Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 40

Sponsored Links

MIJIN MALAMA na kuɗi ne pay before you read….. More information via WhatsApp number 08119237616″Na auri mijinki? Do you want me to marry your husband?” Da wani Expression na tashin hankali take faɗar maganar tana kallon idanun Latifa Omar. Latifa ta watsa hannunta cikin rashin damuwa ta ce “To mene na tashin hankali a nan? Bayan iyayena dake, babu abinda nake a cikin duniyar nan irin mijina, amma wallahi na amince miki hundred patient da ki auri Aliyu, ki auri mijina mu zauna tare, ba zan taɓa yi miki kallon kishiyata ba, don Allah ki rufa mini asiri ki auri Aliyu” Latifa ta faɗa muryarta na rawa. Miƙewa Majeederh ta yi tana ɗaukan handbag ɗinta da wayarta ta nufi hanyar fita daga cikin parlourn. Da sauri Latifa Omar ta miƙe tana shan gaban Majeederh ta ce “Ina zaki? Ki tsaya mu yi magana don Allah, this is the right time da zamu kawo karshen matsalarki Majeederh” Murmushin takaici Majeederh ta yi hawaye na sakko mata a a kumatu ta ce “Well-done Latifa Omar, sbd na tako ƙafa da ƙafa har cikin gidan ki na faɗa miki matsalata shi ne zaki dubi idanuna kika ce i should come and marry ur husband? Are you mad?” Magana take amma hawaye ne ke zuba daga cikin idanunta. Latifa ta girgiza kai itama hawaye ya shiga sauka daga cikin idanunta ta riƙe hannun Majeederh sosai cikin nata ta ce “Wallahi that’s not what i mean, tun kafin yanzu ayi miki maganar fitar da miji nake son faɗa miki ki auri mijina ina tsoran abinda zaki faɗa, Majeederh na san halinki nasan how hard you’re, You have a deep heart, even if the worry will kill you, you will never tell anyone, na kasa jure yanayin na kasa fahimtar cewa jarrabawa ce, maganganun mutane akan ki ya fara yawa, me ya sa ina da maganin damuwar ki a hannu zan zuba idanu kina cutuwa? Aliyu na da kyau, ilimi both boko da Arabic, yana da kuɗi ko kuɗin mahaifinsa bai damu da shi ba, Hajia Mahaifiyarsa na da kuɗi, Ubangiji ya hore masa arziƙin da zai zauna da mata har huɗu ba biyu ba, Zan iya mallaka miki komai na rayuwa daga ciki har mijina If that makes you happy,if that will make you look like any other woman in her husband’s house,Please marry my husband, Aliyu!” A hankali Majeederh ta zare hannunta daga cikin na Latifa Omar ta durƙoshe a wajan tana sakin wani irin raunataccen kuka, mai cin rai da ciwo a zuciya. Wani irin kuka take Wanda ta jima ba ta yi irinsa ba, ga ƙoshi ga kwanan yunwa,ga maganin matsalarta amma ko duniya da abinda suke cikinta zasu haɗu ba zata taɓa auren mijin Latifa ba, bata taɓa kawo hakan ba ko da, da wasa. Zubewa Latifa ta yi itama ta rushe da wani irin kuka kamar an musu mutuwa ta ce
“Ashe ba zan iya rufa miki asiri ba? Ashe zumuncin banza muke? Ashe ban zama ƙawar da zata ɗauki damuwar ƙawarta matsayin tata ba? I have been friends since we were children, we trust each other, we know each other’s behavior,Even if you marry my husband, there will be no worries between us, wlh ko Aliyu kika aura babu ɓarakar da zata gilma tsakaninmu, babu wani yaƙunanne ko shegen kan lafiya da zai sako lalataccen bakinsa, zamu zama abu ɗaya, zuri’a ɗaya one single family mu zama Matan Aliyu, ki haifa masa yara tunda har yanzu Allah bai bani haihuwa ba” Majeederh kuka take sosai kamar ance Abbu ko Little ko Aaliyyah wani ya mutu, ta kasa cewa komai sai jikinta dake mahaukacin ɓari da ƙyarma kamar an jona mata shocking.
