Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 21

Sponsored Links

Zaro idanu tayi tace ina sukaje” yarfa hannu yayi yace “Iya Baba na tarar shima shigarsa gidan kenan” tashi tayi zaune tace “Ya jikinsa” murmushi yayi mata ya lura a duniya batada damuwar data wucce mahaifinta duk wata mgnrta Baba shigewa yayi dakin baccinsa ya ɗebo tarkacensa ya fito har yanzu tana inda yabarta ko miƙewa batayi ba suka haɗa idanu ya kanne mata ɗaya ya ajiye system ɗinsa da wayoyinsa ya matsa kusa da ita ya ɗagota ya zare mata mayafin ya tura hancinsa cikin gashinta ƙamshin sumarta yana kashe masa jiki tuni wata kasala ta fara saukar masa ya lumshe idonsa tare da ɗora bakinsa a kunnenta yana lasar bayan kunnen nata.
Wani yanayi me kashe jiki ta shiga daya nemi kaita ƙasa yayi saurin riƙeta tare da ɗagata ya zaunar da ita a kujera ya tsugunna a gabanta ya sanya hannunsa ya ɓalle bottle na rigarta ya sanya hannunsa cikin rigar ya kama nipples ɗinta idanunsa cikin nata, hawayen da yaga ya zubo mata ne ya sanyashi lumshe idonsa ya ɗora kansa a cinyarta yana sauke numfashi ta janye ta miƙe ta fice daga Parlourn bin bayanta yayi da kallo yana haɗiyar yawu babu yanda ya iya haka ya miƙe yabi bayanta da trolly ɗin ya buɗe mata mota ta shiga ya shigar da kayan yaja motar suka fice daga gdan.

 

Suna tafe tana ajiyar zuciya lkc zuwa lkc tana sharar hawaye sunyi tafiya me nisa ta sauke idonta akansa tace “Abdul-Ahad ina zaka kaini?” Taune lips ɗinsa yayi yana kallon titi ta cikin mirrow yace “Inda kika sani na kaiki” rushe masa tayi da kuka tace “Na haɗaka da girman Allah wanda ya halicceka ya halicceni yayimu jinsi jinsi kayiwa Allah ka barni a garinmu banason zuwa ko ina banason barin jahata…..”
Hannunsa ya ɗora a bakinta yace “Shine me kenan don kin bar Kano meye kike tsinta a Kanon” kukanta taci gaba da rerawa baya ƙaunar kukan nata saidai ya rasa kalmar da zai tausheta da ita ya fahimci Aneesah tanada taurin kai batajin rarrashi tsakanin Kano da Niger birnin Minna akwai tafiya yana sane yaƙi amincewa su hau jirgi har booking Kin Abdul’Mutallab yayi musu amma ɗan nasa yaƙi aminta da hakan.

Related Articles

 

Har suka isa Minna babu wanda ya ƙara yima wani mgn ya nufi wata unguwa me kyawun gaske tun daga hanya taga ana ɗaga masa hannu duk da glass ɗin motar baƙine hakan bai hanashi shima ɗagawa mutane hannu ba har suka isa gidan sarautar wani katafaren gini ne na asalin sarakai mai fasalin gaske yanayin iskar gdan ma me sanyi da ƙamshi ta daban ce batasan sanda wata ajiyar zuciya me ƙarfi ta ƙwace mata ba daidai lkcn da yayi parking wasu mutane da green ɗin uniform Suka zagaye motar bai damu da mutanen da suka zagaye motar Ba ya riƙo hannunta ya sanya hannu ya ɗago fuskarta idanunta sun kumbura sun kaɗa sunyi jawur saboda kuka yayi ajiyar zuciya yace “ki ware ki saki ranki banason damuwa”
Bata bashi amsa ba ya buɗe motar ya fita yayi gaba wasu mata suka buɗe mata motar suka riƙo hannunta yanayin gajarta da girman matan saida ya firgitata dukkanninsu babu me riga a jikinsu sai daurin ƙirji zaninsu iya gwiwarsu biyu ne suka ja mayafinta suka rufe mata fuska suna wani waƙa da yarensu da bata gane komai ta kuma shiga tashin hankali ta rushe da kuka me tsuma zuciya wannan wacce irin masifa ce take tunkaro rayuwarta a duniyarta kalar waɗannan mutane bata taɓa gani ba ga gajarta ga faɗi saikace kwaɗi”

 

Wani sashi na gdan suka nufa da ita duk inda suka wucce zubewa sukeyi suke gaisuwa da wannan yare nasu da bata fahimtar komai suna tafe ne itadai Aneey batasan inda take sanya ƙafarta ba a haka har suka isa inda suka nufa buɗe idanunta tayi da sauri saboda jin suna taka wata matattakala mamaki da tsoronta ya ƙari maimakon suna taka matattakalar suna sama su ƙasa sukeyi abin mamaki sai gasu sun bayyana cikin wata babbar fada me zubin kyawun gaske jan mayafinta taja ta sake rufe fuskarta don ta samu damar karewa gurin kallo.
Wata ƙofa taji an buɗe suka tsaya waɗannan mata suka zube a ƙasa suna kwasar gaisuwa wani dattijon mutum ne sanye da koriyar doguwar riga tanajan kasa fuskarsa da kansa duk farin gashi, tsayawa yayi a gabanta wata kujera ta bayyana ya zauna a kai sai lkcn tayi ƙasa ta durƙushe kamar yanda taga kowa yayi wannan dattijo yakai hannu ya dafa kanta tuni kanta ya fara juyawa ya soma karanto mata wasu surkulle da batasan me suke nufi ba wani jiri ya ɗebeta daga zaune kawai ta kife daga haka bata sake sanin meye yake faruwa ba.
Wai ashe wannan suma shine shaidar amaryar tazo da ƙashin arziƙi a camfinsu daga wannan lkc biki ya ɓalle raye² da kaɗe² da yanke² dabbobi abin kamar bazaa daina ba sai dare sosai Aneey ta farka ta tashi zaune da sauri tanabin jikinta da kallo cikin mugun mamaki taganta ɗaure da wani zani blue me ratsin ja da baƙi a ƙirjinta babu ko bra a ƙirjinta sai have vest a ciki itace ta riƙe mata nonon duk da kasancewar dama a tsaye suke wuyanta sanye da murzani nadi huɗu sai hannunta shima an ɗaura mata shi an cika matashi hagu da dama harda zobensa ƙafafunta dukka an ɗaura mata tsakiya hatta kanta shima duk kwalliyar wannan kwarankwacaman ne zubawa kanta idanu tayi ta mudubin dake facing ɗinta tana ƙarewa kanta kallo a fili tace.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button