Garkuwa Hausa NovelHausa Novels

Garkuwa 35

Sponsored Links

ByTa konta, kamar maiyin bacci kamar wacce ta suma.
Cikin mamaki suka bita da ido kana suka juya suka kalli juna,
Cikin mamaki Jamil yace.
“Ummi suma ta kumayi ne?”.
Kai ta jijjiga mishi alamar a a.
Kana tasa hannun damanta ta gyarawa Shatu’n.
Kwanciyarta.
Tare da cewa.
“Bacci ne tayi”.
Kai ya kuma gyaɗawa cike da mamaki yace.
“Wannan baiwar Allah’n, itama da akwai abin al’ajabi tare da ita.
Da akwai abinda yake a duhu wanda bamu sanshi ba a kanta.”

Cikin gamsuwa da bayan shi Ummi ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Na daɗe da dasa ayar tambaya a kanta, sai dai bani da mai bani amsar dole sai zaman yauda kullum zai ƙara fahimtar dani ko wacece ita.
Yanzu dai Jamil wannan mgnar ta zama sirri tsakaninmu.
Da Allah kada kowa yaji!”.
Cikin nitsuwa yace.
“In Sha Allah Ummi babu wanda zaiji”.

To da haka dai sukaci gaba da hira a wurin.
Cikin Sa’a baccin nata baiyi nisaba ta farka.

Related Articles

Lokacin sallan azahar nayi suka watse.

Bayan sunyi salla da jimawa ne, ta miƙe a hankali ta nufi ɗakinshi.
A falo ta tsaya, tana nazarin to in ta shiga ta sameshi idonshi biyu fa?
Akwai abinda take son idonta ya ƙara gani dan ta tabbatar.

Shi kuwa Sheykh yana ciki, a kwance kamar mafi akasarin lokuta, waya yakeyi da Aunty Hafsat.
Tana ce mishi ya haɗata da amryar zasuyi mgna.
Cikin sanyi yace.
“Bacci, Aunty Hafsat Bacci fa zanyi, afwan ki bari sai anjima mana”.
Cikin sanyinta tace.
“Oho Jazlaan, nace ka haɗani da ita shine wannan magiyar yanzu Yezeed yazo ya nuna min hotunanta wai Hibba ce ta turo mishi.
Tamin kyau sosai, ina son yarinyar.
Zakiya ma tana amshi number ta, wurin Hibba tana kira kuma bata ɗagawa.
Jazlaan haɗani da ita nace ko!”.
A hankali ya yunƙura ya tashi zaune.
Cikin sanyin baccin daya fara yi yace.
“To ɗan katse kiran in naje zan kiraki.”
A hankali ya miƙe tsaye. Al’kyabbar sa ya ɗauka, tare da nufar bakin ƙofar.
Yana mai sa hannunshi cikin rigar al’kyabbar.
Har yazo bakin ƙofar bai gama sa hannun rigar ba ya buɗata da faɗi.

Ita kuma Shatu a hankali ta tura ƙofar.
Ta sako kai ciki dai-dai lokacin kuma shima ya sako kai waje.
Ba zato ba tsammani sukaji sunyi kiciɓis da juna ta faɗa cikin faffaɗan ƙirjinshi.
Cikin sauri ya sauƙo da hannayeshi dake buɗe kuma al’kyabbar na buɗe da faɗinta sanadin sauƙo da hannun da yayine sai ya zama ya sauƙe hannunshi kanta, yayi mata ƙawanya da faffaɗan al’kyabbar jikinshi ya haɗasu wuri ɗaya ya rufesu.

Wani irin harbawa zuƙatansu suka farayi da ƙarfi-ƙarfi, suna jam junansu i ziwa jikin juna tamkar mayen ƙarfe.

A hankali Shatu taji jikinta na macewa.
Kanta ta manna a ƙirjinta kunnenta na dai-dai kan ƙahon zuciyarshi.
Lumshe idonta tayi tanajin wani irin masifeffen ƙamshi turare mai daɗin shaƙa dasa baccin daɗi cikin ƙanƙanin lokaci, koda yake baccin nata baya rasa nasaba da abinda ke wujijjigata.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, shiru yayi yanajin yadda tasa hannunta, ta zagayo ƙugunshi ta riƙe gam-gam da iya ƙarfin ta.
Sai kuma ya ɗan sunkuyo cike da mamaki yakkali fuskarta, tuni tayi bacci cikin ƴan second nin nan.

Cike da mamaki ya zubawa fuskarta kallon tuhuma.
A hankali yasa yatsunshi ya fara ɓanɓaro hannunta,
yanayi yana ja da baya-baya yana komawa cikin ɗakin.

Ita kuwa binshi take amman ba bi irin na takuba,
Cike da mamaki ya ƙara leƙa fuskarta.
Tabbas bacci tayi.
Janyeta yayi daga jikinshi kana ya saketa a hankali ta tafi zata faɗi, bai tareta ba, sai dai yasa ƙafarshi ya tare dai-dai inda yaga kanta zai bugu.
Cikin Sa’a kanta ya sauƙa kan rumfar ƙafarshi.
A hankali ya ajiye ƙafar tashi a ƙasa.
Kana ya janye ƙafarsa, kanta ya konta a ƙasa.

Cike da mamaki, ya juya ya koma can inda yake konciyar.
Bai cire al’kyabbar ba ya konta yana mgnar zuciya.
“Mutun kamar mayya, wannan baccin kuma na meye to”.

A haka shima yayi baccin da yasan in bai yishiba, zaiji ciwon kai.

Kiran sallane ya tadashi.
Tanan konce har yanzu.
Al’wala yaje yayi kana ya fito ya kimtsa ya fesa turare.
A hankali yazo kusa da ita.
Ɗan sauran ruwan dake tafin hannunshi ya yarfa mata a fuska.

A hankali ta buɗe idonta, kana ta kuma lumshesu haka tayi kusan sau uku ganin hakane a hankali yace.
“Ke kasa uwar bacci tashi kiyi salla”.
Miƙa tayi a hankali tare da cewa.
“To”. Shiru yayi yana nazarin muryarta, ba haka muryarta yakeba.
Wannan shine abinda su Ummi basu ganeba, shi gashi ya gane a take,
Su kuwa basu gane cewa muryarna ba tata bace.

Kanshi ya ɗan juya tare da cewa.
“Uhummmm”. Daga nan ya fita, ita kuma Shatu da ido ta bishi.
Yana fita ta miƙe kalle-kalle tayi a ɗakin nashi sosai har ƙarƙashin gado ta leƙe.

Tana gamawa ta shiga Bathroom nashi.

Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
“Komai nashi mai kyau da tsabta”.

Al’wala tayi kana ta fito, a falo ta samu Ummi da Hibba da alamun a nan sukayi salla.

Sosai Ummi tayi mamakin kenan, tana ɗakin Sheykh ne, murmushin jin daɗi tayi a ranta tace.
“Ikon Allah kenan”.

Ita kuwa Shatu hijabin Hibba ta amsa tayi salla.
Suna zaune a nan ya shigo.
Wayarshi na kunne cikin nitsuwa yace.
“To Aunty Hafsat gata nan ɗazu bacci takeyi”.
Cikin murmushin tace.
“To bata”.
A hankali ya iso tsakiyar falon wayar ya miƙo mata tare da cewa.
“Aunty Hafsat ce ƙanwar Umaymah saura kiyi mata rashin ta ido”.
Ya ƙarishe mgnar a hankali yadda ita Aunty Hafsat bazata jishiba.

Ita kuwa amsa tayi tare da karawa a kunne cikin nitsuwa tace.
“Assalamu alaikum”.
Fuska a sake tace wa alaikissalam ɗiyata, ya gida ya sanyi”.
Muryar matar sak irin ta Umaymah shiyasa cikin jin daɗi tace.
“Lfy lau Alhamdulillah Aunty ya gida da aiyuka”.

“Alhamdulillah”. Tace kana ta ɗora da cewa.
“Sunana Hafsat Jalaluddin Muhammad Sultan”.
Cikin jin daɗi tace.
“Eh Aunty na sanki ai Umaymah ta gaya min sunanki ta nuna min hotonki da Aunty Rahma da Zakiya da Yezeed dama duk sauran”.
Cikin jin daɗi tace.
“Masha Allah, to ki amshi number ta data Rahma da Zakiya a wurin Hibba, ɗazuma Zakiya taita kiranki ashe kina bacci ne”.
Cikin nitsuwa tace.
“To Aunty yanzu kuwa, ngd matuƙa”.
Cikin jin daɗi Aunty Hafsat tace.
“Allah ya muku al’barka ya baku zaman lafiya.
In Sha Allah zamuzo auren Haroon zaki gammu mu ganki”.

“Amin Amin. Aunty Allah ya kaimu lokacin ya kawoku lfy”.
Tace kana sukayi sallama.

Daga nan suka shiga kitchen.
Jamil kuwa tuni yaje yayiwa wani mai musu aikin gidansu.
Yasa ya nemi irin wannan tayis ɗin. Yace gobe da safe misalin sha ɗaya zaizo ya ɗauke shi.

