Garkuwa Hausa NovelHausa Novels

Garkuwa 37

Sponsored Links

*GARKUWAR FULANI*Hannunshi bisa suman kanta dake zube a kafaɗunta.
Yana karatu cikin daddaɗan sautin shi mai ratsa jiki da zuciya.
Yana mata tofi a hannun.
Ita kuma tasa hannun hagun ta.
Ta saƙalo wuyanshi ta cusa yatsunta cikin tattausan sumar dake kwance a ƙeyarshi tana maida numfashi a hankali.

Wasu irin abubuwa yakeji sunayi mishin yawo a jiki yana zaga jinin jikinshi gaba ɗaya.
Yar-yar haka yakejin tsikar jikinshi na zubawa.

Hancinsa ya ɗan cutsa kan suman kanta, ƙamshin ya ɗan shaƙa tare da lumshe idonsa yana nazari maijin wani irin sassanyan abu a zuciyarshi.

A haka bacci ya ɗauke su gaba ɗayansu.

Ummi da Saratu ne suka shiga kitchen sukayi girki
Umaymah kuma ta share mata ɗakinta fes.
Kana ta kira Jadda ta sanar mishi duk abinda ke faruwa.

Yace zai turo mai magani.

Tana gama waya da Jadda ta kira ƙanwarta Aunty Hafsat itama ta gaya mata.

Nan dai ta ɗan kwanta itama tayi bacci.

Bappa kuwa ya kamo hanyar zuwa masarautar Joɗa.
Hakama Barun ɗan aiken Ba’ana.

Sai sha biyu saura suka farka, a tare.
A hankali ya buɗe kyawawan idanunshi, miƙa ya ɗanyi a hankali tare da yin addu’a.
“Alhamdullazi ahyana, ba’adama a mautana wa ilaikal nushur”.
ajiyan zuciya mai sanyi ya sauƙe tare tsurawa kwanciyar da sukayi ido, cikin sanyi yace.
“Wash tashi na gaji”.
Cikin jin kunya ta ƙara lumshe idonta tare da shaƙar ƙamshin jikinshi. dan batasan ya akayi ba kuma ta yayane tazo ɗakinshi har suka kwanta hakaba har sukayi bacci.

A hankali ta mirgina gefe ta kwanta.
Shi kuwa ido ya zubawa hannun tare da ɗan tashi zaune hannunshi ya ɗan sa ya taɓa hannun nata idonshi ya zuba mata cikin nata a hankali yace.
“Ban amince ba, Sarkin baka ya sake baki wani mgnin kisha ko ki shafaba.
Bana so, tunda ya fara baki mgnin ciwon gaba yakeyi ko baya?”.
A hankali tace.
“Gaba”.
Kanshi ya ɗan jingina da jikin kan gadon acikin lumshe ido yace.
“Saida ya shafa miki hannun ya fara kumɓura, da ya kara ya sake ƙara kumɓura, dan haka bana so kada ki sake bashi jikinki ya shafa miki komai kinji ko?.”
Ya ƙarashe mgnar cikin sigar kula

Cikin sanyi tace to.
Tana kallonshi ya sauƙa kan gadon.
Shi kuwa Sheykh Bathroom ɗinsa ya shiga.
Ya rage manyan kayan
Kana ya rage dagashi sai boxes.
cikin mamaki ya sunkuyo ya kalli boxes ɗin, jin damshi da wa kuma harbawa da Sheykh ɗinsa keyi.
Baki ya kuma tsokewa tare da cewa.
“Uhumm tooh abin har ya kai hakane?”.
A haka yayi wonka kana ya fito.

Bata ɗakin shiyasa yayi shirinsa yadda ya kamata.

Kana ya fito yayi break
Sannan ya fito.

A falo ya samu Lamiɗo da Galadima da Sarkin bakan.
Cikin tsuke fuskarsa ya nunawa sarkin baka hanyar fita tare da cewa.
“Tashi kaje. Maganin ya isa haka”.
Da sauri Umaymah tace.
“Gsky kam a barshi haka tunda anayi ba sauyi sai ci gama yakeyi”.
Murmushi Lamiɗo yayi kana yace.
“To shike nan Khadijah.”
Sai kuma ya kalli Sarkin bakan yace.
“Kada ka damu jeka kawai”.
To yace kana ya fita.
Bayan ya fitane Lamiɗo yace.
“To anyi maka yadda kakeso hankalinka ya kwanta.
Amman munyi mgnar da mahaifinta yace min.
Yana zuwa da wani mai mgnin”.

Shi dai gyara al’kyabbar jikinshi yayi, kana ya sallamesu ya tafi.
Daga bisani su Lamiɗo suka tafi, bayan sun tattauna da Umaymah.

Ranar ma dai haka Aysha ta wuni yanzu da sauƙin anjima sai a hankali.

Ƙarfe goma na dare Ummi ta taimaka mata tayi wonka.
Kana tazo tasa wata doguwar ribar baccin.

Hijabi ta zura a kai kamar koda yaushe.
Miƙewa Umaymah tayi tare da cewa.
“Zo mu tafi”.
To kawai tace kana ta miƙe tabi bayanta.

Da mamaki take kallonta.
Ganin sun nufi Side ɗinsa.
A falo suka sameshi da jallabiya a jikinshi.
Cikin mamaki yace.
“Lfy kuwa Umaymah?”.

