Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 51

Sponsored Links

51
????????????????

A hankali yake ratsawa ta cikin layin nasu har zuwa qofar gidan da yake mallakinshi ne,kuma a halin yanzu yake zaune a ciki,yayi kyau sosai cikin qananun kaya wanda ya dira jibgegiyar rigar sanyi a kai,yana saka key yana shirin bude qofar gidan wayarshi tayi qarar shigowar saqo,basu jima da gama waya da anni ba wadda ta tashi zuwa saudiyya don tayi umara,wayar ya zaro daga aljihunsa yana dubawa,murmushi ya saki a hankali yana karanta abinda saqon ya qunsa,a qalla ya dauki wasu kwanaki bai.maida.mata da amsa,yayi kuma hakanne saboda ya auna yadda ta damu dashi,shin abinda zuciyarsa take raya masa haka ne?,wani irin yanayi da bai taba hasashen shiga irinsa ba akanta ya samu kansa,bashi da shakku kuma ko kokwanton cewa wannan ba komai bane soyayya ce,yadda yake ji din ya tabbatar da cewa ba qaramin kamu tayi masa ba,yaushe hakan ta kasance duka bazaice ba,yana tsoron kar yayi zurfi da yawa abun ya zame masa matsala,ya kasa samun goyon baya yadda ya kamata daga gareta.

Sosai saqon yayi masa dadi,don har ya shiga parlour din gidan maimaita karanta saqon yake yana murmushi kafin daga bisani ya samu wajen zama.

Related Articles

Daga bangarenta kuwa tana zaune gefan gadon anni bayan sun dawo daga rakiyarta airphort,wadda ta bar mata muqullin dakin nata a hannunta saboda ta tashi ne ran asabar sanda ayshan ke zuwa gida hutu,kasa aje wayar tayi daga hannunta sai juyata take tana jin wani iri babu dadi a ranta,batasan me yasa a duk sanda ta tura mishi saqo take kasa samun amsar sa ba,batasan dalili ba tana jin babu dadi sosai cikin ranta,ko wani laifi tayi masa?,damuwarta tana ganin ko bata rasa nasaba da qoqarin kyautata matan da yake yasa batason itama tayi masa wani abu da yake ba dai dai ba?,duk dai bata sani ba.

Gauruwar ajiyar zuciya ta sauke,jiki a sanyaye ta miqe ta soma kintsawa annin dakinta gami da gyara duk wani da tasan zai iya samun matsala kafin dawowarta,a qalla ta kusa kashe minti ashirin qwarara sannan ta sanya key ta kulle dakin ta sauko zuwa falon gidan.

Rahama,amal maryam harma da zeenrat dukkansu na zaune darshe darshe a falon,kowacce na sabgar gabanta kamar wadda ta samu gidan gyatuminta,hannun ayasha harde a qirji tabi kowaccensi da kallo ba tare da sun ankara ba,dukkansu mamaki suke bata,baya ga wani abu mai kama da haushi haushinsu da yake tasiei gami da mintsinarta can qasan ranta,saidai babu wadda ta taba nunawa haka cikinsu,saboda tana ganin nata da wannan hurumin.

Bata cewa kowa komai ba ta ratsasu zata shige,saboda kacokam amanar gidan anni ta danqa a hannunta ne,wanda hakan tasan ya bata ransu duk da basuyi magana ba,saidai fuskokinsu sun nuna,wani tsaki taji rahama ta ja,bata waiwayo ba bare ta nuna tasan da ita take,tunda suke sallama da annin take wani cika tana batsewa.