Washe gari da safe.
Misalin karfe tara, Sheykh ya fito cikin shiga ta al’farma, yau ba al’kyabba a jikinshi riga da wondone sai malum-malum gariya mai kyau.
Getzner ce mai masifar kyau Brownish red color mai ɗan karen kyau da sheƙi, gariyar tasha aiki mai ɗan karen kyau da zaren surfani mai sheƙin piash color.
Hular kanshi da red and piash color, takalmin shi kuwa fatar ta kifa kalar red ɗin.
Yayi kyau sosai ya kafa hular nan cas a kanshi. Kekyawan suman kanshi ya konto gefe da gefe da ƙeyarshi sai sheƙi da ƙelli yakeyi.
Sajenshi ya kwanta lib, gashin girarsa dana gemunshi ɗan cas dashi misalin kamu ɗaya, sai sheƙi suke zubawa.
Ɗan madai-daicin bakinshi mai jajayen laɓɓa sai sheƙi sukeyi.
Yar ƙaramar jakar na’urar System ya riƙe a hannunshi, sai wani ƙamshi mai daɗin ji yake fiddawa, ɗan farin siririn Glass irin na manyan Doctors ya manna a fuskarshi kana ya fito.

A falonshi ya sameta, tana jera mishi breakfast.
Ganin zai wucene ta ɗan biyoshi a hankali ya zama suna tafe a jere.
Cikin kallon suman ƙeyarshi tace.
“You are breakfast is ready”.
Bai kulata ba yaci gaba da tafiya.
Ita kuma ƙeyanshi ta mannawa harara.
A haka suka fito.
Ya sallami Ummi da Jamil da tunda suka karya bai tafiba.
Da sauri Jamil yabi bayanshi yana cewa.
“Uhum Dakta sai yaushe zaka dawo ne?”.
Juyowa yayi ya kalli Jamil sai kuma yace.
“Kanada matsala ne?”.
Da sauri ya jujjuya kanshi tare da cewa.
“No. I’m very fine”.
yayi mgnar yana jijjiga jikinsa.
Kai ya kaɗa ya juya zai fita,
Da sauri Jamil ya kuma tambayarsa.
“Dakta yaushe zai dawone”.
Cikin tsuke fuskarsa yace.
“Ban sani ba”.
Daga nan ya fita, shi kuwa Jamil tsalle yayi tare da cewa.
“Yesss, Dakta Allah ya kiyaye hanya, a wuni lfy a asibiti”.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
“Yi maza to ka ɗauki shi”.
To yace kana ya miƙe ya fita.
Sanin cewa yanzu Sheykh yana sashin Hajia Mama ne.

Haka yasa ya rigashi fita.

Ummi kuwa miƙewa tayi taje ta rufe ƙofar sabida bata son wani yazo ya shigo.
Kiran Jamil tayi a waya tace in sun isoma ya kirata a wayane zata buɗe mishi.

Tana katse kiran ta juyo ta kalli Shatu dake zaune gefenta tana ce mata.
“Yauwa to Ummi muje mu fara aikin kafin ya iso mun kusa cimma aikin.”

Cikin mamaki tace.
“A a keda kikace sai an matsar da gadonshi sannan aikin tono ai bazamu iyaba. Dole sai mazan”.
Cikin muryar da har yau Ummi ta kasa banbance shi da asalin muryarta tace.
“A a ba matsala Ummi muje zamu iya”.
Ta ƙarishe mgnar tana yin gaba, ganin hakane yasa Ummi Binta a baya.
A hankali suka shiga falon.
Tana mai cewa Ummi.
“A nan ma an mishi wani aikin amman shi bai shiga jikinsa ba, sabida yanada Garkuwar addu’o’in da yakeyi yau da kullum.
Shiyasa duk sabbin sihirurruka basa shigarsa.
Sai dai waɗanda akayi mishi tun bai gama girma ba.”
To kawai Ummi ke ce mata sabida jin kamar muryarta na canza mata.

A haka ta kuma nuna mata wani wurin.

Tare da cewa.
“Uhumm Ya Jafar suke nema, su maida majanunin kan bola sai kuma sharrinsu ya zame mishi al’khairi,
Tsawon shekaru baya mgn sai ambaton Allah. Bashi ba zunibi sai tarin lada da yake samu na karatun al’ƙur’ani da ya zame mishi abokin hira.

To ita kuma me take nema a duniya da zata cutar da baiwar Allah da ahlinta duka haka.
In banda lalaci da son duniya na miji ya lalace da bin matsafa yana sawa ana sabauta ɗan uwanshi da yayanshi.”
Ita dai Ummi binta takeyi da ido da ƙafa har suka isa bedroom ɗin shi.

Ɗan lungun da ɗaya Bedside drower’n take ta shiga.
Kana ta kalli Ummi fuska a juye tace.
“Naɗe min carpet ɗin nan.
To Ummi tace da sauri ta fara naɗe carpet ɗin.
Bayan ta janyeshi da kyar ne, ita kuma Shatu.
A hankali tasa hannun damanta bisa jikin gadon ba tare da ta ɓallashi ba ko, ta cire wani abu a jikinshi ba, ta yunƙura ta tura gadon tare da cewa.
“Bismillahirahamanirahim”.
Da sauri Ummi taja da baya cike da mamaki da tsoron ganin yadda take tura tamfatsetsen gadon mai ɗirkekiyar katifa da ko tura katifar kawai aikine.

Guuuuuuh haka sautin tura gadon yake badawa.

Saida ta turashi har jikin Waldurob.
Kana ta tsaya a tsakiyar inda gadon yake kafin ta turashi.
Dai-dai lokacin kiran Jamil ya shigo wayarta.

Da sauri taje ta buɗe mushi.

Kana suka shigo,. A falon suka bar Ɗalha mai tayis,
kana Jamil ya amshi kayan aikin yabi bayan Ummi yana cewa.
“Yauwa ɗalha ɗan jirani bari inzo mu isa kaga wurin”.

To ɗalha yace kana ya fara cin abincin da Ummi ta saka mishi.

Suna shiga suka maida ƙofar falon suka rufe.

A inda Ummi ta barta a han suka sameta.
Da sauri ta miƙawa Jamil hannun tare da cewa.
“Bani gudumar da ma’ɓamɓarin.”
Cikin sauri ya iso tare da ajiye ɗan buhun ya fito da gudumar da Maɓamɓarin yana mai mamakin yadda aka tura gadon yace.
“Bari Aunty Shatu nuna min ina zan fasa”.
Da sauri tace a a, ku ɗan matsa gefe, musamman ma kai koma can”.
Ta nuna mishi gefe.
Sake mata gudumar yayi jin ta fizgeshi.
A hankali ya tashi sabida cewa da tayi ya tashi.
Ido suka zuba mata, ita kuwa, gudumar tasa ta rinƙa buga tayis ɗin dake wurin saida ta fasa uku lafiyeyyu.
Kana ta ture fasassun tasa maɓamɓari tana ɓalle sauran, saida ta ciresu kab.
Sannan ta fara fasa fulon simintin dake ƙasan.
Da mamaki Ummi ke kallon wurin sabida tasan babu wani fulo da akayi kafin asa tayis ɗin.
Fasashi tayi kana ta fara caccaka ƙasan wurin da matonin, tanayi yana fito da ƙasa.

Shiru sukayi ganin ramin yayi zurfi kuma ba komai.

A haka taci gaba da tono tana kuma faɗaɗa ramin ta ƙasa.

Wani irin zabura Jamil da Ummi sukayi lokacin da suka ga wani baƙin hayaƙi yana fitowa cikin ramin.

Ita kuwa Shatu da sauri tasa hannun damanta taci gaba da tonon.
Tare da yin mgna da sauri tace.
“Jamilu buɗe windows da sauri hayaƙin nan ya fita”.
Cikin rawan jiki yace to.
Kana ya fara buɗe wa da sauri sabida, hayaƙin ya fara cika ɗakin.

Yana buɗe windows ɗin kuwa hayaƙin ya fara fita.
Tonon taci gaba dayi tare da cewa.
“Inama da akwai wani yardajjen mu a kusa, bayan ku biyun nan da yabi hayaƙin nan zaigane mana ina zai shiga cikin sashukan mutanen gidannan shaidar aiki ya koma kan wanda ya yishi.”
Da sauri Jamil yace.
“To ko in fitane inbi hayaƙin”.
Cikin sauri tace.
“A a kada ka fita ku tsaya kaida Ummi.”

Numfashi suka fara sauƙewa, a hankali lokacin da sukaga duk hayaƙin ya gama fita.
Sai kuma suka fara takowa suna zuwa inda take ganin yadda hannunta dake cikin ramin yake karkarwa.
Ga wata zufa dake keto mata kamar da bakin kwarya.
Wani marfin tukunyar ƙasa ta ɗago.
Kana a hankali ta ɗago tukunyar.
Ta ajiyeta gefe kana ta koma ta jingina tana mai jan numfashin.
Cikin sauri Ummi taje ta kunna sauran wutan ɗakin duka, ya zama kamar farin wata.

