Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 26

Sponsored Links

XXVI…
(26)

*Munayamaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank. Evidence of payment to 07082281566 (Dan Allah idan baki shirya siya ba, don’t chat Me)*

Doctor Abbas Yace “Masha Allah, Allah ya raya mana ita”
A hankali ya shiga yi wa jaririyar adhan a kunnen dama da iqamah a kunnen hagu kamar yadda Annabi saw ya koyar, ya hango dabino dake wani kwalba a office ɗin doctor Aaban din, ya nufi wajen ya dauko ya tauna hadi da latsa wa yarinyar a baki, ta shiga tande bakin ta.
Barrister Abrar dake kallon su tun dazu ta yi dabarar goge kwallar daya zubo mata, bawa baya wuce ƙaddara sa, amma taso wanna ya ta zo a yar halak, ta kuma yi sha’awar dama yar ta Abbas ce, domin shi ya dace da amsa sunan Uba ga wannan jinjirar.

“Babu wata matsalar a tare da munayan ko?” Wanna karon ya fada yana kallon doctor Aaban.

“Toh Ta karu an mata dinki, amma babu wata matsala in sha Allah”

“Toh alhamdulillah” doctor Abbas ya kara furta wa fuskar sa da murmushi domin a hakan ma yaji dadi, saboda yanda munayan ke da hawan jini ga karancin shekaru bai taba tunanin abubuwan zasu zo da sauki haka ba.

Yarinyar nan acici za’a yi, yanzu za’a samo mata ko ruwan xamxam ne ta Fara sha” barrister ta fada tana dariya hadi da kallon yanda jaririyar ke shan hannun ta sai lalube take da bakin ta.

Doctor Abbas shima yayi dariya da cewa”karbe ta, bari na fita na samo mata ruwan zam zam din”

“Toh angode” barrister ta fada tana karban ta.
Doctor Abbas ya juya ya fita.

“Pure heart na yiwa Junior kamun yarinyar nan, she’s so cute wallahi” ta fada tana taɓa kumatun ta.

Doctor Aaban ya mata wani kallo, ta kwashe da dariya, yayi murmushi yana girgiza kai.

Doctor Abbas ya dawo daga siyo xamxam ɗin, ya haɗa da *Madarar infant* cikin kankanin lokaci barrister Abrar ta haɗa wa babyn zam zam ɗin a feeder, tas yarinyar ta shanye, tana neman kari, ta saka ta a kafada tana jijjiga ta.
Doctor Abbas Ya karbe jinjirar a hannun barrister ya zauna ya shiga yi mata hotuna kala kala, ya ƙiyasta irin farin cikin da Shakur zai ji idan yaji labarin haihuwar munayan.

Ya mayar Wa barrister Abrar yarinyar, kana ya shiga manhajar WhatsApp, hoton daya fi kyau, ya kuma fito tar ya tura wa Shakur da
caption din

_munaya has put to bed(a baby girl)_

Bayan ya tabbatar da cewa sakon ya shiga kana ya yi offline.
Daidai lokacin aka shiga kwankwasa kofar office ɗin, doctor Aaban ya bada izinin shigowa barrister Hanan ce da ya’yan ta hudu hadi da miemie, Hammad da Junior, su miemie suka yi ihun murna suka zagaye barrister, Kowa so yake ya taba babyn, Junior kam hannun babyn ya kama fuskar sa da murmushi. Barrister Hanan tace “ina kiran wayar ki bakya dagawa, sai fa dazu na tuna ashe kin ce min wayar tana gida, mun shirya tahowa tun dazu sai nayi baki ina take yanzu?”

“Tana dakin hutu, sannu ku da zuwa” barrister ta Abrar ta fada.

“Yawwa sannu, ina wunin?” Tayi jam’in gaida su.

