Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 7-8

Sponsored Links

 

Wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauke lkcn da yasa tisue yake tsane jinin tare da rufe ciwon sosai dutsen ya shigeshi hakance tasa Bai iya jan motar ba sai Zahran ne yaja Kai tsaye suka nufi Asibiti anan Zahran yayi masa dressing na ciwon.
Duk dagowar da Zahran zaiyi sai yaga shi yake kallo har ya gama Masa yace “angama Dr yau ka gamu da sharrin yayan talakawa narasa me muka tare musu sukejin haushinmu nasan da zaa Basu dama zasu iya kashemu su hut….” daga Masa hannu yayi a fusace jikinsa na yace “ka nemomin gdansu yarinyar nan a duk inda take a fadin garin Kano” da sauri Zahran ya Mike yace “in kasan gdansu me zakayi Mata” ya dade yana kallon Zahran kafin yayi murmushi ya miqe yace ya fara tafiya yana dingisa qafa yace.

 

“Nasan ba kowa bace ita face almajira mabaraciya yar jagoran makauniya so inason sanin asalinta need saboda nayi ramuwar gayya da hujja tabbas ko Ina yafe komai bazan yafe laifin fitarmin da jini a jikina ba hannun daya dauki dutse ya fasamin yatsa ya ciremin farce saiya goge takalmina” ficewa yayi ya shiga motarsa ya fuzgeta da mugun gudu ya nufi unguwarsu dake Shagari quarters yana parking ko rufe qofar baiyi ba ya nufi cikin gdan ya bude parlourn ya shiga Mimee matarsa dake zaune da cup a hannunta ta miqe da sauri da niyyar taroshi ganin Yana dingisa qafa yasata dafe qirji tace “Na shiga uku Life meye ya sameka a qafa?”
Kallonta kawai yayi ya wucce dakinsa ya fada gado yana huci kamar yaci Babu tunda yake Babu mahaluqin daya taba karambanin daga hannu ya mareshi har mari biyu a lkc daya da sauri ya miqe tare da kallon qafarsa cikin wani mugun quncin zuciya yake furta “Wacece ce ita meye take taqama dashi wacece ita!?” Yana mgnr ne da qaraji abinda yasa Mimee shigowa da sauri tace “lfy Life?” Iska ya furzar tare da cewa da ita “Asma’u Hussain wacece Asma da ta iya daga hannu ta mareni wacece ita data fitarmin da wani bangare na jikina?”

 

Duban qafarsa yayi tare da cewa “wlh saita gane kurenta saina koya Mata hankali saina wulaqantata ita da danginta gabadaya saina rusa Mata burikan rayuwarta” fuuuu ya shige bathroom Sarai Mimee tasan halinsa idan yanakan tsini bajin rarrashi yakeyi ba shiyasa batayi yunqurin rarrashinsa ba ta nemi guri ta zauna da tunanin meye ya hadosa da mace shida magana ma ko da maza ba damunsa tayi ba da har takaisu ga wannan tsamar tabbas bayan tiya akwai wata caca banza batakai zomo kasuwa.
Miqewa tayi ta fita ta hado masa abinci don tasan ba fitowa zaiyi ba yau an taba mazan fama Aseem rikici ne gabadayansa tunda ya dauki ragamar ramuwar Nan to gara tayi masa fatan nasara don idan ta cika mgn kanta fadan zai dawo. Zama yayi yana tsane jikinsa yace “meye wannan din?” Murmushi tayi tace “bansan zaka dawo da wuri ba jallop din taliya ce” zuba masa ta farayi ya karba Yana tauna abincin kamar Yana tauna magani ajiye flat din yayi ya miqe a gado tana kallonsa yanata qwafa ganin bazata iya ba ta miqe ta debe kayan ta fice dasu ta hada me aikinta dasu ita Kuma ta shige dakinta itama ta kwanta.

 

Wayarsa ya janyo ya kashe don yasan zaayita kiransa a hospital Kuma ba iya zuwa zaiyi ba yau gabadaya Asma’u ta Bata Masa lissafin ranar dole haka zata tafi a banza. Haka ya yini kwance saidai daganan ya juya nan sallah kadai ke tashinsa hudu da rabi na yamma Zahran ya kirashi yace “ya fito yanada lbr game da aikin daya sanyashi” miqewa yayi ya dauki rigarsa yasa ya dora hula ya fito a harabar gdan ya ishe Zahran ya qarasa fuskarsa kamar ta sa tsabar damuwa mota ya bude ya shiga suka dubi juna Zahran yace “Kamar yanda ka fada Sunanta Asma’u Hussain Babanta Mal Hussain talaka ne na qarshe domin kuwa tunda ya taso aikinsa Bai wucce dako da faskare ba mahaifiyarta Amina itace babbar Matar Mal Husaini sai sauran matan babanta su biyu Lamunde da Lantana su Hudune Yaya a gidansu Mudansir sai Zabba’u sai Dijangala sai ita qarama Asma’u wadda ake Kira da Ma’un Inna ko ace Ma’un Sadiqu autace a gdansu duk da kasancewar uwarta ba komai bace a gdan Amma hakan bai hanata samun gata daidai na talaka ba duk da kasancewar Babu abin sisi da Mal Husain yakewa yaran saidai suyi sana’a da iyayensu suyiwa kansu ita Inna da kake ji macece me qoqari gaya akan yayanta tayi qosai tayi aikatau gdan masu kudi tayi surfe tayi dakau sannan tayi wankau zamanin tanada idanunta har abincin siyarwa tayi duk da tanada ya mace Bata Dora Asma’u talla saidai Mudan da ita su dauka suje su siyar a bakin kasuwa a cewarta ita ya mace kadara ce me tsada Kuma abar farauta ce idan kayi wasarairai da ita kamar dawisu take inda yafi yalwal bishiyoyi da Ni’ima nan take fakewa tace zatayi rayuwa a cikinsa idan akayi rashin saa sai asamu mafarauta su kameta shikenan rayuwarta ta lalace:

 

Yarinya ce me qwazo tun tana qarama hakan yasa uwarta taci burin sai tayi karatu me zurfi lkcn da aka makantar da Inna lkcn Asma’u ta gama primary daganan abubuwa sukayita lalacewa dan abinda ake fita a Nemo na rainawa babu halin fita a nemoshi Nan suka shiga Ni yasu abinda zasuci ma yakan gagaresu akwai wani yaro Sadiqu da tun tasowar Asma’u yakeyi Mata wahala shine rakata makaranta shine komanta saiya zamana idan yasai da rake ko ya dauki tallan yalon bello yaje ya siyar ne yake samu yabasu abinda zasuci.
Ana hakane wata Ladi almajira tayiwa Inna tayin fita bara tunda dai Allah yasani batada mataimaki da farko Inna taqi abin Amma lkcn da Asma’u ta farayi mata mitar duk qawayenta sun tafi makarantar secondary ita tana gda saita farabin Ladi bara suna samo na batarwa a hakadai har suka Tara kudin makarantar lkcn har anci zango daya suka kaita Prime school dake Inna tun dacan Bata yarda yaranta sunyi makarantar gwamnati ba tace Babu karatu ita Kuma so take yaranta suyi karatu, daga lkcn da Asma’u ta fara zama budurwa saiya kasance idan sunje neman taimako mutanenmu sai suka fara nuna maitarsu akan yarinyar itakuma uwar tana nuna Mata aibin hakan musamman dake Asma’u tana zuwa islamiyyar dare, matsalar Asma’u daya ita tun tana qarama batada hqr Kuma Bata yafiya indai kayi Mata saita rama so da mutane suka fara gwada rashin imaninsu akan mahaifiyarta sai ta dauki gabarar duk Wanda yayi Mata ko waye a duniya saitayi Masa kalmarta daya itace “ka jira ZARRAH ta ranar da zan zama babbar likita zanyi fada da uban kowa a duniya Kuma zan nuna maka kaiba komai bane” yanzu haka zancen da nakeyi maka burinta na gab da cika domin kuwa takusa kammala secondary Wanda Innarta tafi shekara biyar tana adashin gata domin Asma’u ta wucce makarantar da zatayi karatunta na likitanci”

 

Murmushi Dr Aseem yayi yace “aikinka yana kyau Kuma meye yanayin ubanta da kudi sannan a wacce unguwa suke zaune?” Jinjina Kai Zahran yayi yace “wanda yayimin bayanin tarihinsu yace kirarin mahaifinta Mal Husaini idon cin naira indai kanada kudi to kanada cikakken mutumci a gurinsa idan kuwa baka dashi to kashinsa yafika daraja anan Tukuntawa gdansu yake shikuma babanta a sabuwar gandu majalissarsu take gefen rumfar wani me nama suna zaune idan ansiya suyi sudi aikinsu kenan”
Jinjina Kai Aseem yayi yace “ka gama magana inason kwadayayyen mutum saboda buri yana saurin cika Asmah ki jirayi zuwana burinki bazai taba cikaba zan rusanki duk wata walwala da farin ciki zaki rayu da qunci zan massheki baiwa a gdana saikin lashe tafin qafata da harshenki…… Dafashi Zahran yayi yace “tabani haushi dazu Amma da naji tarihinta sai tabani tausayi please ka hqr da daukar fansar nan kabarta don Allah akwai quruciya yarinya ce qarama fah…..” Hannu ya Dora Masa a baki yace “karka qara bani hqr wlh bantaba tausayin wani Abu kamar yanda na tausayawa yarinyar nan ba Amma hakan bazai hanani daukar mataki akanta ba saita Raina kanta Kuma sai tasan tasa Wasa da Aseem Shaheed”………..

 

Vote
Comments
Share

 

*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*

_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*

_Bismillahir Rahamanir Rahim_

_Free Page 9-10_

*_Wattpad realfauzahtasiu_*

Telegram
👇
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

_____________________________
_____________________________

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button