Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 70

Sponsored Links

Bayan sallan Isha ya shigo gidan da takeaway yatasa ta agaba taci abincin da kyar ya dauko magani yabata tasha, wayarshi ce tai ringing ya dauka ya kalleta tareda nuna mata wayar yace “Abba ne and is video call” da sauri ta dawo kusa dashi, ganin dan shimi ne ajikinta yasa ya nuna mata hijabi tasaka sanan yay picking call din Abba ne da duka yayin ta Ya Abdallah Ibrahim harda Sameer auta bakaramin dadi taji data gansu ba tanata murna suma sai murnan fara maganan ta suke sunamata ya karfin jiki tace “Alhamdulillah taji sauki, Abba yamusu addu’a sosai suka amsa da Ameen ahankali tace “Abba ina Faree?” janye fuskar shi Khaleel yay daga wayar yana mata wani irin kallo, bama ta lura dashi ba sabida yanda take kallon wayar Abba “yace gatanan itama dukta damu zatai magana dake” Bama Farida dake gefe wayar yayi hakan ya bayyanar da fuskar Farida, hannu Islam tasa abaki jin kuka yazo mata ganin yanda Farida ta chanza ahankali tace “Faree wat happen to you like this? Innalillahi bakida lpy ne?” murmushi Farida tayi with so much regret yar uwarta data damu da ita hakane ta cutar sabida namiji da kyar ta iya girgiza kai sabida kukan dayazo mata ahankali tace “Islam dan girman Allah kiyafe mini na cutar dake sosai, wlh wlh dis time dagaske nake natuba Islam natuba, dan Allah kiyafe min bazan sake abinda nayiba” takarashe maganan tana kuka sosai itama Islam din kuka tafashe dashi ta sauko daga kan gadon ta zauna akasa tana kuka da kyar tace “Faree nima am sorry, wlh bakimin komi ba, I understand your actions, nadade dayafe miki u are my only sister ke kadai gareni I can do anything for you, tell me bakida lpy ne meya sameki kika rame haka?” girgiza mata kai Farida tayi tareda goge kwallan dake zuba tace “bakomi kawai zafi zuciyata kemin ne koda yaushe amma ko ciwon kai banayi” sosai Islam ta fashe da kuka tace “sorry Faree” kasa daure yanda take kuka yayi hakan yasa ya sakko kasan yazo kusa da ita ya zauna tareda daura hanunshi akan kanta ya kwanto dakan nata kirjinshi yana bubbuga bayanta kokarin tureshi takeyi sabida yanda Farida ke kallonsu amma shiko fuskar wayar baima kalla ba danko fuskarta bayason gani, tarin dasuka ji Farida nayi sosai yasa tajuya ta kalli wayar sosai Farida ke wani irin tari Islam tace “sorry are you ok, kisha ruwa” dan murmushi tayi tana kokarin hadiye tarin takai hannu bakinta jini tagani da sauri Islam da kaman idanunta zasu shiga wayar tace “Faree blood, tarin jini kike?” hannu taga Farida ta daura akan kirjinta tana wani irin tari tana kallon fuskar Khaleel dahar lokacin baima kalli screen dinba hasalima lumshe ido yayi tareda jingina da gado yakai hanunshi cikin hijabinta yana wasa da jelar gashin ta, sosai Farida ke tari jini nabin bakinta takama zuciyar ta da hannu daya tana kallonshi har lokacin, Islam tace “Faridaa, Abba” ta kwalama su Abba datake jin hayaniyan su kira, da sauri su Abba da Ya Abdallah suka zo wajen daidai ta lumshe ido ahankali tace “M.. K” banbare wayar Abba yayi daga hanunta ya kalli Islam yace “bari mu kaita asibiti, Allah kara sauki Islam” katse wayar yayi Islam tafashe da kuka sosai sai a lokacin yabude idonshi ya kalleta bakaramin cin ranshi kukan nata yakeba yacire mata hijabi ya ijiye hanunshi yakai saman kan idonta yana share hawayen datake yi yajawota zai rungume cikin kuka ta turemai hannun tace “bakaji yar uwata bata da lafiya bane” dan bude ido yayi ya kalleta da kyau sanan yace “to ai naji Abba yace zaikaita hospital ko” kara fashewa tayi da kuka ta tashi taje gaban wardrobe tana ciro kayanta tace “ni wlh nigeria zamu koma yanzu nan Farida batada lpy I need to be with her” “babu inda zamu” yafada cikin kakkausar murya yana kokarin cire rigar jikinshi da sauri tadawo gabanshi ta kalleshi tace “sabida ba kanwar kabace ko?” wani irin kallo yamata sanan yace “yes” kan gado yahau yaja bargo abinshi tareda lumshe ido bakaramin ciwo maganan yamata ba tsugunnawa tayi ta dinga kuka akasan wajen takai kusan minti biyar sanan ta tashi bargon daya rufa dashi ta yayemai ta jefar hakan yasa yabude ido ya kalleta, daure fuska tayi ta tsayar da kukan datake tace “wlh bazakayi baccin ba bayan kaine sanadin ciwon nan datakeyi, is all ur fault, Kaine kasamata wanan ciwon am sure ciwon zuciya ne yakamata, tunda nahadu dakai matsaloli keta faruwa dani, tunda nahadu dakai farin cikina yaragu, karabani da my only sister, is because of you yar uwata takusa kasheni, ta tsaneni, taso kashe kanta sabida kai, ni bana sonka Farida ke sonka, ka sakeni dan Allah ka aureta karta mutu da ciwon zuciya, are you dat wicked dabaza sota Koda sau daya bane? Karka kashemin yar uwa, kasaken… ” kasa karashe maganan tayi sabida wani irin mugun mari daya dauketa dashi.
[7/1, 2:02 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button