Duk suka amsa, ta karɓe babyn a hannun barrister Abrar tana fadin “masha Allah da balarabiya” suka yi dariya, kana ta kara da cewa “Allah ya raya mana.
Da “Ameen suka amsa.
“Anty muyaya, anty muyaya” Junior ya fada Domin hakurin rashin ganin munayan sa Ya ƙare.
Yanda yake kiran munayan na basu dariya, suka dara.
Doctor Aaban ya mike yace duk su tafi dakin da munaya take, cikin doki su miemie suka yi gaba, doctor Aaban ya bude musu kofar dakin da munaya ke kwance bayan ya ja wa su miemie kunne kan kada su yi hayaniya, nurses dake dakin suka mike, cikin bin umarnin doctor Aaban suka fita, munaya da bata jima da tashi ba ta bude gajiyayyun idanun ta, ta shiga bin kowa da kallo, a karshe ta sauke kan hannun barrister Hanan dake ɗauke da babyn, idanun ta ta tsayar cak tana kallon bayan babyn kasance a kafada Hanan ɗin ta ɗora ta, ta rufe idanun ta wasu hawaye Masu dumi suka zubo ta gefe da gefen fuskar ta, duk suka shiga yi mata sannu cikin kulawa, ta rasa na wa zata amsa, kawai ta shiga jinjina musu kai, wani irin zafi take ji a Kasan ta ko kwakwaran motsi bata son yi, kasusuwan ta ciwo suke mata,
Barrister Abrar ta karɓe jinjirar a hannun barrister Hanan ta taka a hankali zuwa gaban gadon munaya, a hankali ta ɗora mata jinjirar a kan kirjinta, munaya bata san meye sa ba, duk wani tsana da take ji a kan babyn yana barin kirjinta a sa’ilin data ji dumin yarta, tausayin kansu ya kamata, ta ɗaga hannun ta mai dauke da cannula ta daura a bayan babyn, wani mugun kuka ya kufce mata, ta shiga rera shi, Ita ma babyn sai ta canyara kuka, suka shiga yi ita da munaya, Junior ma ya matso jikin gadon ya fara matso hawaye yana kiran “anty muyayaaa”hakan ya kara karye zuciyar munaya sautin kukan ta ya karu.
Cikin sauri barrister Abrar ta ɗauke yar a jikin ta, ta mikawa barrister Hanan, kana ta zauna ta ɗora kan munaya a cinyar ta ta shiga bata baki, tausayi ya sanya doctor Abbas barin dakin, da kyar tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, mijin barrister ya kara duba ta ya tabbatar da komai lafiya, yayi Mata fatan samun lafiya su barrister suka amsa shima ya fita. Dakin ya rage barrister Abrar da Hanan da Kuma ya’yan su.
“Anty muyaya” Junior ya ƙara fada ganin ko kula shi bata yi ba.
Ta kalle shi da jajayen idanun ta ta riko hannun sa cikin nata amma ta gagara furta komai.

“Hmmmm Ni bana manta na kawo muku abinci ba yana mota, barin je na dauko” barrister Hanan ta fada tana mikewa hadi da mikawa barrister Abrar babyn.

“Anya wanna mantuwar taki ta lafiya ce kuwa, kodai kodai?” barrister Abrar ta fada Cikin tsokana.

Barrister Hanan tayi dariya sosai tace “toh ba komai, yar sharri kawai”

Itama barrister Abrar dariya tayi ba tare da tace komai ba.

Babu jimawa ta shigo da babban basket mai dauke da warmer’s, sai madaidaicin flask, ruwa, drinks, da kayan tea a ciki.
Ta zuba wa munaya Farfesu ta kuma haɗa mata tea mai kauri.
Ta kalli barrister Abrar tace “ga abincin ku har ya Aaban, na san baku ci komai ba tun safe”

“Wallahi Kamar kin Sani, kin kuwa kyauta”
Ta nufi munaya ta taimaka mata wurin kishingid’a tana fadin
“kina yi a hankali kin ji ko? Akwai dinki a jikin ki” munaya ta jinjina mata kai tana cizon labbanta da suka kara jaa.

