Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 35

Sponsored Links

Tai sasan ta Abba yabita da kallo zaiyi magana Abban Ra’is yace “kayakuri iyayen mune, babu yanda zamuyi dasu sai hakuri kawai, ko zaka mata ba yanzu ba, kabari anjima koda da daddare ne saika mata magana kaji” gyadamishi kai kawai yayi Abban Ra’is yace “muje gidan kaji kawai” fita kawai sukayi waje suka shiga mota suka tafi..

Zama Kaka tayi akan kujera tana kallon kayan daidai nan Mama da Anty Lami suka shigo, da mamaki suke kallon kayan Anty Lami tace “kayan waye wayan nan haka Kaka?” cikin tsananin murna Kaka tace “dukna Hamida ne wlh, mai sunana nada kashin arziki wlh, mutanen jiya nakirawo suka dawo dan sunban tausayi nabasu auren Hamidan ansa rana sati hudu, wanan akwatunan fa duk na sa rana ne, akwai na asalin aure na nan zuwa gab da biki” shiru daga Mama har Anty Lami sukayi dan maganan ta mugun basu mamaki bama tasan tayaya zasu amshi maganan ba. “dalla kuzo kuyatayani bude akwatin” ahankali suka shiga Mama ta kakalo murmushi Anty Lami tafara bude akwatunan suna dubawa kayane hadaddu bana wasaba, Kaka tabasu su sweet da dabino da goron tace “gashi nan a kulla a aikawa makota sati hudu, akwatin anan shashina za’a barsu ni yanzu fita zanyi akwai abinda zanje nayi” tai maganan tana Jan babban gyalenta dake kan kofa Lami tace “Allah kiyaye” ameen tace tafice, ahankali Mama ta share hawayen daya zubomata ta tashi fuuu da sauri Lami tarike mata hannu tace “zonan Maman Ayush ina zaki?” cikin fushi da Anty Lami ta dade bataga Mama cikiba tace “haba Anty, haba Anty dan sunga nai shiru komi ina kawaici na dauki Kaka a matsa yin mahaifiyata saisu nemi su takani, nice mahaifiyar Hamida inada right akanta haba Anty yarinyar da gata sai ahankali ne bamata da baki shine zasu dauka subama mahaukaci, wlh bazan yarda a cucen min Hamida ba, tausayin yarinyar nan nake bana wasaba, duka duka guda nawa take, shekaran ta ashirin fa, ki barni naje nakira mahaifinta Allah yau zaiga bacin raina bana wasaba” riketa gam Anty Lami tayi hakan yasa tafashe da kuka tafada jikinta, rungumeta Anty Lami tayi tace “calm down yanzu ranki abace yake don’t take any decision a haste, am sure ko Abban Hamidan baiso hakan ba, Bakiga uwar tashi bane, jarababbiyar uwa taga kudi, kiyakuri kinji ki tsaya kiyi tunani kibari har anjima yadawo saikimai maganan kinji” Gyadama Anty nata kai tayi ahankali trying to calm herself down ta zauna kan kujera zama gefenta Anty Lami tayi tana shafa bayanta hartai shiru sanan Tace “bari na gyara kayan ko saimu kwashi goron da sweet din mutafi dashi karya zama wani abin maganan kuma” gyadamata kai tayi ahankali, hakan yasa Anty Lami ta tattara ta gyara kayan ta kawshi sweet din dazata kwasa da chocolate daidai ta kalli Mama dake kallonta asanyaye duktai wani iri sanan tace “muje” tashi Mama tayi ta tayata rike wasu suka fita daga dakin suka rufo kofan suka fice sukai sasan su Hamida suka samu daf Zainab dake wasa da filon kujera sai dariya suke Ihsan na tsalle, da sauri Hamida ta yarda filon ta kalli Mama da manyan eyes dinta da kitson kanta dasukai shegen tsufa tace “Mama kinga Anty Zainab na tsokanana ko” hararan su dukansu Mama tayi ta wuce tai ciki dan ranta abace yake duk sukabi Maman nasu da kallo, Anty Lami ta ijiye su sweet din tace “Zainab dagake har Ihsan kuzo kutaya Hamida tsefe shegen kitson nan yay tsufa dayawa” da sauri Zainab da Ihsan sukazo duk suna kallon su chocolate din hanunta batare dasun rokaba dan anhanasu roko tun suna yara, ajiyewa tayi ta bude ta debo dayawa ta basu suka karba suna murmushi sanan tawuce ciki wajen kanwarta sukuma sukai zamansu a falo suna kallo amma bini bini Aadil ke fado mata arai bana wasaba tarasa mesa takasa mantawa dashi.

 

 

Bayan la’asar Kaka ta shigo gidan tareda yara sun kwaso mata kaya a ledoji, kwalama Hamida kira tayi. “Hamida, Hamida” dakama Hamidan duka dake bacci zainab tayi hakan yasa tabude ido ahankali ta kalli Zainab din. “Kaka na kiranki” tashi tayi daga kan gadon ta sauko tafito daidai Kaka takaraso bakin kofar su ta kalleta tace “uwar bacci wuce kije kiyi wanka ki shirya kici gayu kifesa turare yanzun nan zanyi salla nafito, fita zamuyi” gyada matakai tayi ahankali tana murza ido sanan tawuce Kaka ma tabita da kallo kafin tasaki labulen tawuce sasan ta.