Cikin lambun gidan ta samu waje ta zauna,tana son yanayi da iskar wajen,ita kadai wajen shuru,jifa jifa tana tunanin rayuwa da abubuwa da dama da suka shude daga cikin rayuwarta,tun wancan sati taso ta sake zuwa gida taga daddy har ta gayama khalipha saidai bata samu zuwa ba,sabida wancan karon tun ranar lahadi ta koma makaranta saboda monday takwas na safe tana da lacture,ajiyar zuciya ta sauke ta soma danna wayarta,number din anty safiyya ta nema ta kirata,don sukanyi waya duk bayan wasu kwanaki,ko bata kira ta ba ita zata kira,bugu uku aka daga,murmushi ta saki saboda kukan al’amin daya fara yi mata sallama
“Me aka.yiwa dan gida na anty?” Cewar aysha tana murmushi
“Hmmm,rigima kawai yakeji aysha wannan dan gidan naki sai a hankali”
“A lallabamin shi al’amin baya kukan banza” dariya antyn tayi sannan suka soma gaisawa
“Kin shiga wajen daddy ne?jiya ban ganki ba inata tambayarki mummy bata cemin komai ba”
“A satin nan nakeson shiga”
“A’ah,karki cemin bakisan baida lpy ba,jiya fa a asiniti muka wuni daxu da safen ya koma gida” idanu ta fiddo cikin mamaki,don ita ba wanda ya gaya mata
“Me ya sameshi anty?,wallahi ban sani ba ba wanda ya gayamin”
“Wani irin zazzabi ne mai naci wlh sai da aka qara masa ruwa”
“Subhanallah,ai kuwa yau ba sai gobe ba zanje na ganshi,wallahi anty banda na kiraki mummy bata gayamin ba” ajiyar zuciya anty safiyya ta saki,wato har yau mai hali baya fasa halinsa kenan
“Allah ya kyauta,shikenan idan na samu dama nina zan shigo,idan ban shigo yau din ba sai gobe”
“To aunty,Allah ya bashi lafiya” suna kammala wayar ta miqe,hankalinta duk sai taji yaqi kwanciya,tana qaunar daddy kamar nata mahaifin,shine mutumin daya soma saka maqullin alkhairi ya budewa rayuwata dukkan wata qofa da a yanzu ta samu kanta a tsaye,kai tsaye cikin gida ta nufa ta isa sashensu,cikin qanqanin lokaci ta shirya tsaf,kana dubanta kasan ta samu dukkan wata dama ta rayuwa,duk aninda ke sanye a jikinta mai aji da tsada ne,har yau tana jin gajiyar kayanta dake jibge ne cikin gidanta wanda ita ka ta batasan iya adadinsu ba,saidai ba makeup ko daya a fuskarta.

Daya daga cikin muqullan motarta da anni ta damqa mata ne sanda zata tafi take mata fadan ajiyesu da tayi bata taba hawan ko daya ba,saita gangaro zuwa sashen annin,zuwa yanzu daga maryam sai amal da zeenart a falon,amal na kwance tana charting,maryam.na zaune tana kallo,yayin da zeenart ke riqe da kwanon farfesun kayan ciki wanda yake a mazaunin abinda za’a hada cikin anincin dare aci amma tsabar zalama da son zuciya da aka saba ta kasa jira,sam ta kasa zaman gidansu duk da jan kunnen da babanta yayi mata na kada ya sake ganin qafarta gidan annin tunda har khalipha ya wulaqantasu amma ta kasa jurewa,don tace ko dadin da take ci gidan annin ai babu a gidansu,ko iya shi ta samu ai ta more,qasa qasa amal ke kallon ayshan,tayi mata kyau komai nata mai aji da burgewa,duk abinda tayi saiya nuna maka ita din ta dabance mai ilimi da kuma aiki dashi,kitchen ta wuce ta tadda bara’atu daya mai aikin tasu,don inna atika da ita aka tafi umarar wannan karon,da fari anni cewa tayi yayi visa din mutum biyu bayan ita,ko amal da zeenart,ko amal da maryam din,ya amsa mata da to kawai,amma harga zuciyarshi baya jin zai iya cire kudinshi ya biyawa wata daga cikinsu zuwa saudiyya,kosu ko iyayen nasu,saboda haka kawai sai passport din ya aiko mata dashi da komai da komai na baba atika,dama ya jima yana son kai matar,saboda yadda anni kejin dadin zama da ita,uwa uba riqon amana da gsky,hakanan annin bata taba kuka da ita ba,itama annin data gani bata ce masa komai ba bare tayi qorafi,tasan wannan abubuwan da suka faru shekarun baya har yau ke tsikarinsa,ba abu bane na mamaki,dafi ne ko ace gubace da duk sanda ya tuna take taso masa,tama godewa Allah da yakanyi musu alkhairi lokaci bayan lokaci na abinci da sutura,don da fari yadda ya birkice bata zaci tsinkensa zai bari su mora ba,shi kuwa yayi hakane saboda darajar annin da umarnin data bashi wanda bazai iya tsallakewa umarninta ba,da shawara ce da da sauqi.

