Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 45

Sponsored Links

Yunkurawa tayi ta tashi yasa hannu ya kwato da kanta kan kirjinshi yana shafa bayanta ahankali yace “sleep” gabaki daya atakure take sabida yanda yawani riketa hakan yasa ta lumshe ido kirjinta na bugawa fat fat fat tafi hour daya takasa bacci sabida yanda yake shafa bayannata sai mutsu mutsu take daga bayane baccin dole yasace ta, hakan yasa tai relaxing gabaki daya ajikinshi tana ajiyar zuciya ahankali. Jinyanda jikinta yasaki yasa yagane tai bacci, ahankali gudun kada ta tashi yamika hanunshi ya kunna bedside lamp yana kallon fuskarta yaune rana ta farko daya tabamata kallon kurinla haka, gani yake kaman Eeshan shi yake kallo, dan lumshe ido yay ahankali yace “Allah ya gafarta miki my Eesha” ahankali ya bude ido tareda sa hannu asaman gashin ta yana shafawa jin gashin taushi gashi warawara, d’ayar hanunshi ya mika ya kashe bedside lamp din sanan ya mayar da hanun yanata shafa kanta ahaka wani bacci mai mugun dadi da natsuwa yay gaba dashi.

Wuraren 3 nadare ta farka sabida fitsarin datake ji, jinta datayi akan mutum yasa ta tuna inda take, kokarin cire hanunshi daga bayanta take takasa gashi dakin duhu batagani ko kadan ahankali taji yace “mekike so” bata ganin idonshi da kyar cikin muryan bacci tace “hanunka” hannu ya mika ya kunna bedside lamp din da sauri ta dauke kai ganin yanda idanunshi suka kara kyau sundan kankance sabida baccin dasukayi, ahankali yasaketa hakan yasa ta sauka daga jikinshi da sauri sanan ta zauna daga bakin gadon tana waige waige neman hijabin ta dan bataso ta tashi agabanshi ahaka ganin bataga hijabin ba gashi fitsari takeji sosai yasa tadan juyo ta kalli fuskarshi a lumshe taga idanunshi hakan yasa ta mike tsaye harda dan gudun ta tashiga bathroom din jin kaman fitsarin zai zubo, bata wani dade ba tafito tsayawa tayi tadan kallai ganin har lokacin idanunshi a lumshe yasa tafara tafiya ahankali tadan kwanta ta baki bakin gadon taja bargo ta rufa murmushi yay ahankali. Hartadan fara gyangyadi taji yamata peck a kumatu ya tashi ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito, jallabiya yasaka ya shimfida dadduma yafara salla tun tana kallonshi har bacci yay gaba da ita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button