Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 5

Sponsored Links

5…..

Hakanan Ihsan taji tanajin wani irin, zuciyarta taki natsuwa sai kawo mata Anty Hamida take aranta da sauri ta kutsa kai tafito daga dance floor din tabi hanyar dataga Hamidan tabi tana kalle kalle har itama takai gaban jirgin amma bata ganta ba, babu ma alamunta awajen da sauri tace “to ina taje” sosai taji tanajin wani iri a zuciyarta tashiga wani irin damuwa hakan yasa ta juyo ahankali tana tafiya tana tunani, yar budurwa da saurayinta data gani a wajen takarasa wajensu tana murmushi kafin ma tai magana saurayin yace “cute girl wakike nema anan ki koma ciki karki fada ruwa, small girl doesn’t suppose to be here” murmushi tamai tace “please Uncle have you seen my sister Anty Hamida anan?” da sauri dagashi har budurwanshi sukace no, hakan yasa tajuya tana magana ita kadai tace “to a ina kikaje kika boye Anty Hamida?” komawa hall din tayi but still she’s not herself karasawa wajen Zainab dake rawa abinta tayi tarike hanun Zainab da sauri Zainab ta kalleta, ganin idanunta sun cika da kwalla yasa ta duko dakai cikin daga murya dan karan waka yay yawa tace “Ihsan leave me alone, if you are hungry dau plate ga wajen abinci chan serve ur self ne babu mai hanaki, kici duk abinda kikeso, am having fun please karki daman da rigiman ki auta pls” sakinta Ihsan tayi cikin fushi tai gaban hall din chan inda Ayush ke zaune da handsome mijinta agefenta sunyi kyau sosai, tana ganin Ihsan suka mata murmushi da sauri ta karasa wajen kaman zata fashe da sauri Ayush tarike mata hannu tace “menene auta?” hawaye ne ya gangaro daga idanunta tace “banga Anty Hamida ba nabi inda tayi banganta ba” dan shiru Ayush tayi tana kallonta hakan yasa mijin Ayush yadan duko dakanshi yace “menene Baby” ahankali tace “wai bataga Hamida ba” shiru yayi saikuma yace “bari nasa a bincikata” ya kalli Ihsan din dake share hawaye yay murmushi yace “cry cry Auta, bari nasa anemo miki ita tunda you are missing her dama gashi kunfi kama” yana maganan ya juyar dakai yama wani abokinshi dake sanye da kayan security alamu da hannu yazo yana zuwa yace “Man please ga Ihsan anemo mata Hamida duk inda, am sure ta buya a jirgin nan ne somewhere just help her find her” ya kalli Ihsan yace “follow him kinuna mai Hamidan inkin ganta” washemai baki tayi tabishi da sauri suka fita daga wurin tanamai surutu tace “Uncle dukna duba saman nan bata, muje kasane” murmushi yamata dan d girl is so cute yace “okay fine girl muje” kasa sukayi dan duba dakunan dake kasan…..

 

Wani irin tumble tayi ta shige chan cikin ruwan takai kafin wani wave mai karfi na ruwa yay sweeping dinta with force gaba dawani irin mugun gudu, sanan ruwan yawani irin wuntsulota sama kanta yafito space wani irin nishi tayi tana daga wuya. “iy..yyuuu” tabude baki tana wuntsila kafa da hannu sama tana juye juye tana kokarin bude idanuwanta da ruwa duk suka shiga, da kyar ta bude idanun tana juye juye amma bata hango jirgingu ba tadai ganta a tsakiyan ruwa, gaba ruwa baya ruwa, gefe ruwa ko ina ruwa, gashi sai kasa kasa take kaman ruwan najanta ciki ta nitse, ruwan har habanta, da kyar cikin tsananin tashin hankali gwanin ban tausayi tace “Ma…m” wani irin wave na ruwa yakara zuwa kaman ana aikoshi yahau kanta yay sweeping nata away with force fiye da nada gabaki daya kawai tasadakar ta mutu dan tama kasa bude ido tana kokarin bude baki danta iya numfashi ruwa na shigan bakinta ga ruwan so salty, gawani irin ruwa dake shiga hancinta da kunnuwanta taji kanta yay dumm, yanda take kasa kasa kasa tana bubbuga kafa tana fighting da ruwan dataji gabaki daya yawani irin matseta ya shaketa ya murdeta sosai kaman an kulleta da chain yasa fishes din ruwan duk suka rude suna neman wurin guduwa……

 