Bar Aliyu Sufyan Alhassan da tunda ya yi parting da motarshi ya shigo gidan ya tsaya cak a ƙofar da zata sada shi da main parlour na gidan nasa, tun daga farkon conversation ɗin su har kawo yanzu ya ji komai, zufa ce kawai take yanko masa all over himself, jira yake ya ji me Majeederh zata ce akan requesting ɗin Latifa?.
“Majeederh say something, ki daina kukan hakan” Majeederh ta kalli Latifa Omar da rinannun idanunta wanda ba lafiya ya cika ba, ta ce
“Dole na yi kuka Latifa, ban taɓa tunanin watarana da zata zo ace zan auri mijinki ba, me ya sa kike tunanin zan iya auren mijinki, why should I do that? Me mutanen unguwa za su ce? Me ƴan-uwan ki za su ce? Su ce na zama munafuka, maci amana mayaudariya, wacce ta aure mijin aminiyyarta? That’s what you want? Sbd ina kawo miki matsalata ashe ke tunaninki mijinki zan aura? Sbd ƙaddara ta faɗa mini shi ne zaki manna mini hauka ki zautar dani da gurɓataccen tunaninki mara amfani a gareni, zaki forcing mijinki ya aureni? Bayan kin san mazan guduna suke, basa ƙaunata, balle muradin aurena, banda Imran daya taɓa furta kalmar so a duniyata babu wani ɗa namiji da ya ce yana so na, ko da sunan iskanci ne….,” Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanya ya kasa ci-gaba da maganar ta haɗe kanta da qiwwa kamar ƙaramar yarinya. Latifa kukan take sosai ta ce “Ba zan taɓa forcing Aliyu ba, nasan ba zai gujewa maganata ba, ku zauna da juna na 1week am sure zaku ƙaunaci juna, mutanen gari kuma ki barni da su” Majeederh ta miƙe tare da goge hawayenta tas ta saki liƙab ɗinta. “Kin Amince?” Aliyu dake tsaye cikin zuciyarsa ya ce “Say Yes, Hawwa’u”
Har bakin ƙofa Lafita ta biyota amma Majeederh bata kulata ba, lokaci ɗaya suka saka hannu akan handle jin an murɗa ya sanya Majeederh saki tare da komawa baya, a hankali ya buɗe Ƙofar ganinsu a har gitse ya sanya Aliyu dake cikin nevy suit hannunsa ɗaya riƙe da rigarsa ta lauyoyi sai zabga ƙamshi yake, a hankali ya ce “What did i miss?” Latifa ta ce
“Ka tsayar da ita” Muryarta bata fita sosai ta ce “Bani hanya” Gefe ya koma ta raɓa ta shige abinta, muryar Latifa na rawa ta ce “Me ya sa zaka bata hanya, ba zata taɓa dawowa ba fa, kuma na ce ka tsayar da ita” Bai ce mata komai ba ya mayar da ƙofar ya rufe, hannu tasa zata buɗe Ƙofar Aliyu ya yi sauri riƙo hannunta ya ce “Let her go, Wife” Kuka ta fashe masa da shi ya jawota jikinsa “Sorry” kawai ya samu zarafin faɗa sbd zuciyarsa da tayi masa nauyi, ganin taƙi yin shiru ya sa ya jata har zuwa bedroom ɗinsa dake tashin wani cool ƙamshi na air-freshener, cikin dabara ya shiga bata saƙo albarkacin Majeederh Aliyu ya samu abinda ya daɗe bai samu ba a wajan matarsa Latifa tsayin wata wajan goma. Yana zaune saman wata ƙatuwar kujera ya harɗe ƙafafuwanshi saman sofar idanunsa lumshe breathing ɗinsa na sauka a hankali alamar bashi da lafiya, ya ƙara yin wani farin idanunsa sun faɗa, cikar haiba da da zati da kamalar shi na nan zaune daram a jikinsa. Wata Embroidery Islamic jallabiya ce a jikinsa fara tas, sai jiramin daya ɗora akansa looking so good. Rohaan dake tsaye cikin damuwa ya ce “Allah ya ƙarawa Mai martaba Ajlaal Sultaan lafiya, wannan tunanin da kake isn’t good for ur health” Mai martaba Ajlaal bai magana ba sai