Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 49

Sponsored Links

49

Tana tsaye tamkar jiran shigowar ayshan take,koda yake hakanne ma,dafeta tayi tana dan ihu,wanda hakan ya sanya zubewarsu saman gadon maman hunaifa,qoqarin qwace kanta aysha take
“Hanan….hanan what r u doing ne?,pls” sai data gama ihunta sannan ta saki qaramar dariya
“Wallahi banga laifinki ba,wannan halitta haka aysha dole ki susuce ki sauya lokaci daya,wallahi kunyi masiiiiifar dacewa,hadin ya hadu wallahi” dubanta aysha take tana hadiye dariyarta,yayin da a zahiri tadan hade gira
“Wai….akanme kike magana ne?dawa muka dace?”
“Ban sani ba ‘yar gaba da rainin hankali,kinsan Allah gulmarku kawai ke tashi a varender dana hau,ina can nemanki wajajen department dinku ina zuwa nan nace ke nake nema aka nunan inda kike,kaiiii aysha ashe ba banza ba kike figawa maza dawa ashe ke kin gama gwangwajewa abinki,kai ma sha Allah wallahi d’an d’ashi,dole mmn hunaifa tasha wannan labarin” ta lura idan bada gaske tayi ba hanan zata mata kwaroroto,kusan halinsu daya da aliya,banbancin dan kadan ne
“Wai da kiketa wannan surutun ce miki nayi saurayina ne?,toki rage zumudi wanda dai kika gani yaya na ne,kuma ga abinda yazo kawomin nan” ta fada tana nuna laptop din data aje kan dan teburin da take dora littafanta tayi karatu,dariya sosai hanan ta saki bayan fa kalli system din harda tafa hannu sannan ta samu gefan ayshan ta zauna,hannunta ta dora kan kafadarta
“A qalla na doshi shekara takwas ko bakwai ina soyayya,kin manta wace ce hanan?,to bari kiji wannan tatsuniyar taki bata samu wajen shiga ba,ko wanda ya fara soyayya yau kallo daya zai muku yasan cewa ba qaramin narkewa kukayi cikin son junanku ba,idan ma ba saurayinki bane bari na gaya miki ku binciki kanku,don ba shakka dukkaninku kuna yiwa junanku soyayya mai zafi,idanunku kawai sun isa su gayawa koma waye haka,saidai wataqila kun afka son junanku ba tare dakun sani ba,ko kuna daga cikin masu qaryata cewa sun fara son waninsu” idanu aysha kawai tasa tana kallon hanan gami da yunqurin faffasa maganar cikin kwanyarta,wanne ne a ciki?,wanne ne ba wanne ba?.

“Wa akewa irin wannan sharhin haka?” Mmn hunaifa dake shigowa ta fada bayan ta zauna saman gadon aysha
“Kinzo a dai dai,wallahi yarinyar nan ba banza ba taqi ayi mata maganar kowa,mmn hunaifa kinga guy dinta kuwa?,hasbunallahu wa ni’imal wakil,wannan shi ake kira da komai yaji,kinga wata iriyar soyayya da ake bugawa mai sanyi” ai aysha batasan ta durmawa hanan dundu ba tana fadin
“Zubaida….mmn hunaifa karki yarda da sharrinta
” a’ah nima fa dana shigo daga waje na danji ana qushin qushin,ko maganar ce?”
“Itace daiiii mamn hunaifa,hostel din nan duka ya dauka” ganin yadda hanan ke faman zubawa mmn hunaifa lbr kawai saita barta ta miqe ta cire rolling din kanta ta daurashi a matsayin dan kwali ta hau dora musu girki,don shaf ta mance ma tana jin yunwa sai yanzu,tana aikin amma tunanin maganganun hanan ke mata yawo a ka,da gaske idanunsu na bayyana soyayya kamar yadda hanan din tace?,to wai shin yama soyayyar take bare har ta ganeta,kalma daya da bata santa ba a rayuwarta wato soyayya.

A bun mamaki a daren saita kasa barci,tayita juyi tana tuna zuwan khalipha a yammacin dazu,duk wani motsai daya faru tsakaninsu sai data tunashi kar a kanta,miqewa tayi daga kwancen ta janyo syatem din daya kawo mata ta kunnata.

