Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 69

Sponsored Links

Da taimakon shi tai wanka ta tsarkake kanta sanan yanado ta a bathrobe yafito da ita sai wani murmushi yake ya zaunar da ita abakin gado, yar doguwar riga maidan kauri yaciro mata sabida sanyi sanan yakawo mata mai ya shafa mata yadau rigar zaisa mata ta fizge tana turo baki murmushi kawai yayi yajuya yafita daga dakin, kitchen ya shiga yadauko egg yasoya mata dan abinda kadai ya iya kenan aduka girki sanan yahada mata tea yadau bread dukya jera akan tray din yakoma dakin, shi yadinga bata tanaci harsaida ta sanye tea sanan ta kauda kai, magungunan ta ya dauko mata da paracetamol yabata tasha sanan ya zauna gefenta ya rike mata hannu gam yana kallonta dan dago kai tayi kadan ta kallai zata kawad dakai yasa hannu yajuyota yana murmushi yace “thank you Islam” kunya sosai yabata hakan yasa ta boye kanta ajikinshi kwantar da ita yayi yace “bari naje nai wanka nima” yawuce bayi hakan yasa ta gyara kwanciya ta lumshe ido tana tunanin su Abba da Farida ahaka bacci yay gaba da ita. Ranan gabaki daya haka yawuni yana kulla da ita duk idan zatai wanka saiyasa takara shiga ruwan zafi.

Washegari bata wani tashi da zazzabi ba shiya taimaka mata ta shirya cikin doguwar riga baka tai gayu kaman irin larabawan nan sai kallonta yake kaman zai hadiyeta hakan yasa ya jawota jikinshi ya rungumeta sosai sanna ya rike mata hannu suka fita daga gidan bayan ya kulle gidan hospital suka tafi inda Dr Om ya dubata he was so happy da yanda tai maganan yace musu ai tariga da ta warke zama su iya tafiya basai sun kara dawowa ba unless akwai any complication. Khaleel ya kasa daina murmushi nan yama Om godiya suka fito wani hadadden saloon ya kaita yana rike da hanunta suka shiga da sauri turawan suka tarbesu suna musu sannu da zuwa zama yayi akan wani kujera sanan yace “a kwance mata kitso a gyara mata gashin kar amata wani kitso” zaunar da ita sukayi akan kujeran gaban madubi suna kwance kitson duk idan zata dago kai ta kalli mirror sai sun hada ido hakan yasa ta murguda mai baki ya nuna kanshi ta madubin irin ni? Takara murguda mai tareda gyada kai murmushi yayi ya mata kwafa tamai fari da ido baki yadan bude yana kallonta kafin ya dauke kai ya jawo Jaridar dake nan tsakiyar dakin kan center table ya bude zai karanta yakara dago kai ya kalli fuskarta ta madubi gwalo tamai hakan yasa yay maza ya maida kanshi kan Jaridar yana murmushi kasa kasa.
Kusan 3 hours ya dauke su gama tsifan da wanke gashi da gyara shi danhar stretching gashin saida akai mata gashin yakara tsawo saiwani kyalli yake sanan suka juyomai da ita sukace “sir yamaka haka kokuma akara wani abu?” dagokai yayi tareda rufe jaridar hanun nashi yana kallonta yanda gashin ya bazu a bayanta dan basuyi mata pakin ba, ba karamin kyau tamai ba ya kalli baturiyar yace “is fine amma kimin parking gashin sanan kima bakin gashin coils, nafison hakan” dariya baturiyar tayi sosai ta kalli Islam tace “wanan mijin naki yama fiki sanin abinda zai miki kyau” yanda yafada hakan ko tayi aiko ba karamin kyau hakan yamataba sanan Matar tasake juyo da ita tace “Ya yanzu?” dago kai yayi ya kalleta tawani turomai baki wayar hanunshi ya maida aljihun gaban riga sanan yama Matar alamun perfect 👌 da hannu, tashi Islam tayi daga kan kujeran ahankali dan duk ta gaji da zaman adan hankali tai tafiya jin zafi zafi akasan har zuwa inda yake yana kokarin bude wallet dinshi ahankali yace “muje gida saiki shiga ruwan zafi zai dena miki zafin gabaki daya” gyadamai kai tayi yaciro kudi dayawa yabama Matar aiko ba karamin dadi tajiba tace “musu come back soon” suka fito mota suka shiga ta daura kanta akan kafadar shi sabida yanda tagaji gyara mata kwanciyar yayi gabaki daya ajikinshi nan nan da nan bacci yay gaba da ita, sai Wuraren 6:50 suka kai gida sabida yanda dan holdup yakamasu ahanya.
Ahankali yay tapping fuskarta hakan yasa tabude ido ta kallai kofa yabude mata tafita sanan shima yafito ya sallami mai motar yabude musu kofa suka shiga gidan, zata wuce daki ya kamo hanunta ya matseta ajikin bango yana mata wani irin kallo “wakike ma gwalo and all sort of things dazu?” dan turo baki tayi kafin tasaki bakin da sauri tace “sorry” girgiza kai yayi yace “inaa naki saina.. ” bakinta yakama ya shiga kissing dinta kaman zai cinye bakin jin tsayuwa na neman gagararta tafara kokarin silalewa kasa ya rikota ya zaunar akan kujera batare daya saki bakinba kiran sallan da aka kirane yasa ya saketa yana kallonta da idanunshi dasuka dan chanza launi yace “jekiyi wanka kiyi salla bari natafi massallaci” tashi yayi yawuce yafita tadade zaune daga baya ta tashi duk jikinta yay tsami ga zafi zafi datake ji, bayi ta shiga tahada ruwa mai zafi sosai tashiga sanan tai wanka tafito tai salla.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button