“Gashi ki daure ki fara shan tea din” ba musu munaya ta karba, ta shiga sha a hankali duk da baƙin ta baya so, amma cikin ta is so empty.
Ta sha Fiye da rabi kana ta dire sauran, barrister Abrar ta ce taci Farfesu din, kaɗan ta iya ci ta ajiye, tana sauke rarrarauniyar ajiyar zuciya. Barrister Abrar ta bawa babban dan Hanan da miemie warmer da abin sha tace su kaiwa su doctor Aaban. Ita ma ta zuba taci nata.
Babyn ta fara kuka sosai tana neman abinci, duk da akwai Madara amma ita barrister Abrar tafi son babyn ta fara shan Mama domin a matsayin ta na uwa ta san amfani da alfanon da maman uwa ke da shi a jikin babyn ta musamman na farko irin wanna.
Ta kalli barrister Hanan dake jijjiga babyn tace “ki bawa munaya ita” munaya ta karɓe ta, a hankali ta tsurawa babyn ido, mugu mugun so da bata san daga ina ba na jinjirar na shiga ko wani huda na gashin jikin ta, Amnah is back, ta san cewa her younger sister as gone for ever, but she will name is innocent soul da take kallon after Amnah, sunan Amnah dinta zai cigaba da existing kamar yadda soyayyar Amnah ke manne a zuciyar ta, ta cigaba da kallon yanda babyn ke ta fafutikar neman abinci da baƙin ta…
Ba tare da ta lura ba har barrister Abrar ta zo gefen ta, cikin lallashi tace “bata Mama ta sha munaya”
Munaya ta fito da manya Manyan idanun ta waje tamkar zasu fado, cikin rawar murya tace “Mami bazan iya ba” sai hawaye suka zubo a idanun ta.

“Zaki iya munaya kin ji ko?” Barrister Hanan ta fada cikin tausayin ta kana ta shiga gaya mata yanda shan Mama musamman na farkon nan ke da amfani a jikin jariri, da kyar suka iya convincing munaya Kafin ta yarda zata shayar da jinjirar, da taimakon barrister Abrar munaya ta sanya wa babyn Mama a baki, cikin wani sauri yarinyar ta kama ta fara tsotsa, wani zafi ya ziyarci ƙwaƙwalwar munaya, ta yarfe hannu, su barrister suka shiga bata baki kan ta daure, zai daina zafin, wasu hawaye suka zubo mata har ya digo a kyakkyawar fuskar babyn, munaya ta saka yatsun hannun ta wurin ɗauke hawayen, bayan wasu mintuna zafin ya ragu har kwakwalwar ta na iya jurewa, ta sauke numfashi, tana kallon yanda babyn ta ɗora hannun ta kan maman ta yan madaidaita, ta lumshe idanun ta tana ƙara rike yar da kyau a jikin ta.

Kiran wayar doctor Abbas da aka yi ne ya katse hirar musu da suke da doctor Aaban, *AA Shakur* ya gani a rubuce, ya saki murmushi domin ya tabbata ya ga abinda Ya tura masa ne ta WhatsApp.
Ya daga wayar yana karawa a kunnen sa, cikin wani doki kamar Shakur zai shigo ta cikin wayar yace “doctor! Yanzu nan na hau online na gani, ya Allah na gama mace wa a soyayyar yarinyar nan tun kafin na ganta I’m so so happy wallahi, Allah ya raya mana, ina ta kiran munaya but she’s not picking, ina fatan tana lafiya babu wata matsala a tare da ita ko?”

Doctor Aaban yayi karamar dariya kana yace “munaya is fine, muna asibiti Ina tunanin kuma ta bar wayar ta a gida.”

“Yanzu zan taho a wani asibiti kuke?”

