Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 2

Sponsored Links

*YANCI DA RAYUWA*

©️®️Hafsat Rano

Page 2

Related Articles

*****Tun kafin ayi kiran farko ta tashi saboda tarin ayyukan da suke jiran ta a kitchen din gidan, a yanzu itace trusted cook da Hajiya ta amince da ita shiyasa abubuwan suka sake yi mata yawa gashi kusan kowa na gidan da abinda yake ci as breakfast, wanka ta fara yi dama tun kafin ta kwanta ta gyara dakin ta, ta fito da uniform dinta da school bag dinta ta ajiye su a gefen gado. Ana kiran farko ta fito zuwa kitchen din gidan domin ta fitar da komai ta gyara wanda zata gyara kafin a kira sallah, kasancewar aikin ya riga ya bi jikinta yasa take da mugun sauri, bata son abinda zai shiga lokacin karatun ta shiyasa ta tsara komai take yin sa da wurwuri ba tare da bata lokaci ba.
Karfe bakwai da rabi ta fito cikin shigar uniform dinta, white hijab da light blue riga da wando, sai I’D card dinta da ta makale a wuyan ta. Ta gate din baya duk masu aikin gidan suke fita dan haka kanta tsaye ta nufi gate din bakin ta dauke da adduar fita daga gida. Ba kasafai ta fiya haduwa da mutane ba a lokacin sai masu fita training suma ta san hanyar da take bi ta guje ma haduwa dasu, sannan da yanayi yadda unguwar take tsit ta manyan masu kudin kasar. Tafiya take a nutse kanta a kasa tana irga sauran subject din da suka rage mata. Bata ji tahowar sa ba, sai ji tayi mutum ya bangaje ta, a tsorace ta kalle shi, wani irin kallo yayi mata yayi saurin cewa

“I will call you back, naga wata fine babe.” Be jira amsar sa ba ya danna airpod din ya katse wayar yana mata wani silent kallo. Ganin haka yasa tayi gaba zata wuce yayi saurin shan gabanta

“I’m so sorry please, ban ganki ba waya ta dauke min hankali.”

“Ba komai.”

Tace da sauri ganin haduwar shi bata taba zata zai tsaya bata hakuri, bata kuma so a samu wata matsala har labari ya koma. Gaba tayi da dan sauri tunawar da tayi 9:30 zasu shiga exams gashi tana yin tafiyar kusan awa daya kafin taje in da zata hau taxi dan taxi basa shigowa unguwar. Tsayawa yayi rataye da hannun sa a bayan sa yana kallon ta, ta cigaba da sauri kamar zata tashi sama. Zai iya rantsewa be taba ganin me kyawun ta ba, wani irin musulmin kyau me matukar daukar hankali da fusga, yana tsaye har ta bacewa ganin sa, ya sauke ajiyar zuciya, yasan idan har a area din take zasu sake haduwa, nan kusa kuwa dan a da yana dan yin wasa wajen fitowa gudu da safe amma daga ranar zai maida shi kullum. Sai ya sake murmushi ya juya yana sake kiran Rafeeq
Yana zaune akan aikin da yake kiran Asim ya sake shigo masa, sai da ya ja siririn tsaki sannan ya daga

“Ina jinka?” Yace yana dan ture system din

“Sorry wallahi wata babe na gani, guy ka ganta kuwa?”

“Akan ta ka katse min waya?”

“Ba zaka gane ba, idan ban katse ba zata iya katse numfashi na.”

“Mts! Baka da aikin yi, in dai yaran Abujan nan ne, zaka bata ma kanka lokaci ne kawai.”

“Noo wannan daban ce.”

“Kai ka sani.”

“Allah kuwa.”

“Naji, ina muka tsaya a maganar mu?”

“Yadda dai muka ce ne, idan ka dawo sai mu ga abinda za’a kara kai, but komai na office din ya kammala.”

“Ok, karshen week din nan zan siya ticket in sha Allah, later bari na karasa wani aiki.”

“Alright, sai munyi magana. ” Suka ajiye wayar a tare. Sake matsawa yayi gaban system din ya dauki glasses dinsa ya saka ya cigaba da duba aikin.

Direct toilet Asim ya wuce ya sakar ma kansa ruwa sannan ya fito da shirin fita office ya wuce dining area, a saman d-table ya tarar da Anisa tana shan tea da pancake tana danna wayar hannun ta. Kusa da ita ya zauna cook din dake tsaye daga gefe ya matso ya shiga serving dinsa shi kuma ya maida kallon sa kan Anisa da ta cigaaba da danna wayarta kamar bata ga sanda ya zauna ba.

