Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 15

Sponsored Links

MIJIN MALAMA
Paid book ne.
Book 1 and 2 1kne
0811923761616
Maganganun Imran su ka yi wa Majeederh dirar mikiya a kunne. Duk yadda take so tayi shiru ta kuma daure amma har zuciyarta ta kasa yin hakan gani take da zarar Imran ya fasa aurenta babu wanda ya yi saura zatai ta tabbata a gida. Majeederh ta runtse Idanunta a hankali cikin muryar dake nuna zallar abin da zuciyarta ke buƙata ta ce “Imran ba tsofa na yi ba, am just 20, na fi kowa kyau a gidanmu” ta ƙare maganar tana sanya duka hannunta tare da dafe kanta dake juya mata tana ganin komai bibbiyu. Imran ya miƙe ƙafafuwan a saman office ɗin shi idanunsa buɗe cikin isgili ya cewa Majeederh. “Tsari na ne haka, ina son auren macen da bata haura sha bakwai zuwa takwas ba, lokacin da na zo neman aurenki wanne irin rashin mutumci ne ba a nuna mini ba? Ko an faɗa miki ke kaɗai ce mace Majeederh, ki je kici karatu daman ni wayewar ki tsoro take bani karatunki ya yi yawa” ya juya kaɗan sbd ya ƙara sanyawa zuciyarta dafi, dafi irin wanda ta sanya masa, domin har ranshi yana ƙaunar Majeederh a shekaru biyun da suke shige “Ki roƙi Allah kada ki tsofa a gida, domin darajar mace gidan mijinta gadai ƙannenki….,”
“….Stop it, ya isa..”
Ta kashe wayar da sauri tana zubewa a gefen gado, ta kasa tantance wanne kalar yanayi zuciyarta ke ciki, da gaske ta tsofa ko kawai faɗar Imran ce? mene abun iliminta na addinin? Ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana ambaton sunan Allah. Aure take so da gaske yanzu ta fahimta kuma shi ne dalilin da yake sawa tayi azumi domin riƙe kanta.
Tana jin wayarta na ƙara ta shareta domin babu wanda zai kirata idan ba Latifa ba, mai kiran nata al’amuran bikin Widad ya sha kanta. Sai da ta kwashe adadin mintina kusan goma kafin ta ji sauƙin zuciyarta, ta miƙe a hankali tana cire kayan jikinta kai tsaye bathroom ta nufa ta yi wanka tana fitowa ta goge jikinta tare da zura night wear masu ɗan kauri sbd sanyin hadarin dake fusawa, ciwon Limoniyarta yana ƙoƙarin tashi, bata jin daɗin komai rayuwar tayi mata juyin wainar tan da wannan shi ake kira da gwara na yi bara a bulayi yin bara a kofai.
Jikinta sai fitar da ƙamshin Nivea men active clean shower Gel yake. Ta juya kaɗan tana jan pillow ƙarar ƙofar da ta ji ya sa ta yi saurin rufe Idanunta tana jiran ta ji wannan karan kuma mene? Waye kuma?.
Mami ta dubi Majeederh tana sakin murmushi ta ce “Hawwa’u shiru ke ɗaya? Sau zan faɗa miki ki daina zama haka, bakya gudun abin da zai taɓa lafiyarki 24hrs kowa na shira banda ke rayuwa za tayi haka?”
Majeederh ta lumshasshun Idanunta kamar tana jin bacci so romantic domin gabaɗaya idan bata yanayi na jin daɗin zuciya shagwaɓewa take kamar ba ita ce babba ba, bata taɓa riƙe da nuna shagwaɓarta ga abin da take so. “Ina magana ki na ji? Oh! Ni Asabe Allah ya ye miki wannan miskilanci maza tashi ki kwashe kayan dinner ɗin can” da tsananin mamaki wanda Majeederh ta kasa shanyewa ganin ita ko hannu bata saka cikin abinci ba. A hankali cikin jan idanunta tana lumshewa ta ce “Kaya? Dinner?” Ta furta cikin sanyin murya wacce take always cool and so romantically.