Ajiye Aysha tayi bisa kujera kana ta juyo ta kalleshi tare da cewa.
“Lfyar kenan! gata ku kwana ana kaga zahirin yadda take kwana”.

Kafin yayi mgna ma ta juya ta fita, taja ƙofar ta baya gim ta rufesu.

A hankali ta jingina da kujera tana mgnar zuci.
“Uhumm ni in Bappana yazoma gwara na bishi mun tafi tare.
Ummey ma zatayi min komai da gatana ba sai anyi ta min hakaba”.

Ta gefen ido ya kalleta dan bata san mgnar ta fito fili ba.

A hankali ta miƙe kan kujerar tare da lumshe idonta.

A hankali bacci ya saceta.
Shi kuwa kallon da yakeyi tashar ƙasashen Larabawa, shi yaci gaba dayi.

Sai sha ɗaya da rabi ya miƙe yana kallonta murmushi ya ɗan yi kana ya juya ya shiga Bedroom.

Wonka yaje yayi kana ya dawo.
Ya zura jallabiya kan boxes ɗin shi bnnarshi ya cikashi bam.

A hankali ya fito falon ganin tana baccine, yasa ya koma ɗaki ya kwanta.

Sha biyu nayi ciwo ya tasheta,
Cikin bacci ta miƙe da ƙarfi tare da cewa.
“Innalillahi, wahhhhhhyoohhhhhh Shyyyyyyt”.
Sai cikin kunnenshi yaji sautin.
Shiru yayi yana kasa kunne can kuma sai yaji tana.
Kuka tare da alamun tana zirga-zirga.
A hankali ya miƙe kana ya fito.
Ganin yadda ta ɗaura hannun a kaine yasashi.
Jan ɗan gajeren tsaki jawota yayi suka nufi bedroom.
Bisa gado suka zauna.
Hannun shi yasa ya tallaɓe nata.
Kana ya fara mata tofi.

Yanayi tana jin abin na lafawa,
har saida yaga ta daina shishitan.
Sannan yace.
“Kwanta to”.
Cikin jin daɗi abin ya lafa ta kwanta.
Shima konciyar yayi ya bata baya.
Mitti biyar tsakani.
Ta miƙa zaune da sauri tare da cewa.
Wayyo Allah na yana dawowa.”
Fuskarshi ya kwaɓe kana shima ya tashi zaune.
Hannun ya kuma jawowa.
Ya fara yi mata tofi cikin 15 minutes sai gata tana lumshe idonta alamun bacci zatayi.

A hankali yace.
“Kwanta to”. Ba musu ta kwanta.
Kamar da fari bayan 15 minutes ta kuma zabura ta tashi.
Harda kuka wannan karon dan dare ya fara nisa ciwon zai fara tsananta.
Da sauri ya miƙa zaune tare da jawota ta faɗa jikinshi sabida ganin alamun guduwa zatayi.
Cikin sanyi yace.
“Yau naga ta kaina yanzu bazaki barni inyi bacci ba, kiyi addu’a mana”.
Jin yadda take shirin ɓare baki zatayi kukane ya sashi.
Fara yi mata tofin still kuwa abu kam ya lafa.

Umaymah kuwa da Ummi sun kasa bacci sai kasa kunne sukayi.

Ita jin shiru-shirun ba motsinsu ba kuka bata kuma dawobane yasa suka ɗan samu nitsuwa suka kwanta bacci.

Sheykh Jabeer kuwa ranar haka suka kwana ba bacci.
Yayi mata tofi har yawun bakinshi ya kafe.

Sai asuba bacci ya saceta.
Shi kuma kawai wonka yayi yazo ya fara nafilfilinshi.
Ana kiran assalatu ya nufi masallaci.
A falo ya samu Umaymah cikin kula ta kalleshi tare da cewa.
“Jazlaan ya jikin nata ka samu kunyi bacci kuwa”.
Cikin sanyi yace.
“Ni ai yau kamar jemage na kwana idona biyu bakina bai huta da tofiba.
Yanzu dai tana bacci nayi ta tashin ta ma taƙi.
ki leka ki tasheta.”
Yana faɗin haka ya fice.

Sanin bazai dawo da wuri bane yasa da aka idar da sallan.
Umaymah taje ta tasheta.
Suka dawo nan Side ɗinta.
Sosai sukayi mamakin ganin hannin ya ɗan sace kaɗan kumburin ya ragu.

Da kyar aka taima mata tayi wonka tasha tea.

Shi kuwa Sheykh sai bakwai da rabi ya dawo.
Yana dawowa ya konta bacci.

Ita kuwa Aysha tuni rana na tashi ciwon na tashi.
Gashi wani irin masifeffen yunwa takeji tamkar taci babu.
cikin sauri ta miƙe, daga zaune da take da sauri Umaymah ma ta miƙe tare da cewa.
“Bismillah, ya tashi ko?”.
Ganin ta nufi hanyar falonne tayi maza ta bita a baya tare da cewa.
“Tsaya Aysha kada ki fita kinji ko?”.
Cikin muryar wahala tace.
“Umaymah zanje wurin Yah Sheykh ne yayi min tofi, in yamin tofi yana rage ciwon sosai”.
Cikin sauƙe numfashin tace.
“To jeki”.