Jamil ne ya fara leƙa cikin tukunyar.
Da sauri yace.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun. Ummi zo ki gani”.
Ya ƙarishe mgnar yana sunkuyowa da kai hannunshi zai kama tukunyar ƙasan cikin sauri da ƙarfi Shatu ta buge hannunshi da hannunta na hagu tare da cewa.
“Jininka ɗaya da Yah Sheykh in ka taɓa duk abun zai iya dawowa jikinka.”

Ta ƙarishe mgnar da ɗago hannun ta na dama tasa a ciki.
Tukunyar da sauri ta rumtse idanunta sabida wani irin masifeffen tsikara da taji an mata a hannunta.

A can ƙasar Cameroon kuwa cikin Rugar Duno dake, kusa da Rugar Malam Babayo.
Ba’ana ne zaune bisa buzun aikinshi.
Da kasko a gabanshi yana kallon cikin kaskon gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi cikin tashin hankali da fargaba yace.
“A’a A a Mata kada ki taɓa, baki amince na baki mgnin kariyar tonar sihiriba, iya ganin idan a zuba sihiri a abinci yake na shayar dake shi nanma a bisa dole baki saniba.
Kada ki taɓa zai cutar dake”.
Ya ƙarishe mgnar hawaye na zubo mishi, Allah ya sani baya son abinda zai cutar da Shatu ko kaɗan.

Ita kuwa Shatu a hankali ta fara fito da wasu irin tabka-tabkan layu wanda aka liƙesu da yadin al’kyabba daga gani kasan na Sheykh ne sabida shi ɗaya kesa irinsu a masarautar Joɗa tun yana ɗan yaro matashinsa.
Wani dogon ajiyan zuciya taja tare da fizgo wani dogon maciji a cikin tukunyar ƙasar.
Da sauri Ummi taja da baya, shi kuwa Jamil sai leƙowa yakeyi.

A dai-dai lokacin kuma Sheykh dake cikin Office dinshi na cikin Genaral Hospital Ɓadawaya shi ɗaya, dan yau ba mutane sosai dudu mutun biyar ne kuma ya gama dubasu ya musu komai, yana zaune ko za’a turo wasu.
Wani irin zabura yayi ya miƙe tsaye da ƙarfi tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun”.
Sai kuma ya sunkuyo yana kallon yadda babbar yatsarshi ta ƙafar dama wacce zanen maci ke kanta take rawa kar-kar.
Da sauri ya juya ya nufi bathroom ɗin cikin Office dinshi.
Cikin sauri ya zare malum-malum ɗin jikinshi juyowa yayi ya ajiyeta saman kujerarshi.
Kana da sauri ya nufi Bathroom sabida yadda yakejin ana fizgo wani abu kamar jijiya a jikinshi tun daga saman cikinsa kusa da ƙirjinsa, har zuwa kan ɗan yatsarshi.
Da sauri ya cire rigarshi da snglet ɗin, da ido yabi zanen dake jikinshi wanda samanshi zanen kan macijine.
Gaba ɗaya jikinshi rawa ya farayi tamkar mazari.
Duk wata jijiya dake jikinsa saida ta tashi tsaye.
Cikin tashin hankali yake ambaton sunayen Allah da duk addu’o’in da sukazo bakinsa.
Hannunshi yasa ya damƙi bnnarshi data miƙe tayi wani irin harbawa da masifar ƙarfi, riƙeta yayi da kyau jin yadda take tashi tana kumbura da cika tana tsawo tamkar zata faso boxes ɗin shi ta fito woje.
Wannan shine babban tashin hankalinshi dan tsawon shekaru kusan ashirin bai sake ji ko ganin bnnarshi ta miƙe kamar hakaba sai yau.
Karkarwa duk jikinshi keyi, hatta jijiyoyin kanshi dana damatsan hannunshi tasowa sukayi ruɗu-ruɗu jijiyar goshinsa har harbawa takeyi”.
Innalillahi wa innailaihi rajiun yaketa maimaitawa, yanajin kamar ana jan jijiyoyin jikinsa.
A haka ya maida kayanshi kana ya fito.
Sai dai bai samu damar maida gariyar ba, zama kawai yayi bisa kujerar yana rawan sanyi.

A haka abokinshi Dr Arabi ya shigo ya sameshi cikin mamakin ganin yadda yake karkarwa yace.
“Dakta Jabeer lfy kuwa meya sameka”.
Cikin muryar alamun zazzaɓi yace.
“Zazzaɓi ne Arabi. Sanyi nakeji”.
Da sauri ya iso inda yake taimaka mishi yayi ya saka mishi gariyar.
Kana ya kamoshi ya kawoshi bisa tattausan kujerar 3 str dadake cikin Office ɗin ya kwantar dashi.
Aunashi yayi tare da kiran wata Nurse ya gaya mata magungunan da zata amsa musu a Pharmacyn nasu, cewa Dr Jabeer ba lfy.
Ai lokacin ɗaya sai gata da manyan likitoci har uku.
Cikin tarin kulawa, suka fara dubashi ganin yana gab da fita haiyacinsa ne, yasa suka mishi allurar bacci.
Da sauri Dr Arabi kuma ya kira, Jalal ya sanar mishi.
Jalal kuwa dake falon Hajia Mama ba tare da ya gaya mata ba ya miƙe da sauri ya fita.
Tana tambayarshi lfy.
Yace lfy sabida baison tayar mata da hankali.
A bakin ƙofar fita ya haɗu da Ya Affan da sauri ya kamo hanunshi suka juya yana cewa.
“Ya Affan Hamma Jabeer ba lfy, yana Genaral Hospital Ɓadawaya, yanzu Yayan abokina Umar Dr Arabi abokinshi ya kirani ya gaya min yace baida lfy sosai fa”.
Ai da sauri Affan ya fara lalubo car key dake cikin al’jihunsa cikin kiɗima da tashin hankali yace.
“Muje, muje da sauri mu tafi a maidashi Valli Hospital yafi kwararrun likitoci”.
Kusan a tare suka shiga motar Affan suka tafi.

Kafin suje kuwa tuni bacci ya ɗauke shi, an ɗaura mishi ruwa da allurai.
Sauran Doctors ɗin sun fita.
Sai Dr Arabi da yake zaune gabanshi.
Da sauri Affan yasa hannun shi ya taɓa jikinshi tamkar wuta.
Jalal kuma yatsarshi daketa karkarwa yake kallo tare da rauni a fuskarshi yace.
“Yah Arabi meya sameshi ne?”.
Cikin sanyi Dr Arabi yace.
“To wlh nima shigowa kawai nayi na sameshi yanata karkarwa, yace min zazzaɓi yakeji sanyi na damunshi.
Na kira Nurse ta kawo min injections and drip kafin muyi mishi allurar ma tuni ya kusa suma, abun yafa bani tsoro.
Amman Alhamdulillah kunga yanzu kuma da sauƙi”.
Ajiyan zuciya sukayi kana suka zauna a nan, ba tare da sun gayawa kowa ba.

A can masarautar Joɗa kuwa.
Cikin tarin firgici da al’ajabi Jamil da Ummi ke kallon Shatu.
Data fizgo macijin da ƙarfi cikin tukunyar.
wurgar dashi tayi a ƙasa sai gashi yayi wutsul-wutsul sau biyu, shike nan ya mutu.”
Mazargin mondo ta fitar da kuma hula wanda duk na Sheykh ne.
Cikin murya mai rauni tace.
“Yanzu Jamil zaka iya taɓasu.
Haɗasu kaje in akwai inda zaka wurgar dasu ka wurgar dasu, ka fasa tulun.
Kada ka binne macijin ya bushe akeso.
Ummi ɗauki Hular Yah Sheykh da zariyarshi a wonkesu.

Da sauri Jamil yace.
“Eh akwai inda zan wurgar dasu”.
Nan ya tattare macijin da da layun ya saka cikin tulun ya fita.
Key ɗin ƙofar baya ya ɗauka ya buɗe ya tafi cikin Garden ɗin.
Tafiya yayi sosai saida yaje can cikin dajin ya fasa tulun macijin da layun suka watse kana ya juyo ya dawo ba tare da ko waiwaya ba sabida tsoro.

Ita kuwa Ummi bathroom ɗin shi ta shiga a take ta wonkesu kana ta fito dasu.
Cikin sanyi Shatu tace.
“Wai hannuna Ummi yi sauri ki wonko gero ki kawo min ruwan tsarin.”

Da sauri Ummi ta fita.
Murmushi tayi ganin Ɗalha mai gyaran tayis yaci yayi haniƙan yana kallon tv.
Cikin sauri tace.
“Yi haƙuri dan Allah Ɗalha muna tattare ɗakin ne da yake tayis ɗin ƙasan gadone ya fashe”.
Cikin shan iskar yace.
“Ba komai Ummi”.
To tace kana taje ta wonke gero, sannan ta fito da ruwan tsarin tazo.
Tana zuwa ta bawa Shatu cikin ramin ta watsa ruwan.
Kana ta fara tura ƙasar da kuma fashesshe-fashesshen tayis da fulo ɗin tanayi tana yayyafa ruwan.

Dai-dai lokacin Jamil kuma ya shigo.

