Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 5-6

Sponsored Links

Page 5-6_

 

 

Related Articles

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_Telegram Link_*
👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

 

 

____________________________
____________________________

Daquwa Inna ta watsa Mata tace “wato dana hanaki tsokanar bakiji ba kenan aikuwa tabbas zan hadaki da yayanki yacimin qaniyarki ni banason sakarcin banza Shiru tayi saboda tsoran kada Inna ta fusata ta hadata da Mudan tasan kashinta tsaf zai bushe ta miqe sumsum ta nade kayan gugarta ta sanya a jakar kayanta ta fice ta dauki bokati ta tafi debo ruwa sawu uku tayi ta qyale kasancewar dare ya riga ya fara tana shigowa sallar Isha kawai tayi ta shimfida taburmarta ta kwanta tana addu’a bacci ya dauketa.
Da safe ta riga Inna tashi saboda zumudin kudin makarantar da zaa biya Mata tayi wanka aka dauki kwalliya aka dau jaka ta fito cikin shirinta tsaf Ma’un Inna idan taga dama yar gayuce ta gaske komanta qwas-qwas Amma idan taso iskanci tafi kowa iyashi dumamen taliyar data boye jiya ta dauka taci ta kora da ruwan koko ta miqe tace “inna zan tafi”
Fito da kudin Inna tayi ta miqa Mata ta qirga zari sha hudu ta miqawa Inna uku da biyar tace “saura uku da biyar idan na dawo saimu siyo abinda zamuke ci kafin Allah ya kawo wata hanyar” Jinjina Kai Inna tayi tayi Mata fatan alkhairi ta fice ta nufi gdansu Jidda dake yafi nasu kan hanya nan suka dunguma suka tafi sunata hirarsu Asma’u na bata labarin irin wulaqancin da akeyi musu idan sukaje neman taimako sosai jiddah ke tausayawa qawar tata.

 

Da wannan hirar suka qarasa suka shiga aji suka fara daukar darasi Saida aka fito break sannan Asma’u ta nufi Office din Principal tayi sallama ta shiga principal din tanason Asma sosai saboda yanda malaman bangaren kimiyyar suke yabawa da qwazonta da ace makarantar tatace ma da tuni ta yafewa Asma kudin makaranta saidai kash batada iko.
Rusunawa tayi ta gaisheta ta amsa sannan ta fito da kudin makarantar ta miqa Mata tayi rubuce rubucenta ta miqanta receipt ta miqe har takai bakin qofa taji a bayanta ance “Asma’u Hussain” tsayawa tayi adan tsorace tace “yes mAh” murmushi tayi tace “meye yasa duk biyan kudin makaranta kece qarshe ne meyesa iyayenki sukewa karatunki ruqon sakainar Kashi bayan Kuma Ubangiji ya Basu dama domin yabasu ke me qwazo da son karatu?” Idanunta ne ya kawo ruwa tayi saurin daukewa tace “na gode mAh kawai ta juya ta fice daga office din principal din ta nufi inda sukecin abinci yau batada ko sisi sai kudin motarta don haka ta nemi guri nesa ta zauna tana kallon daluban wani na siyan wainar fulawa wani na siyan cake kowa dai da abinda yakeso. Jiddah ta hango ta nufota ta zauna kusa da ita tace “yadai naganki anan” dubanta tayi tace “to da Ina kikeson ganina?” Share zancen jiddah tayi da cewa akwai wani guy dana tama a bayan makarantar nan yau indai mun ganshi saina goge Masa hadda”

 

Zaro idanu Asma tayi tace “kayy Kinga ki rufa Mana asiri Principal tace mu daina kula mazan bayan makarantar nan yawancinsu duk yan shaye² ne” harararta Jiddah tayi tace “kefa wani lkcn farar kura ce me suka Isa suyi Mana basai mu gudu ba mu jasu har area mu hadasu dasu Sadiqu suci ubansu” Shiru tayi tana nazarin kalamanta kafin ta dago tace “nidai Babu ruwana bazanje garin goge musu hadda su su gogemin tawa ba” dariya Jidda tayi tace “bansan yaushe kika zama matsoraciya ba wlh Ma’u Allah ya shiryeki” bata Kuma cewa komai ba har suka koma aji Basu suka tashi a makaranta ba sai uku Wanda a qa’ida biyu suke tashi wani mugun malaminsu ne yabasu assignment me wahala shine suka bata lkc haka gashi yace a lkcn yakeso dukkan fuskokin daluban daka gansu kasan sun jigata da yunwa musamma Ma’u da batayi karyawar kirki ba gashi babu kudin break sun riga kowa something suka fito duk ta galabaita suka nufi get megadi ya Kuma taresu akan cewa principal tace kada su fita da daidai su bari su tashi gabadaya,