Hotonta ne ya mamaye screen din,wanda batasan inda ya samu hoton ba,hakanan ba zata iya tuna sanda aka dauki hoton ba,a nutse ta dinga shiga ma’ajiyar adana hotuna,hotunanshi zallah a ciki wadanda yayi masifar kyau kamar a kirashi ya amsa,ya rabata da duk wani hoto na haidar sai nashi zalla me kenan?,
“Kishi” zuciyarta ta bata amsa,kanta ta kada tana qaryata hasashen zuciyar taya,kishi ana yinsa ne ga abinda akeso ai,yaushe khalipha yace yana sonta ma da har zata zaci ganin kishi a qwayar idanunsa?,amma sone kawai yake haufar da kishi aiko?,zuciyarta ta jeho mata tambayar,saita ture gaba daya tunanin gefe guda.

Wajen videos ta shiga,films ne na soyayya sunfi talatin,kuma duka na jaruman nan da ranar ya tayata kallon fim din ta gudu ta barshi,murmushi ta saki ita daya tana rufe fuskarta kamar yana ganinta,wato yana sane kenan,shi da yace aure takeso?,yace kuma me take gani haka,wani murmushin ya sake subuce mata ba tare data shirya ba,tuna maganarshi ta dazun tayi,hakan ya sanyata zama dirshan ta jawo wayarta,a qalla ta kusa kashe minti talatin tana rubuta saqon tana gogewa,inda daga bisani tayi bismillah kawai ta tura,saikuma tayi tsam tana tuna abinda ta tura din,kamar ta wuce makadi da rawa,tunda ya riga daya shiga haka ta haqura ta koma ta kwanta tana kunna daya daga cikin fina finan ta soma kalla.

Gurine da sau tari yakan je ya zauna kawai idan zaiyi karatu ko zai duba wasu mihimman abubuwa da suka shafi kamfaninsu wanda ya zama dole ya duba din,a yau dai babu ko daya daga ciki,yana zaune ne kawai yana shan ni’imar da Allah ya yiwa wajen,bai jima da gama waya da anni ba a nan ya jiyo kamar hayaniya,ta gaya mishi su amal ne ke rigima da zeenart,dama dazun nan ta gama yi musu shari’a,sosai ranshi ya baci ya dinga fada yana fadin basu isa su hanawa uwarshi zama lafiya ba,don haka kowacce ta kama gabanta,dama shi sun isheshi baisan ubanme suke zaune gidan sukeyi ba,annin ce ta dakatar dashi,tace suma duk abinda zayayi zai zama ne saboda Allah ya fifitasu a kansu,bayan basu suka tsamo kansu daga halin da suke ciki ba ganin dama ce ta ubangiji da baiwarsa,hakan ya haqura,amma yayi waya da haidar ya gaya mishi lallai kome ake ciki zaman kowa ya saitu a gidan,amma karya bari anni ta sani saboda zata hana ruwa gudu ne,ya sani haidar din kome zaiyi tamkar yana nan ne,da wannan tunanin da baci da ranshi yayi yaji shigowar saqon,da fari banza yayi dashi sai wani bari na zuciyarshi ya dinga azalzalarsa da ya duba din,fuska a tamke ta soma danna wayar sai gashi ya buge da sakin sassanyar murmushi,gyara zamanshi yayi sosai ya soma maida mata reply.

Tsaida kallon tayi da taji shigowar saqo cikin mamakin ganin number khalipha ce,tana duba saqon tana murmushi,wani abu ya dinga tsumata,saita biye mishi ta sake maida masa amsa,wasa wasa sai da suka dauki mintuna goma suna musayar saqonni,wanda sai daga baya aysha ta dinga duba saqonnin tana zaro ido,ya akayi ta rubuta wannan kalaman?,sai taji kamar yana gabanta saboda kunyar data kamata.

????????????????

Suna kan hanyar dawowa daga daga aji ita da hanan da suka kammala daukan karatu kisan lokaci daya wayarta ta dauki kida,tana dubawa taga mero ce,cikin zumudi ta daga wayar ta kara a kunneta,gaisawa sukayi daga bisani take shaida mata ta haihu jibi suna,cikin bata rai aysha tace
“Yanzu qawa ki haihu kamarni sai yau kwana biyar nake ji?,ai shikenan babu komai na gode
“Don Allah indo kiyi haquri,wallahi wayarce ta samu matsala saida habu ya sauyamin wata yanzu yanzu aka kawota kena fara kira wallahi” sai a sannan aysha ta saki ranta,hira suka dan taba daga bisani tayi mata alqawarin halartar sunan.

Sai data zo kwanciya ta tura masa masa saqo kamar yadda ta saba koda yaushe ya kuma zame mata jiki,ta gaya mishi zuwa takai din,tana kwance idanunta a lumshe tana tsammanin jin reply kamar yadda ta saba sai taji shuru,duka sai taji yau babu dadi wani banbarakwai,tun tana sauraro har bacci ya dauketa.