Ganin yadda hannunta yaketa karkarwane yasa ya tayata tura ƙasar saida suka gyara komai fes kamar ba fasawan ganganci akayiba.
Kana ta miƙe tare dasa hannun hagunta ta riƙo na damanta tana cewa.
“Shima Yah Sheykh dole zaiji wani abu a jikinshi duk inada yake”.
Sai kuma tayi shiru tare da rumtse idanunta tace.
“Wash hannuna”.
Cikin sauri Ummi tace.
“Sannu hannun ya gaji ko”.
Kai kawai ta gyaɗa mata.

A haka suka fito falon. Kai tsaye bedroom ɗin ta ta nufa.

Shi kuwa Jamil yayiwa Ɗalha jagoro,
Suka shiga suka gyara wurin da aka fasa ɗin fes.
Kana Ummi ta share wurin ta goge, sannan suka tura gadon suka maidashi.

Nanma ta ƙara gyara ɗakin Jamil kuwa ya ɗauki Ɗalha ya maidashi wurin aikinshi.

Ummi na gamawa taja ƙofar ta rufe tana al’ajabin wannan abu da ta gani da idonta.
Kitchen ta wuce ta ɗaura musu Lunch tana kiran Umaymah ta gaya mata duk abinda ya faru.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kaɗan daga cikin mafarkan da nakeyi kan Sheykh ya auro ba fulatar daji sun fara tabbata.
Ya Allah kasa abinda zai faru a sanadin shigowar Shatu masarautar Joɗa ne kake nunamin a mafarkaina”.
Umaymah ta faɗi lokacin da Ummi ta mata bayanin abinda ya faru.
“Amin Amin, Ummi tace kana ta katse kiran jin muryar Aunty Juwairiyya da Hibba.”

Umaymah kuwa da sauri ta kira Lamiɗo ta gaya mishi abinda ya faru.
Murmushi yayi irin nasu na manyan sarakuna yace.
“Alhamdulillah warakafa nan shigowa masarautar Joɗa baki ɗayanmu zamu rabu da mugun iri a cikinmu, kada ki gayawa kowa Khadijatu kinji ko”.
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
“In sha Allah kuwa ko Jadda bazan gaya mishi ba”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Masha Allah, Allah ya miki al’barka Khadijatu da ace duk ƴan uwa haka suke riƙe ƴaƴan yar uwarsu da zumunci ya ƙara ƙarfi kin musu abinda mahaifiyarsu bazata iya musuba”.
Amin Amin tace kana ya katse kiran.

A cikin ɗakin Shatu kuwa.
Wani irin…!

Wani irin zufane ke tsastsafo mata.
Tako wani hudan gashin jikinta.
Gaba ɗaya ji takeyi hannunta na dama wanda dashi ta buɗe tukunyar ƙasan yana wani irin suka kamar ana tsikarinta da allurai masu dafi.

Jiki na rawa ta konta bisa gadon.
Wani zazzafan zazzaɓi ne ya rufeta a take.
Cikin rawan jiki tasa hannun hagunta ta jawo tattausan blanket ɗin ta rufe jikinta.
Rumtse idanunta tayi da ƙarfi tanajin zafin na ratsa mata jiki a hankali take addu’o’in cikin ranta. Jikinta na ci gaba da ɓari.

Ita kuwa Ummi a kitchen ita da Hibba da Aunty Juwairiyya sukayi girki suka gama.
Saratu ta share ko ina.

Ganin azahar tayi ne, sukaje sukayi salla kana suka dawo falon.
Shiru-shiru Shatu bata fitoba, hakane yasa Ummi tace Hibba take ta kirata.
Hibba na tafiya Jamil ya shigo.
Nan suka zauna.
Juyowa Ummi tayi tana kallon Hibba dake cewa.
“Ummi! Ummi!! Aunty Shatun kamar bata da lfy, naga sai rawan sanyi takeyi.”

Da sauri Ummi ta miƙe ta nufi cikin ɗakin bisa sallaya ta sameta alamun tayi sallan azahar kenan.
Da sauri ta nufi inda take tare da cewa.
“Shatu meyake damunki”.
Cikin sanyi murya tace.
“Zazzaɓi ne Ummi”.
Cikin tausayawa tace.
“Subahanallahi sannu ko! Barin in Sheykh ya dawo sai ya dubaki, yanzu muje ki samu kici wani abu”.
Cikin rawan murya tace.
“Na ƙoshi Ummi”.
Hannunta takai ta taɓa jikinta kamar wuta cikin kula tace.
“To me kikaci da zakice kin ƙoshi?”.
Danne kukan dake son kubce mata tayi, wanda halittartace dama in ɓata da lfy dai to kuka kuma zata shashi.
Cikin rawan murya tace.
“Na ƙoshi bazan ciba”.
Cikin jin ba daɗi Ummi tace.
“To tashi in taimaka miki ki koma kan gado.
Sai anjima kici abincin”.
Ta ƙarishe mgnar dasa hannu ta kamo hannun daman Shatu.
Da sauri ta miƙe tare da saƙin ƙara a hankali tace.
“Wayyo Ummi hannun zafi, kamanin wannan in tashi”.
Ta ƙarishe mgnar hawaye na zuba.
Cikin tsoro Ummi tace.
“Ayyah sannu. To amman kin bige hannune ko kin yankene?”.
Cikin karkarwan zazzaɓin tace.
“A a”.
Konciya tayi a kan gadon.
Borgo Ummi taja ta rufeta dashi.

Kana ta fita tana cewa.
“Allah ya sauwaƙa”.

A falon ta samesu zaune, cikin sanyin jiki tace.
“Jamil ina Jalal naga kai kaɗai”.
kanshi ya ɗago ya kalli Ummi tare da cewa.
“Yau tun da mukayi breakfast ban ganshi ba.
Bari in kirashi”.
To tace kana ta zauna. Shi kuma wayarshi ya zaro ya kira layin Jalal.
Bugu biyu ana uku ya ɗaga sabida baya son sautin kiran wayarshi ya tashi Hamma Jabeer ɗin nasu daga baccin da yakeyi.
“Hello Jalal ina kake ne, yau tunda safe ban gankaba”.
Cikin sanyi yace.
“Jamil Hamma Jabeer baida lfy, yanzu haka muna asibiti dashi nida Yah Affan”.
Cikin ruɗani Jamil ya kalli Ummi kana ya kalli wayar tare da cewa.
“Meya sameshi? Wanne asibiti kuke?”.
Affan ne ya amshi wayar Jalal tare da cewa.
“Jamil kadafa ka gayawa Mama hankalinta zai tashi.
Jikinshi da sauƙi sosai zazzaɓi ne kawai yanzu kam ma bacci yakeyi, yana farkawa dai zamu dawo gida”.
Cikin ɗan samun nitsuwa yace.
“Ka tabbatar Ya Affan?”.
“Zan maka ƙarya ne?”.
Affan ya amsa mishi tambaya da tabaya.
Kana yace.
“Bawa Ummi wayar”.
To yace kana ya miƙa mata wayar.
Nan yace mata. Sheykh ba lfy, amman jikinsa da sauƙi.
Su kontar da hankalinsu in ya farka zasu dawo.
To Ummi tace tare da mishi addu’a kana sukayi sallama.

Shiru sukayi a falon suna nazarin to meke faruwa.
Musamman shi Jamil da yaji Ummi na cewa Aunty Juwairiyya cewa Shatu ba lfy.

A haka dai sukaci abinci.

Sheykh Jabeer kuwa, sai ƙarfe Shida na yamma gab da magriba ya farka.
Da sauri Affan ya matso kusa dashi.
Tare da kama hannunshi yace.
“Sannu Hamma Jabeer, ya jikin naka? Da sauƙi ko? Me yake maka ciwo?”.
Shiru yayi yana kallonsu yana tuna lokacin da yayi baccin.
Jalal ne ya ɗan kalleshi cike da rauni yace.
“Hamma Jabeer ya jikin naka.
Me zakaci in kawo maka?”.

A hankali yace.
“Meyasa baku tadani ba nayi sallan azahar, la’asar, gashi har magriba ta kusa.”
Ya ƙarishe mgnar yana miƙewa zaune da alamun ɓacin ran rashin tada shi da basuyi ba.
A hankali Affan ya miƙe tare da kamo hannunshi alamun zai tallafa mishi ya tashi.
“Janye hannunshi yayi tare da kallonshi cikin alamun faɗa yace.
“Lokacin Sallah yayi kuna ganina ku barni ina baccin asara baccin yammaci sabida baku ɗauki salla da mahimmanci ba, ai ko bana gani bana mgn zaku tasheni kuyi min alamun lokacin salla yayi inyi niya kuyi min al’wala inyi salla.
Bare ina cikin hayyacina, ku jinyarku sai kace jinyar kafurai babu tada majinyaci batun salla”.
Ya ƙareshe mgnar yana nufar hanyar bathroom.
Da ido suka bishi suna cewa.
“Kayi haƙuri”.
A hankali yake taku sabida har yanzu yanajin kamar ana zare mishi jijiya a jikinshi dai-dai inda zanen tafiyar macijin nan yake.
Al’wala yayi kana ya fito, yayi salla.
Sannan yace.
“To mu tafi ko”.
Cikin sauri sukace to sukabi bayanshi.
Suna sauƙa ana kiran sallan magriba a masallacin cikin asibitin.

