Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 60

Sponsored Links

Zaune suke adakin itada Ihsan dake karanta mata wani novel tana kwance kan gado suka bude kofa suka shigo hakan yasa ta dago kai ta kallai shida Dr Om ne suna dan magana, murmushi Dr yay ya kalleta suna karasowa jikin gadon yace “how’s my patient doing” dan murmushi tamai tana kokarin gyara kanta akan filo, ya makala mata wani abu kaman camera karama a hannu sanan yace “Gud, I need you to do something for me, inaso kitashi ki tsaya naga” karamin tablet din hanunshi ya daddana sanan ya kalli Khaleel yace “dago min kanta” ahankali Khaleel ya dago kanta ya zaunar da ita, kafarta Om yanunamai hakan yasa ya sauko da kafarta kasa yana kallon fuskar ta, kallonta Dr yayi yace “now try and stand on your feet” dan dafa bango tayi Khaleel ya tsaya kusa da ita dan karta fadi ya sakin mata murmushi tare da nunama ta thumb dinshi alamun good, ahankali take daddafa bango harta dan tsaya amma aduke tana dan ciccije lebe sabida zafin datake ji, dadi Dr Om yaji yace “gud now try and raise ur head, stand straight, inaso naga inda yarage dabai warke bane acikin” fuzar da iska tayi tareda karasa mikewa ahankali ahankali Khaleel yace “sorry wife” Dr Kuma na duba tab din hanunshi, kasa daurewa tayi jin zafin yay yawa tacire hanunta daga bango tai luuu zata fadi Khaleel yatare ta da sauri hakan yasa ta fado kanshi wani irin shocking yaji tunda ga yatsar shi har brain dinshi sabida yanda hanunshi yakama kirjinta mistakenly, itama wani iri yarr taji duka karfin ta tasa tadan juyar da jikinta ta yanda abin ya sauka daga hanunshi ta lumshe ido tana sauke numfashi, yafi 3minute ahaka sanan ya kwantar da ita ahankali yaja bargo ya lullubamata yana kallon idonta dasuke alumshe, maganar Om ce yadawo dashi daidai yace “Khaleel zokaga” zuwa yay ya kalli tab din yace “kaga wanan mucus dinne keda inflammation dazaran ya sabe shikenan zata iya tana mikewa tana komi saimuyi focusing kuma a dawo da maganarta” rungume shi Khaleel yayi cikeda murna yace “Alhamdulillah, Dr am grateful” fita Om yay daga dakin yanata dariya.
Cikin sati daya cikin ya warke fess, takan tashi tai tafiya ahankali ta shiga bayi da kanta tai alwala tai salla, kuma takanci abincin dan har tuwo ranan nan Ihsan tamata Kuma taci sosai danyamata dadi, Khaleel ko babu wanda ya kaishi murna harda yima nurses kyauta.

Zaune suke adakin yana bata tea abaki kiran Om daya gani yasa ya dauka ahankali yace “okay” sanan ya katse wayar Ihsan yamika mug din tea yace “zoki bata am coming Om nason ganina” fuskar Islam ya kalla dake kallonshi da idanunta masu kama danamai jin bacci yace “am coming wife” fita yay yawuce office din Om shiga yay ya zauna, Om ya bashi wayansu hotuna yace “kaga wanan hoton damukama wuyan tane, babu any damage a vocal dinta so Ina suspecting infection ne awuyan dake hanata magana, yanzu abinda zanyi shine zan bata magunguna sanan zan sallameku inyaso every every week zaka dinga kawota chech up tunda for now ai babu wata matsala saita maganan ko” kasa boye murnanshi Khaleel yayi hakan yasa Dr yafara rubutu akan paper asibiti yace “ko aje ai amarce hmm” yagama rubuce rubucen ya mikamai yace “your discharge letter, I will be expecting you guys next week Thursday” ahankali ya karba yana murmushi sanan ya mikamai hannu sukai musabaha tareda kara godemai sanan yafita daga dakin, dakinsu ya shiga Ihsan dake zaune agefen gado tana nunama Islam wani hoto yazo ya daga yana jujjuya ta yana murmushi dariya tayi tace “Ya Khaleel menene wai?” murmushi yamata yace “an sallamemu” yay maganar yana kallon fuskar Islam ahankali yaga taja bargo ta rufe fuskarta tana murmushi dan wlh tagaji da asibitin sosai itama. Ihsan ya kalla yace “tashi kitayata shiryawa bari naje nakira taxi” fita yay daga dakin yana Satan kallonta, shiryawa tayi cikin dogon black skirt din kanti na jean tasa shimi fari tadaura sweater akai pink dan garin da sanyi sanan Ihsan tamata rolling black gyale sanan tasamata flat slippers, tahade yan littatafai da kayansu dasu tea dake dakin ajakan trolley ta kulle ta daga, shigowa dakin yay yana kallonta tana zaune akan gado kanta akasa hanunta rike da teddy daya saimata kallon Ihsan yayi yace “fita da jakan taxi din na waje” jan jakan tayi tafita shikuma ya karasa cikin dakin har gaban gadon ahankali ya daura hannayen shi akan nata ya dagata tsaye ya karbi teddy ya ijiye akan gado kasa daga kai tayi ta kalleshi, jinta tayi kawai ajikinshi ya rungumeta tsamtsam tareda kissing gefen wuyanta.
[6/25, 2:22 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button