Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 4

Sponsored Links

Page 4*

★★★~~~★★★~~~★★★

Tsaki Najeeb yayi yana huci kamar kububuwa ya fice daga gdan gabadaya shikuma ya nemi guri gefen katifarsa ya zauna shima yana fitar da iska me zafi sosai kalaman Najeeb sun taɓa zuciyarsa kwafa yayi ya miƙe ya shige bayi ya watso ruwa.
Ba ƙaramar gajiya yayi ba ashe haka manoma sukeshan wuya lallai dole a gaida manoma sallar magrib yayi domin yasan ba kiran sallah zaiji ba Saida yayi Isha yayi shafa’i da wuturi sannan ya haɗa tea yasha dake shi ba ma’abocin abinci me nauyi bane indai da shayi to lfy lau ne.

Related Articles

 

Tunda ya kwanta yake sakawa da warwarewa majigin hoton Habeeba yanayi masa gizo a idanunsa, tashi yayi ya zauna baisan meye ya tafi da ruhinsa gareta ba ba kowacce mace tafi komai ba ganinta kwana ɗaya yanajin kamar yayi shekara guda da ita baiji zai iya rabuwa da ita ba, saidai abubuwa biyu suna mugun kada masa hantar cikinsa baisan da yaya Sarki Khalil da Hajiya Kilishi mahaifiyarsa dama sauran danginsa na gdan sarautar dutse zasu karɓi wannan zabi nasa ba.
Karfafawa kansa gwiwa yayi da sama kansa ƙumajin nasara tabbas zaiyi duk mai yiwuwa ya kafa kansa a wajen Habibah da iyayenta duk da suma a yanda suke da tsattsauran ra’ayi yasan za’aja daga kafin su bashi damar auren ƴarsu.
Numfashi ya sauke ya koma ya kwanta daidai lokacin da wayarsa ta ɗauki ruri, gabansa ya faɗi ya mike ya ɗauki wayar numfashi yaja me ƙarfi ganin sunan mahaifiyarsa na yawo a saman sensor ɗin.

 

Cikin mutuwar jiki ya kara wayar a kunnensa ta sauke ajiyar zuciya tace “Autan Mama kaji daɗin garin arna ka manta dani ko kiran ma da kakemin tun jiya da safe banjika ba ince dai lfy kake?”
Wani wahalallen numfashi ya sauke ya shafa sumarsa yace “sorry My love wlh abubuwa ne sukayi min yawa shiyasa lissafin komai ya kwace min ya kike ya Mai martaba da sauran ƴan gida ina Hajiya da Inna duk ince dai suna lfy?” Lfy Alhmdllh ya jikin naka ina labarin surukata….”
Wani damm ƙirjinsa ya bayar da sauri ya basar da cewa “Ohhh Mama wai nikam na dameki ne duk kunbi kun damu sai kun ɗora min nauyi nawa nake ne har yanzu ban rufa 30 years ba” katseshi tayi da cew.

 

“Kai ar ɗan ƙaniyar uwa to so kake sai kakai ka wucce duk mazan gdan nan waye yayi girmanka babu aure? Faɗamin shi haba ubana shi aure ai ƙima ne kuma garkuwa ne ga ɗa namiji nikam gsky nima inason ganin ƴaƴan auta na kada ka manta fah ku biyu gareni maza daga babban yayanku sai kai yan uwanku duk mata ne ai Yakamata ku karɓi girman tunda wataran kune iyayensu duk girman mace ƙasan namiji take domin raunin mu faɗaɗɗe daga bakin ubangijinmu….”
Wa’azin nata yaji zaiyi tsayi yace “Is ok Mama kin kusa samun suruka indai suruka ce very soon kinji” murmushi tayi tace “Ubana kenan Sarkin daɗin baki shikenan Allah ya kawo mana rabonmu na alkhairi” ajiye wayar yayi yana murmushi Hajiya Kilishi kenan kullum maganarta Habibunta yayi aure zaidai yi auren nan ko ta sake masa mara yayi fitsarinsa a nutse.

 

******

Ɗagowa tayi jikinta a mace tace “Na rantse da abar dogaro ba Rabe bane ya rakani gona baƙo ne ɗan birni muka haɗu dashi a hanya shine yace yanaso ya koyi noma Jumme saida nace karya bini yaki ji to ya zanyi masa tunda kince babu kyau jayayya da babba”
Shiru ce ta ratsa gurin Jimo Ciwake ya ɗago yace “Shikenan amma dai banason wannan tarayyar taku saboda ƴan birni basu da gsky idan kin sake haduwa dashi ki faɗa masa nine nace banason alakarku ya nemi wata abokiyar bandake wannan sakarcin da shashancin shashatau ɗin baza ayisa dani ba”
Jinjina kai tayi tace “Na gde zan kiyaye” miƙewa tayi ta koma ɗaki tayi tagumi a haka Kande da Lantai suka shigo suka ishe ta Lantai ce ta sanya hannu ta cire mata tagumin tace “yo yau naga watsiyar watsewa Jimo ne ya mutu ko Jumme da zaki rafsawa mutane tagumi haka?”