Da sauri taci gaba da tafiya.
Tana yarfa hannunta na hagu.
Kai tsaye bedroom ta wuce.
Cikin borgo ta hangoshi konce.
Da sauri ta iso.
Hannu tasa ta saman borgon da niyar ta tasheshi.
Dai-dai kan bnnarshi dake neman hudo borgon ta sauƙe hannunta tare da kamawa.
Da nufin jan borgon.

Wani irin azabebben abune yajin ya zirta mishi daga tsakiyar ƙoƙon kanshi har zuwa kan babbar yatsar ƙafarshi, lokacin ɗaya yaji wani fitinenne abu ya diro mishi.
Jin yadda ta cabki Sheykh ɗinshi
Ido ya bude cikin magagin baccin da baƙon yanayin da yaji ne ya kwaɓe fuska kamar zaiyi kuka yace.
“Wash Allah na ni Muhammad me kuma zan miki? Me kikeso in miki? Dan Allah ki barni inyi bacci”.
Yaye borgon tayi, tare da zama kusa dashi ta miƙo mishi hannun kusa da bakinshi tare da cewa.
“Uhum yimin tofi”.
Cikin bacci ya zuba mata ido a hankali yace.
“Ke ba baki iya addu’a bane da bazaki rinƙa yiwa kankiba”.
Cikin rawan murya tace.
“Naka yafi, samar da sauƙin da wuri .
Dan Allah Yah Sheykh kayi min ai addu’an miji yafi karɓuwa da wuri”.
Kanshi ya meda ya konta kana yace.
“To kawo hannun fitinenneya kawai”.
Miƙo mishi hannun tayi shi kuma ya fara yi mata.
Tofin
Cikin ikon Allah kuma zogin ya fara lafawa.
Da ya bari sai zogin ya dawo haka dai dole ya rasa baccin.

Kasan cewar yau jumma’a ne, sha biyu dai-dai.
Yace.
“To tafi wurin Umaymah tayi miki Ni zanyi shirin jumma’a.”

To tace kana ta fita ta tafi.

Shi kuwa wonka ya shiga yayi kana ya fito ya kimtsa tsab cikin jallabiya Royal blue.
Al’kyabbar kuwa ruwan madara.

Yayi kyau sosai yana fitowa su Jalal na isowa nan suka tafi masallacin.

Cikin ikon Allah kuma yau hannun da sauki kukan ba sosaiba kumburin ya ɗan ragu.

Yauma da dare can Umaymah ta kaita wurin shi suka kwana kamar jiya.
Da gari ya waye kuma kasan cewar asabarce.
Babu inda zaije nanma ta tsareshi ta hanashi bacci.

Yunwa da ciwo sunsa bata iya baccin.

Cikin sanyi tace.
“Yunwa nakeji”.
A hatsale yace.
“To cinyeni mana kawai ki huta”.
Cikin share hayenta tace.
“Yimin tofin inje inci abinci”.
Haɗe fuskarshi yayi kana ya fara mata tofin.
Hannu tasa ta damƙi cikinta
Yau kwana biyar kenan rabonta da wani abu mai nauyi sai tea taketa sha kamar yar yaye.
Tana ganin ya koma ya kwonta.
Ta miƙe ta fito a falonshi ta samu Umaymah na jera mishi abinci a Dinning area.
Tana ganin ta fito tace.
“Aysha ya hannun?”.
A hankali ta juyo tare da cewa.
“Umaymah yunwa nakeji, bazan iya shan tea ba na gaji dashi.”

Da sauri tace.
“To zo nan.”
Ta ƙarishe mgnar buɗe Foodflaks ɗin.
jolof ɗin taliyace ce da kifi da jan nama, yaji kabeji da karas ga kuma dafeffen kwai an ɓare an jera a sama.
Shi ta zuma mata a plate.
Kana ta buɗe ɗaya kular gasasshen jan namane mai ɗan romo mai kauri.
sai kuma biredi, da flaks ɗin shayi.
Zuba mata gasashen naman tayi da romon mai ɗan yawa kana tace.
Shigo kizo ki zauna kici.

Da sauri ta haɗiye yawun bakinta.
Tare da shaƙan ƙamshin girkin.
hannunta mai lfyar ta saka.
Tsakankanin ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu nan da sukayiwa wurin labule.
Ta buɗe hanya tasa kai ta shiga tana kare hannunta mai ciwon.
Cikin rashin sa’a igiyoyine suka dauwo suka biyota suka bugi hannu mai ciwon.
Cikin wani irin masifeffen zafi.
Ta fara kada lafiyeyyen hannun tana cewa.
“Innalillaheeeeeeeee, wayyo Allah na.”
Sai kuma ta fara zagayawa cikin Dinning area.
_Duk wanda ya taɓa ciwon hannu ko yatsa shi kaɗai zai iya sanin halin da mutun ke shiga in ya fame._
Da sauri Umaymah ta ƙamato, ta riƙe tana jero mata sannu kana tana rabkawa Sheykh Jabeer kira.
“Jazlaan! Jazlaan!! Jazlaan!!!”.
Da sauri ya buɗe idonshi tare da dirowa kan gado ya nufi hanyar fita jiyo yadda Umaymah ke auna mushi kira.

