Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 2

Sponsored Links

PAGE 2

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Related Articles

Yanda suka shigo garin ya janyo musu kallo gurin jama’ar dake kai kawo kowa mamakin dalilin wannan gudun mara iyaka yakeyi,
Saida suka isa ƙofar gidansu Lantana sannan sukaci birki suna mayar da numfashi daƙyar suka kai ga wani kurutturen itace dake ƙofar gdan wanda da gani kasan an ajiyeshi ne don hutawa.
Sun jima suna sauke numfashi daƙyar Kande ta kawar da shirun da cewa yau naga masifa ke waɗannan bakin anya ba aljanu bane Nifa tunda nagansu gabana ya rinƙa faɗuwa” fasali Bibo ta sauke tace “wlh Nima bakiji yanda suka tsoratani ba ni saida nayi tunanin ma sace mu suka zo zasuyi….”
Kekam da daukowa mutane ɗaukakkiya Ni wannan kyakkyawan ne ya firgitani da surkullen da naji yana ambatawa

 

Dariya Bibo tayi tace “ke dallah ba surkulle bane addu’arsu ce ta addininsu kwanaki naji da Jimo Ciwake yayi baƙi yan burni sunayi a wannan abar da suke karawa a kunnensu….”
Mgnr ce ta tokareta a maƙoshinta lkcn da sukaga machine ya tsaya a nesa dasu kaɗan idanunta ya sauka kan wannan kyakkyawan inji Lantai da faɗa,
Sauka yayi daga babur ɗin ya zubanta idanu daga nesa yana ƙarasowa garesu sukuma suna ja baya suna ƙara matsar gdan nasu Lantai, takun maza dana mata ba ɗaya ba hakan ne yasa su cimma su juyawa Bibo tayi da sauri zata kwasa da gudu taji numfashinta ya tsaya cak ƙirjinta ya fara lugude ta ɗago da mugun sauri ta tureshi jikinta na rawar mazari ta shiga waige² kawai sai hawaye ya tsiyayo mata tayi ƙasa da sauri tace “Na shiga uku kayi hkr ka yafemin koma laifin meye nayi maka na rantse da uwa me tsarki idan Jimo Ciwake yaji hakuma tazo nemana ruwan wankin zunubi zai jefani shikenan rayuwata ta galgalce….”

 

Wani ihu ta saki jin ya sake sanya hannunsa ya riƙe ta sosai da sauri ya ɗauke hannunsa daya ya rufe mata baki tare da zaro mata manyan idanunsa.
Motsa bakinsa yayi kamar zaiyi mgn batasan meye ya tuna ba taga ya sake ta yayi gaba sakin baki tayi da rawar jikinta da taki barinta tasa hannu ta share hawayenta ta koma ta zauna Lantai dake laɓe ta fito dafe da ƙirji tace “Yau naga abinda yasa buzu ture naɗinsa nikam Bibo mutumin nan ba ɗan yankan kai bane kinga fah aradu irinsu ake bamu lbr suna shigowa jeji da motoci suna satar mutane suna zuwa sunayin kuɗi dasu”
Sharrrr hawaye ya sake zubowa Bibo tace “ni ba wannan bane matsala ta kinga fa har taɓamin jiki yayi nashiga ukuna ya zanyi yanzu Jimo Ciwake ina shiga zaiji warin maza a jikina…..” Sai kuwa ta kuma rushewa da kuka zama Lantai tayi itama ta rushe da kuka tace “Nima na gani naji Miki wannan tsoron amma kinsan me? Tashi muje gidanmu in dafa Miki ruwa me zafi kiyi wanka bazaiji ba ai an ce ana watsa ruwa warin yake bajewa”

 

Wani numfashi ta sauke me nauyi ta mike suka nufi cikin gdan suka ɗebi yayi suka haɗa wuta suka dafa ruwan komai cikin gaggawa suke yinsa saboda kar Kakatu tazo ta tarar dasu,
Man gyaɗa ta shafa suka fita tanata sauke ajiyar zuciya suka isa gidansu Bibo sunata raɓe² Ɗantala ƙanin mahaifinta ya sawo kai ganinsu tsaye cirko² ya dakansu tsawa yace “durun uwarku kukeyi anan da kuka tsaya kuna tsinkawa mutane hanji” zabura sukayi Lantai ta kamo hannun ƙawar tata suka shiga gda sumsum, wuf suka faɗa ɗakin Jumme ta miƙe da sauri sukayi dako² kamar sunwa megari ƙarya da sauri Bibo tace “ba abinda kike tunani bane muna tafiya ta zame ta faɗa dagwalon kwatami shine muka biya gidanmu ta wanke jikinta” riƙe haɓa Jumme tayi tace “anya kuwa Habibah…” Nan suka kama rantse rantse da duk wani abu da zaisa a yarda dasu wannan ya kwantar mata da hankali tace.

 

“Ai shikenan ga abinci can na ajiye muku a madafi ki dauko muku kuci ki ɗauki kunun zaƙin kikai dandali” zama sukayi suka fara cin abincin kusan Lantai kecin abincin idan taga ta tafi tunani ta zungureta da haka suka gama sukayi kwalliyarsu anan suka dauki bahon kunun zaƙin suka fice suka nemi ɗan dako ya ɗauka.
Ko a dandalin batada wata walwala ɗan wasan da sukeyi da gaɗa duk bata da walwala kowa dake gurin ya fahimci hakan damma Lantai nata tausarta suna zaune ta rafsa uban tagumi wani almajiri ya iso ya tsaya yace “Bibo wai kizo inji Manuwa yana bakin tukuba”
Tsaki tayi ta kalleshi ta watsar Lantai tace “Kai kaje kace tana zuwa” miƙewa tayi ta zari bahon kunun zaƙinta tayi gaba tana cewa “ɗan baƙar jaraba kutumar ubansa zanyi masa ɗan Shegiyar”
Binta Lantai tayi ta riƙeta tace “bai kamata ba abinda kike yi ni banga uwar da Manuwa ya nema ya rasa ba da baki ƙaunarsa kinga fah babansa Sarkin Noma ne….”

 

Wani uban tsaki taja tayi gaba tana ƙara jan zaninta sama suna tafe Lantai nayi mata mitar wulaƙancin da takewa Manuwa.
Can nesa sukaga an haskesu basusan sanda suka rungume juna ba tsabar tsoro da firgici, ƙamshin daya gauraye hancinsu ne yasa su buɗe idanunsu a tare suka saukesu kan Najeeb dake tsaye a gabansu yanayi musu kallon wulaƙanta wulakantacce ya dubi Bibo yace “Meye sunanki?”
Ɗagowa tayi me arhar hawayen har idanunta ya kawo ruwa tsawa ya daka mata yace “banason ƙauyanci tambayarki nayi meye sunanki?” Cikin in…ina tace “Ha…bee…bah….” Lumshe idanu Najeeb yayi yace “Da gaske?” Kaɗa kai tayi yaja numfashi yace “ok dama Mun zo wani aiki ne nan shine ubangidana yakeson ƙulla ƙawance dake….” Zaro idanu sukayi sukace “ƙawance?” Ɗaga masu gira yayi yace “wannan shine gsky duk inda mukaje mukanyi ƙawaye Abokina kuma ubangidana baya ƙawa baitaɓa ƙawa ba amma yasoki kasance ƙawarsa kada kice a’a domin wannan abu ne da bazaki iya kaucewa faruwarsa ba”………….
[3/30, 7:32 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

 

*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci, zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.

 

*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.

 

*Sanarwa*
Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma.
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button