Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 1-2

Sponsored Links

Page 1-2_____________________________
____________________________

 

_Farkon labari_

_1/3/2007_

Harabar gdan attajirin cike yake da mabarata maza da Mata yara da manya kowannensu yayi jungum jumgum Yana tsumayin fitowar Alhaji Qasim Wanda ya kasance shine mamallakin gdan Wanda ya kasance baya goya marayu jarumi Kuma adali me taimako da taimakon Allah da’ira da’ira almajiran sukayi kowa yana tattaunawa da abokin shawararsa inda a can nesa kadan da mutanen na hangi wata dattijuwar makauniya da wata yar kyakkyawar budurwa da shekarunta bazasu haura 17 ba sanye take da hijjab ruwan qasa Wanda dadewa da kodewa tasashi dole ya koma toka toka rigarta da zaninta ma gambal habaru ne ma’ana wari da wari tanada matsakaicin tsayi duk da kasancewarta a jigace Kuma a wahalce kallo daya zakayi Mata kasan alamu sun nuna tana tsananin ji da wannan mahaifiya tata fiye da tunanin Mai tunani.
Ba fara bace kallon farko zakace Mata baqa saboda dauda da rashin samun nutsuwar kula da Kai saidai idan ka qura Mata ido zaka gano cewa ba baqar bace kamar yanda idanu ya nuna a farko saboda roɗi roɗin hasken da zakake hangowa ta wasu bangarori na jikinta, tana da fasali da diri na bam mamaki Wanda a qananun shekarunta zakayi al’ajabin qirar da ilahi qadiran ala mayyasha’u yayi Mata so dake lamarin Allah yafi gaban misali da mamaki dole ka aje tunaninka ka Kama abinda ke gabanka.

 

“Asma’u! Asma’u!! key Asma’u!!! Tunanin me kikeyi ne dalla malama tun dazu Alh sai miqa Miki kudi yakeyi….” Abinda ya dawo da ita hayyacinta kenan ta durqusa har qasa ta karba ta bude baki cikin siririyar muryarta tace “mun gode baya goya marayu Allah ya tsare gabanka da bayanka ya hana maqiyanka ganinka sai bayan ka wucce Allah ya tare maka zafin hassadar maqiya da mahassada ta koma kansu…..” hakanan ta rinqa jero addu’ar kamar yanda takanji Ummah tanayiwa duk wanda yayi musu ihsani.
Dadin addu’ar da Alh Qasim yaji tasashi qara zarar naira dubu goma ya sake miqa Mata kawai saita fashe da kuka bayan ta karba tayi masa godiya da fatan alkhairi, ya wucce ita Kuma ta dugungune kudaden ta tura a bra dinta ta Kama hannun Ummah tace “Ummah yau Allah ya dubemu ya amsa addu’ar ki ta jiya ya kawo Mana dauki dama tunda muka fito nake tunanin idan bamu samu sadakar Nan ba yau Ina muka Kama bamuda abinda zamuci ko na garin kwakin yau babu gashi gobe ance kar naje makaranta idan ban kawo kudin tearm ba, nikam Ummah badon kince na daina roqonki ba da sai nace kiyi hqr ki mayar dani makarantar gwabnati tunda na samu horon farko a ta kudin Ummah kudin sunyi yawa 14 thausand per team gashi babu mataimaki a gareki sai Allah da bayinsa zababbu….”
Lalubo bakin yar tata tayi tace “Asma’u komai kikaga ya faru da sanin Allah kada ki damu ba wayonmu ko dabararmu ke rayamu ba burina ko bana raye kiyi karatun bokon nan me zurfi kema kamar yanda kikekan na addini Asma’u burina ki zama likitan ciwona saboda na fara gajiya da wulaqancin da likitawa sukeyi Mana duk lkcn da ciwona ya tashi muka rasa mataimaki Asmah bani da tabbacin amfanar karatunki Amma inaso ki amfanar da al’ummah don Allah kada rudin duniya yasa kema kibi wancan sahun kinji?”

 