Qarfe uku na yammacin washegari suna tsaka da kammala shirinsu na tafiya takai,hanan ita zata mata rakiya wannan karon,ana ya gobe suna ta shirya zasu daman ta dawo ranar sunan saboda washegari tara na safe zasuyi presentation,saidai gaba daya hankalinta kacokam yana kan wayarta,tun jiya data tura mishi saqo har yau bata ji daga gareshi ba,sai taji gaba daya bata dokin tafiyar.

Tana riqe da powder tana shafawa wayar tata ta dauki ruri,da sauri ta aje powder din ta rarumi wayar tana duba mai kiran,khalipha ne kamar yadda tasa capital K a sunanshi,cikin hanzari ta daga ta kara a kunnenta tana aje boyayyar ajiyar zuciya,saidai tuni ya jita,sallama yayi mata sai a sannan ta tuna cewa batayi masa sallama ba,a kunyace ta amsa tana gaidashi,ya amsa mata,shuru tayi tana saurarenshi sanda yake amsa mata gaisiwarta,sai taji muryarshi ta canza ba yadda ta santa ba,kamar ma baida lafiya
“Tun jiya banji daga gareka ba,Allah yasa lafiya”
“Naga saqonki amma ban iya maida reply ba,bana jin dadi ne” hankalinta ne taji ya tashi,take zuciyarta ta karye
“Subhanallahi,me ya sameka ya khalipha?” Karo na farko bakinta yayu subutar ambatar sunanshi,raunin dake muryarta ya fiti qarara,yadda ta ambaci sunan nasa yayi masifar yi masa dadi,har yaji me yasa tunda baice mata bashi da lafiya ba don ya samu irin wannan kukawar daya samu a yanzu?
“Dont bother….ciwon kaina ne ya tashi,kuma baiyi wani worst ba” hawaye ne taji yana son sauko mata saboda tuna silar samuwar ciwon kan nashi,karo na farko da taji bakinta da zuciyarta na Allah wadai da masu hali irin na ahalinsu ita da khalipha,mutanen da basu san qima da martabar zumunci ba,mutanen da basu haifarwa da rayuwarsu komai ba face wani tabo da miki da suka bar zuciyoyi da rayuwarsu,take tafiyarta takai ta fice mata a rai baki daya fit,banda daraj da qimar da mero keda ita a wajenta da ta fasa ba zata dara koda nan da can ba
“Dont cry mana pls…so kike ki daga min hankali?” Ya tambayeta da sassanyar muryarshi da ciwon ya sake sanyayar da ita,cikin mamakin yadda ya fahimci kukanta ba tare daya ganta ba ta goge qwallar data soma sauko mata
“Am sorry” ta fada a hankali
“Allah ya baka lafiya….amma karkace zaka zauna a gida hakanan da ciwo,pls i beg you”idonsa ya lumshe yana jin gardin kulawa daga wajen wata mace baya ga uwa
“In sha Allah,but pls stop crying….will you?” Kai ta kada sannan tace
“Is ohk”
“Ma sha Allah,kin shirya tafiyan?”
“Eh,yanzu muke shiryawa”
“Yayi…..bana son tafiyarki ke daya”
“Eh tare da hanan ne,yanzun zamu wuce tasha mu samu qaramar mota”
“What!,motar me?,no…ki jira nan da minti arba’in akwai wanda na turo zaizo ya kaiku,ban yarda ki sake hawa motar haya ba”
“Thank you” ta fada cikin wani tune mai sanyi wanda ya ratsa zuciyarshi har ya sashi lumshe idanu,ya dora hannunshi saman kanshi ya shafeshi kadan,sai yaji kamar an rage masa ciwon dake damunsa.

Minti arba’in da biyar dai dai ta sake ganin kiran khalipha
“Ki sameshi a wajen hostel ya iso”
“Ohk,shukran” ta fadi tana sauya yanayin muryarta
“Eheeenn” ya iya fadi kawai ta katse wayar ta dubi hanan
“Mu wuce ya iso”, ga mamakinta motoci uku ne tsaye suna jiranta,idanu suka hada da hanan dariya ta saki
“Wannan yaya naki yana ji dake,wannan ‘yar uwa ce da alama ta musamman wadda babu kamarta” ta fadi tana sheqewa da dariya,shuru ayshan tayi mata kawai tana murmushi don nata da abun fada,kamar yadda suka saba treating nata cikin girmamawa idan khalipha na nan yanzu ma haka ne,su suka bude mata gidan baya suka shiga ita da hanan kana suka rufe suka tashi motocin a hankali har suka fice daga cikin makarantar kana suka harba kan titi.