Doctor Abbas ya fada masa, Shakur yace “na ma san asibitin, i will be on my way now”

“Alright sai ka zo” doctor Abbas ya fada yana sauke wayar daga kunnen sa.

Daga can bangaren kuwa Shakur ya fara biyawa supermarket yayi siyayya masu yawa wa babyn da munaya kana ya karasa asibitin.

Ya kira doctor Abbas Yace masa yana waje, doctor Abbas ya fito haraban asibitin yana bashi hannu suka yi musabaha kana ya mai iso zuwa dakin da munayan ke ciki.

Doctor Abbas ne a gaba, Shakur ya mara masa baya bakunan su dauke da sallama,
Munaya na kwance wannan karon, ta kalli su, duk maza biyun suka mata murmushi, kana Shakur ya hango babyn dake kwance gefen munaya, ta ɗauke hankalin sa cikin wani irin sauri ya karasa ya dauke ta, sai ya ga tama fi kyau a fili, abin kamar almara, wai yau shi ke rike da gudan jinin dan’uwan sa Maleek? Ya kara rungume yar da kyau yana jin son da yake wa baban ta na reflecting zuwa gare ta, farin cikin sa ya gagara boyuwa, ya kalli inda Munaya take, ya ga doctor Abbas na mata ya jiki, gaba-daya babyn nan ta dauke masa hankali, amma da niyyar fara duba munaya ya shigo.

“Sannu munaya, ya jikin ki?”

“Da sauki” munaya ta amsa tana yin kasa da idanun ta.

“Sorry, Allah ya baki lafiya kin ji” duk yan dakin suka amsa, jin murya mabanbanta ya sa ya ankara da cewa akwai mutane a dakin.

“Au barrister kuna nan ashe?”

Barrister Abrar tace “Ina zaka gan mu Shakur, y’a ta tafi da hankalin ka”

Yayi dariya cikin jin kunya, suka taya shi kana ya gaida su, suka yiwa juna Barka da samun karuwa, idanun munaya a rufe tamkar mai Bacci amma ta na jin duk abinda suka cewa, bazata taba manta hallacin barrister Abrar da iyalanta ba, ba Kuma zata taba manta na doctor Abbas har ma da Shakur ba, hakika sun nuna mata so da kulawa, Irin na dangi, wanda she will forever be grateful, kawai tayi imaging cewa bata hadu da su ba ƙaddara nan ta fada har ta haihu da ya zata yi da babyn ita kadai? amma dukkanin su suna nan domin ta, yau da yake ranar Sallah kowa na gida wasu kuma na zumunci amma sun kashe komai na su suna tare da ita a asibiti, how on earth will she ever forget this?

Sai bayan magrib Shakur ya mike domin tafiya, yace wa yaran dakin su zo su taya shi daukan abu a mota, yaran suka biyo shi, sau biyu suna zuwa suna dawowa kafin kayan dake bayan motar ya kare, basu yi mamakin kayan ba, domin sun san cewa Shakur zai iya aikata fin haka, Allah ya bashi wata zuciya ta zinare mai wuyar samuwa.
Ya kara zuwa inda yarinyar ke kwance ya sumbaci kamatun ta, ya kalli munaya yace “munaya i will take my live now, take care of yourself kinji, gobe zan dawo”

“Nagode ya Shakur, Allah ya biya ka da aljanna” ta furta a hankali cikin rawar murya wanda baya tunanin wani a dakin ya ji bayan shi saboda yanda Muryar ta tayi bala’in sanyi.

“Ameen thank you Allah ya kara miki lafiya, toh Ni zan tafi” ya karasa da yiwa su barrister sallama.

“Toh an gode sosai Shakur, Allah ya kara budi”

Yayi murmushi kawai kana ya fice daga dakin, domin bai ga abin godiya ba, tamkar kansa yayi wa, bai san ina doctor Abbas ya shiga cikin asibitin ba, tun dazu daya bar dakin, ya daga waya ya kira shi, hadi da sanar masa ya tafi.