Nan suka tsaya a masalacin asibitin sukayi sallan magriba.
Kana suka nufi gida.
Ana kiran salla. Isha’i suna shiga masarautar Joɗa shiyasa kai tsaye suka wuce masallacin.

A cikin masarautar kuwa, sosai jikin Aysha yayi zafi da zazzaɓin.
Da kyar Ummi ta taimaka mata tayi al’wala kana tayi salla.
ana ta zauna saida tayi sallan isha’i kana itama tayi.
Sannan ta kalli Hibba tare da cewa.
“Hibba haɗo min koda tea ne ki kawo in bata tasha”.
Cikin rauni ta girgiza kai alamun bazata shaba, murya na rawa tace.
“Ummi zan kwanta”.
Cike da mamaki tace.
“To Aysha jinya ba abinci kuma ai shike tsananta jinyar.
Ki ɗan sha koda tea ɗin ne in Sheykh ya dawo ya dubaki.
Shiyama ɗin baida lfy yau wuni yayi kwance a asibiti”.
Cikin rumtse idanunta tace.
“Ba matsala zaiji sauƙi, dama dole zaiji a jikinshi alamun a kunce abubuwa da yawa a jikinshi”.
Sai kuma ta miƙowa Ummi hannu tare da cewa.
“Ummi zan kwanta, kaina ciwo kamar zai rabe gida biyu hannu ciwo kamar zai tsinke”.
Cikin tausayawa tace.
“Aysha ko dai taɓa abun nanne da kikayi ya jawo wannan abun”.
A hankali tace.
“Wata ƙil”.
Amsar kofin da Hibba ta miƙo mata tayi tare da cewa.
“Yauwa amshi kisha kinji ko Aysha”.
Cikin sauri ta girgiza kai sabida bazata iya ci ko shan wani abun a yauba irin zafin da takeji”.

Ganin haka ne yasa Ummi ta taimaka mata ta miƙe tsaye kana ta koma kan gado.
Sannan ta rufe mata jiki tace.
“Bari inje in sanarwa Gimbiya Aminatu kafin Sheykh ya dawo”.
Cikin sanyi tace.
“To amma Ummi kada kice mata na cire wani abu”.
To tace kana ta juya ta fita.
Tuni dama Hibba ta fita.

A falon ta samesu harda Jalal Affan da kuma Sheykh yana zaune da alamun jinya a jikinshi.
Jamil kuwa tamkar likita haka ya tsareshi da tambayoyin meke damunshi meke mishi ciwo.
Ummi kuwa babbar yatsarshi da har yanzu take motsine ta kalla tare da cewa.
“Sheykh sannu ko! Ya jikin naka? Da sauƙi ko?
Me zan kawo maka kaci?”.
Cikin lumshe ido yace.
“Alhamdulillah da sauƙi”.
Aunty Juwairiyya da Ya Jafar da yanzu suka shigone,
Ya Jafar ne ya zauna a gabanshi.
Yana kallon yatsarshi. Murmushin yayi wanda ya bawa su Jalal Jamil Affan mamaki yayi kana ya kalli Sheykh sai ya kuma miƙa ya zauna gefenshi ya ruggumeshi.

Ummi ce ta kuma kallonshi tace.
“Sheykh me kakeso in dafa maka”.
A hankali yace.
“Ummi bani nono mai sanyi da zuma, insha ya isa”.
Da sauri ta juya ta nufi kitchen, Jim kaɗan kuwa ta fito da cup a cike da haɗin mai sanyi.
Amsa yayi tare da riƙewa.
Yana kallon Hibba da ke cewa.
“Hamma Jabeer Aunty Aysha ma bata da lfy, yau babu abinda taci tun safe”.
Uhum yace tare da kai kofin burgeggen kinɗirmo da zuma a madadin sugar bakinshi.
Zuƙa ya ɗan yi, a hankali ya lumshe idonshi jin sanyin nonon ya ratsashi.
yaji zafin da yakeji cikin jikinsa yana raguwa.
Hakane yasa yaci gaba da sha, idonshi ya ɗan ɗago ya kalli Ummi jin tana cewa.
“Sheykh Aysha fa babu lfy sosai.
Dama kai nake jira, ka dawo ka dubata”.
Maida idonshi yayi bisa kofin
Yayi kamar baijiba, saida ya shanye madarar ne, ya ɗan miƙe tsaye cikin sanyi yace.
“Affan je ka ɗauko Dr Kubra tazo ta dubata”.
Da sauri Affan yace.
To kana ya miƙe ya fita.

Shi kuwa Sheykh a hankali jiki a mace ya wuce Side ɗinsa.
Cikin jan ƙafa ya ƙarasa bedroom ɗinsa.

Kai tsaye kan gado ya faɗa sabida har yanzu allurar baccin tana ɗan fizgarshi ko dan haka ya haɗu da rashin lafiyar ne.

Ko gariyarsa bai cireba ya kwanta.
Yana konciya kuma ya fara tasbihi kamar koda yaushe.
Lokaci ɗaya daddaɗan bacci ya kwasheshi.

A falon kuwa bayan ya shiga ne.
Aunty Juwairiyya ta miƙe ta tare da cewa.
“Ummi bari in koma na bar yara su kaɗai”.
Ta miƙewa Ya Jafar yabi bayanta.
Jalal kuwa da Jamil Dinning area suka nufa dan cin abincin dare.

Ba jimawa Affan ya dawo.
Da wata Kekkyawar mata yar duma-duma mai sakin fuska.
Bayan sun gaisa da Ummi ne Hibba ta gaidata kana suka wuce ɗakin Aysha.
Bisa jagorancin Ummi.

Da sauri ta ɗan yaye borgon tare da kife tafin hannun ta kan goshin Aysha da yake kamar wuta.
Da sauri ta zauna kan Bedside.
Cikin kula ta kamo hannunnta mai ciwon.
Da sauri ta buɗe idonta tare da tashi zaune, murya na rawa tace.
“Wayyo Ummey na”.
Cikin tausayawa tace.
“Afwan hannun yana ciwo ne?”.
Kai ta gyaɗa mata alamar eh.
Ita kuwa ido ta zuba mata tana kallon kekyawar fuskarta tace.
“Dame kuma yake miki ciwon?”.
A hankali tace.
“Kaina sai kuma zazzaɓi da hannun”.
Ɗaya hannunta mai lafiyar ta kamo tare da cewa.
“Shi wannan baya ciwo ne”.

“Eh baya yi”.

“To faɗuwa kikayi ne hannun yaji ciwo”.

A hankali tace.
“A a haka kawai yake ciwo”.

Jakarta ta jawo tana kallonta.
Ta buɗe.
abubuwan buƙatar ta, ta ɗauka.
Jininta ta ɗiba, kana.
Ta gwada BP’n ta a take.
Bata da matsalar hawan jini.
Bugun zuciyarta ta gwada.
Shima Normal.
Ganin hakane ta kalli Ummi tace.
“Zan tafi zamuje Valli Pharmacy.
Zan bawa Affan magunguna ya kawo mata, tasha.
Gobe da zafe zan zo.
Ni yanzu asibiti zan wuce.”
Cikin gamsuwa da hakan Ummi tace.
“To mun gode Dr Kubra a gaida yara”.
Murmushi tayi jin Aysha na cewa.
“Banda allura ko?”.
Kai ta gyaɗa kana ta fita.

Koda sukaje da kanta ta shiga ta sai magungunan ta bawa Affan.
Shi ya wuce gida ita kuma ta nufi asibitin.

Cikin ikon Allah kuwa datasha mgnin zazzaɓin da ciwon kai ɗin ya ɗan lafa.
Har ta samu tayi bacci.

A nan Ummi ta kwana a ƙasa.
Hibba na sama gefenta.
Kamar dai randa ta faɗi a ɗakin Sheykh.

Washe gari da safe, kuma tana tashi ta tashi da ciwon hannun.
Kuma bai kumbura ba bai kuma yi ja ba.

Zazzaɓi kuma da ciwon kai da sauƙi.

Bayan Ummi ta gama aikin kitchen ne tazo da kanta ta haɗa mata ruwan wonka.
Ta shiga.
Sannan ita kuma ta fito mata da zani rigar atamfa mai gajeren hannu da maya finshi, da siket da bra and pant.

A cikin bathroom ɗin kuwa,
gaba ɗaya ta kasa yin yadda takeso.
Sabida ko motsa hannun tayi sai taji kamar ta ɗaura hannun a kai tayi ta kurma ihu.

Gashi shine hannun dama, haggun bai iya abubuwa sosaiba.

Cikin tsoro da zubda hawaye take cewa.
“Wayyo Ummey na, shike nan zan zama mai hannu ɗaya,
Wa zai taimaka min bakya kusa Junainah bata nan.
Ya zanyi iyi wonka inci abinci”.
Ta ƙarishe mgnar tana goga sabulu a jikinta da hannun gadun.