A falon ya tsaya tare da juyowa ya kalli Dinning area.
Ganin yadda Umaymah take kiɗime mene yasashi nufarsu da sauri.

A can babban falon kuwa. Ummi da Hajia Mama da Aunty Juwairiyya dake falone suma suka shigo da sauri jin yadda Umaymah ke abkawa Sheykh kira da alamun a razane a kiɗime.

Suna shigowa falon suka nufi Dinning area ɗin inda suka hangisu.

Shi kuwa Sheykh yana isa yasa.
Hannunshi ya jawo Dinning chair tare, da tallafawa Umaymah su ajiyeta bisa kujerar.
Dan idonta duk ya tafi sama yana ƙafewa kamar zata suma.
Ganin haka, Ummi ta iso da sauri hakama Hajia Mama da Aunty Juwairiyya wanda taketa maimaita innalillahi cikin ruɗanin, ganin halin da Shatu ke ciki.

Shiko Sheykh Ganin Umaymah da Ummu bazasu iya bane,
yayi maza ya kamoto, cak ya ajiyeta kan kujerar.
Umaymah kuwa Fridge ɗin shi ta buɗe goran ruwan zam-zam mai sanyi ta miƙo mishi.
Ummi ce tasa hannunta ta amshi gororar sabida shi yasa hannunshi duka biyu ya tallabe kagaɗunta.

Ita kuwa Shatu cikin tsananin azabar da takeji idanunta ke tafiya can sama takejin muryoyinsu.
Ido ta buɗe jiki na rawa, ta kalli Hajia Mama data matsota tare da cewa.
“Sheykh matsa bani ita nan ta sumane”.
Ta ƙare mgnar tana ƙoƙarin kai hannunta bisa hannun Shatu mai ciwon.
Hakane yasa cikin karkarwan jiki ta ɗora hannun nata saman kanta tare da cewa.
“Bana so kada ki taɓani, ku fice min daga nan, cutar da kumkayi mijina na bayama bai ishekuba ne?”.
Cikin sauri ya ƙara sunkuyowa tare da cewa.
“Keh ki nitsu ki tsaya ciwo yasa kinawa kowa kallon mugu, Hajia Mama ne zata cutar dani?”.
Sabida ya lura kamar bata haiyacinta.
Ita kuwa Shatu ganin Hajia Mama na ƙara matsotsune yasa tayi maza tasa hannunta mai lafiyar ta ruggume ƙugunshi cikin rauni da rawan muryar azaba tace.
“Shi mugu idan ya cika mugu ai baya bayyanawa duk mugun da ya baiyana kanshi bai cika muguba.
Sai kuma ta fara jujjuya kanta.
Da sauri ya
mshi goran zam-zam ɗin da Ummi ke miƙa mishi, tare da tareta ta gaba ganin alamun zata faɗi.
Taretan da yayine yasa ta afka kan cinyoyinshi kasan cewar a tsaye yake ita a zaune.
Buɗe gorar yayi ya sa a hannunshi ya watsa matashi a fuska.
Da ƙarfi taja numfashin, tare da meda idonta ta lumshe.
diba yayi ya kuma watsa mata.
A karo na uku ne daya watsa matsamata ne tasa hannunta na hagu ta zagayo ƙugunshi da ƙarfi.
Sabida ruwan zam-zam ɗin.
Daya taɓa hannu mai ciwon sai taji.
Wani irin sanyi ya ratsa hannun.

Shiru yayi yana tsaye a gabanta.
Tana ruggume dashi.
Tana sauƙe numfashi murya can ƙasa tace.
“Umaymah zanci abinci”.
Sunkuyowa yayi cike da kunyar ganin yadda ta ruggumeshi.
Ummi da Hajia Mama da Aunty Juwairiyya kusa kasake sukayi suna kallonsu.
Shi kuwa janye jikinshi yayi.
kana ya koma gefen Fridge ɗinsa.
ita kuma Umaymah hamdala tayi tare da cewa.
“To”.
Matso da plate duka biyu tayi gabanta.
Kana ta jawo ɗaya kujerar tace.
“Jazlaan bata abinci taci.
Bari inje in kawo mata kunu.
Tunda tace bata son tea”.
Jin haka su Ummi sukayi gaba, ita kuma ta bisu a baya.
Da sauri yace.
“In bata kuma Umaymah”.
Cikin faɗa tace.
“Yes! Sabida bata iya kai abinci bakinta da hannun hagu.
Kuma baka yarda da a baka bayi a Side ɗinkaba bare su bata taci.
Dan haka sai ka batan”.
Tana faɗin haka ta fita.

Ita kuwa Aysha cikin jin yunwar na neman illatamata rayuwa.
tasa hannun hagun ta ɗauki Fork ɗin.
tsakiyar plate ɗin ta sokashi kana ta murɗa.
Sannan ta ɗago hannun a kaikace kafin ta isar dashi bakinta baifi tsalli shida ya rageba.
Gashi har jikin rigarta duk ya zube mata.

Loma biyu tayi ana iko idonta ya cicciko da hawaye.
Sabida tausayin kanta da kanta.
In ba cutaba me zai sata cin abu da hannun hagu tanaci kuma yana zube mata a jiki da baki kamar yarinya.
Shar-shar hawaye suka fara kwaranyo mata.
Hannunta tasa ta shere hawayen tare da ture plate ɗin.
Kana ya kife kanta bisa table ɗin.
tana shessheƙan kuka a hankali.
Ga yunwa kamar zai kasheta an rasa mutum ɗaya da zai tallafa mata.