“Neesa?” Ya kira sunan ta

“Umm…” Tace a gajarce still idon ta kan wayar.

“Ba gaisuwa?”

Ture plate din tayi ta mike, ta sauka daga wajen ta wuce parlour ta zauna. Murmushi yayi kadan ya dauki fork ya shiga yin breakfast dinsa hankalin sa a kwance, ya riga yasan fushin da take, ba zai gaji da fada mata gaskia ba, dan yaga alamar kamar bata san in da yake mata ciwo. A nutse yayi breakfast din abincin na masa dadi sosai shiyasa baya taba missing, baa taba samun cook irin wannan lokacin ba tunda ake yin su a gidan. Tashi yayi bayan ya goge bakin sa da tissue ya sakko zuwa parlourn ya zauna a gefen ta.

“Mummy fa?”

“Gani nan.” Tace tana tako stairs din. Mikewa yayi da sauri yana murmushi

“Mum good morning.” Yace yana karasawa ya jira ta gaban staircase din ta sakko, hannun sa ta kama maimakon ta amsa fuskarta dauke da murmushi.

“My son, ka tashi lafiya?”

“Lafiya kalou ma.”

“Good, ka gama shiryawa ne?”

“Eh mummy, zan wuce office.”

“Ok… Karfe biyu jirgin baban ku zai sauka, dan haka sha biyu tayi musu a airport din su jira shi, kasan baya son delay.”

“Ok ma, zan yi handling komai.”

“Good boy, sai ka dawo.”

“Ok.” Yace yana yin gaba yana kallon aneesa da ta ki kallon sa, har yayi gaba sai ya tsaya

“Mum…”

“Uhum?”

“Feeqq zai dawo next week ko upper week.”

Da sauri ta kalle shi, aneesa ta dan zabura itama jin abinda yace, idon sa akan su dukka biyun yana karantar yanayin da suka shiga.

“Da gaske Ya Asim?” Aneesa tace fuskarta na fadada da murmushi, banza yayi mata kamar be ji ba, ya cigaba da kallon Mum din yana jiran yaji me zata ce

“Me yasa zai dawo? Ya gama abinda ya kamata ne?”

“Yes ya gama, wani aiki ne ma ya rike shi, amma next week zai dawo gaba daya.”

“Oh ok, Allah ya kaimu. Ka wuce office karka makara.”

“Ok ma, sai na dawo.”

Yana fita ta juya wajen Aneesa ta kai hannu ta rankwashe mata Kai tana hararar ta

“Kanin ubanki zai dawo ai, dole ki firgice.”

“Moommmmm.” Taja sunan ta, tana bubbuga kafarta

“Sai na kakkarya kafar na zubar idan wannan iskancin zaki yi, ki kama kanki tun kafin ranki ya baci.”

Tashi tayi tana bubbuga kafa ta haye saman. Tsaki taja ta zauna ranta na baci, ta tashi da good mood amma wannan labarin ya bata mata rai matuka. Da kyar tayi breakfast ta fice daga gidan dan tana so ta gama abinda zata gama kafin dawowar Alhaji.

***Paper daya sukayi 9-12. Tana fitowa bata jira kowa ba, ta nufi gate dan bata so ta bata lokaci musamman lokacin nata da yake a tsare, dan haka bata da lokacin batawa. Tana so taje taga babanta, ta duba jikinsa duk da ko jiya sunyi waya ya kuma kwantar mata da hankali, amma dai still tana son ganin sa. Weekend zata roki masu gidan taje ko na awa daya ne, hankalin ta zai fi kwanciya.
Kamar yadda ta saba tana dawowa sallah kawai take, ta wuce kitchen hakan tayi yau ma, cikin shigar uniform din kamar kullum, duk sanda tasa sai ta tuna bayanin da masu gidan sukayi mata farkon zuwan ta

_”Wannan uniform din shine yake banbance masu gida da yan aikin gida. Dan haka ya zama dole ki saka su, rashin sakawar na iya jawo babbar matsala.”_

Har ta mike sai ta sake cewa

_”Bana bukatar ganin fuskarki, dan haka duk sanda zaki shigo part din nan ki tabbatar kin rufe fuskar taki.”_