A haka dai tayi wonkan a karkace

Koda ta fito.
Dole siket kawai da pant ɗin tasa,
bra ɗin barinshi tayi sabida bazata iya juya hannun ta saƙalashi ba.
Rigarma da kyar ta sata nanma saida tai hawaye.

Yunwa takeji kamar zai kasheta,
Hakane yasa ta yafa gyalen.
Ta nufi falon.
A gefen Ummi ta zauna.
Da sauri Ummi ta kalli Hibba dake Dinning area tace.
“Hibba kawo min tray’n nan.”
“To”. tace kana ta ɗauko tray’n.
A gabanta ta ajiye.
Tea Ummi ta haɗa mata, ta miƙa mata cup ɗin.
Da sauri tasa hannun hagun ta amsa.
Kana ta kai bakinta dan har wani duhu-duhu take gani.
Bakinta ta nufa da kofin.
Amman sai taji abin a karkace hannun kuma sai rawa yakeyi.

Cikin rawan hannun ta manna kofin a bakinta.
Idonta ta ɗan rufe, sabida zafin shayin.
Daurewa tayi ta fara zuƙanshi tanayin abin a karkace.
Hannun daman kuwa shima rawa yakeyi.

Cikin sauri ta shanye tea ɗin.
Wani na ɗan bin gefen lips ɗinta, sabida a karkace kofin take.
Ajiye kofin tayi tare dasa hannun hagun ta goge baƙin ta.

Sam tea ɗin bai isheta ba,
dan jikinta sai rawa yakeyi alamun yunwa.

Fahimtar hakane yasa Ummi sake haɗa mata wani tea ɗin ta miƙa mata cup ɗin tare da cewa.
“Amshi ki ƙara sha kafin Dr tazo”.
Cikin sanyi tace.
“Hannuna ya gaji Ummi ajiye min shi in ɗan huta.”
Ajiyewan tayi kana ta jawo Foodflaks ɗin,
soyayyan Arish da kwai ta saka mata a plate kana tasa mata.
ferfesun kaɗan a ɗan side plate mai ɗan zurfi.
Kana tace.
“To kici wannan sai kina ɗan shan tea ɗin a kai”.
Kallon plate ɗin tayi.
Cikin sanyi tasa hannu ta ɗauki fork sokawa tayi a cikin plate ɗin.
A karkace ta kaishi bakinta tare da dawo da cokalin ta ajiyeshi.
Kana ta fara taunawa. Tare da kora tea ɗin.
A haka dai ta ɗanci kana ta ture plate ɗin tace.
“Alhamdulillah”.
A hankali Ummi tace.
“Ki ƙara mana kiga ko rabinshi baki ciba.
Gashi ferfesun ko taɓawa bakiyi ba”.

Cikin maida numfashi, tace.
“Alhamdulillah Ummi na ƙoshi”.
Kai ta jinjina mata.
Hibba ce ta kalleta tare da cewa.
“Sannu Aunty Aysha”.

Kai ta gyaɗa, tana mai taune lip ɗin ta na ƙasa.

Jamil da Jalal ne suka iso tsakiyar falon,
Cikin kula Jamil yace.
“Aunty Aysha ya jikin naki?”.
“Da sauƙi”. tace a taƙaice
Jalal ne ya ɗan kalleta ganin yadda taketa tsastsafo zufa yace.
“Sannu Allah ya sauwaƙa”.
Amin tace.
shi kuwa maida dubanshi yayi kan Hibba yace.
“Ƙara gudun AC mana”.
Cikin sauri Hibba ta miƙe ta ƙara ƙarfin AC’n

Daga nan suka fita, sashin Affan suka nufa, koda sukaje basu daɗe ba sabida sun samu Mami Bata nan bata dawo gidansu ba.

Ummi kuwa miƙewa tayi tare da cewa.
“Hibba zauna da ita. Bari inje in sanarwar Lamiɗo halin da ake ciki”.

To Hibba tace. Har Ummi ta juya zata tafi sai kuma ta tsaya, jin wayarta na rigin.
Amsawa tayi da sauri ganin Umaymah ce.
Bayan sun gaisa ne Umaymah ke ce mata.
“Ya jikin Jazlaan da Aysha.
Jiya Jalal ke gaya min wai duk biyu basu da lfy”.
“To Alhamdulillah jiki da sauƙin, shi kam Sheykh naga ya wore sosai.
Amma fa Aysha kam, sai hannun yayi kamar ya lafa sai kuma kiga ta fara haɗa zufa, can kuma sai ya fara tsikarinta hannun yayi zafi jau kamar wuta, sai kiga yanata karkarwa.”
Cikin tsoro Umaymah tace.
“Subahanallahi, abin har hakane, to wai hannun ya.
Kumɓura ne ko me yayi”.
Da sauri tace.
“Wlh kuwa bai kumburaba ciwo kawai yake mata.”

“Subahanallahi, haɗani da ita”.
Da sauri tace to. Kana ta miƙawa Aysha wayar.
Ita kuma ta nufi Sashin Lamiɗo.
Nan ta sanar wa Gimbiya Aminatu, a take tayi mata jagora ta gayawa, Lamiɗo abinda ke faruwa da kanta.

Tare suka koma da Gimbiya Aminatu.

Ita kuwa Aysha cikin wahala tace.
“Ina kwana Umaymah”.

“Lfy lau Aysha ya jikin naki?”.

Cikin sanyi tace.
“Da sauƙi”.
Cikin kula tace.
“To Allah ya ƙara mana sauƙi.
Bari zanyiwa Jazlaan mgn ku tafi asibiti”.

Cikin rawan murya tace.
“Umaymah ba ciwon asibiti bane bafa”.

Cikin tausayawa tace.
“To bari zanyi mgna da Lamiɗo, karki damu in sha Allah zaki samu lfy kinji ko ɗiyata”.

To tace tana zubda hawaye.

Tana katse kiran tayi mgna da Lamiɗo, ta gaya mishi yadda sukayi, yace to ba matsala.

Ita kuwa Ummi da Gimbiya Aminatu da Dr Kubra kusan a tare suka shigo.
Zuwa lokacin kuma zogin hannun ya tashi.
Sai jujjuya hannun takeyi tana cewa.
“Wash- wash Allah na wash Ummey na”.

Shigowar sune Yasa ta miƙe tsaye gaban Ummi ta tsaya tana jujjuya kai da taune baki tana ɗan bubbuga sawunta a ƙasa.
Da sauri Ummi ta kamo hannun ta mai lfyan ta ajiye ta kan kujera.
Da sauri Dr Kubra ta matso tare da cewa.
“Subahanallahi hannun ne”.
Hibba ce ta gyaɗa kai cikin zubda hawaye tace.
“Eh”.

Gimbiya Aminatu kuwa gefensu ta zauna, hakane yasa Aysha ta ɗaura mata hannun kan cinyarta tare da zubda zafafan hawaye tanayi tana haɗa zufa.

A hankali Dr Kubra ta kai hannun ta kamo hannun tana mai cewa.
“To kodai kin taɓa karyewa tsohon karaya ne ya tashi”.
Wani irin zillo Aysha tayi tare dasa ƙara ta miƙe tsaye gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.

Dai-dai lokacin kuma, Sheykh Jabeer ya fito cikin shigar jallabiya da al’kyabbar.

Ido ya zuba mata ganin yadda take karkarwa ga kuma hawaye dake shatata a fuskarta.
Ga zufa da ya jiƙata cakab dan azaban zafi.”

Da sauri Dr Kubra ta motso kusa dashi cikin tausaya mata tace.
“Dr ko zamu wuce asibiti da itane”.
Da sauri Dr Kubra da sauran duk suka zuba mata ido jin tana mgn murya na rawa take cewa.
“A a ni bazan je asibiti, bazan jeba, bazan jeba”.
Kanshi ya girgiza tare da taɓe fuska kana yace.
“To ai shike nan kunji ko”.

Gimbiya Aminatu ce, ta miƙe ta kamota
Zaunar da ita tare da cewa.
“Aysha zauna ko”.
Kai taketa juyawa, hawaye na zuba.

Shi kuwa Sheykh Jabeer fita yayi.
Dr Kubra kuwa, cikin tausayawa tace.
“To Ummi ciwon kan da zazzaɓin kam da sauƙi ko”.
A hankali tace.
“Eh sosai ma kuwa. Yanzu hannun ne kawai ke ciwo”.
Numfashin ta fidda tare da cewa.
“Zan turo Dr Imam likitan cancer ne zai zo ya duba hannun.”
Cikin sanyi Ummi tace to.

Daga nan Dr Kubra ta fita.
Gimbiya Aminatu kuwa Hibba ta kalla tare da cewa.
“Ke Muhibbatu kira min Umaymah”.
To tace kana ta kira mata ita.
Bayan sun gaisa ne tace.
“Khadijah ki kira Jabeer kiji me zaice ayi kan ciwon yarinyar nan, ya fito ya wuce ko kallo bamu isheshiba bafa nason iya hege”.
A hankali Umaymah tace.
“Kiyi haƙuri Gimbiya in sha Allah zanyi mgna dashi kuma ma nayi mgna da Lamiɗo yace gobe zai shigo da mai magani. Tunda tace bata son asibitin.”
To tace kana ta kashe kiran

A wannan ranar dai haka ta wuni da hannun. in anjima ya lafa anjima kaɗan ya taso.
Haka kuwa da dare ta kwana ita da Ummi ba baccin kirki, domin kuka takeyi sosai sabida azabar da takejin.