Sauƙa yayi daga saman steps ɗin a nan ya haɗu da Umaymah.

“Taƙi ci”. Yace tare da wucewa ya nufi bedroom ɗinsa.

Ita kuma Umaymah gefen Aysha, ta zauna hannun tasa ta dafa kafaɗunta tare da ɗan ɗagota.
Cikin sanyi tace.
“Karɓi kisha kunun kinji ko, Aysha”.
Cikin jin yunwar dake azalzalar ta, ta amshi kofin tasha fiye da rabi kana ta ajiye kofin tare da miƙewa tsaye tace.
“Ya isheni, zanje in kwanta bacci nakeji”.
To Umaymah tace kana tabi bayanta.
Har ɗakin ta raka kana ta fito falon.

Shi kuwa Sheykh yana shiga bathroom ya shiga.

A can cikin fadar masarautar Joɗa kuwa a sashin baƙi na musamman,
Bappa ne da wani matashin saurayin da bazai gazasu Jamil ba, sai kuma Barun
Sosai aka karramasu aka tarbesh a mutunce.
Abin ci da sha aka jera musu.
Sai dai Fulakun asalin fulani yasa basu ci komaiba, sai ɗan ruwa suka kurɓa.
Sai dai barun da yaci yayi haniƙan ya cika ƙundunsa.

Bayan Bappa sun gaisa da Lamiɗo da Galadima ne, yayi musu bayanin abinda ke tafe da batun.
Jin hakane yasa Lamiɗo ya kira Umaymah.
Yace mata ga Baban Aysha yazo su zo da ita nan.

Umaymah dake tsaye bayan Aysha da tun ɗazu ta tashi taketa zirga-zirga ne tace.
“Allah rene bazata iya zuwa ba.
Sabida zogin hannun ya tashi.
Tun ɗazu zirga-zirga takeyi tana kuka.
In babu damuwa ayi musu jagora su zo nan ɗin kawai”.
Cikin nitsuwa Lamiɗo yace.
“Assha Allah ya sauwaƙa.
Turo min Jakadiya sai tayi musu jagora”.
To Umaymah tace kana ta katse kiran tabi bayan Aysha data nufi falon.
Suna fitowa ta kalli Ummi tace.
“Ummin Jabeer Lamiɗo yace kije akwai baƙin da zakiyiwa jagora.”
To tace kana ta miƙe da sauri ta fita.

Ita kuwa Umaymah tsaya tayi tabi bayan Aysha da ido ganin.
Ta nufi falon Sheykh tasan zataje tace ya mata tofinne.

Ita kuwa Aysha kai tsaye ta nufi bedroom nashi ganin baya falo.

Shiru babu kowa a bedroom ɗinma, yan waige-waige tayi, kana ta nufi bakin ƙofar bathroom jiyo motsin ruwa.
Bubbugawa ta farayi tare da tura ƙofar tana cewa.
“Yah Sheykh! Yah Sheykh buɗe ƙofar kazo kayi min tofi.”
Da sauri ta juya ta bar ƙofar Bathroom ɗin sabida,
azaban zuƙa da tauna da taji hannun yanayi.

Falon ta dawo wurin Umaymah.

A can sashin Lamiɗo kuwa.
Ummi na zuwa ta juyo dasu Bappa.
Tana gaba suna binta a baya.
Bappa da saurayin nan suna tafiya a nitse kansu a ƙasa.
Barun kuwa sai waige-waige yakeyi da yake dama harda ƙarewa masarautar kallo aka turoshin.

A cikin Falon kuwa a hankali Umaymah ta kamo hannun Aysha ta zaunar da ita bisa kujera tare da cewa.
“Sannu ko Aysha yi haƙuri zauna.
Kinga Bappanki yana zuwa”.
Zaman tayi kamar dai yadda Umaymah ta umarceta,
sai dai hannunta mai ciwon yana saman kanta.
jikinta duk karkarwa yakeyi tamkar mazari.
idanunta nata zubda hawaye.

Jim kaɗan kuma ta miƙe tsaye ta fara zirya a tsakiyar falon.

Sheykh Jabeer kuwa yana fitowa wonka ya shirya cikin shigarsa da yanzu.
Yake ganin tana rufa mishi asiri da ɓoye Sheykh ɗinsa dake tsaye dare da rana, wanda da tsayuwar ne kaɗai baijin komai to juya da yau kuma lamarin ya fara sauya salo.

Hajia Mama kuwa, wani irin taku tayi har ta isa falonta, kai ta jinjina cike da yarda da kai.

Ummi kuwa.
Suna isa bakin ƙofar Bappa ya ɗan tsaya ganin hakane yasa Ummi juyowa cikin martabawa tace.
“Bismillah, ku shigo ba komai ku taho”.
Cikin nitsuwa Bappa ya kalli wannan saurayin tare da nuna mishi hanya yace.
“Al’amin bismillah”.
Cikin nitsuwa wanda aka kira da Al’amin yabi bayanta.
Kana shi kuma Bappa yabi bayanshi.
Barun ya biyo bayansu ita kuma Ummi tana gabansu.
A haka suka shiga falon.
Fadawan dake binsu a baya kuwa suka tsaya a nan.