idanunsa ya buɗe yana kallon ɗan uwan nasa Rohaan, ganin kallon da Mai martaba Ajlaal Sultaan yake masa ya sa ya ce “Ba tare da sanin abinda ke faruwa ba, a karo na farko wani jininmu ya sako ƙafa zuwa Nigeria, ka matsa yanzu kuma gashi ka ce mu tafi ba tare da yin abinda ya kawo mu ba” Nan ma Ajlaal bai ce komai ba, Rohaan ya numfasa ya ce “Idan akwai abinda ke damunka yana da kyau ka faɗa, tunda kasan idan har a duniya yake dole zaka same shi, ka tsallake Zaytoon, da Mimi wacce kai kaɗai kake controlling ciwonta idan ya tashi, ka bar Fulani Ƙhulud da tagwayen yaranta, Palace ba kowa sai Hadiman, Meke faruwa dakai Mai martaba? Yana da kyau ace….,” “Rohaan” Ajlaal ya kira sunan Rohaan da ɗan ƙarfi a kuma taushashe, Rohaan ya ce “Tuba nake Mai martaba” A nutse Ajlal ya duba agogon Rolex dake hannunsa yana mai kikewa tsaye cikin izza har ya je bakin ƙofa sai ya tsaya ya juya kaɗan ya kalli Rohaan, da sauri Rohaan ya durƙosa ya ce “Prvt jet ɗin na hanya, ban san ya akai aka samu labarin zuwanka Nigeria ba, gabaɗaya zuwan naka shi ne latest new in the world” Da wani irin Expression Mai martaba Ajlaal Sultaan yake kallon Rohaan jin abinda ya ce, zufar dake tsastsafo masa a tsakiyar goshinsa ita ke nuna tashin hankalin jin mummunan labarin, ya dunƙule hannu tare da kallon Rohaan alamar ƙarin bayani.
Rohaan ya ce “A karo na farko Sarki makka Mai martaba Ajlaal Sultaan magajin Ex Sarkin Makka Sultaan ya sauka a Nigeria, har yanzu ba a san dalilin zuwansa ba, ana kyautata zaton zuwan sirri ne ya zo ganawa da wani ɗaya daga cikin sarakunan Nigeria, zuwan nasa ya ja hankalin dubban mutane ganin tun ƙarnin baya na kafuwar masarautar Saudiyya jininsu bai taɓa zuwa ƙasa Nigeria ba, ko mene dalilin zuwan nasa?” Daga nan Rohaan ya kashe T.v da remote ɗin hannunsa ya ce “Ire-iren wannan sune news ɗin da suke trending a duniya da Social media tare da photonka, alamarin ya fi tsamari a Al Jazeera, BBC World News,CNN International da kuma Arise News” Duk maganar da Rohaan yake a tsorace yake yinta, Ajlaal ya zame idanunsa yana riƙe kansa da kyau, duk da tashin hankalin da yake ciki, a taushashe cikin tarin ilhamarsa nutsuwa da kamalar dake zaune a jikinsa cikin kamilalliyar muryarsa yana lumshe idanu ya ce
“A san yadda aka yi, aka dakatar da news ɗin” Ya shiru yana juyawa can ya ƙara fesar da iska ya ce
“Kowa na Palace, ya zama lafiya, a san yadda akai aka ƙaryata zuwan namu Rohaan” Da girmamawa Rohaan ya ce “An gama Mai martaba, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana” Tuni ya kai cikin bedroom ɗinsa yana hana kansa jin abubuwan da suke masa yawo a jiki… Majeederh na zaune a ƙasa an haɗa family meeting kowa da kowa yana nan cikin babban parlourn na gidan Abbu, Uncle Isma’il da Uncle Bello, Innati,Yaya Bilkisu, Maman Alpha, Anti Hajiya Maryama, Sona, Du’a, Widad, Raihana, Ruma, Aaliyyah, Mami, Jawaad,Sahar. Kaf Familyn Khan General Alpha ne kawai babu a ciki, Idanun Maman Alpha ya nuna tsananin kewar ɗanta da take shekaru sun ja, babu ko labarinsa gashi abin mamaki fur Uncle Bello ya rufe ido akan bai yarda ayi cigiyarsa ba, ko headquarters na sojoji ba a maganar shi har sun yi replacing nasa da wani, kamar wanda aka rufe musu baki aka saka makulin a ruwan maliya. Bayan Addu’a da Anti tayi kasancewarta malama ita ma Yaya Bilkisu ta gyara zama ta ce “Ina Hawwa’u?” A sanyaye Majeederh ta ɗaga kanta ta kasa amsawa, a hankali kuma ta juya zuwa direction ɗin Abbu taga sam ba ita yake kallo ba, ko fahimtar yanayinsa ma ba zakai ba, ya sha shadda Light blue ɗinkin Jamper da babbar riga ba zaka ce haifi ƴar shekaru 31 ba, kullum ƙara fresh yake kuɗi sun zauna jiki ya murje. Yaya Bilkisu ta ce