Wanka tayi duk jikinta ba karfi kaman ciwo nason kamata, wani material lace tasaka red sanan ta tsaya gaban madubi taja eyeliner saman idonta sanan tasaka man baki daya fito da pink lips dinta sosai saika rantse jan baki tasaka ta gyara gashin giranta tai carving dinshi da brush yay wani irin kyau har kyalli yake sanan taciro black hijabinta har kasa tasaka tafito da hannayenta tasaka flat sandals dinta na vintage sanan tadan fesa body spray dinta tafito, bakaramin kyau tayiba bakin hijabin yakara fito da hasken ta sosai kaman wata yar larabawa dama gashi anmata tsifa ta taje gashin tai parking sai hijabin da hulan sukai wani irin das ajikinta, fitowa tayi jin Kaka ta kwala mata kira ta shiga dakin Mama da sauri suna zaune suna magana da Anty Lami tace “Mama Kaka tace wai na shirya narakata wani wuri” tabe baki Mama tayi tace “saikun dawo” kallon Maman ta tsaya yi ganin kaman ranta abace yake jin Kaka ta kwala mata kira yasa tafita da sauri harara Kaka ta watsa mata tace “bazaka fitobane” ahankali tace “yakuri” Kaka tai gaba tana binta abaya tamika mata wani leda ta karba tace “hadaddiyar fura ce mai sanyi sosai mukaje sai kibashi” da sauri tace “wane Kaka?” bude gate Kaka tayi tasakai tafice tace “wanda zaki aura” da sauri tana wani irin kallon Kaka tace “wanda zan aura?” daidai Kaka ta tare napep ta shige ta kalleta tace “wai bazaki shigo ba kin isheni da shegiyar tambaya” ahankali ta shiga tace ma mai keken asibitin prestige suka yatada suka tafi, kusan tafiyan minti ishirin ya kaisu asibitin suka fito Kaka tabada kudi sukai ciki itadai bin Kaka kawai take dan batasan inda Kaka zatakai taba to wama takeda shi mara lafiya, har sukahau bene hakanan taji gabanta yasoma fadi, wani daki Kaka ta dosa tace “yauwa ga dakin chan” suka karasa sallama Kaka ta kwada tareda bude kofan, Baffa ne kawai da Mami adakin sai Aadil dayawani irin rame kwance akan gadon yana bacci dan tunda akamai allura wuraren shabiyun rana bai farkaba, kallo daya Hamida tamusa ta saukar da kanta kirjinta nawani irin bugawa, cikin tsananin murna Mami tazo da sauri tadan duka ta gaida Kaka. “sannu da zuwa Umma, kunsha hanya, ina yini” tai maganan tana kallon Hamida da kanta ke kasa, dan buge Hamida Kaka tayi cikin style hakan yasa tace “ina yininku” kamo hanunta Mami tayi ta shigo da ita dakin ta zaunar da ita kan kujera tace “welcome daughter na” Kaka ta shigo dakin tana kallon Aadil din tace “Allah sarki jibi yanda yarame Allah ubangiji yabashi lpy” Baffa yace “Ameen” cikin wasa Kaka tace “mudai kutashi mufita mubama yaranmu waje anjima ma dawo” murmushi Mami tayi, cikin fara’a Baffa yace “dama akwai wajen shan iska bari mu sauka, muje Maryama” yama Mami magana, fuskarta Mami ta shafa tace “feel free kinji bari muje mundawo” gyadama Mami kai tayi ahankali duk suka wuce suka fita aka rufo kofan dakin yarage daga ita saishi, ahankali ta dago kanta ta sauke manyan eyes dinta akanshi yanda yake kwance kaman wani maraya yay wani irin kyau a kwance yana sanye da white riga mai dogon hannu sabida sanyin ac dakin sai dogon wando da bakin safa akafanshi, gashin sajeshi sun wani irin kwanta lublub na idanunshi sunyi shar sun wani mike yana sauke ajiyan zuciya ahankali, wani irin taji tundaga kanta har dan yatsar kafarta ahankali ta ijiye ledan cup din furan hanunta akasa ta tashi dagakan kujeran ahankali ta zauna a danta bakin gadon tana kallon fuskarshi kirjinta nawani irin bugawa, dan runtse ido tayi dan sosai duk idan yana bacci ta kalleshi takejin wani irin shakkan shi saidai idan idanunshi biyu ne yanamata abin yaranshi takeji normal harta iya wasa dashi, bude idanun tayi ahankali ta saukesu akanshi asanyaye samin kanta tayi da kiran sunanshi cikin siriruwar muryanta batare data shiryaba dan sosai tai wani irin kewanshi gani take kaman yakai shekara daya rabon ta dashi. “Aadil” dan motsi yayi kaman yaji kiran sunanshi datayi zatai magana kenan taji anbude kofan dakin da sauri ta dago kanta ta kalli kofar ido da ido tayi da Aabid dake sanye da white riga mai dogon hannu irin na Aadil da dogon wando hanunshi rike da wayarshi iPhone 11, wani irin faduwa gabanta yayi sabida kallon dayake mata da sauri ta sauka daga kan gado zata wuce taji Aadil yarike wrist din hanunta gam hakan yasa arude ta kallai taga idanunshi a lumshe kasa koda motsi tayi saima kanta datamaida kasa kirjinta na dukan uku uku, ahankali Aabid yakaraso tsakiyar dakin ya tsaya agabanta kamshin turarenshi nawani irin shiga hancinta tana kokarin karban hanunta da Aadil yarike gam takasa, rungume hanunshi yay akirji yana kallonta tundaga tsakiyar kanta danyafita tsawo sosai har kafafunta cikin wani irin low voice yakira sunanta. “Amatullah”.
_🌹IN BANI🌹_

 

Maman Abd Shakur

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button