 

Numfasawa tayi ta ɗago idanunta ya ciko da kwalla tace “yauma shine ya aiko ku?” Zama Kande tayi ta kama hannunta tace “Na rasa wannan wacce irin masifa ce kwana ukun nan kullum sai yazo dandali yasa an kiramu ya tambayemu meye yasa bakya fitowa? Munce masa baki da lfy to yau dai sakomu yayi a gaba wai sai mun rakosa munyi masa iso ya dubaki….”
Dafe kirji tayi tace “Na shiga uku kada ku barshi ya shigo kuje kuce masa na tafi hayin badarawa gdan kakata kuma ba’a bin hanyar da dare saboda akwai wata mahaukaciyar damusa da take kashe mutane…..” Zaro idanu sukayi.
Lantai ta matso tace “Tabɗi bakisan yanda mutumin nan yake da naci ba ai na rantse da abar dogaro cewa zaiyi mu rakashi garama kiyima su Jumme wayo muje ku gaisa saiki dawo….” Motsin shigowar Jumme ne yasa su miƙewa cikin zaurancensu na ƴammata tayi musu nuni da suje su jashi bayan gidansu.

 

Jumme ce ta dubeta tayi ƙasa dakai tace “don darajar Baba Tsauri uwarki kibarni yau naje dandali da Lawai me kura ake wasa inason wasansa” murmushi Jumme tayi tace “kin gamani da ƙarshen daraja jeki saikin dawo Allah ya tsareki” tsalle tayi ta saki ihun murna ta fice da gudu.
Bayan gdan nasu tayi da sauri ta nufeshi duk wata gaɓa ta jikinta tana rawa ta baza gashin nan nata me taushi da aka ƙawatashi da kitso kananu iyakar gaban bayan aka barshi duguzunzun rigarta iya ƙirjinta ta rufe cikakku tsayayyu masu faɗin tushe da ɗaukar hankali ta killace su ɗamɗam cikin rigar saƙin.
Cibiyar ta a waje take shafaffen cikin nan zanen tatu na kibiya anyi mata zanen flower me ɗaukar hankali ƙugun nan yaci uwar jigida kusan naɗi kusan hawa talatin ta cika mata faffaɗan ƙugun nan zaninta iyakar gwiwarta tukatukin ƙafar nan an ƙawata su da nadin duwatsu.

 

Tunda ta taho ya zubanta manyan idanunsa da suke lumshewa fari tas yake jin zuciyarsa tana isowa ta tsugunna a gabansa ta kama ƙafarsa ta ɗaga ƙafarsa ta ɗora tafin ƙafarsa a tafin hannunta ta ɗago kyakkyawar fuskarta ta sakar masa murmushi da yaja dimple dinta ya lotsa Jan lips dinta suka baje a fuskarta tace “Aminci da nasara su tabbata gareka mutumin birni inata kewarka banganka ba banjika ba har rashin lfy nayi da Jimo Ciwake ya hanani fitowa saboda ka rakani gona….”
Hannunsa yasa tsakanin ƙirjinta da hammatarta ya ɗagota suka fuskanci juna damdam haka ƙirjinta yake bugawa inda shima yake jin wata muguwar faduwar gaba ƙamshin wani turare daya kasa tantance wanne irine yana tashi a jikinta ya hadu da sanyin yanayin damunar ya saukar masa da wata sihirtacciyar kasala baisan sanda ya hadeta da jikinsa ba yasa hannunsa biyu saman ƙugunta ya kwantar da kansa a saman nata ya sauke wata mahaukaciyar ajiyar zuciya da baitaɓa jin fitar irinta a cikin rayuwarsa ba.
[4/2, 2:43 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

*Ramadan promo*
Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma wannan tasa nayi muku discount nrml group 300 ya koma 200 PC 700 ya koma 500, wannan garaɓasar ta iya satin farko na Ramadan ne
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241.

*Sanarwa*

Maganar tsarin post da kuke tambaya ta insha Allahu na tsara shi yanda bazai shafi ibadarmu ba zan rinƙa post kullum 9:30pm wato tara da rabi na kowanne dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button