Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 3

Sponsored Links

*YANCI DA RAYUWA*

©️®️Hafsat Rano

Page 3

Related Articles

****Karfe daya da rabi ya karasa wajen, sai da ya tsaya ya fara yin sallar la’asar sannan ya shiga meeting din. Hour biyu ya dauke su zuwa 4 suka gama ya sake wuce mosque yayi magriba wajejen hudu da ashirin sannan ya dauki hanyar gida. A kafa yake tafiya kansa rufe da hular jacket din jikinsa, ya dora headphone a kansa yana tafiyar sa a nutse. Mubarak ne ya tsai dashi, suka gaisa sannan suka cigaba da tafiya suna tattauna yanayin da aka samu na change of time na sallah and everything har suka karaso apartment dinsu. Shi Mubarak a 5th floor yake shi Kuma Rafeeq a 10th floor sai kawai ya bishi 10th floor din idan sukayi isha sai ya dawo at least ya rage zaman kadaitar da take damunsa.
Kamar kowanne lokaci bashi da matsalar abincin dan private chef ne dashi dan haka suna shiga suka tarar da komai a tsare ya gama. Zama Mubarak yayi a lounge din shi kuma ya wuce first floor in da bedroom dinsa yake ya chanja kayan jikin sa, sannan ya sauko sukayi dinner tare suka dan taba hira bayan sun yi sallar isha ya tafi. Da farko bashi da niyyar sake fita a ranar amma kuma yana da bukatar zuwa shopping gashi gaba daya week din zai zama so busy ne wajen tattare komai duk da babu abinda zai dauka sai yar karamar bag dinsa sauran kayan zai tattara su ya kai chan main house dinsu inda suke sauka sanda suna yara idan sun zo kasar. Duk da hakan kuma yana da bukatar gama komai kafin ya wuce din, shiyasa kawai ya kara dora jacket a kan kayan jikin sa, ya dauki wayarsa da wallet ya fito.
Yana tafiya a hanya Asim ya kira shi, a kullum idan Asim be kirashi sau biyar ba, zai kirashi sau uku. Har baya gajiya da kiransa abu kadan zai kirashi dan ko dazu da suna meeting yaga kiransa be dauka ba. Daga wayar yayi daidai lokacin da zai tsallaka dayan side din titin.

“Ina ka shiga ne?” Yana dagawa abinda ya fara ce masa kenan.

“As usual, mun shiga meeting din dana dawo gida kuma Mubarak yana nan shiyasa ban kira back ba, yanzu kuma na fito shopping.”

“Oh ok. Ya meeting din?”

“Not bad… As usual dai kawai.”

“Great, yanzu wanne ranar ka yi deciding tahowar? I’m thinking of buying a ticket for you.”

“Da ka taimaka min, but bari na koma na sake duba schedules dina, I will text you the date, sai ka siya min but inason Saudi air, zan fara tsayawa nayi Umrah first kafin na karaso. Ka duba date me layover kaman three days to 4days haka, sai kayi min applying e-visa.”

“Why not ka dawo sai muje daga baya?”

“No please, nasan idan na dawo zan zama very busy, kuma dai inaso yanzu din.”

“Shikenan, zan duba yanzu idan na koma gida.”

“Thank you.”

“Baka tambaye ni new girlfriend dita ta jiya ba.”

“Girlfriend?”

“Yes, wadda na hadu da ita last time muna waya”

“Ohh, shine har ta zama girlfriend dinka?”

“Ba zaka gane ba, da kyar nayi bacci jiya ina ta tunanin ta, har mafarkin innocent cute face dinta nayi.”

“Lallai, kila ma aljana ce.”

Ya fada tunanin sa na tafiya chan baya,duk ganin da yai mata da murmurshi a kwance saman kyakkyawr fuskar ta, waya sani ko itama aljanar ce? Ya tambayi kansa da kansa tunanin ta kadai na sashi jin shi so down.

_”no mutum ce, I can feel it.”_ ya sake bawa kansa amsa yana son assuring kansa da kansa.

“Allah ko?” Asim ya tambaya yana dariya. Murmushin yayi shima sannan yace

“Wasa nake maka, but kafi kowa sanin waye AJI, dan haka kabi komai a sannu.”

“I will try, dan da gaske ta kama min heart, gashi ko sunan ta ban sani ba, bare house number dinsu. Yau tun 6 na fito jogging ko zata wuce amma shiru.”

“Nazo supermarket I will call you idan na koma.”

“Ok.”