A hankali ya sauke wayar yana tariyar muryarta da maganganunta a kwanyarsa yana sakin murmushi,sai yaji wani sauqi na musamman ya samu a gareshi,zamewa yayi ya kwanta ta gefan damanshi idanunshi a rufe yana ci gaba da tuna ta.

A hankali yaji kamar ana shafashi,da fari yayi tsammanin irin mafarkin da yakanyi lokaci zuwa lokaci ne,sai kuma yaji sam ba haka bane wannan ya wuce mafarki,da hanzari ya bude idanunshi,sai yaci karo da lili,tube take haihuwar uwarta tana masa wani mayen kallo,cikin azama da zafin nama ya zabura ya miqe wanda hakan yayi sanadiyyar harbata da yayi ta fado daga saman gadon,cikin tsananin bacin rai yake huci,fuskarnan tuni ta hada ja,dubanta yake zuciyarsa na masa zafi ya soma mata magana cikin harshen turanci
“Ban hanaki zuwa min gida ba?,ke wace iriyar shaidaniya ce?” Duk data bugu hakan bai hanata tashi ba tana daurewa zafin data ji,don a duniya bata da burin daya wuce ta mallaki khaliphan,jikinta ta soma girgizawa cikin son jan hankali
“Bazan iya daina zuwa gidanka ba khalipha,ka saki ranka da jikinka mu more rayuwarmu,wai meye kake tsoro a ciki ne kodon kai farin shiga ne?,babu komai fa,ko masu irin addininku nawa ne muke tare dasu,saikai ne zaka dinga wani nuna addininka ya hanaka bayan munsan komai,kawai ka saki jiki saika fara zaka gane me nake nufi” (‘yan uwa musulmi mu kula da kyau,duk lokacin da kaje ka aikata wani abu ba dai dai ba tamkar kana wakilatar sauran musulmai ‘yan uwanka ne,duk sanda kayi wani mummunan abu kana sunan musulmi kamar kayi tarnishing image na musulmai ne,don duk wanda bai taba cin karo da mumini na qwarai ba sai ya fara cin karo da gurbatacce zai ma dukkan musulmi kudin goro ne yace halinsu daya,Allah ya tsare mu ya tsare mana imaninmu gaba daya amin).

Gigitacciyar tsawa ya daka mata yana gaya mata karta qaraso inda yake,saidai bata ji kashedinsa ba taci gaba da takowa cikin wani shu’umin murmushi har ta iso gabanshi,hannunshi yasa gaba daya ya hankadata baya ta kifa,wanda hakan yasa ta bude sosai ta kuma ji zafi,cikin kakkausar murya yace ta fita daga gidan gaba daya ya bata minti biyar,idan kuma ta wuce haka zata gamu da fushinsa da bacin ranshi,yana gama fada mata haka ya wuce toilet ya kulle kanshi.

A toilet sit ya zauna yana dafe da kanshi da ya sake tsananta masa,tabbas badon mace bace babu abinda zai hanashi yi mata dan banzan duka,shu’umancin lili yana neman wuce tunaninsa,lallai dole ya yiwa kansa rigakafi,saboda shi dan adam ne kamar kowa,zuciya kuma bata da qashi,hakanan tana tare da shaidan.

Sai bayan minti goma sha biyar ya fito daga toilet din bayan ya daura alwala,ba kowa cikin dakin don haka ya fita ya dudduba gidan ko ina ya tabbatar ta fita sannan ya kulle gidan ya koma bedroom dinsa ya samu waje ya kwanta yana maida numfashi.

Tsakanin takai da wudil ba wani nisa bane ko tazara mai yawa,saboda haka nan da nan suka iso

Kai tsaye gidan gwaggo asabe ta yiwa dirvern kwatancen ya kaita,tunda suka shigi cikin garin ido ya dawo kansu,kafin kace meye wannan labarin indo tazo ya fara yawo.