Washe gari ma haka ta Wuni Dr Aliyu da kanshi ya shigo ya dubata.

Da yamma Lamiɗo da Galadima da Sarkin bakan masarautar suka shigo.
Bayan sun gaisane Sarkin Bakan ya duba hannun sai yace.
“Laah ba matsala ai wannan abu mai sauƙine bari yanzu zan baku mgnin sai dare in zata konta ku shafa mata a hannun.
A kuma bata tasha, da izinin ubangiji zatayi bacci lfy”.
Cikin jin daɗi Ummi ta amshi mgnin tare da cewa.
“Mun gode, Allah ya kaimu daren.”
Amin Amin sukace.
Kana Lamiɗo ya tashi sannan suma suka tashi suka bi bayanshi.

Shi kam Sheykh baima san anyi hakaba.

Ƙarfe takwas na dare. Ummi na zaune gaban Aysha daketa zubda hawaye tare da karkarɗa hannun.
Maganin da sarkin bakan ya basu ta kwaba da ruwan zafi kamar yadda yace musu.
Kana ta jiƙa ɗayan da ruwan ɗumi, da kuma citta guda uku.

Miƙa mata tayi tare da cewa.
“Sannu Aysha amshi kisha ko, Allah ya baki lfy”.
Da sauri tasa hannu ta amshi kofin a karkace ta kafa kofin a baki ta shanye ruwan fes.
Kana ta miƙawa Ummi ƴan ƙwaryar.
Kana ta miƙa mata hannu mai ciwon cikin rauni tace.
“Gashi Ummi shafa min”.
Ta karashe tana zubda hawaye.
Cikin tausayawa Hibba tace.
“Sannu Aunty Aysha”.
Kai ta iya gyaɗawa.

Ita kuwa Ummi a hankali ta fara shafa mata mgnin.
Saida ta shafe hannun duka, sannan ta ɗago ta kalleta tare da cewa.
“Allah yayi mana mgni”.
Amin tace.
Tare da miƙewa tsaye, hannunta mai lafiyar tasa ta tallabe mara lfyan da ta fara jin wani sabon abu na tsikararshi.
A hankali ta rinƙa taku, har taje gaban dreesing mirror.
Kana ta juyo a hankali ta dawo bakin ƙofar ɗakin.
Cikin kula Ummi tace.
“Sannu ko Aysha zoki zauna ki nitsu”.
Kai ta kaɗa ba tare da ta bar zirga-zirgan ba.

Hibba kuwa ido kawai ta zuba mata, tana binta da sannu.
Cikin sanyi ta kuma juyowa hawaye na kwaranya daga cikin manyan fararen idanunta da suka juye zuwa ja.

A hankali ta fara salati tare da kiran sunan Allah.

Jikin gini ta jingina kanta tare da sakin shessheƙan kuka mai cike da azaba murya na rawa take cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun.
Hasbunallahuwani’imal wakil, la haulawala ƙauta illabillah.
Wayyo Ummey na, Wayyo Bappa na, zan mutu baku sani ba.”
Wasu zafafan hawaye masu ɗumine suka zubowa Ummi saboda tsananin abin tausayi da ta gani a tare da yarinyar.

Hibba kuwa cikin kuka ta kira Umaymah tana kuka tace.
“Umaymah Aunty Aysha tanata kuka tana cewa, zata mutu Ummeyn ta bata samiba, tunda aka shafa mata mgnin da sarkim baka ya bayar bata sake zamaba sai zirga-zirga takeyi”.
Cikin kiɗima Umaymah tace.
“Innalillahi. Ina Ummin ku? bata waya”.
Cikin kuka tace.
“Ummi ma kuka takeyi”.
A hargitse Umaymah tace.
Ki bata waya nace dan ubanki”.
Da sauri ta miƙawa Ummi wayar.
Cikin raunin murya Ummi tace.
“Khadijah Aysha ba lfy, azaba yayi mata yawa fa. Ta ƙasa zaune ta kasa tsaye”.
Cikin sauri Umaymah tace.
“Ina Jazlaan!?.”
Cikin sanyi tace ban san inda yajeba, amman tunda magriba bai dawoba.”
Da sauri Umaymah ta katse kiran
Number Sheykh tayi ta kira.
Sai dai duk layukanshi suna shiga baya ɗagawa.

Cikin tashin hankali ta kuma kiran.
Lamiɗo tayi mishi bayani.
Anan take Lamiɗo ya kira sarkin baka yace mishi, ga halin da ake ciki.

Sai ya bawa Lamiɗo tabbacin.
Eh dama zaiyi iya zafin da anjima zai lafa.

To nan Lamiɗo ya kira Umaymah ya gaya mata.
Ita kuma ta kira Ummi ta gaya mata yadda Lamiɗo ya gaya mata,
ta ɗora da cewa.
“In sha Allah gobe zan biyo jirgi inzo.
Kuma ko ban samu jirgiba Haroon zai kawoni a mota, zanzo Ummin Jabeer hankalina yayi matuƙar tashi kan matsalar nan”.
Cikin kukan tausayi Aysha daketa ɗan bubbuga sawunta tana cewa.
“Wahyyy wahhyy”.
Tace.
“Eh gsky kam kizo, Umaymah ɗazu ko Hajia Mama da tazo saida tayi ta kukan tausayin Aysha”.
Katse kiran Umaymah tayi.
Tare da wucewa turakan Abban Haroon nan ta gaya mishi abinda ke faruwa.
Nan take ya bata izinin zuwa.

Sheykh Jabeer, kuwa sai ƙarfe sha ɗaya saura ya shigo gidan.
Lokacin kuma Ummi ta rufe ƙofar ɗakin Aysha sabida hanyar fita take kamawa.
To hakane yasa sam baiji motsin komaiba ya wuce Side ɗinsa.
Wonka yayi kana yayi nafilfilinshi sannan ya kwanta baccin.

Ummi kuwa da Aysha kwanan tsaye sukayi.
Aysha tana kuka tana zirgani.
Sai can gabanin asuba irin iskar sanyin asuba ɗin nan ta fara kaɗawane wani sassanyan baccin azaba da wahala ya saceta.
Hibba ma sai lokacin tayi bacci.
Nanne Ummi ta samu ta koma ɗakinta tayi al’wala.
Jin ana salla a masallacin ne yasa tace sai tayi salla taje ta tashesu kafin nan ta ɗanyi bacci kaɗan.

Bayan an idar da sallane.
Ta miƙe a hankali cikin magagin baccin da batayi ba, ta nufi ɗakin Aysha.
A hankali ta wuce bathroom.
Abun buƙatar yin wonka duka ta motso matashi kusa,
Hatta makilin saida ta matsa matashi bisa Brosh.
Sannan ta fito, a ta sunkuyo kan Hibba tare da cewa.
“Hibba! Hibba!! Muhibbat!!!”.
A hankali ta buɗe idonta.
Cikin sanyi tace.
“Je kiyi al’wala kizo kiyi salla sai ki maida baccin”.
Miƙa tayi a hankali tare da cewa.
“Ummi nayi salla”.
Jin hakane Ummi ta gane kenan tana fashin salla.

Kai ta gyaɗa kana ta isa inda Aysha take.
A hankali ta sunkuyo kanta tafin hannunta ta kife kan goshinta.
pit-pit haka jijiyoyin kanta ke harbawa.
A hankali tace.
“Aysha! Aysha!! Cikin sanyi tayi ajiyan zuciya mai tsawo tare da buɗe kumburarrun idanunta a hankali.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Ya jikin”.
A hankali tace.
“Alhamdulillah”.
Cike da jin daɗi Ummi tace.
“Masha Allah. Allah ya ƙara mana lfy, yanzu tashi kiyi wonka al’wala kiyi salla sai kizo kiyi baccin ko”.
A hankali tace.
“To”. Kana ta yunƙura zata tashi da sauri ta zaro idonta waje cikin tsoro take kallon hannun nata.
Ummi ma cike da tsoro take kallon hannun.
Ya kumbura yayi jazir.
Cikin tsoro da jin raɗaɗi cikin fata da naman hannun tace.
“Ummi kalli”.
Cikin danne fargabanta, dan kada ta razanata tace.
“Yauwa ba komai kinga abin cikin ya fito ko.
Tashi kije kiyi wanka kizo kiyi salla.
Kisha tea kafin nan ki konta zuwa sha ɗaya dai sarkin baka zaizo shida Lamiɗo.

Cikin sanyi ta miƙe tana mai kallon hannun ta nufi Bathroom ɗin.
Da ido Ummi ta rakata.
Ganin ta maida ƙofar ta rufe ne yasa.
Ummi juyawa durowarta ta buɗe wata doguwar riga ta ɗauko mata mai taushi hannunta guntu kuma tanada ɗan fadi da ɗan kwalinta.
Wondon irin mai tsayuwa iya guiwa nar ta fito mata dashi sai bra turare ta fesa musu kana ta ajiye mata su kan gadon.
Sannan ta fita ta nufi kitchen.

