Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 27

Sponsored Links

After 8 year’s…. Nigeria*
Aminu Kano airport…30
*After 8 year’s…. Nigeria*
Misalin ƙarfe 6 na yamma jirgin sama na Emirates ya sauka a fili tashi da saukar jirgi na Aminu Kano airport, mai ɗauke ɗaliban ƙasar wanda suka kammala karatun su na scholarship da gwamnatin baya ta samar musu. Ɗalibai ne suka ta sakkowa maza da mata ko wanne fuskarsa ɗauke da wani irin farin ciki bayan shekaru takwas yau sun dawo ga iyayensu. “I couldn’t believe Aunt Jeederh would come back from Egypt today” cewar Aaliyyah daga gefe aka ce “Me ya sa?” Ta kalleta “Haka nan” Aaliyah ta bawa Widad amsa. Ko wanne banza idanu yake yaga ta ina Malama Majeederh zata fito… Jawaad ɗan gidan Anti da Uncle Isma’il ya ce “Finally” Jin hakan yasa gabaɗaya suka kalli direction ɗin jirgin inda ake sakkowa. A hankali take sakkowa kanta a ƙasa tana sanye da wata Abaya ruwan sararin samaniya wacce akaiwa feshin dutsuna na masu ruwan huda, tayi rolling kanta da vail sai liƙab ɗin data sanya a fuska da wani sirrin farin photochromic ɗin Glasses a Idanunta. Hannunta ɗaya yana jan ƙatuwar trolley ɗinta ɗaya kuma riƙe da hand bag a nutse take sakkowa, lokacin data sakko ta tsaya cak ta lumshe idanu sbd wani daɗi daya ratsa, farin ciki ya wanzu a zuciyarta. Da ace tana da iko kuma zata iya da buɗe fuska za ta yi ta shaƙi ƙamshin iskar ƙasarta wacce rabonta da ita shekara takwas kenan, tun tana shekara ashirin a duniya yanzu kuma tana dab da cika shekaru talatin domin kaɗan ne ya rage mata 28 take yanzu going to 29 tunda end of the year suka kammala Final exm.
“Ma sha Allah” Majeederh ta furta cikin lallausar murya. A hankali ta shiga rarraba idanu taga ko akwai wanda ya zo tafiya da ita, domin komai ya sauya mata. Ihu ta ji an kurma tare da ƙanƙameta ana faɗin “Wlcm back Anti Jeederh” Majeederh ta ware idanunta akan Aaliyah cike da mamakin ganin yadda ta girma sosai ta yi murmushi tana hugging nata back.
“Sannu da dawowa ƙasa Nigeria” Widad ta furta murmushi kawai Jeederh take sbd tsantsar farin ciki. A hankali ta ɗaga kanta sai a lokacin taga tarin jama’ar da suka zo tafiya da ita, Anti, Ruma da Raihana sai Jawaad da Uncle Isma’il da Innati. Ta dinga ware idanu ko za taga Abbu amma babu shi sai jikinta ya yi sanyi. Tana zuwa Ta faɗa jikin Anti ta ce “Na yi kewa Anti”
“Mu ma mun yi rashin yarinyar arziƙi barka da dawowa” A hankali ta dinga bin kowa tana bashi hug Uncle Isma’il ya shafa kan Majeederh ya ce “Kin zama abin alfahari, Ubangiji ya baki zuri’a masu hali irin naki” Majeederh ta kalli Uncle Isma’il a ranta tana maimaita kalamar “Zuri’a” Ganin motoci har guda huɗu duk na familynsu ya bawa Majeederh mmki musamman da taga Ruma ta shiga wata kuma matsayin driver, motar Uncle Isma’il ta shiga ita da Anti a baya sauranma duk suka shiga mota, On their way back home, Majeederh kept looking at the road, everything has changed for her since she went to Egypt until now, eight years after returning. Ta ɗan ware idanu ta ce “Yaushe akai wannan a Government house?” Anti ta ce “Mefa?” Ta nuna musu roundabout Uncle Isma’il ya ce “Bayan tafiyarki da shekaru biyu, gwamanti data sauka” Ta jinjina kai Calmly ta ce