Yayi saurin katse wayar saboda wani irin zafi da zuciyar sa ta soma yi masa, a zahiri ba wai ya karasa in da zai je bane, ya yi hakan ne dan ya katse wayar, baya so Asim din ya fuskanci wani abu ya san shi sarai da saka damuwa a kansa. Ya dan dade a wajen har ya soma jin daidai,sai ya karasa ya siyo abubuwan da zai siyo ya koma gida. Yana zuwa shirin kwanciya yayi ya haye gado. Yana kwanciya sai wayar sa tayi kara, ya manta gaba daya be sakata a silent ba, dan duk ranar da ya kwanta da wuri irin haka toh a silent yake saka wayar dan yana so ya dan samu baccin kafin lokacin tashin yayi. Bedside lamp ya kunna haske ya gauraye dakin ya jawo wayar ganin sunan dake yawo a saman wayar yasa shi saurin mikewa zaune yana sakko da gaba daya kafafun sa suka taba kasa.

“Barka da dare AJI.” Yace cikin matukar kamewa da nutsuwa.

“Ka kwanta ne?” Ya tambaya kai tsaye

“Eh inaso na kwanta zuwa 2am sai na tashi akwai abubuwan da zan karasa.”

“Yayi, kun gama magana da Robin?”

“Eh mun gama,har ma yasa hannu.”

“Yayi… Kar ka kwanta kayi ta bacci, kayi abinda ya kamata.”

“In sha Allah.” Yace kafin yayi wata maganar ya katse wayar. Rike wayar yayi a hannu zuciyar sa na kuna. idan be manta ba, yau kusan sati biyu kenan basuyi magana ba, babu tambayar ya yake? Mecece damuwa ko matsalar sa? Duk babu wannan, business kawai da dukiya, sune kadai ne yaren da mahaifin sa yake ganewa, yana ganin sune kadai jin dadin rayuwar, a ganin sa bashi da wata matsala tunda suna da tarin dukiyar da ko mutuwa sukayi jikokin jikokin su ba zasuyi talauci ba, sai dai be sani ba, bature yace “the rich also cry.” Kuma duk dan Adam yana da life challenges nasa, sai dai na wani yafi na wani. Amma shi babu ruwan sa, be damu da wacce irin rayuwa yake shi kadai anan ba, be damu ya sani ba duk kuwa da yana da yakinin duk wani motsin sa a tafin hannun sa yake, duk kuwa da kin zaman da yayi a main house din su, yasa waye mahaifin sa, irin sanin da ake kira na ciki da bai, ya tabbatar yana da masu kai masa rahoton duk abinda yake yi, da duk wani motsin sa.
Fasa kwanciyar yayi, ya shiga photos din wayar sa, cikin fovourite folder dinsa, ya bude hoton da yayi mata daga nesa ranar karshen da ya ganta wanda shi kadai ne abinda ya ke dashi da yake rage masa zafin abinda yake ji akanta, duk kuwa da bashi da tabbacin ita din wacece.
Wani tsoro ne ya darsu a cikin zuciyar sa, har sai da yaji sanda zuciyar tasa ta buga da karfi. Da sauri ya mike tsaye yana kokarin karyata hasashe da tunanin zuciyar tasa, ya shiga furta duk adduar da tazo bakin sa

“Allah karka dora min abinda yafi karfi na Ya Allah, idan da alkhairi a taraiyar mu, Allah ka kawo mana komai cikin sauki.”

_”Idan tayi aure fa?”_

zuciyar ta sake dawo masa da wanchan tunanin. Da sauri ya shiga zagaya dakin, dan tunanin hakan kadai zai iya sashi a matsananciyar damuwa. Da kyar ya samu ya saita kansa, ya tattara kayan aikin sa ya sakko first floor dan shine kadai zai saka tunanin sa ya koma wani wajen daban. A saman sofa ya dora komai ya wuce dining area ya dauki mug a cikin glass display cabinet din dake dinning area din da wuce wajen da coffee maker dinsa take ya hada coffee ya dauko shi ya dawo ya zauna akan sofa din ya kunna system dinsa yana kurbar hot coffee din zafin sa na shigar sa. Tunawa da maganar da sukayi da Asim yasa shi shiga schedules dinsa ya duba ranar da zai kammala komai ya dauki date din ya tura masa ta facetime message ya kashe wayar gaba daya dan yasan sai ya kirashi yayi masa mita wadda be shirya mata ba.

*****

 

 

🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
08030811300

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button