“Kardai fita zakiyi?” Bara’atu ta tambayeta
“Eh wallahi zanje dubiya ne….don Allah saqo zan baki,idan haidar ko mus’ab wani daga cikinsu ya shigo kice masa ina gidan daddy,amma bazan jima ba can zan dawo,akwai tamfofi da anni ta bayar za’a dinka guda uku tace telanta zasu kaiwa su sun sanshi”
“To a dawo lafiya,Allah ya tsare”
“Yauwa amin” nan ta juya ta fice,koda tazo fita itama bata bi takan kowa ba,sai kallo da kowacce take binta dashi a sace cike da baqinciki kishi qyashi da kuma hassada,maryam ce taja tsaki tana gyara kwanciyarta
“Shi abba yasan khalipha zaiyi kudi ya kasa taimakonsa,ai gashinan yanzu suna ganin arziqi saidai asan mana” take fada cikin zuciyarta
“Ya isheki haka malama,ya muna zaune muna hutawa zaki damu mutane da tsaki ne?,wai shin dawa ma kike ne?”
“Da uban wanda ya tsargu” ta fada tana gallawa zeenart harara,ai kuwa saita aje kwanon hannunta ta miqe tayo kan maryam din
“Ni kike zagi ko uba na?”itama tsaye ta miqe
“duk wanda kika zaba,aikin banza kawai,da kike wannan haqiqancewar wani kika fi har da zaki yiwa wani iyaka dayin yadda yaso,kin isa ki hanani tsaki ko cika gidan nan zanyi da tsaki?,ina cewa babu wanda gidan yake mallakinsa a cikinmu bare wani ya damu wani” nan fada yaso kacema tsakaninsu,sai suka hau ‘yar gore gore,rahama ce ta leqo ta gansu sunayi,kallon banza ta watsa musu sannan taja tsaki ta juya ta koma dakinta ta maida qofar ta rufe,ita yanzu duka ba wannan ne yake damunta ba.

Aysha kam bata masan me suke ba,sanda ta fita gidan ba driver ko daya,duk sun tafi rakiyar anni kuma babu wanda ya dawo,malam shehu kuma ya tafi kasuwa cefane,hakanan ta taka zuwa bakin daya daga cikin motocin nata,ta tsaya gaban qaramar ciki tana dan dubanta,bismillah tayi ta saka muqullin ta bude ta shiga mazaunin driver,sai take jin fargaba,tana jin kamar ba zata iya ba,karon farko da zata soma driving,duk da ta jima da iyawa amma bata taba tuqi ba,saita rufe idonta ta karanto addu’ar hawa abun hawa,hakan yasa mata nutsuwa,ta maida qofar ta rufe,ta tashi motar ta daidaitata ta dan danna horn,mai gadi ya bude nata gate din ta fice a hankali cikin nutsuwa.

Sanda take fita su haidar na shigowa,mus’ab ne ya nunawa haidar ita,mamaki ya kamasu,suka dinga yi mata dariya mus’ab na fadin
“Wai yau anty da driving?ko ina zata oho,bari ta dawo yau zata sha tsokana”
“Ni kaina naso muna nan zata fita” haidar ya fada yana dariya,don basa manta yadda take da tsoron driving da kanta,taga shigowar motocin,sai taji kaman ta tsaya ta yiwa daya daga cikin direbobin magana su kaita,sai kuma kawai ta wuce abinta.

Tun daga harabar gidan haidar ya soma jin kaman hayaniya,saboda haka yabar mus’ab anan ya shige zuwa ciki,sanda ya shiga sa’insa tayi nisa,cikin fusata ya katsa musu tsawa nan take kowacce tayi shuru
“Wannan wanne irin iskanci ne da zaku maidawa mutane gida gidan karnuka?,toko wacce ta shiga taitayinta bana cike da rashin mutunci,ku bace ku bawa mutane guri da’alla ko kowacce ta wuce gidansu” hakanan maryam da zeenart suka wuce zuwa dakin suna qananun maganganu da gunguni,amal ya duba wadda ke zaune duk taqaddamar da ake
“Ke ba zaki tashi ba kenan sai nayi quli quli dake!” Ya fada.mata a zabure,ba shiri ta miqe itana ta wuce daki,don tasan halinsa sarai idan ya juye kaman khalipha haka yake komawa ba sauqi,dogon tsaki yaja sanda mus’ab ya shigo yake tambayarsa abinda ke faruwa,yana shafa tsakiyar kanshi yace
“Wadan nan mahaukatan yaran mana,ni na tsaya ma tambayarsu neke faruwa na kora kowacce,zasu zo suna mana hauka kaman gidan su” yana fadin maganar yana wucewa kitchen.