“Amma kamar ba hanyar gida ba, ko ni ce na manta?” Anti ta yi murmushi ta ce “Daman kam za a sha tambaya, nan ai hanyar Lodge Road ne bari mu ƙarasa za kiga komai” Murmushi kawai Majeederh ta yi tana jin sauƙi a ranta ganinta kusa da ƴan uwa shi ya sa bakin nata ya buɗe a taushashe ta ce
“Uncle yanzu ya yanayin garin yake, waye Governor da mataimaki?” Uncle Isma’il ya ce “Engineer Dr. Muhseen Bagayya” Ta yi saurin cewa “A’a ai daman shi ne Governor har lokacin dana bar ƙasar” Uncle Isma’il ya ce “Yes, ai shekara takwas ya yi yanzu ake ƙoƙarin yin zaɓe duk sun tashi hankali”
“Kenan wanne jam’iyyu ne?” Uncle Isma’il ya ce
“Yaushe Hawwa’u ta zama Talkative ne? zamanta a Egypt?” Murmushi kawai ta yi Anti ta ce “A’a ka barta ta tambaya ai ta zama maƙowa, kuma tana da ikon sani ai” Majeederh bata ƙara cewa komai ba har suka isa Lodge Road suka isa street ɗin da zai kai su har gida, Majeederh ta waro idanu waje ganin sun nufi wani tamfatsetsen gida mai mugun kyau, ta kasa ɗauke Idanunta daga gidan domin kaf unguwar babu na biyun gidan, gida ne iya gida 200by 200. Uncle Isma’il ya danna horn gatekeeper ya miƙe da sauri yana buɗe musu, shi kansa jikinsa rawa yake yau zai ga Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Mamaki bai gama sakin Majeederh ba idanunta ya sauka akan wasu lafiyayyiyun motoci na alfarma har guda huɗu a rumfar ajjiye motoci. Parking Uncle Isma’il ya yi yana fitowa Anti ta buɗe ta fito, a hankali Majeederh ta fito tana lumshe idanunta tare da bin cikin compound ɗin da kallo, a hankali kuma sauran motocin suka shigo. Aaliyyah ta kalli yadda Majeederh ke kallon komai ta ce
“Mamaki ko?” Ta jinjina kai Aaliyah ta ce “Ai zaki sha labari” Gabaɗaya suka shiga gidan a Main parlour suka zauna ita dai Majeederh kallon komai take cike da mamaki. “Ya kamata a cire mana liƙab ɗin” In ji Ruma murmushi ta yi ta cire liƙab ɗin, Gabaɗaya suka tsora mata idanu ta waro nata ta ce “Lafiya?”
“Wallahi baki da maraba da Balarabiya Anti Jeederh kin ga mahaukacin kyan da ki kai, sa maza hatsari a titi” Majeederh ta ce “Kyau ya zama Annoba idan har za ai accident” Suka saki dariya Mami ta ce “A bar mini ƴa ta huta haka nan, ta ci abinci” Innati ta ce “Azaba ji munari nabi abinci da gudu ba wando” Aaliyah ta fasa ihu ta ce “Rufa mana asiri ki saka wando” Innati ta ƙanƙance idanu ta ce “Da ubanki kike mara zuciyar nan, mai yawa ƙasa ƙasa yawan kasuwanci, ƴar banza da idanu fiƙi-fiƙi kamar malafar kwaɗo” Aaliyah ta murguɗa baki ta ce “Bani da lokacinki, Allah ya sa kiga fatalwa yau” Tsit Innati ta yi bata sakewa cewa komai ba. Anti ta sassauta murya ta ce “Majeederh jeki wanka ki sallah kici abinci” Ta marairaice fuska ta ce “To ban san ina zan shiga ba” Ruma ta ce “Zaman house ya dawo kenan” Ba wanda ya kalleta Aaliyah taiwa Majeederh jagora zuwa wani part mai kyau sosai da tsari With so much surprise ya dinga kallon komai kana ta cire kaya ta shiga bathroom a hankali ta saukewa kanta shower tana sauke numfashi, ta ɗaura alwala wata duguwar riga mai sauƙin nauyi ta saka, ta saka hijabi bayan tayi sallah ta ɗauki vail tare da rolling kanta kana ta nufi main parlour duk suna zaune saman dining area ta ƙarasa tare da jan kujera ta zauna. Spoon ɗin kawai take juyawa ta kasa cin abincin can dai ta runtse idanu ta ɗan ci kaɗan. Innati ta ce “Shi ya sa kike kamar kazar matsiyata firit a fige ba tsiya ba arziƙi, tirrr” Hira aka dinga yi har su Anti suka yi sallama tare da komawa gida.