A falon kuwa, cikin wani irin azaba da gigita, Aysha ta miƙe tsaye kife kanta tayi a jikin garu.
Ta saki wani irin kuka mai cike da rauni.
Jikinta duk rawa yakeyi

A hankali Ummi tayi sallama.
Kana ta kutso kai Al’amin na biye da ita a baya.
Da sauri Umaymah ta juyo ya kallesu cikin girmamawa tace.
“Maraba lalale marhabin da zuwa masarautar Joɗa”.
Cikin nitsuwa Al’amin yace.
“Yauwa”.
Ummi ce ta nuna musu kujeru tare da cewa.
“Bismillah ga wurin zama”.
Bappa ne ya zauna bisa kujera.
Al’amin kuwa ya zauna a ƙasa.
Kusa da Bappa.
Barun ma a ƙasa ya zauna.
Cikin tarin tausayawa Bappa da Al’amin suka zubawa Aysha ido.
A hankali cikin tsananin kula tausayawa da jinƙai Al’amin yace.
“Parvina!”. Shiru bata amsaba bata juyoba, sai kuka da takeyi da sauti mai rauni
Cikin sanyi Umaymah ta kamo hannunnta ta juyota tare da cewa.
“Aysha yi haƙuri kinji ko kalli ga Bappanki yazo”.
Cikin azaban da takeji ta bude idanunta dake cike tab da hawaye.
Ta kalli Bappa da Al’amin.
Cikin sauri ta nufi inda suke.
A ƙasa ta zauna dirsham ta kife kanta jikin guiwowin Bappa kana ta ɗaura hannunta mai ciwon kan cinyar Al’amin.

Dai-dai lokacin Sheykh Jabeer kuwa ya fito falon.

Cikin kuka da disashewar muryar take cewa.
“Wayyo Bappa na hannu na zai ruɓe.
Yah Al’amin mu tafi gida Abboi yasa a yanke min hannun nan in huta”.
Cikin rauni Al’amin ya rumtse idanunshi da suka cika da zafafan hawaye,
a hankali yasa hannunshin ya kamo hannunta mai ciwon zafi jau-jau.
Baisan sanda hawayen suka kwaranyo bo
Shi kuwa Bappa hannunshi yasa yana shafa kanta tare da cewa.
“Sannu ko Shatu yi shiru. Dukkan tsanani yana tare da sauki zaki samu lfy”.

Cikin nitsuwa Sheykh ya matso fuska a ɗan sake yace.
“Marhabin sannun da zuwa Bappa.
sai kuma ya rusuna tare da cewa.
“Bappa mu isa ciki sannunku da zuwa”.
Ya ƙarishe mgnar yana kallon agogon Daimond dake ɗaure a sinsiyar hannun Al’amin wanda ya tabbatar da wuya ba fulatanin daji makiyayi ya cire shanu kusan goma ya saida dan sayar wannan zazzafan agogon.”

Cikin sanyi Bappa yace.
“Nanma yayi”.

Ita kuwa Aysha da sauri ta miƙe jin muryarshi.
Hannunta ta miƙa mishi tare da motsawa gabanshi alamun zata abka jikinshi.
Da sauri yasa hannunshin ya riƙo hannunta mai lfyar.
Kana ya zauna a ƙasa gaban Bappa sannan ya zaunar da ita.
Cikin kuka da alamun gigita ta manna kanta a kafaɗanshi.
Tare da cewa.
“Yah Sheykh kayi min addu’a kamin tofi zanji sanyi”.
Ummi da Umaymah kuwa da Hibba suna gefe suka zauna.
Dan basuma Hausa dasu Bappa ba tukun. Hibba da Umaymah da Ummin sai kallon Al’amin t
Sukeyi sabida kamarshi da Shatu ya wuce zaton mutum.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya kamo hannun ya ɗan dagashi sama.
Kana ya fara karatu yanayi yana tofi da ɗan hura mata sassanyan iskan bakinshi.
A hankali ta fara sauƙe ajiyan zuciya.
Tana lumshe idonta hawaye na siyaya.

Shiru sukayi falon gaba ɗaya sai sautin muryarshi dake tashi yana karatun Alqur’ani yana mata tofin.

Cikin ƙanƙanin lokaci komai ya lafa zogin ya bari, Al’farma Annabi da Alqur’ani.

Ganin ta nitsu tayi shirune.
Yasa Bappa sauke ajiyan zuciya tare da cewa.
“Alhamdulillah”.

Al’amin kuwa hawaye ya matse yana mai jin tausayinta na ratsa mishi zuciya.

Cikin sanyi yace.
“Parvina!”. A hankali ta yunƙuro ta matso gabanshi cikin disashewar muryar da kewar sunan da ya kirata dashi wanda ta dade bata jin an kirata da shiba tace.
“Na’am Yaya Al’amin”.
cikin zuba mata ido yace.
“Sannu ko ya jikin naki?”.

Murmushi tayi tare da cewa.
“Alhamdulillah da sauƙi, Yah Al’ameen ya ahlin Abboi?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”. Shi kuwa Sheykh ido ya zuba musu.
Yana karanto wani kamanni dake tsakaninsu.