Ita kuwa Aysha, a hankali ta tsaɓule kayan jikinta, kana ta goge bakinta, fes sannan tayi wonka.
Saidai duk abinda takeyi hannun na gefe sabida tana jin yana ɗan zuƙa da tauna.
Wurin yin al’wala ne tayi ta zubda hawaye tana tausayawa masu hannu ɗaya.

Koda ta fito a bakin gado ta zauna.
Wondon ta saka, sannan ta zura doguwar rigar dake mai faɗice.
A hankali ta sa hannunta ta ɗaura ɗan kwalin a kanta a kaikaice.
Bra ɗin kuma, medashi tayi cikin wodurob.

Da kyar tayi salla, tana idarwa.
Ummi na shigowa da kofin tea a hannunta.
Amsa tayi tasha.
Ajiye kofin tayi tare da yin gyatsa a hankali tace.
“Alhamdulillah”.
Sannu Ummi tace tare da kallon agogon dake jikin ginin ƙarfe Shida da minti arba’in.
“To yanzu konta ni, bari in shiga kitchen inyi mana breakfast”.
Kai ta gyaɗa kana ta miƙe ta dawo, kan gadon ta kwanta.

Ita kuwa Ummi juyawa tayi ta nufi kitchen.
Nan ta samu Saratu tazo fara aikin sukayi.

Ita kuwa Aysha, a hankali ta buɗe idonta data lumshe, sabida jiyo zafin da ta kwana dashi daren jiya, yana tasowa a hankali take jinshi.
Ɗis-ɗas sai kuma ya ɗanyi shiru.

A hankali hasken rana ya bayyana a sararin samani.
Wanda haka yayi dai-dai da bayyanan ciwon da taji jiya, ya mamaye hannunta da jikinta da zuciyarta.
Wani irin yunƙuri tayi tare da tashi zaune.
Cikin zafi tace.
“Sheehhhhhhh Wayyo! wayyo!! wayyo!!! Ummi hannuna yana dawowa.”
Wani irin tsalle ta daka tare da miƙewa tsaye.
Cikin tsananin zafin da taji ya mamaye illahirin jikinta ne yasata, sakin wani irin kuka mai baiyana azabar da takeji.

Kife kanta tayi a jikin wodurob, tana bubbugashi tare da cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun.”

Da sauri Ummi ta fito daga kitchen ta nufi falon Aysha, jin Hibba na rabka mata kira.
Da sauri ta iso tare da cewa.
“Suhanallali!. Aysha hannun ne kuma”.
Da sauri ta ɗago hannun ta nunama Ummi shi, gaba ɗaya hannun rawa yakeyi kar-kar tamkar mazari.

Wani irin juyi tayi da ƙarfi tare da kife kanta jikin gini.
Tare da sakin shessheƙan kuka mai sauti, tana cewa.
“Wayyo Allah na, Wayyo Ummey na. Wayyo Bappa na, zan mutu”.
Sai kuma ta kuma muƙewa cikin azabar rawan jiki da alamun a gigice take, cikin rawan murya tace.
“Wayyo Allah na, Ummi ku kaini wurin Bappa na ku maidani gidanmu ku kaini wurin Ummey na”.
Ta ƙarishe mgnar tana wani irin tsastsafo zufa mai zafi.
Safa da marwa ta farayi tare da cewa.
Wayyoooooooo hannuna zai tsinƙe”.
Sai kuma ta juya a gigice cikin kiɗima da fitar hayyaci.
Ta nufi falo, sabida yadda rana ke ƙara zafi, haka ciwon ke ƙara tunzura da ruruwa.
Da gudu Ummi tabi bayanta tana cewa.
“Shatu! Shatu!! Tsaya mana”.
Amman ina kafin ta fito falon tama ita kuma ta isa babban falon.
Ganin hakane yasa Ummi da Hibba biyota a guje.
Da sauri Ummi tasa hannu ta kamo hannun ta, mai lafiyar tana cewa.
“Shatu ki nitsu ki tsaya ina zakije”.
Wani irin kuka ta saka mai cike da rauni hannunta ta fizge a hannun Ummi kana ta ɗaurashi tsakiyar kanta.

Dai-dai lokacin Sheykh ya turo ƙofar falon ya shigo.
Jamil da Jalal na binshi a baya,
Cikin al’ajabi ya zuba musu ido.
Jalal da Jamil kuwa da sauri suka nufi inda suke.
Shi kuwa shigowa cikin falon yayi ya ɗan tsaya gefen hanyar fita.

Ita kuwa Aysha aza hannunta tayi tsakiyar kanta, tare da kife kanta jikin gini tana bubbugawa tare da buga sawunta tana cewa.
“Wayyoooooooo Allah na wayyoooooooo hannuna. Ummey zan mutu”.
Ta ƙarashe mgnar cikin rauni, abin gwanin ban tausayi.
Hibba kam da Ummi tuni kuka sukeyi.
Hakama sara.
Ummi kuka takeyi tana cewa.
“Sheykh zata fasa kantafa zata yiwa kanta illa”.
Wani irin zabura tayi ta juyo a firgice sabida wani irin masifeffen ciwo da suka da raɗaɗin da taji yana ratsa jiki da jinin da zuciyarta.
Hannu tasa ta ture ɗan kwalin kanta, tare da yamutsa gashin kanta, fit ta fice cikin haiyacinta, wani irin juyawa da sassarfa tayi ta nufi hanyar fita tare da buɗe bakinta da ƙarfi zata kurma wani irin gigitaccen ihu.

Cikin wani irin zafin nama.
Da tamkar gilmawar walƙiya Sheykh yasa hannunshi ya kamo hannunta na hagu.
Tare da fizgo ta ya tsaida ita gabanshi.
Da sauri yasa tafin hannunshi ya rufe bakinta data buɗe da niyar kurma ihun.
Wani irin fizge-fizgen azaba ta farayi tana ƙoƙarin ƙwace kanta.
Tuni su Ummi sun cika falon da kuka ganin tamkar ta zauce.
Jalal da Jamil ma tuni idonsu ya cika da hawaye tab.

Ganin yadda take fizge-fizge ne.
Yasashi janta ya nufi Side ɗinshi da ita, amman ina abin ya wuce zaton mai zato.
Ganin yadda takeyine, yasa suna shiga cikin corridor’n.
Ya ɗan juyo ya kalleta jin yadda taketa fizge hannunta.
Idonshi ya tsura cikin nata,
da sauri tayi ƙasa da kanta, tare da ƙara sakin kuka.
Ganin haka ne ya cicciɓeta ya nufi bedroom ɗin shi kai tsaye.
Yana shiga ya sauƙeta tare da maida ƙofar ya rufe ya jingina da ƙofar yana kallonta.
Ita kuwa cikin kuka da fita haiyacinta.
Ta nufi bakin ƙofar gefen ƙofar ta fara buga kanta.
A hankali yasa hannunshin ya jawota gabanshi.
Ido ya zuba mata yana kallon fuskarta data kumbura tayi ja dan yawan kuka, ga zufa daketa tsastsafo mata ga jikinta daketa karkarwa.
Taune lip ɗin shi na ƙasa yayi tare dasa hannunshi kan ƙugunta ya zagayo ƙugunta da hannun nashi kana ya jata ya mannata da jikinshi tare da ruggumet….!

 

🤣🤣🤣🤣 Hahaha ko ya wannan salon jinyar zata kaya?

Ko meye Ba’ana zaiyi kan jinyar Shatu?.

To ina hayaƙin daya fita ya shiga a part’s ɗin masarautar Joɗa?

Anya kuwa Sarkin bakan masarautar Joɗa ba Magauta yakewa aikiba?

Shin Ɗalha mai gyaran tayis ma zuwa yakewa aiki?

Wacce nasara ce kan shiga tsakanin Sheykh da Shatu a zaman jinyar?

To wai ina lbrin Boleru ne?

Shin waye ne ya jinyaci su Junaidu wanne asibiti aka medasu?

Jalal da Jamil kam menene sana’ar su ko aikinsu?

Meyasa Shatu ke zargin Hajia Mama da Aunty Juwairiyya?

Shin menene gsky abinda Lamiɗo da Galadima ke son ƙullawa?

Menene manufar Arɗo Bani nayin kalaman da suka tunzura Lamiɗo har akayi gasar Shaɗi kuma har akayi aure?
Me suke son cimwa a masarautar Joɗa?

Su waye baiyannun da boyayyun magautan Sheykh da ahlinsa?

Me yasa Yah Jafar ke ji da Shatu?

Shin Jazrah da Batool zasu haƙura da burin ransu na son Sheykh?

Wai waye Sheykh ya gani a harami lokacin yin ɗawafin ban kwana?
Waye ya kuma gani a Airport?

To wai ina lbrin su Yah Giɗi, Seyo, Gaini? Yayun Shatu? Ina suke suna raye ko sun mutu!

Waye Boleru?

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button