Ya shige motar sa, kana ya shiga hoton nan da doctor Abbas ya turo masa dazu, ya danna zuwa status, a caption ya saka emojin heart da jini, ya kashe datar sa, kana ya tada mota ya fice daga asibitin.

_10:02pm_
Bayan ya gama dukkanin wani abu daya zame masa al’ada a ko wani dare ya hau gadon sa ya kwanta yayi pillow da karfaffan hannun sa, ya tsura wa hadadden pop’n dake saman dakin ido tsawon wasu mintuna, da alama nazarin wani abun yake, ya sauke ajiyar zuciya a sa’ilin da hankalin sa ya dawo jikin sa, ya mirgina, hannun sa ya danne wayar sa ya dauke hannun hadi da daukar wayar, duk da is not a WhatsApp fan sai ya dade bai shiga app din ba, Amma a wanna daren yaji yana sha’awar shiga, messages masu yawa suka shiga shigo masa, ya ajiye wayar tsawon mintuna biyar kana ya sake ɗaukan wayar ya ga sakonnin da suka shigo sun kai almost 3k, bai bi ta kan su ba, ya shiga bangaren status, status ɗin Shakur ya gani a farko, daga dan circle din nan na status yake kokarin gano menene Shakur ɗin ya daura, domin hasken abun ya ja hankalin sa sai dai ya gagara ganowa, kamar zai wuce sai kuma ya danna ya shiga, numfashin sa yayi wani irin seizing a lokacin daya sauke idanun sa kan kyakkyawar jaririyar nan cikin kyakkyawar shiga, idanun ta na rufe, ya ga bakin ta ya dan fadada da irin murmushin da jarirai ke yi, idanun sa ya sauka kan curling hair ɗin ta daya dan fito ta Dalilin hular daya zame kadan, idanun ta kawai ne bai gani ba, ya kara sauke idanun sa kan hancin ta mai kyau, karamin labban babyn da yayi pinkish ya tsura wa ido, tsaf irin na sa, zuciyar sa ta buga domin wanna babyn, lalle baya bukatar a masa bayani, wanna gudan jinin sa ne, yar sa ce. Sai a yanzu yayi nadamar furucin sa da yace ayi aborting babyn, da haƙa zai rasa wanna cute innocent baby din? Lalle daya tafka babban asara, ya lumshe idanun sa, wani so na yarinyar nan na shiga jinin jikin sa, yana bin jijiyoyin sa, ji yake kamar ya ganta a gaban sa yanzu domin yaji dumin ta, ya bude idanunsa da suka dan Kada ya cigaba da zooming hoton, amma sai ya ga kamar WhatsApp na hana shi kallon hoton yanda yake so, dan haka ya saki hoton ya dawo yanda yake kana ya danna screenshot, ya fita daga WhatsApp ɗin ya koma gallery din sa ya shiga hoton, ya cigaba da more kallon sa, different thoughts running his mind, a hankali ya motsa labbansa, tamkar jaririyar tana gabansa ne yace “You are the precious jewel I have ever laid my eyes on, rayuwa ta na da matuƙar amfani a gare ki, hakan yasa yake da amfani a tare da ni ma, zan kasance tare dake, i will give you the best, so that you will grow up to be the best in life.” Yana matukar jin takaicin soyayyar sa da bata samu ba tun tana ciki, amma taya zai bata soyayyar bayan baya muradin kasancewa ko ganin wacce ta kawo ta duniya?
Sai da misalin ƙarfe ukun dare ya iya dauke idanun sa da suka yi matukar ja daga kallon screen din wayar sa, har wani yaji idanun ke masa, a kuma lokacin ne ya motsa daga zaman da yayi kamar gunki, ya kwanta hadi da rufe idanun sa.

The game has begin…
Wasan ya soma readers, team Maleek, team munaya, team Shakur, Abbas, kai har ma da Sa’adah 😂 how market?😉🙃

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button