Da sauri ta amsa da toh, bata da matsala da hakan, idan dai zata tsira da aikinta, zatayi komai, dan haka bata taba damuwa ba, ko kadan. Babban burin ta, mahaifin ta ya samu lafiya, ita kuma ta samu ilimi, in dai ta samu wadannan abubuwan guda biyu, burin ta ya gama ciki.
Yadda ta saba aikinta, haka tayi yau ma, ta riga ta horu matuka har bata jin wahala ko gajiyawa, idan ka cire karatu babu wani abu da yake sata farin cikin kamar ta ganta a kitchen tana dafa abinci, yana daya daga cikin abinda ba zata taba mantawa dashi ba a zaman ta da Hajiya Maryam, ta koya mata girki sannan tayi sanadiyyar zuwan ta gidan da ko a mafarki bata taba tunanin rayuwa a cikin sa ba.
Ba ita kadai bace me aiki a gidan, suna da yawan da ba zata iya tantance su ba, sai dai tana cikin masu muhimmanci a gidan, shiyasa aka ware musu bangare na musamman, suke rayuwa sannan take karatun ta, wanda shine a matsayin rabin kudin aikin ta, rabin kuma yana tafiya ne wajen neman lafiyar mahaifin ta, mafi soyuwa a gareta. A gajiye ta dawo dakin, sai ta kwanta lamo a saman gadon cikin kadaici. Baka da ikon zuwa wajen wani bare har ku samu doguwar tattaunawa a gidan, hakan dokar gidan ce, shiyasa babu ruwan wani da wani musamman ita, dan sauran suna haduwa wajen karba abinci, ita kadai ce take ci a irin wanda ta dafa dan haka bata da wata alaka dasu. Hakan ya kara yawan rashin maganar ta, ko a makaranta da wuya kaji bakinta idan an hadu ana hira.
Sai da tayi la’asar sannan ta taci abincin, ta sake komawa ta dan kwanta kadan kasancewar bata da school gobe saura exams biyu su gama gaba daya, tana kwance har lokacin shiga kitchen yayi ta mike ta rufo dakin ta nufi kitchen din.

***Yana zaune a parlourn yana kallon champions league final, tunda ya dawo daga office be fita ba saboda yana son kallon ball din. Wani tunani ne ya fado masa, ya tashi da sauri ya nufi kitchen din. A kofar ya tarar da Ben ya matso da sauri

“Did you want anything sir?”

“No, thank you.” Yace ya wuce kitchen din, handle din ya kama ya murda sai yaji shi a rufe. Jin an taba kofar yasa ta fasa cire nikaf din ta tsaya tana jiran ayi magana.

“I can help you sir.” Ben ya sake matsowa, sai yayi knocking kadan a kofar

“Open it.”

“Ok.” Tace da sauri ta bude. Shine a gaba yana kallon cikin kitchen din, idanun nan nata da ya gani jiya su suka sake masa togaciya, ya zuba mata nasa idanun yana son gano ina ya san su? Da sauri ta sauke kanta kasa cikin ladafi tace

“Good evening sir.”

“Thank you.” Yace yana wucewa ciki, be san me ya shigo dashi ba, kawai yaji yana son shigowar ne, voice dinta yanzu ya sake shigar masa kai ya saka shi tunanin ina ma? Tsayawa yayi jikin Iceland din kamar me neman wani abu, sai kuma yace yana nuna fuskarta

“I don’t like this thing, remove it.”

Diriricewa tayi jin abinda yace, jikinta ya fara rawa. Dan jim yayi ganin yadda ta rude, sai kuma ya tuno abinda Aneesa tace masa jiya

_”Rules din Mummy ne.”_

Yasan halin Mum dinsa, zata iya sacking dinta akan taka dokar da ta kafa mata.

“Don’t.” Yace mata da sauri yana yin hanyar fita, sai da ya kai kofar sannan yace

“Don’t lock it again.” Ya fice ba tare da ya sake waiwayowa ba.
Yana fita Mummyn na fitowa daga hallway din da zai sadaka da part din AJI.

“Kana bukatar wani abu ne?” Tace ganin ya fito daga kitchen

“Na samu ma.”

“Ok, next time ka kira helps din nan suyi maka, bana son kana shiga kitchen da kanka.”

“Ok Mum, zanyi.”

“Good, idan Son ya siya ticket din sai ka fada min date din, kasan ba zai taba fada ba. Shekara biyu kuma ba kwana biyu bace ba, dole ne ayi masa tarba me kyau.”

“Ok ma’am, zan kirashi idan na gama kallon ball, idan ma be siya ticket din ba ni zan siya masa kawai, dan bana so ya kara ko kwana daya ne. I need him a kusa, more over aikin yana neman yi min yawa.”

“Yayi.” Tace tana yin gaba takaici na neman kai ta kasa.

 

🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
08030811300

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button