Cikin zuciyarta take hamdala sanda take shigowa layin nasu,sai kuma ta sakarwa kanta murmushi tana dariyar tsoro irin nata,yadda ta dauki abun ma duka ashe baikai haka ba,horna tayi cikin minti daya mai gadin gidan daddyn ya bude mata qifa ta sanya motar tata ciki,tana cikin rufe motar bayan ta fito adaidaita ta shigo gidan,saita daga kai cikin mamaki tana duban adaidaitan,asma’u ce ta fito daga ciki tana miqawa mai adaidaitan kudinsa,canji ya miqo mata saita watsa masa wani kallo
“Kai bana son iskanci yanzu zan saka ayi ma duka kana dai ganin cikin gidanmu ka shigo,yaya za’ayi ka dauki dubu daya daga inda ka daukoni zuwa nan,ko an gaya maka satar kudin ake?”
“Amma dai hajiya aiba haka mukayi dake ba ko?,drop kika ce bakyason na dauki kowa,a qa’idama kudinki sunfi haka,kuma wallahi kibar ganin gidanku na shigo baki isa ki dakeni akan haqqina ba” ashar ta maka mishi tana fadin
“Yau zakasan ubana waye zakaga qaryar iskanci” shi kuwa ganin haka saiya fito daga adaidatan nashi yana fadin idan ta isa tasa a dakeshi din saiya farke mutun wallahi ko waye,kallo daya aysha tayi masa ta karanceshi,irin matasan nan ne masu zuqe zuqe,askin kanshi kawai ya isa ya gaya maka wayeshi,a hankali ta tako ta saitin matashin tayi sallama,saiya tsaya da hayagagar da yake yana dubanta cikin dan layi,kwarjini tayi masa,haka shigarta ta banbanta data asma’un,amsawa yayi ta bude jakarta ta ciro dubu biyu sabbabi kar,wanda tun wancan satin ta ciro su a atm ta yiwa anni siyayyar tafiya a matsayin tata gudunmwar,duk da babu abinda ta rasa amma ance gaida mai gaidaka,miqa masa tayi sannan tace
“Kayi haquri don Allah malam,dauki motarka ka tafi” saiya amshe yana cewa
“Allah dai ya biya,kinga inda akasan arziqi,da alama wannan ba matsiyaciya bace irinki,ke ina jin ma ke ‘yar riqo ce ko mai aiki a gidan don irinku sunfi kowa yin haka,matsiyaciya mai qaryar arziqi” ya shuga babur dinsa zai tayar,saita yunqura zata biye masa da sauri aysha ta damqe hannunta,qamshin turarenta da laushin tafin hannunta ya sanya asma’un waiwayawa tana dubanta
“Ba girma da mutuncinki bane anty,bakiga a yanayin da yake ciki ba?” So tayi ta wanke ayshan tas,saboda maganganun daya yaba mata sun qona mata rai sosai,to amma da wani abu ya fado mata a rai wani quduri da ayau takeson ta cimma saita hadiye komai
“Da kin barni na nunawa dan iska iyakarsa ai,basu da mutunci ‘yan adaidaitan nan,koda yake ke dakike hawa saikinfi kowa sani ai”murmushi kawai ta saki
“Ki qyaleshi kawai,mun yini lafiya?” Ayshan tace da ita sanda suka soma takawa zuwa ciki,da qyar asma’un ta hadiye abinda ke damunta ta dan saki fuska ta amsa,wanda hakan yayi mata dadi
“Indo motarnan bata rufu ba fa” cewar usama wanda ta barshi yana duba motar daddy data yi parking kusa da ita
“Oh,ohkey,ina sauri ne zanwa mai adaidatan can magana naga kamar a buge yake,don Allah dan rufemin usama idan ba damuwa ka miqo min key din cikin gida”
“Toh ba matsala” ya karba yana yin gaba,su kuma suka cu gaba dayin cikin gida,saidai asma’u ta kasa cewa komai,mota kuma wacce iri?,ina ayshan ta samu mota?,kasa haqura tayi sai data waiwaya taga motar sanda usman ke rufeta,daskarewa tayi wani malolo ya taso mata wanda ta kasa hadiyeshi
“Mota kikayi aysha?”murmushi tayi
“a’ah,tunta lokacin bikina khalipha ya bani,bana hawa ne dai kurum” kan uba,wanne irin kudi wai gayen nan ke da shi ne?,asma’u ta furta cikin ranta,kaman baisan ciwonsu ba?,ko baisan nawa motar take ba,lallai ba shakka ya zame mata dole tayi wani abu,ita ya kamata ace tana cikin wannan yanayin ba aysha ba,taya zata zamewa aysha tsanin da zata taka ta cimma wani abu a rayuwarta?,da wannan saqe saqen zucin suka isa falon,wanda asma’u bata samu damar sake cewa komai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button