Gwaggo asabe na cikin yin rude na tuwon dare sukayi sallama farfajiyar makeken tsakar gidan nata,wanda aka yiwa gidan wani gyara na musamman aka shafeshi da sumunti yayi mul gwanin sha’awa,fuskarta qunshe da wadatacciyar fara’a ta aje muciyar hannun nata ta miqe
“Wai wai wai,amaryar muhammadu yau a garin namu,lallai yau farar asabar ce” dariya aysha take sosai
“Kai gwaggo,kamar bani zuwa?”
“A’ah to wannan zuwa na yammaci haka?,yaushe rabonki da takan ma” ta fada tana yin gaba suka bita a baya zuwa rumfar dake gaban dakinta wanda ke shimfide da tabarma da alama bata jima da tashi ba akai,lale take musu wanda tana shirin tashi ta debo musu ruwa ayshan ta dakatar da ita,da kanta ta isa bakin randar gwaggon taba debo ruwan cikin kofin silba
“Wannan randa taki gwaggo da tsahon rai take,har yanzu kuma sanyi yake bata fasa ba”
“Ai ‘yar amana ce wannan randa ni kaina na shaida….” Bata kai aya ba yara suka fara sallama dauke da kwalaye a kansu
“Wai gahi,kayan indo ne inji wasu mutane a waje a mota” kallonsu aysha take sanda take takowa riqe da kofin sulbar ta aje gaba hanan tana kallon kwalayen,dukkansu na kamfaninsu khalipha ne donga tambarin kamfanin nan rubuce baro baro a jiki,tana tsaye tana kallon ikon Allah sai da aka sauke kwalaye guda goma cif,jakarta ta bude ta dauko dubu daya ta baiwa yaran su raba,suka amshe suna godiya suka cilla suka fice a guje yayin data qarasa saman tabarmar ta zauna tana kallon kwalayen.

Sam batasan da kayan ba har suka zo garin,daga gaya mishi tafiyar kenan zuwa turosun da yayi har yasa aka sayi kaya irin wannan
“Wannan bawan Allah wannan bawan Allah akwai hannun alkhairi,bamu da abinda zamuce saidai ubangiji ya albarkaci aurenku,ya baku zuriyya ta gari,ya yalwata dukiya da arziqi” gwaggo asabe ke fadin haka sanda ta duba kwalayen taga kayan da aka nade da sunanta,dubanta hanan tayi da sauri jin gwaggo ta ambaci aurensu
“Aur….” Da hanzari aysha ta mata alama da ido kan tayi shuru don Allah,hakanan hanan ta hadiye maganar tana duban ayshan cikin mamaki,dama ayshan matar aure ce amma basu taba sani ba?,to meye dalilinta na boyewa?,haka taci gaba da duban ayshan cikin mamaki,wanda ta lura da hakan itama,dariyarta take ta dannewa kawai,don tasan yau za’a sha cakwakiya kam,nan gidan gwaggo sukayi sallar la’asar.

Tana saman abin sallarta taja waya ta soma neman number din khalipha,don tun dazun hankalinta na wajensa,tana son taji yanayin da yake ciki,saboda hanan na wajen da gujewa yawan tsiyar data shirya yi mata saita miqe ta fita daga dakin sanda wayar ta fara ringing.

Har zuwa sannan yana kwance rigingine saman gadon nashi dafe da kanshi,a lokacin ya jiyo qarar wayar saidai sam bashi da kuzarin da zai iya tashi bare ya daukota,haka ga qaraci ringing dinta ta gama,har wajen sau uku tana kira ba amsa,hakan ya sanya a sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta ta rubuta masa gajeran saqo
_ya jikin naka?,ina fata dai lafiya,Allah ya qara afuwa yasa kaffara ne a gareka_

Sai data tabbatar yaje sannan ta juya don komawa ciki,sai taci karo da hanan dake tsaye harde da hannayenta tana kallonta
“Sannu mrs khalipha” dariya aysha ta sheqe da ita,don tasam cewa maganar nata cin hanan,don ba yadda zata yine yasa tayi shurh,qarasawa tayi ta kama hannun hanan din
“Me kike ci na baka na zuba?,abinda zamu kwana tare zaki ji komai”murmushi hanan tayi donta qagu taji labarin daga bakin ayshan,tana hango bala’in dacewar ayshan da khaliphan ne,ta hangi cewa wata iriyar soyayya ce ke riqe dasu duka su biyun mai tsayawa a rai
“Promise?” Ta tambayeta tana dariya dariya
“Nayi…muje mu qarasa gidan inna yelwa,itace ta haifi abbana”
“Uhmmm” hanan ta fada suna shigewa ciki.

Sanda suka fito da niyyar wucewa saitaga ashe dukka motocin na tsaye suna jiranta,cikin hanzari suka taso,mamaki ya rufeta,yanzu ashe dama wai suna tsaye,saita kasa shuru ganin kamar hakan bai dace ba,sam sai taji wani iri,suma fa mutane ne kamarta,ita din wace da za’a dinga bata wani tsaro da kulawa haka
“Ai da kunyi tafiyarku,idan yaso in zamu koma kwa zo ku maida mu,ai duka inda zanje ba mai nisa bane duk kusa suke da juna”

*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*ko kuma*
07067124863
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button