 

Neman guri sukayi suka zauna kawai Jidda taga qawar tata na kuka Asma’u babu juriyar yunwa ko kadan tasan dalilin kukan don haka ta miqe da sauri ta nufi shagon me gadi ta siyo musu biscuits pure blues dan saba’in ta siyo musu lemo jarka daya sukaci Saida sukaji dama dama asmai ta dubeta tace “dama kinada kudi shine kikaqi ki siya Mana break?” Harararta Jiddah tayi tace “wanne kudi ke gareni kudin motarmu ne naga zaki mushe na taimaka na siyo Mana muka taba Kinga malama an gama fitowa kawai miqe mu yanki burtali”

 

Takaici ne ya hana Asma’u magana saboda tana cika magana zuciyarta fadowa zatayi haka suka rinqa dabawa a qafa gashi da nisa tsakanin unguwarsu da makarantar sosai suna tafe Jiddah nayi Mata hirar tura haushi taqi kulata sunzo daidai wani guri da ruwa yake taruwa kawai basuyi aune ba sukaji ruwan dagwalon kwata ya fallatso musu ya bata musu jiki musamman Asma’u da ruwan yafi batawa ta sunkuyar dakai ta kalli kanta tun daga sama har qasa ta dago kanta ta sauke akan motar da aka tayar ana Shirin tafiya zuciyarta na azalzala taga me motar yaja zai qara gaba ai batayi wata wata ba ta dauki wani dutse qato dake gefensu ta jefi motar akwaita da mahaukacin saiti kuwa ji kake taratsatsa glass din bayan 4matic din ya tarwatse hakan yasa me motar cin uban birki a fusace na kujerar me zaman banza ne ya fara fitowa daidai lkcn data nufo gurin itama tana fadin “ba iyanan naso ya tsaya ba sonayi ya ishe kan daqiqin dakejan motar yayi masa Ramin da jini zai hade da qwaqwalwar shege muga ta gadara da dagawa….” Sauke tafin hannunta tayi a fuskarta jin shu’umin Marin da aka dauketa dashi ta Jima dafe da kuncinta kafin tayi qarfin halin dagowa tana tuna Marin da Aseem Shaheed yayi Mata jiya kwatankwacin azabar da taji kenan aikuwa tabbas saita rama wannan koma uban waye ya daga hannu ya Mari fuskarta me daraja,
Idanunta ta rintse ta dage ta daukeshi da Marin da shima Saida ya dafe gurin kafin ya dago ta sake sauke Masa wani ta daga hannu zatayi na uku Wanda ya fara fitowar ya riqe hannunta da sauri jikinta na bari ta bude idonta daidai lkcn da Dr Aseem ya bude nasa shima tar a kanta lebensa datse da haqoransa ya saita injin idonsa akanta tare da sanya hannunsa ya zame hannun Zahran daga nata ya riqe na yan sakonni sannan ya saki Yana qara kallonta itama shi take kallo cike da mamaki da Kuma tsana.

 

Kafin yayi mgn tayi da cewa “au dama Kaine shaidanin daya batamin uniform dina lusari kawai kagani dai kaga irin aikina dama Saida na fada maka zamu sake haduwa gashi kuwa mun hadu ko banza zuciyata ta dan sauka daga radadin
Daka Bata sauna kawai ka dauka ana tabani aci bulus ne jiya kaci mutumcin mahaifiyata da tafi taka uwar don alamu sun nuna kaikam taka jefar dakai tayi wata me tsautsayin ta tsinta. Sannan yauma ka batani da ruwan kwata Kuma kayi tunanin wuccewa salin alin haba yaro kayi kadan ka taba ma’un Sadiqu ma’un Inna ka zauna lfy gashinan kayi ta glass din motarka Kuma dole aje akaiwa me gyara yaci kudi nidai nasan ko kaina ka siyar bazai gyara maka ba……
Tana maganar tana qasa qasa da hannunta ta sake daukan wani dutsen me nauyi tayi kamar zata wucce kawai ta sakar masa a babban yatsansa yakuwa yi qasa da sauri tare da sakin wata siririyar qara kafin Zahran ya Ankara ma’u takai a dari da sittin ba Zahran ba hatta Aseem da jini yake ambaliya a qafarsa Saida ya dago ya dubeta lkcn da take cewa su Corona virus aje ayi treating kafin mu sake haduwa na daujeta Wawa da kace bakaji………

 

Vote
Comments
Share

 

*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*

_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*

 

_Bismillahir Rahamanur Rahim_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button