Juyowa tayi ta kalli Bappa cikin sanyi tace.
“Bappa na. Ina Ummey na, ina Junainah na meyasa baku zomin da itaba nayi kewarta”.
Cikin jin daɗi Bappa yace.
“Duk suna lfy Ummeynki da Junainah suna lfy sunce in gaisheki da jiki”.

Ciki sanyi tace.
“Ina amsawa ngd”.
Sai kuma ta kwantar da kai cikin sanyi tace.
“Yah Al’ameen ina Dedde na?.”
Cikin sanyi yace.
“Tana lfy ta gaisheki sosai”.
Ido ta lumshe tare da sauƙe numfashi
Sai ta kuma kalli jerin ababen da aka jera musu a kan santa table.

Ummi kuwa cikin sakin Fuska tace.
“Ina kwana Bappa kuzo lfy”.

Fuska a sake yace.
“Lfy lau Alhamdulillah.”

Sai ya kuma juyo ya kalli Umaymah dake ce mishi.
“Sannu da hanya, ya mutan gida?”.
“Lfy lau Alhamdulillah. Ya mai jikin sannunku da jinya mungo matuƙa”.
Bappa yace cikin kamala.

Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
“Yiwa kaine ai”.
Al’ameen ne ya ɗan kalli Umaymah cikin nitsuwa yace.
“Ina kwana”.
Ido ta ɗan zuba mishi tare da cewa.
“Lfy lau ya gida”.

“Alhamdulillah ya mai jikin”.

“Da sauƙi”.

Shiru sukayi dukansu suka maida idonsu kan Aysha data kalli Al’amin cikin shogoɓa tace.
“Yah Al’amin zanci abinci”.

Kallonta ya ɗanyi tare da juyowa ya kalli Ummi sai kuma yayi shiru.

A Sheykh ne ya miƙa tsaye tare da cewa.
“Bappa bismillah mu isa can falona.”
Ya ƙarishe mgnar yana kallon wayar iphone 12 pro dake hannun Al’amin.
Cikin nitsuwa Bappa yace.
“To bisimilla”.
Juyawa yayi gaba kana suka bishi a baya.
Itama Aysha binsu tayi a baya.

Suna shiga shiga falon nashi Bappa ya zauna bisa kujera.
Su kuma duk suka zauna a ƙasa a saban carpet.

Ita kuma Aysha tsakanin Al’amin da kuma Sheykh ta zauna.

Barun kuma ya ɗan zauna gefe.

Cikin girma Bappa ya gyara zamanshi tare da cewa.
“To Jabeer ban saniba ko zaka amince wannan ya duba hannun matar taka, mu gwada nashi mgnin ko Allah zaisa mu dace”.
Shiru Bappa yayi tare da zuba mishi ido.
Shi kuwa Sheykh kanshi a sunkuye yana kallon tattausan yadin jikin Al’amin yace.
“Duk yadda kace Bappa ba damuwa, in ka aminta dashi”.

Shiru Bappa ya ɗan yi yana nazartan kalaman shi da fuskarshi kana yace.
“In sha Allah ba damuwa”.
Kai ya gyaɗa.
Lokacin Umaymah kuma ta shigo da manyan Foodflaks da plate ta ajiye a tsakiyarsu.
Zata fita kenan.
Bappa yace.
“Zauna mana”.
To tace kana ta zauna.

Shi kuwa Al’amin cikin kula ya kalli Aysha tare da cewa.
“Matso ya duba hannun ko”.
A hankali ta matso kana ta miƙa mishi hannun.

Barun kuwa. Gyara zamanshi yayi tare da kallon su sannan yace
“Wannan ba wani abun tashin hankali bane, yanzu zan mata mgnin kuma zata samu sauƙi sai dai bisa shanu hamsin da nace.
Gsky yanzu ɗari za’a bada”.
Ido Sheykh ya zuba mishi cike da tuhuma.
Al’amin kuwa murmushi yayi tare da cewa.
“Kai dai kayi aikinka in ta samu lafi ka faɗi adadin duk shanayen da kakeso bazai gagara ba da izinin ubangiji”.
Kanshi ya gyaɗa cikin jin daɗi.
Kana ya zaro wayarshi kamar yadda suka tsara da Ba’ana.
Kiranshi yayi.
Ya saƙala wayar a kunne ya matseta da kafaɗarshi.
Kana ya kalli Umaymah yace.
“A kawo min madarar shanu mai sanyi”.
Da sauri Umaymah ta miƙa tare da cewa to.

Shi kuwa Barun. zabirar magungunan da Ba’ana ya haɗo mishi ya buɗe kana ya fara fito dasu.
Jim kaɗan Umaymah ta dawo da madarar shanu mai sanyi ta mika mishi.
Ajiye wayar daya matse a kafaɗa yayi tare da amsar nonon.

Kana ya zuba wani garin mgnin a ciki.
A take nonon ya fara zama kinɗirmo mai kauri.
Kana ya matsar dashi gefe.
Sannan ya fito da wani mgnin yana kwashi da man shanu.
Kiran da akayiwa wayarshi ne yasa ya dakata ganin sunan Ba’ana.
Amsa wayar yayi ya kara a kunne tare da fara mgn ba sallama.
Tsareshi da ido Sheykh yayi ya lura cewa wannan mutumin ba musulmi bane.

Al’amin kuwa hannun Aysha ne riƙe a hannunshi yana mata sannu.

