafa saboda yasan Maleek na da taurin kai bazai tafi ba, idan ya cigaba da magana kuma hayaniyar zata dame Shakur shiyasa yayi shiru.

Maleek ya Saki ajiyar zuciya, ya ga likita ya fito daga dakin, ya riga Alhaji Dawood tarar likitan da tambayar ya Shakur yake yanzu? Doctor ya kalli Alhaji Dawood ya Kuma kalli Maleek sannan yace “zaku iya ganin sa, amma banda hayaniya Please” tuni Alhaji Dawood ya shige wajen, Maleek kuwa ya shiga tambayar menene yake damun Shakur ɗin, a takaice likita ya masa bayani, hankalinsa ya tashi sosai amma Sam baza ga hakan a jikin sa saboda yana da daure abu, amma daga ta ciki yafi wanda yake bayyana damuwa cutuwa.

Yayi jim a tsaye cikin murza yatsun sa, sannan ya taka a sanyaye ya nufi dakin da Shakur yake, ya buɗe kofar ya tsaya, Alhaji Dawood na zaune a gefen kan kujera, ya kai idanun sa a gado ya ga Shakur, ya kasa cigaba da tafiyar saboda halin ɗaya ga Shakur ɗin a ciki, zuciyar sa ta yi lugudan bugu, bai san haka jikin Shakur ɗin tayi muni ba, na’urori ne da wayoyinsu ke joni a jikin sa, yayinda aka saka masa oxygen wurin taimaka masa yayi numfashi.

Shakur dake kwance har ya fada cikin kwana ɗaya ya sauke oxygen din kasa ya kira Maleek da hannun sa fuskar sa ɗauke da murmushi.

 

_Assalamu alaikum paid groups reader’s wanna sakon naku ne, ina baku hakuri da baku update a dare, ba’a son raina hakan ke faruwa ba. Ina gidan yayata data haihu ne kuma kun san yanda zama da masu jego ke kasancewa, a jiya dadaddare kuma na zo gidan mu, Yau kuma da yamma zan koma can, kun ga bambancin yanzu? Amma ko da na koma can ina sha Allah zan yi kokarin na dinga baku kan lokaci. Dalilina na yin wanna maganar saboda wandanda su ke min korafi a dm dina kan cewa ina ja musu rai, sai na zo waje mai dad’i nake katse chapter din, amma Sam ba haka ne, bana hakan da gangan, nan Allah yayi zan datsa aya, duk Masu karanta books dina sun san cewa bana wasa da posting, wani rana ma update biyu nake bayarwa a rana a free books fa kenan, lokacin ma dana yi paid book na hoorain shi ma bana wasa da posting, taya zan yi wasa da hakkin mutane fisabillahi? A duk lokacin dana daura alkalami na fara rubuta hankalina zai kwanta har sai na gama saboda ina tsoron hakki, dan Allah kuna yin min uzuri, in sha Allah zan yi iya kokarina gurin ganin update ya zo muku a kan lokaci, nagode da soyayyar da kuka nuna min ta hanyar siyan book dina, Allah ya kara muku buɗu na alkhairi, NoorEemaan_💖

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button