“Wannan zaman naki ne, dominki akai, Majeederh ɗago kan ki sosai ki dubeni” Majeederh ta kalli Yaya Bilkisu “Dubi a gabanki aka haifi Widad yaranta nawa? Du’a, Sahar, Raihana, Ruma gabaɗaya akan idanunki suka zo duniya yanzu ko wacce tana ɗakin mijinta ta rufawa kanta asiri, ke kuma kina nan zaune kina tsofa a gida, Hawwa’u mene damuwarki ne? Kina da kyau, ilimi, boko da arabic, kina da kuɗi kina da asali kowa yasan waye mahaifinki, yau a gabanmu a gaban iyayenki ki faɗa mana mene ya hanaki aure?” A wannan karan ma Majeederh ta kasa cewa komai sai kanta data ɗaga zuwa direction ɗin Abbu cikin sa a Idanunta ya shige nasa daya jima yana kallonta, ya zame idanuna ya miƙe tsaye zai bar wajan Uncle Isma’il ya ce “Daka zauna ai” Ya zubawa Uncle Isma’il ido a hankali ya ce “You can handle it” Ya faɗa tare da gyara zaman babbar rigarsa ya shige cikin part ɗinsa, gorar y ɗauka ya ɓalle wani chaset ɗin magani ya watsa a baki a hankali ya kwanta kan bed yana rufe idanunsa feeling relieved. Majeederh zata tarwatsa masa zuciya da issues ɗinta, Allah ya ware masa ita matsayin ƙaddararsa yaran dake neman ɓata masa suna a duniya, she really disappointed him, actually. Sosai Yaya Bilkisu ke faɗa kamar zata ari baki ta ce “Mun gaji da sanya miki idanu, tunda ke baki amfani da iliminki ba, wallahi wallahi idan baki fito da miji in few days ba zaki sha mamaki, wannan ƙannen naki duk sun fiki martaba a idanun jama’a, kuma tunda haka kika zaɓa aiki da neman kuɗi da kurɗa kurɗa ya fiye miki aure ga Sahar zata haihu sai ki ma zaman daɓaru mutuniyar banza” Anti ta ce “Ki yi haƙuri Yaya Bilkisu komai fa lokaci ne” Yaya Bilkisu ta ce “Saurara Maryama wannan yarinyar dole mu nuna mata ikonmu na iyaye” Maman Alpha ta ce “Haka ne, amma dole a fara binciken daga ina matsalar take?” Mami ta ce “Wacce matsala? Kawai ba auren a ranta tafi gane yawon Ngo ɗin nan da Foundation” Uncle Bello ne ya ce duk yaran su fice, su kaiwa Majeederh faɗa sosai kana ya ce “Ki shiga ki bawa Mahaifinki haƙuri bashi da lafiya” A sanyaye ta miƙe ta nufi ta nufi part ɗinsa tsaye ta gabashi hannunsa riƙe da waya kamar yana kallon wani abu ko dannawa. “Abbu” Cikin sauri ya kifa wayar ba tare da ya ce komai ba, Majeederh ta zube a ƙasa ta ce “Abbu ni mai laifi ce a gare ka, don Allah ka yafe mini In sha Allah zan yi abinda kuke buƙata” Ya juya da sauri ya kalleta a hankali ya ce “Zaki me?” Ta ce “Zan kawo mijin aure” Wani dugun numfashi ya sauke ya ce “Are u sure?” Ta jinjina kai ta ce “Kayi haƙuri Abbu, na sanya maka damuwa a zuciya ban zama yarinyar arziƙi ba, ina ladama da kasancewata mara amfani a gareka, ka yafe mini ka dinga amsa gaisuwata” zuciyarsa ta kare tausayin ƴar tashi ya kamasa ganin ko hawaye ta kasa sai ƙirjinta dake harbawa, ya miƙa mata hannunsa