_Elagushi Beach Lagos_

Zaune yake agaban Beach yana kallon ruwa, he’s d sunset type, there’s something about sunset that gives him goosebumps, tun yana yaro when ever he’s outside d yamma he always stare at the sun idan yana faduwa, saisa yau ya shigo beach da yamma just to have fun and watch the sun set.
Sanye yake da summer beach pant dayadan wucemai cinya kadan ya dameshi yabi kakkauran cinyarshi, jikinshi ba riga sai fadaddan huge full kirjinshi irin na maza masu work out, idanunshi sanye da ocean cabaretti sunglasses daya wani irin fitar da dogon hancinshi kaman karas, ga wani round black tabon salla agoshin shi daya karama fuskarshi kyau sosai, gashin kanshi dakeda dan yawa jike yake da ruwa dan ruwan ma diddiga yake yanabin gefen fuskarshi alamun daga cikin ruwan yake hanunshi rike da abinda akafi sani a beach da Aqua de coco (danyen kwakwa da aka fere saman akasa straw aciki) ahankali yake sipping coconut water har lokacin yana kallon beach din cool breeze da feshin ruwa na fesomai.

Ahankali take tafiya sanye da bikini pink tadaura beach hat akan long kitson attachment din dake kanta, tana tafiya ahankali cike da rangwada babu takalmi akafa kafafunta na nitsewa cikin lallausar kasar Beach din, hanunta tana rike da nata Aqua de coco tana sipping kadan kadan ta karaso inda guy din yake zaune, fadawa kanshi tayi ta daura kan akan kafadarshi kaman zatai kuka cikin harshen turenci tace “auch Aabid my feets are aching” shiru yayi kaman baijitaba ya cigaba da sipping aqua de coco shi yana kallon ruwan, ahankali ta sakeshi ta tankwashe kafa ta cigaba da sipping nata saikuma ta ajiye ta sake kallonshi tana turo baki takai yatsanta dake sanye da dogon kumba irin na arna tace “talk to me love, I have a shoot today but I abondon it just for you Aabid” ganin ko kallonta baiyiba yasa ta ijiye kwakwan nata a gefe ta tashi ta zagayo ta gabanshi ta shiga ruwan bayanta yabi da kallo tsugunnawa tayi ta dibi ruwan ta watsamai tana murmushi tace “you must talk, say something Aabid, say something, you must talk” takara watsamai ruwan a kirji, dan murmushi yayi daya bayyanar da cute one sided dimple dinshi daidai lokacin wani ma’aikacin beach din yazo yadan dukkar dakai alamun respect yace “sir your sport water bike is ready” dawani irin murya chan kasan makoshi kaman anyi forcing dinshi yay magana yace “okay u can go” ya juyar dakai yana kallon bike din dake cikin ruwan da aka daure igiya a jikin wani karfe awater front din gudun karya gudu, ajiye aqua de coco yayi yamike tsaye da sauri tafito daga ruwan tabiyoshi da gudu takama hanunshi tace “am going too Aabid let’s water dive together since d bike has two seat” dan juyo dakai yayi ya kalleta da baki yanuna mata yaron beach din akasalance yace “then get a life vest jacket, I don’t want you to die before your time” dariya tayi tamai kiss a hanunshi tana wani irin kallon shi cike da so tace “so you care for me” tai maganan tana kallon fuskarshi ganin bai kalleta ba yasa tasaki hanunshi ahankali tajuya da sauri taje wajen yaron beach din karban jacket shikuma yay wurin bike din, there’s nothing dat gives him more fun koyana nigeria koyana outside inhar yana beach shine riding bike a ruwa, dan tsaki yayi dan beach din Lagos dinma is not as blue as he wants it to be, is too local for his liking, shiga ruwan yayi harya kaima gwuiwa kana ganinshi kaga wanda ya kware da ruwa sanna yahau kan bike din yajuyo yana kallon Vanessa that’s coming towards him tanasa life jacket din data karbo akan dan pininin pant da bra na beach dake jikinta bikini, tana gyara beach hat dake kanta, ruwan itama ta shiga tace “yayy am so excited Aabid this ride is gonna be mad fun right baby” gyada mata kai yayi da sauri ta dane ta rungumeshi ta baya ta daura hanunta akan cikinshi tanaji kaman ta cinyeshi dan so, dan yatsine fuska yayi yadan duko yamika hannu yacire igiyan daga bike din ya kunna bike din dawani irin jarababben gudu yana awizo yaja bike din sukai cikin ruwan wave yawani irin dagasu ihu tayi sosai tana kara kankameshi tace “please Aabid we shouldn’t go far okay, am a lil bit scared” cikin husky voice yace “and you shouldn’t have followed me, just keep quiet and enjoy d free ride am giving you” kiss tamai abaya cike da murna takara kankameshi tace “I feel honored Mr Cute, sharing a