Misalin 12:30 na dare Majeederh da Aaliyyah na zaune saman gado Aaliyah ta ce “Bayan tafiyarki babu jimawa Abbu ya ce za a rushe wancan gidan namu a yi sabo, ya ce kuɗi ya samu sama da miliyan biyar, ni dai ban ce komai ba ban kuma nemi sani ba, sbd i don’t have any business with that, kuma ubanwa ya bani ikon tambayar inda ya samu kuɗin ma? Muka tattara gabaɗaya muka koma Gidan Uncle Isma’il Mami Kuma da Ruma suka tafi can dangin Mami, ba a ɗauki lokaci ba aka gina gida haɗaɗɗe aka dinga surutu a unguwa ina Abbu ya samu kuɗi shi ba sana’a ba?? Ya yi burus dai a lokacin akai bikin Ruma da Imran sai Raihana……,”
“Amma na gansu gida?” Majeederh ta katse Aaliyah da faɗin hakan ta ce “I have no idea, amma idan suka zo gida sai su yi wata gudu wai mazajan nasu basa gari” Majeederh bata ce komai ba, Aaliyah ta ɗora da cewa “Daga nan kuma Abbu ya buɗe shago a kantin kwari ya zuba kaya da yara masu kula da komai, ya ɗinka sutturu kamar yaƙi, lokacin da kika samu nasara a Misira da bayan wata huɗu ya ce gabaɗaya tashi za mu yi daga gidan nan zamu koma Lodge Road, haka muka koma bamu da wani option, shekarunki uku da tafiya akai bikin Anti Latifa” Majeederh ta waro idanu waje cike da mamaki sosai kafin ta yi magana Aaliyah ta ce “Wallahi anyi bikin bayan jinyar da Yaya Aliyu ya yi a ƙasar waje tsayin shekaru biyu, to bayan ya dawo akai bikin” Majeederh ta sauke numfashi ta ce “Ikon Allah, ina aka kaita?”…… “Gata nan kusa damu, ita ce neighbor namu fa” Majeederh kamar ƙaramar yarinya tai zuru ta ce “How?” Aaliyah ta ce “Good, bamu san mene ya faru ba daman akwai gida kusa damu dake duk kusan gidan haya ne na masu kuɗi kawai sai mu kaga ana fara gyara, daga nan ne Latifa take cewa Aliyu ne ya ce nan zai zauna yafi kusa da wajan aikinsa, ana yin bikin ya ta tare, amma a ranar auren ana ɗaura auren Aliyu ya tafi Cairo ƙaro karatu maganar da nake jiya ya dawo cikin dare” A gajarce Majeederh ta ce “Allah ya sa albarka, ke fa?” Aaliyah ta zaro idanu ta ce “Tab ai nayi al’ƙawari sai kin yi aure zan yi” Majeederh bata ce komai ba ta yi shiru da sauri ta ce “Abbu bai dawo ba?” Ta ce “Kai ai tun 7 ya shigo gida, baku gaisa ba?” Majeederh ta yi shiru kawai.
“Na manta ban faɗa miki ba” Aaliyah ta gyara zama ta ce “Bro Alpha an ƙara masa matsayi daga Captain zuwa General” Majeederh ta ce “Ma sha Allah, Allah ya riƙa” Daga nan Aaliyah ta nufi ɗakinta ba don ta so ba.
A hankali Majeederh ta miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabi hankalinta yana kan Abbu shi kawai take son gani, taga ya mahaifin nata yake? Kai tsaye part ɗin da aka nuna mata aka ce shi ne nashi ta nufa, sosai part ɗin ya haɗu iya haɗuwa gashi parlourn farko ta gansa buɗe da dinga kallon komai cike da sha’awa da mmki, ganin baya parlourn ta shiga wata ƙofa da zai kai ta ɗaya parlourn wanda daga shi sai bedroom, ta tsaya cak tare da yin knocking ta ɗauki good 10 minutes tana knocking kafin cikin faɗa aka ce “Who is there?”
“Majeederh ce, Abbu”
Abbu ya maimaita “Majeederh?” Ta ce “Eh” muryarta duk rawa take gefe guda kuma farin ciki take zata saka mahaifinta a Idanunta can ta ji ya ce “To ya akai?” Sosai tambayar ta bata mamaki da tsoro ta ce “A’a daman tunda na dawo ban ganka ba, ina ta duba ka ina so mu gaisa” Daga cikin parlourn Abbu yana zaune saman lallausan kujera watching TV hannunsa riƙe da cup yana shan black tea ya ce “Ok bani da lokaci zuwa safiya” Majeederh kamar zata zunduma ihu sbd abin da ya tsaya mata cikin rauni ta ce “Please naga kowa banda kai, shekara 8 ban ganka ba” A ɗan hassale ya ce “Ok na bar abinda nake na fito ki ganni kenan ko Hawwa’u? Bani na ce ki bari sai safiya ba, ni ma ina da buƙatar ganin naki” A sanyaye ta ce “Kayi haƙuri” Tana faɗin hakan ta nufi part ɗinta. Waje ta nema ta zauna a saman bed tana cusa hannunta a tsakanin cinyoyinta tare da yin shiru tana girgiza ƙafa, ita kanta ba zata iya cewa ga abinda take tunani ba…..