ya ce “Stand up” Kama hannu ta yi ta miƙe, yaro a gaban iyayensa baya tsofa ya taka har gabanta ya saka hannu ya riƙo fuskarta a hannayensa cikin kasa da murya ya ce “Hanyar aljanna nake nema maki, ke ɗin tamkar amana ce dake da Aaliyyah” Ta saki kuka ta ce “Am sorry Abbu” Kasa magana ya yi sai buɗe hannunsa da ya yi ya ce “Come” Cikin sauri ta shige jikinsa tana wani irin kukan farin ciki yau Abbunta ya rungumeta rabonta da jin ɗumin jikinsa tun tana ƙarama. Can ya saketa ya juya zuwa bedroom da sauri…. Bayan sallar Issha tana zaune a bedroom ɗinta dake ba sallah take ba, ta jawo wayarta jin ƙara kafin ta ɗauka ya katse miss calls wajan 10 na gani 7 na Son my world, 2 na Latifa 1 kuma babu suna wata mahaukaciyar special number ce da bata taɓa ganinta ba, number Abraham ta kira tana fara ya ɗaga “Assalamu alaika Baby little me” Tana jin sanda ya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya jin bai amsa ba ta ce “Khalil” Nan ma shiru ta ƙara cewa “Baby are you okay?” Harta fara tunanin ko kiran ya katse ta ji can ƙasan maƙoshi ya ce “Are you crying?” Ta haɗe fuska kamar yana gabanta ta ce “Uhm Baka damu da Maminka ba, no calls no text, anyway how are you?” Ya yi shiru ta ce “Zan ajjiye wayata” Can ta ji ya ce “You’re still crying as always, wahh happen?” Ta yi Ignoring nasa ta ce “Khalil ina mahaifinka wai? And ur mother ina ne garinku ina son sani Please kuma dai ba kana cikin wannan yaran bane ko? Baka faɗa da kowa….,” A tsawa ce Abraham ya ce “Stop asking too much, why are crying? What’s happening eh?” Ya faɗa tana jin yadda yake fidda huci kamar ma baya cikin hayyacinsa, haka kawai tsoransa ya kamata ta fashe da kuka sosai tana marairaicewa ta ce “Shi ne zaka mini tsawa Mamin taka?” Ya yi mata shiru cikin faɗa da kuma alamun damuwa ya ce “Don’t let me to repeat myself Mami” Ta ƙara fashe masa da kuka ta ce “To ba cewa akai na fito da mijin aure ba?” Wannan karan a hankali ta ji muryarsa tana sauka ya ce “In english” Duk a tsorace take da tsawarsa cikin turanci ta ce “Abbu da Uncle’s ɗina sun yi faɗa sosai wai na fito da mijin aure kwana nan, na rasa yadda zan yi kuma bani da kowa ba wanda ya taɓa cewa yana so na ko da wasa yanzu Little ya zan yi?” Ya yi shiru ta wayar yana jin tashin kukanta ƙit kuma ta ji ya kashe wayar, da sauri ta sake kira ta ji a kashe, sai yanzu take mamakin yadda akai harta faɗawa Abraham a matsayinsa na ɗanta bai dace ya ji wannan matsalar ba, raba dare ta yi tana tunani daga ƙarshe ta yi addu’a ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta, bata kashe wutar ɗakin ba sbd bata son duhu ko kaɗan… Can cikin dare fitsari ya kamata ta buɗe idanu da ƙyar ganin duhu gabaɗaya a bedroom ya sa gabanta ya faɗi, ko nepa aka ɗauke? Ko ai basa amfani da nepa inji ne 24/7 ta miƙe a hankali ta shiga laluba hanya, can ta ji hannunta ya sauka akan chest ɗin mutum ga suma nan fal kwance luff a tsorace take ƙoƙarin cire hannun ta ji an saka hannu an fizgota ta faɗa ƙirjinta baki ta buɗe za ta yi ihu ta ji ya rufe bakin da na….

 

MIJIN MALAMA pay before you read please….. If you want to Subscribe my book via WhatsApp number… 08119237616.

Related Articles

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button