ride with you is a privilege, no is an achievement” kara lankwashe murya tayi breeze din ruwan na neman fadin da hat din kanta tace “am so happy you choose me acikin all d hot hot celebrities damukeda shi a nigeria, thank you handsome” lashe pink lips dinshi yayi yawani irin yin awizo da machine din ruwa ya feso musu a fuska ihu tayi ta kankameshi tace “am having maddd fun, I love you Aabid” tai maganan tana juyawa daidai lokaci ta hango kafar mutum da sauri ta bubbuga bayanshi tana pointing da hannu tace “Aabid look is that a marmaid leg? A think is a marmaid Aabid let’s leave here” batare daya kalleta ba yadanyi murmushin iskanci yace “they’re no marmaid in Nigeria gurl” ahankali ruwan yadan wurgota sama kadan hakan yasa ta hango fuskan mace, ihu tayi sosai tace “Jesus christ Aabid look is human being, look I think is a girl, Jesus I hope she’s not dead ewooo olorun!” da sauri yadan juyo da kanshi yace “stop enchanting rubbish on my ear” ya yatsine fuska, da sauri ta rikemai kafada tace “look Aabid am serious” ahankali cikin tsananin gajiya da ita ya kalli inda take nunamai fuskan mutum ya hango kadan saikuma wave din ruwa yazo yahau kanta hakan yasa ta niste cikin ruwan, ihu Vanessa takara yi tace “how are we going to save her now Aabid, am not with my phone we suppose to alert the beach authority, are you with your phone Aabi…?” bata gama kiran sunanshi ba ya kashe bike din yawani irin mikar da hanunshi up ya hadasu yay wani irin jumping daga bike din yafada cikin ruwan straight takai ya shige chan kasan ruwan shima hangota yayi ta bude hannu sideways jelan gashin kanta sun mike sun kwanta a ruwan suma tana kasa, kasa, kasa, idanunta a kulle bata numfashi ko kadan, wani irin sauri yayi yana numfashi da baki yana fito da ruwan waje yana swimming kaman fish kafin yakaraso wajen, ahankali ya tsaya ya bude hannayenshi yana wani irin kallon fuskarta tacikin glasses din dake kan idanunshi yanajin wani irin abu da tunda yake in his life betaba jiba, ahankali ya jata da hanun damanshi yahadata da jikinshi ya daura fuskarta akan kirjinshi ya kife fuskar yay sama ya mikar da hanunshi daya sama yana yin kafarshi kaman kifi yay saman ruwan kanshi yafara fitowa kadan saman ruwan, Vanessa dake kan machine gabanta na faduwa sosai sabida tsoro tana hango kanshi nesa da bike dinsu sosai tai ihu tace “thank you Jesus” da sauri ta kwalamai kira. “Aabiddd am right here love” wani irin ciro Hamidan yayi daga cikin ruwan ya daurata akan kafadarshi yana komar da ruwan baya da hannunshi daya yana yin wajen bike din da sauri, tashi yayi daga ruwan yahayo kan bike din da ita Vanessa na kallon fuskarta, zaro ido tayi tace “Jesus she’s beautiful Aabid are you sure she’s not a marmaid?” kunna bike din yayi yana gyaramata zama a kirjinshi yaja bike din dawani irin fitinannen gudu kirjinshi na bugawa fast fast, ko 1min bai daukesu ba tsabagen shegen gudun dayake yi yakaisu gaban ruwan da sauri ya kashe bike din baima damu da kar ruwa yatafi da bike dinba ya diro daga kai rike da ita da sauri Vanessa ta sauko itama ta biyo bayanshi ahankali ya shimfideta akasa yana kallon fuskarta daidai lokacin Vanessa ta karaso dan dago kai yayi ya kalleta tareda jan glasses din idanunshi sama cikin husky voice dinshi yace “get d medic” da sauri tace “o..okay handsome” tabar wajen dagudu, ahankali ya juyo da kanshi ya daura cool brown eyes dinshi akanta, ahankali yay placing hanunshi akan cikinta dayay dan kato sabida ruwa yay pressing gently yana kallon fuskarta, sau uku yana pressing cikinta ganin ba response yasa ya bude bakinta yanadan kallon fuskarta, ahankali yana kallon fuskarta ya daura bakinshi akan nata da sauri ya lumshe ido, ahankali ya hura mata iskan bakinshi cikin nata bakin kafin yadago kanshi ya maida hanun kan cikinta yy pressing but no response, hanunta ya kama yana murza palm dinta sosai sabida yay warming nata yana kallon fuskarta feeling somewhat awkward ahankali yace “hey Jewel, stay with me okay” da sauri ya saki hanun nata yakara dukawa ya daura bakinshi kan nata yasa mata iska sosai this time kafin yakoma adan rude yafara danna cikinta yana kallon fuskarta yace “fight, Jewel don’t go just like that precious, stay with me okay”.
_🌹IN BANI 🌹_

 

 

_M. Shakur_

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button