Bappa kuwa shima hankalinsa na kan Barun.

Hakama Umaymah, shi ko Barun.
Kamar yadda suka tsara haka ya fara mgna. Ta tsigar da dole Aysha ta gane waye Barun kuma waya turoshin.

A hankali ta ɗago kanta jin yace.
“Eh naje har cikin gidan an nuna min mara lfyar, to kafin in mata aikin na gaya mata, ƙetaren sihirine.
Nace mata kin mance cewa.
Yana ce miki Mata ki bari in dafaki da kyau gudun kada wata rana wani ya cutar min da ke.
Mata na baki haɗin da idonki zai iya ganin alamun sihiri na mugunta da baƙin hayaƙi tsari ko wani kafiya kuma da farin hayaƙi.
Na gaya mata cewa.
Yace mata Mata kada kiyi gangancin cewa zaki tone wani sihirin tunda kinƙi in dafaki.
Domin zai iya dawowa jikinki ya cutar da ke.”

Shiru ya ɗan yi yana kallon cikin idon Aysha.
Ita kuwa tuni Aysha jikinta na tsuma.
Bappa kuwa numfashin ya sauƙe tabbatar da zatonshi hakane wannan ɗan aiken Ba’ana ne.
Al’amin hankalinshi na kan Aysha.
Umaymah kuwa shiru tayi tana kallonshi.
Sheykh Jabeer kuwa idonshi ya lumshe yana sarrafa kalaman Barun da wassafasu da basu cikekkiyar ma’anarsu da jimla a kanshi.
Shi kuwa Barun ci gaba yayi da cewa.
“Eh ogo na gaya mata kuma ta gane.
Don a lokacin tayi shiru.
Na kuma ƙara cemata Ogana yace in cemata duk inda take duk inda ta shiga ko wani motsinta yana cikin tafin hannunshi.
Ya kuma ce in.gaya mata ajiyarta yayi a inda yake, yana son ya gama da aikin da yasa a gabane zai dawo kanta zai kuma ɗauke ta.
Nakuma cemata.
Kace in ce mata.
Duk duniya babu mai bata mgnin ciwon hannunta sai mu, sannan zata worke.
Nace mata kace in gaya mata kana raye tare da ita yana sonki tun kina ƙaramar zai kuma ci gaba da sonki har gaban abadan.”

Ba’ana dake can sai murmushi yakeyi cikin jin daɗi.
Yaso ace yana ganin fuskar Shatu to amman wannan mutumin mai shegen hasken ya kareshi.

Aysha kuwa gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Tana mamaki da tsoron taƙadirancin Ba’ana ya akayi ya samu damar turo jakadarsa masarautar Joɗa har cikin sashinta har falon mijinta har gabanta gaban mijinta.

Ido ta zubawa Barun tana mai haɗa zufa.
Shi kuwa Barun kai ya jinjina mata.

Bappa kuwa cikin sanyi yace.
“Wannan wayar taka ba ƙarewa zatayi ba katse kiran ka shafa mata mgnin, lokacin na tafiya kasan mu yau zamu juya.”

Cikin murmushin taƙadiranci Barun yace.
“To Bappa an gama”.

Gyara zamanshi yayi tare da miƙowa Aysha kindirmon mgnin daya kwaɓa.

Shi kuwa Sheykh Jabeer gyara zamsnshi tare da watsawa Barun wani irin kallo mai tarin ma’anoni kana yace.
“Bar mgnin nan naka bana buƙatar shi a jikin matata! Bar min matata.
Jeka kawai kacewa. Ogan naka.
Akwai mganin da zai workar da ita ba sai nakuba,
Zata kuma samu sauƙi cikin ƙanƙanin lokaci da izinin ubangiji.
Kace mishi, sama tayiwa yaro nisa.
Duk tsallen da zaiyi bazai taɓoshi ba.
Kacewa oganka ya tsaya inda yake hurumin yafi ƙarfinshi”.

Cike da Mamaki Aysha, Bappa, Al’amin, Barun, Umaymah suka zuba mishi ido.
Shi kuwa gyara al’kyabbar jikinshi yayi tare da tsare Barun da idanunshi da suka hantar cikin Barun ta kaɗa cikin iya sarrafa harshe yaci gaba da cewa.
“Muda muke da al’ƙur’ani mai girma ai Allah ya bamu dukkan maganin cutar duniya a cikinsa.
*Kada ku sake zaton samun shigowa masarautar Joɗa*, wannan ɗin ma.
Ni naso ku shigo shiyasa ka samu ka shigo ni na bada dama.”
Miƙewa tsaye yayi tare da nunawa Barun hanyar fita cikin dakekkiyar murya yace.
“Tashi ka ɓace min da gani.
In kaje kace mishi idon Muhammad Jabeer a buɗe suke basa bacci. Kada ya sake gigin turo wani ƙazamin kafuru, a tsarkakken.
Masarautar Joɗa Especially nan.”
Cikin tsananin tsoro da mamaki da kaɗuwa Barun ya juya da sauri ya fita.
Da ƙarfi Sheykh Jabeer ya buɗe muryarshi yace.
“…!

 

Kuyi haƙuri dan Allah babban uzurin mgn a wayane ya tsareni sai yanzu.

By
*GARKUWAR FULANI*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button