Washegari misalin 7 na safe Majeederh ta fito tana mustsike idanu sbd baccin daya ɗauketa bayan sallar asuba, ta ci karo da Mami ta ce “Ina kwana?” Mami ta kalleta sosai ta ce “lafiya, me ya samu idanun naki?” Majeederh ta ɗan yatsuna fuska ta ce “Sometimes ya yi ta mini zafi, wani lokaci kuma ban fiya gani ba musamman duhu” Mami ta ce “Kuma Kinga Dr?”
“Eh” Ta bawa Mami amsa a gajarce, Mami ta ce “Result?” Majeederh ta kalli Mami da idanunta ya fara yin ja ta ce “Wai yawan karatu da nake hasken littafi dana computer wajan Research, amma an bani medical Glasses bayan an yanka daidai idanuna sai drugs” Cikin damuwa da alhini Mami ta ce “Subuhanallahi, Allah ya sauwaƙe yanzu dai sai ki haƙura da wasu abubuwan ki huta sosai ki rage duba wayar ko?” Ta jinjina kai a sanyaye kamar jin tsoro ta ce “Abbu fa?” Mami ta ce “Ai tun 6 ya fita wai yana da appointment da wani” Sai duk jikinta ya yi sanyi ta juya zuwa bedroom. Wajan 12 tana zaune wayarta data saka line ɗin Nigeria ya fara ƙara, ganin sunan Latifa Omar ya sa ta ɗan yi cute smile tana answering “Amarya” Latifa Omar ta ce “Ke dilla wacce amarya, ai mun zama tsofaffin hannu” Majeederh bata ce komai ba “Ya hanya? Da Misira da kuma baƙunta?” A taushashe ta ce “Allahamdulillah” Latifa Omar ta ce “Please ki zo mana, ni ban tambayi Sweetheart ba, kuma he alrdy left” Majeederh kamar bata gane ba ta ce “Nazo ina?”
“Wallahi kin gane” Ta yi shiru, Aliyu dake zaune a kujerar dake facing Latifa ya yi mata nuni da hannu ta cewa Majeederh bata jin daɗi ne da tuni ta shigo don Allah ita ta zo, Latifa ta kanne masa idanu ta ce “An gama Sweetheart” Majeederh ta ce “Me?”Latifa ta yi saurin rufe baki ta ce “Wallahi bani da Lafiya ne da tuni na shigo kema ai kinsan ba zan iya jira har haka ba, shekaru takwas ba kwana takwas ba” Majeederh ta ce “Ok” Tana ta zaune sai da ta yi sallar zhur kana ta yi wanka ta shirya cikin abaya ruwan toka tayi rolling kana ta saka Liƙab ta nufi fita daga cikin gidan, mai gadi jikinsa na rawa ya dinga gaida Majeederh murmushi kawai take masa, tana fita ta nufi gate ɗin gidan da akace na Latifa ne. Latifa Omar duk a hargitse take ta shiga gyara parlourn cikin sauri tana fesa air-condition Aliyu dai na zaune cike da mmki yana binta da kallo, yana ƙoƙarin magana ya ji knocking Aliyu ya saka hannu ya danne saitin zuciyarsa yadda take bugawa da ƙarfi ya san cewa ita ce, tabbas Majeederh ce “In”
Ya ce, ta murɗa handle ta shigo cikin sassanyar muryarta mai tasiri a zuciyarsa tana ƙarasa shigowa yana miƙewa tsaye ya zuba duka hannu a aljihu idanunsa kafe a kanta da ɗan sassarfa cikin sauri ya nufi inda take tsaye hakan yasa ta gwalo ido tare da haɗe fuska…

Ƙilan sai bayan sallah🤓 Idan Allah ya saka mini shauƙi kuma ku gani gobe, a samu masu kawo mini naman sallah da barka da sallah domin za ni ƙasa mai tsarki na roƙawa Abbu ya fiyar Ubangiji Allah ya shirya ya ɗangwalawa zuciyarsa tausayin Jeena🙁…. Masu karantawa As free common baby an daina yayin haka ki waye ki biya a saka ki grp albarkacin wannan ranar🙏🏿

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button