Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 55

Sponsored Links

Ya sakin mata light kiss gudun karya ji mata ciwo sanan ya dago kai ya kalleta murmushi kwance akan fuskarshi, jiyay duk wani ciwon kan da yakeji yabace, sake kai hannu yayi ya share hawayen daya gangaro mata tareda girgiza mata kai yace “am here for you now, koma inane I don’t care saina kaiki koda bangon duniya ne inhar zaki sami lpy, zakiji sauki in sha Allah, stop crying…” dan kwankwasa kofa akayi Anty Hindu ta shigo takaraso inda suke ta kalli Khaleel sanan tace “Dr nason ganin ta, za’a wanke mata bakinne, kaga yanzu ma yadan warke tadan iya hadiye tea mai sanyi yau, amma tunjiya babu abinda take iyaci da bakin danyay jajir kaman kuna, bari nakaita” da sauri yatashi yakoma bayan keken yace “zankai ta Hajiya” dan hararan shi Anty Hindu tayi tace “banason gardama Muhammad, ba gamunan ba duka, salla yakamata kayi tukun yanzu sai asan abinyi, oya shiga bayi ka dauro alwala saika wuce massallaci, idan ka Ida aisai kazo kasamemu a dakin nata” tana fadin haka ta gungurata suka fita daga dakin, zama yay akan gado ya dafe kanshi tareda fuzar da iska shikadai yasan yanda yakeji, wayarshi ya dauko dake gefen gado yay dailing wani number yafi minti biyar yana magana aharshen turenci sanan ya katse wayar ya shafa kanshi yana fuzar da iska, ahankali yatashi ya shiga bayin dakin ya dauro alwala sanan yafito yafita daga dakin baiga su Abba awajen ba hakan yasa yawuce massallacin dake cikin asibitin.

Saida ya gama salolin dasuka hau kanshi sanan yafito daga masallacin yana tafiya ahankali dan yay nisa acikin tunani, mutum yagani yasha gabanshi ya tsugunna hakan yasa yadan tsaya yana kallonta ba karamin ramewa tayiba tai duhu sosai idanunta duksun fada ciki, fashewa tai da kuka sosai ta hade hannayen ta tace “dan girman Allah kayafe min, wlh shirin shaidan ne saida nayi sanan hankali na yadawo, am very sorry Mk, dan Allah na tuba kayafemin” tunda take maganan yake kallonta harta gama kara daure fuska yayi kaman baitaba murmushi ba ya matsa zai wuce takara tasowa tasha gaban shi tace “dan Allah, kaga Abba yakoreni daga gida idan kaima baka yafemin ba dame zanji, am very sorry, dan Allah inaso naga Islam na roketa gafarta please” hannu takai zata kama kafanshi hakan yasa yace “wlh if your hand should touch my leg, wlh saina ballasu tass, just stay away from me, kinason ki ganta sabida kibata another poison dinne?” cizon leben shi yayi cikin fushi ya nunata yace “stay away from me dan zan iya..” shiru yay yawuce dan koda minti daya yakara awajen zai iya mata abinda shikanshi bazaisoba, fashewa tayi sosai da kuka ta tsugunna awajen har wani irin ajiyar zuciya take saukewa sabida wahala, gashi ba halin ta shiga sabida Abba yamata mugun warning akan yin hakan.

Dakinta yay daidai lokacin Dr na fitowa hakan yasa yabi Dr office dinshi, zama yay ya nunamai waje ya zauna, kafin ma Dr yafara magana yace “Dr Inaso a sallamemu sabida gobe nakeson nafita da ita, UK 🇬🇧 zan kaita” murmushi Dr yayi yace “dama advice din danake so nabaku kenan, nan Nigeria 🇳🇬 bamuda kayan aiki inda bahakaba aida zamu iya komi, bari nabaka sallaman amma kadan bari anjima kadan saika tafi da ita dan ansamata ruwa sa karfi da kuzari dawasu allurai, kasan she is very weak sabida rashin abinci aciki” rubuce rubuce yay yabashi yace “ga Bill dinku nan kaje account kabiya” karba yay yatashi yafita daga dakin, account yawuce direct da POS yabiya, yaciro ATM card dinshi yabasu nan yabiya kudin komi sanan ya karbi ATM card dinshi ya maida wallet yabar wajen. Ahankali ya bude dakin ya shiga kowa na dakin Ammi na kan gado ta daura kanta akan cinyarta ta mikar mata da hannun da akasa ruwan tana shafamata kai ahankali dan bacci take, ajiyar zuciya yadan sauke ganin tana bacci sanan ya kalli iyayen nasu anatse yace “Abba zan fita da ita waje, gobe nakeso mutafi, and inaso Ihsan tarakamu, nariga nai magana da Omprakash babban Dr ne tun ina school achan na sanshi yace nazo da ita” Ya kalli Ihsan dake zaune tai zuru zuru yace “ke taso muje gida muhada kaya dagangan am going to the airport nai booking first flight to UK gobe” Ahankali Abban Islam yace “inada contacts din ambulance flight, medical transport gwara su, sabida incase of zazzabi ko wani abu suna tareda nurses da doctors dat will attend to the patient acikin jirgin, abokina ne pilot dinsu to inaga shizai fi koya kuka gani” Abban Yusuf yace “hakan yamafi kyau Alaji kamusu magana saimuyi handling komi” Ya kalli Khaleel yace “ku kutafi gida to kuhada kaya da duk wani abu dazaku bukata inyaso matan saisu zauna da ita” shida Yusuf ne suka fita Ihsan tabisu abaya.
Fita Abba yay daga dakin dan kiran abokin nashi kan maganan ambulance flight din hakan yasa Mum ta fuskanci su Abba ahankali cike da girmamawa tace “Alaji dan Allah kitayani rokon shi ya yay hakuri ya yafema Farida tadawo gida, bata dawani uba daya wuce shi, ina zataje yau kwana uku kenan daga yau ta kwana agidan wanan kawa gobe agidan waccan, nasan tai babban kuskure wanan abun datama yar uwarta amma tai nadama wlh sai neman gafara take, kaga yahanata tama shigo dakin nan balle tanemi gafarrar yar uwartata, dan Allah kuyakuri kuyafe mata Alhaji, yarinta da rashin hankali sukasa ta aikata wanan mummunar abin” takarashe maganan tana matse kwalla, ajiyar zuciya Abban Khaleel ya sauke yace “in sha Allah zamu mai magana, gaskiya hukuncin yay tsauri, ai hannunka baya rubewa ka yanke kayar korarta daga gida zai iya jefata cikin wani halakar, tunda dai tai nadama ta yarda tai kukkure ai shikenan komi ya wuce, ita kuma Allah yabata lafiya” yay maganar yana kallon fuskar Islam dake bacci abinta akan cinyar Ammi. Fita sukayi daga dakin hakan yasa Anty Hindu ta zubama Mum wani irin mugun harara, dauke kai Mum tayi tana goge ido.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button