Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 25

Sponsored Links

Gayu Farida taci sosai kaman zataje gasar Islam Kam tanata dariya dan tasan wajen superman dinta zata Bala ne ya kaita har kofar gidan tacemai 5:30 yadawo ya dauketa yace mata to sanan yatafi. Wayar Khaleel dake hannu Yusuf ne tai kara dan tun safe ya dauke wayar ya boye a wurin shi dan yasan Khaleel zai iya yaki daukar wayar idan tazo, tashi yayi yaje wajen Khaleel yace “Bros tana waje fa jeka shigo da ita” wani kallo yamai danji yake kaman ya bindige shi, ganin baida niyyar magana yace “tariga tazo wulakanci ba kyau please ka shigo da ita naji na yarda koma me zakamin inta tafi Kamin please” wani kallo yamai sanan yajuya yafita daga dakin Goggo ahankali, juyowa Yusuf yayi suka kashe da kanin nasu dukan su suna rawan murna Fa’iza tace “wlh nakosa naganta” kara gyaggyara decorations din flowers din dakin sukayi sanan suka zazzauna akan baban lallausan carpet din dasuka shimfida akan tiles.
Gate ya bude yafito tunda yake takowa take kallonshi tafiyar shi kadai gusar mata da tunani yake kayan turawa ne ajikin shi white shirt ne yadan bude boturin saman sai dogon jeans blue daya saka, wani irin murmushi takemai tace “barka da yamma Mk” dan murmushi yamata yace “shall we” yana gaba tana biye dashi abaya cike da kunya har part din Goggo, wani ihu da tafi su Yusuf dasu Ilham suka dingayi hakan yasa Farida ta labe abayan Khaleel tana kukkule fuska dan ba karamin kunya tajiba, wani irin kallo yakema Yusuf dako ajikin shi saima wani dadi dayake ji, Ihsan ne taje bayan Khaleel din ta kalli Farida dake rurrufe fuska cike da kunya, tabata hannu tace “am Ihsan his sister nice to meet you” hanunta Ihsan ta rike ganin taki bude fuska, tajata takaita wajen su sunata ihu sunajin dadi, da gudu Fa’iza ta kunna music suka hau tika rawa, Yusuf yazo gaban Khaleel dake kallonshi yana wani irin kwaso mai shoki harda gwalo, Farida kuma dasu Faiza sun sata a tsakiyar su sunata rawa abinsu. Gabaki dayan su dadi sukeji Khaleel yay budurwa, sosai sukasha rawa abinsu shi waje ma yasamu ya zauna yana kallon su, Farida sai satar kallonshi take, sunyi kusan 15 minutes suna rawa sanna Yusuf ya rage karan music din Ilham ta tashi ta kwaso drinks da chicken kebab din dasuka hada. Juice kawai Farida ta iya sha sabida yanda suke nan nan da ita duk tadinga jin kunya bayan sun gama ne Yusuf yace “okay once again atafa ma our special guest Farida… Daaaa” yawani kara gunna, suka wani kwashe da tafi, sanan yace “oya time for our game” yan matan suka mimmike suna yeee. Akan carpet suka zazzauna sukai circle Yusuf yakamo hanun Khaleel batare daya kalli fuskar shi ba ya zaunar dashi, sanan ya dauko wani bowl dake dauke da papers da akai folding ya daura ma kowa one one paper ajiki harda Farida sanan ya ijiye bowl din ya zauna kusa da Khaleel yay folding leg kaman yanda kowa yayi yace “papers din nan each of them contain a question da dole saika amsa mana ka fadi gaskiya so starting from me bari na duba Naga wats my question” budewa yayi sanan ya karanta “who is your best friend?” murmushi yay yanuna Khaleel yace “dis dude shine best friend dina”
Fa’iza ta bude nata tace “what do you hate most” dan dariya tayi tace “wanke wanke wlh” daka mata duka Yusuf yayi yace “lazy girl” Ilham ne tabude nata tace “izifi nawa kika haddace?” gwalo Ihsan tamata dauke kai tayi tace “ashirin, suratul Ankabut zuwa Nas” Ihsan ta karanto nata “meke saki kuka?” shiru tadanyi tace “ciwo, idan ina ciwo” sai Farida ahankali ta bude nata ta karanto “who do you love?” shiru tayi Yusuf yace “answer now is ur turn” ahankali ta kalli fuskar Khaleel da sauri ya kawad da kai murya chan kasa tace “him” wani murmushi dukan su sukayi Ihsan ne tace “him, waye him?” juyo dakai tai ta kalli Ihsan a kunyace tai murmushi taki magana, Yusuf ne yace “barta tamayi kokari ai, ya kalli Khaleel ya daga mai gira yace” Mk is ur turn” ajiyar zuciya Khaleel ya sauke ya bude takardar shiru yay ganin tambayar, Fa’iza tace “karanto muji question dinka Yaya” ahankali yace “wakake so?” shiru yadanyi kafin ahankali yace “My Eesha” sosai maganar ta daki Farida, hawaye ke kokarin zubo mata da kyar tai controlling dinsu tadanyi murmushin yake daidai kiran Bala na shigo wayanta dan biyar da rabi ya wuce har da kusan minti goma, tashi tsaye tayi ahankali tace “natafi anzo daukana” “dawuri haka ai bamu gamaba” cewar Ilham murmushi tamusu tace “zan dawo wataran” hanunta Ihsan ta kama tace “muje ki gaisa da Umman mu da Goggo mu fita daga dakin tayi tana dan waigen fuskar Khaleel, sosai Umma taji dadi barin ma Goggo sai addu’a take mata saida suka fito Ihsan tace “sis Eeshan dayake magana fa ta rasu, saisa dakika shigo rayuwar shi yanzu muke murna sosai in sha Allah dake za’ayi” batasan Sanda ta sauke ajiyar zuciya ba, ta share kwallan daya zubo mata murmushi Ihsan tamata sanan tarike mata hannu tarakota har waje, Khaleel ta gani da Yusuf jikin motar Bala suna jira su fito, dan murmushi Khaleel yamata yace “thanks for coming” murmushi tamai back yadaga mata hannu ta shiga mota suka wuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button