Jinjina Kai tayi cikin qoqarin sanyawa kanta dakiya da juriya nason cikawa mahaifiyarta burin data rayu dashi taqici taqi sha dominta ita kadai ta hana kanta sukuni dominta, da wannan tunanin ta Kama hannun Ummah ta miqar da ita suka fara fita daga harabar gdan suna tafe suna taba yar hirarsu tsakanin gdansu da gdan Alh Qasim tafiyace miqaqqa Amma haka ummah tace su tafi a qafa kawai don tsoron kada tayiwa kudin makarantar yar tata gibi ta shiga wani yanayi suna tafe suna Hira har sukaci Rabin tafiyar sannan suka tsaya saboda nishin da Asma’u taji mahaifiyar ta ta fara ta riqota da sauri ta zauna ta kwantar da ita a jikinta tace “Ummah kingani ko abinda nake gudu kenan shiyasa nace mu hau dan sahu naira dari zasu kaimu kikaqi…..”
Mgnr ce ta maqale cikin tashin hankali ta rinqa jijjigata tana Kiran sunanta Amma Ina ta Suma nan fah Asma ta dora hannu aka ta kurma ihu tana cewa wayyoh Jama’a a taimakeni Ummana zata mutu don Allah kada ki bari ta mut….” Nandanan saiga mutane sun taru a gurin masu fifita nayi masu surutu nayi, itakuwa titi ta bazama ta fara tsayar da motoci da yawansu basa tsayawa wata mota tazo zata wucce tayi tsalle ta dira gabanta tare da rintse idonta take me motar yaci wani uban birki ji kake qiyyyyyy, abinda yaja hankalin kowa dake gurin kenan suka juyo domin ganin meye yake faruwa Asma da take tunanin ba a wannan duniyar take ba ta bude idonta daidai lkcn da taji an dauketa da wani gigitaccen mari daya sanyata durqushewa a qasa yace “banza mahaukaya zakizo kijamin masifa a banza……” Riqe qafarsa tayi da sauri tace “don girman Allah kada ka tafi ka taimakamin kada Ummah na ta mutu a titi kakaimu asibiti…..” Dagota yayi kamar abin arziki ya qare Mata kallo sannan yayi watsi da ita tare da jan tsaki ya nufi inda Ummah take kwance ya leqa,

 

Tunaninta ya gama bata taimakonta zaiyi taga ya nuna Umman da yatsa yace “dama akan wannan tsumman kikeson kiyi asarar taki rayuwar sakarya kawai to meye yayiwa wannan yamusasshiyar tsohuwar saura ai bazata warke ba qarama ki lallaba taki rayuwar qila tayi Miki amfani a gaba farin magi duk ya kashe tsohuwa” durqushewa ta kumayi a qasa tana qoqarin yimasa magiya ya fincike qafarsa yace “stupid girl banida lkcn batawa akan wannan gawar….” Da wannan kalmar ya fada motarsa ta miqe tana me binsa da kallo tare da Jinjina Kai daidai lkcn Allah yakawo wani dan sahu wani mutum ya tareshi suka tarairayi Ummah suka sakata a ciki suka nufi Asibiti mafi kusa dasu da niyyar abata taimakon gaggawa kafin su tafi gda.
Suna zuwa aka tura Ummah aka shiga da ita ciki suka sanya mata ruwa kafin fitowar babban likita, bayan kamar shudewar awa guda sai gashinan dauke da files a hannunsa ya nufo dakin ta zuba Masa ido cike da wata muguwar tsana shima yana ganinta yaji gabansa ya fadi yayi saurin mazewa tare da juyawa ga daya gadon Yana duba mara lafiyar ya dauki file din yayi rubuce rubucensa ya juya zai fita tabisa da sauri tace “Dr Aseem wannan karon ba alfarma nake nema ba da kudina na kawo mahaifiyata asibitin nan domin a dubamin lfyrta qila taka uwar bata sallama farin cikinta domin nakaba shiyasa kake kallon iyaye Mata a banza koma dai menene kada ka manta ta haifeka ta raineka har zuwa yanzun Bata daina baka shawara ba inhar tana raye just aikin kudi kakeyi a biyaka kazo ka dubamin uwata nasan bakada ikon canza qaddarar Ubangiji Amma kayi wani Abu da zaisa naji a Raina bakada hannu wajen rushewar rayuwata wlh idan ka bari sakacinka ya kashemin mahaifiya sainayi shari’a dakai duk ranar da ZARRAH ta takai inda mahaifiyata ta bata darenta da ranarta domin ganin takai……….”

 

 

Wani murmushi yayi me kama dana rainin hankali ya matso gabanta ta matsa ya tsaya a inda yake yace “au kenan har jiran ranar ZARRAR ki kikeyi Kuma kinaji a ranki zaki sameta okay almajira kin birgeni da kika taro wasan dani saidai inaso ki sani bakikai na farashi dakeba ki bari ZARRAR taki takai tukun samu fara takun dake am bari kiji wani Abu daga kallonki naji na tsaneki saboda idanunki sun nuna bakida tarbiyya wannan dalilin yasa naji bazan taimakeki ba bazan taba taimakonki ba yarinya wannan asibitin nawane saboda haka na baki 10 minutes ki debe tsummar tsohuwarki a qara gaba kar a zubamin qwarqwata” hannu yasa aljihunsa ya zaro raffers ta dari biyar biyar ya jefa Mata yace “ga wannan idan ta mutu a sai geron sadaka” cafewa tayi ta saita tsaiwarta har ya juya zai tafi ta daga murya tace “Aseem Shaheed” juyowa yayi da sauri jin ta ambaci cikakken sunansa ta matsa gabansa ta keta raffers din gda hudu ta watsa masa tayi murmushi me hade da kuka tace “Sunana Asma’u Hussain ka rubutani cikin qaddarorin da zasu addabi rayuwarka wlh saina baka mamaki matsiyaci me taqama da kayan aro shashasha Wawa kada ka damu zamu sake haduwa a gaba wasan baa faraba”……..

 

_Hmmmm Wasan baa fara ba correct Asma’u Dr Aseem a sake shiri_

 

 

*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*

_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*

 

_Bismillahir Rahamanir Rahim_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button