Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 36

Sponsored Links

Matseta yayi yana tsotsar bakinta tare da ɗagata yanason barin gurin da ita ta janye tace “Bbynka cin abinci ne dashi yunwa yakeji” ajeta yayi ya buɗe miyar da take dumamawa ya lumshe ido yace “wannan ba girkin Liyo bane” dariya tayi tace “kwaɗayi ji nayi na gaji da zama shiru na tashi nayi” yawu ya haɗiye yace “nima zanci” yana shafa ciki tayi murmushi ta zuba musu farar taliyar ta zuba miyar a ɗan bowl ya dauka ya fita ita kuma ta tsaya haɗa musu salat ta dauko lemo ta fito suka baje a ƙaramin falonsu sukaci sukayi hani’an ya janyota jikinsa yana shafa mararta yace “badan banson takura miki ba da na sauke girki a gdannan sai naki” zaro ido tayi tana kaɗa harshe yayi dariya yace “zanyi miki uzuri ki haifemin bbyna” Kaɗa kai tayi ya manneta da jikinsa ya miƙa da ita suka shiga ɗaki ya kwantar da ita ya rinƙa sarrafata da ƙwarewa sun bawa juna aiki sannan sukayi wanka suka kwanta.

 

Cikin kwanaki ukun rayuwar ma’auratan gwanin daɗi basa gajiya da farantawa junansu a daren rana ta huɗu ne sukayi wani kwana na wahala kwana Aneey tayi da ciwon mara idan ya motsa saita mike idan ya lafa saita koma ta kwanta shi kuma kansa yayi masa wani nauyi hakanan yaji zuciyarsa na suya baya ƙaunar ganinta ya miƙe ya fita lkcn ta samu bacci me daɗi ya ɗauketa can ciwo ya addabeta ta tashi da sauri taganta ita kaɗai sai juyi takeyi zuciyarta cike da mamakin inda mijin nata ya tafi a wannan daren bayan ciwon ya lafa ta miƙe daƙyar ta fito tana jan ƙafarta ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita ta wucce ƙaramin falon.

Related Articles

 

Ta shiga babban bataji alamun sa ba ta kunna hasken gurin bayanan ciwon marar da bayan ya sake sanyata zama ta durƙushe tana murƙususun azaba tana keta gumi saida ya sake lafawa sannan ta miƙe ta nufi ɗakinsa ta murɗa ƙofar ta shiga ɗakin duhu tayi kasaƙe ƙirjinta na bugawa jin motsi a ɗakin ta nufi sweech na ɗakin ta kunna, kunnawar yayi daidai da bugawar zuciyarta ta zube a jikin bango jikinta yana ɓari ba komai idanunta ya gane mata ba face tashin hankali mijinta kwance da yayarta turmi da taɓarya sai nishi yakeyi wani ƙarin tashin hankalin sunanta yake kira faɗi yake Aneey ki taimakeni kada mafarkina ya tabbata idan kika barni mutuwa zan…..” Bata gama tantance kalaminsa ba ta durƙushe ta saki ƙara saboda azabar da taji jikinta ya ɗauki wata rawa ta riƙe kofar kawai saiji tayi wani ruwa yana zuba a gabanta ɗan cikinta na dannota ƙarar data saki daidai da faɗowar jaririn duniya da kukan daya tsandara ne yasa Abdul saurin janyewa cikin wani yanayi yayi firgigit kamar me bacci sai ya wani zabura ya diro a gadon yace “Kay innanillahi Aneey….” Idanunsa ne ya sauka a jinin dake gudu ya nufota da sauri takuwa sanya hannu ta hankaɗeshi ya zube a gefe daidai lkcn da Hasina ke miƙewa zuciyarta wasai yau burinta ya cika ta cusawa Aneey baƙin cikin da bazai taɓa gogewa ba a zuciyarta.

 

Sake tasowa yayi kukan jaririn na fuzgarsa ya nufota har yanzu jikinta rawa yakeyi ta buɗe baki cikin wata irin murya da batasan tanada irinta ba tace “Billahillazi ka taɓani ko ɗana saina kashemu dukkanmu fasiƙi azzalumi Abdul ka cutar dani wannan wacce irin masifa ce me na rageka dashi yayata Hasina mijina…..” Saita rushe da kuka bai iya bata amsa ba sai kallon Hasina da yayi da wata muguwar tsana yace “meye ya kawoki ɗakina…..” Kanta yayi Aneey ta miƙa hannunta kan mudubi ta janyo wani almakashi ta saita cibiyar yaron duk da bata taba ganin yanda ake yankewar ba amma taji ana faɗa ta datse masa ita ta ɗaukeshi cikin jinin ta yunƙura zata miƙe wani jiri ya ɗebeta kawai ta zube a gurin ya kuwa iso cikin tashin hankali da wata matsananciyar damuwa ya tallafota ina babu hayyaci da sauri ya tashi ya dauki wayarsa ya kira Mother ya faɗa mata kafin ta iso tuni Jimba ta iso ta ɗauke yaron cikin jini Hasina tuni ta sace jikinta tabar ɗakin cikin tsoron irin mugun kallon da taga Abdu yanayi mata…….

 

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

*OUM HAIRAN*
[12/21, 5:18 PM] Oum Hairan&Affan: *_WATA KARUWA_*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button