“Eh, abincin da su Rumana da Raihana suka ci, naga gabaɗaya suna wajan fira sun yi baƙi ke kuma babu abinda ki ke sai zaman banza, to tunda suna wajan mazajen da za su aura ai ke sai ki yi aikin gidan”
Tunda Mami take magana Majeederh ta zuba Idanunta wanda suke farare tas kamar madara. Rayuwa kenan! Zamani riga duk shekaru data bawa su Ruma amma yau ita ake cewa ta kwashe kayan abincin da suka ci sbd suna wajan samari duk sanda su kai aure bata san mene zai iya faruwa da ita ba. Bata ce komai ba ta miƙe tare da ɗaukan hijabi ta saka Mami ta ce
“Allah dai ya yanke kazar wahalar nan, ya kawo ƙarshen zamaninki bana iya bacci sbd tausayinki yanzu ke babu wani daya taɓa cewa yana son ki da aure?” Ba tare data kalli Mami ba tayi gaba tana cewa “Babu”
Washegari da wuri Majeederh ta tashi sbd daman tun Subhi idanunta biyu dalilin azumin data ɗauka ta gyara gidan bakiɗaya, tana cikin haɗa breakfast Aaliyyah ta fito tana murza Idanunta ta ce
“Good morning Anti Jeederh” bata kalleta ba sai data gama haɗa kunun gyaɗar ta juya tana harɗe hannu a ƙirji tana juya idanunta da suke ɗauke da ruwa kamar mai shirin kuka. Sai kawai ta girgiza kai tare da juyawa tana faɗin
“Ki haɗa a parlour” she said. “Ok Maah”
A parlour Majeederh ta samu Ruma na waya tana ganin Majeederh ta ce “My Imran ga Anti Jeederh ku gaisa”
“Antynmu, ok give her the phone” Imran said.
Ruma ta miƙe tana bawa Anti Jeederh wayar ta ce “My Imran zai magana da babbar yaya, yama ce mini wai zai haɗaku aure da ƙanninsa idan Muzayyid ya amince”
Majeederh tayi jim she was so speechless.
Sai kawai tabar parlourn Idanunta rufe zuciya babu daɗi. Kaya ta sauya cikin Nidha abaya dark blue tayi rolling da babban vail kafin ta ɗauki kyakkyawan liƙab ɗinta ta sanya, gabaɗaya yau ta kasa jurewa dole ta isa gare shi, shi ke ɗauke mata kewa. Ta samu Abbu a parlourn shi ta tsuguna har ƙasa ya amsa yana cewa.
“Ya maganarmu dake?” Ta yi shiru ta kasa cewa komai. “Zan iya ɗaukar shirunki matsayin amsa”
“Abbu ka zaɓa mini ko waye, na amince zan aure shi” “…. Karatu na zaɓa miki, ki je nan da shekaru uku zuwa huɗu sai ki aure kafin nan kin kammala karatu”
Ta runtse Idanunta bata san amsar data bawa Abbu ba sai tsintar kunnenta tayi ta jin yana cewa “Allah ya yi miki Albarka, su dai bar su suyi auren tunda shi suka zaɓa”
Fitowa tayi bayan tayi sallama da mutanen gidan kanta a ƙasa tana rungume da ƙirjinta tafiya take a hankali mai cike da nutsuwa da kamala, ilhamarta ta gama bayyana gidan karamcin data fito, tare da tarbiyyar da take da shi. Napep ta tsayar ta shaida masa inda zata, tunda suka shiga kanta ke sunkuye lokaci zuwa lokaci mai napep ɗin ke kallonta ta cikin madubi har ya isa bakin gate ɗin data shaida masa. “Mun iso” ya ce yana karkaɗe kujerar da yake kai da dosta. Shirun da ya ji yasa ya juya mamakin yadsuta zuba tagumi Idanunta rufe yake yatsun hannunta kawai ya kalla yasan za a zuba kyau kuma Ubangiji ya gama tsara halittar shi a jikinta. Ya ce “Malama mun iso” Majeederh ta yi saurin buɗe Idanu, domin sunan da ɗalibanta na makarantar Ahlul Madar suke faɗa mata kenan Malama Majeederh Abdul’aziz Khan!
Ya saki murmushi ta cikin liƙab tare da fitowa tana ɗaukar jakarta ta bawa mai napep ɗin guda ɗari biyu. Ya ɗauki hamsin ya bata ta kalli hamsin ɗin ta ce
“100 ne” “Tab,Yoo maganar da kike wazai kawo ki nan a ɗari inda aka ƙarawa litar mai kuɗi” bata iya musu ba ta juya tare da nufar gate ɗin da aka rubuta.
*”An orphanage for young children”*
Ta faɗaɗa murmushinta tare da ɗan ƙarawa tafiyarta sauri zuciyarta sai janta take Idanunta ya kwaɗaitu ta son ganin abin da su kayi kewa. Kewarta ya yi mata jagora har zuwa office ɗin Akeeth. Yana ganinta ya miƙe tsaye with so much respect na tarin iliminta bawai don ta girme shi ba ya ce
“Your wlcm Majeederh-khan” ta jinjina kai tare da zama kan kujera tana rarraba Idanunta dake cikin liƙab, Akeeth ya ce. “Bar gaigaye za kici tumu ne”
“Uhm” ta furta ta ɗauki Wayarsa ringing ɗin farko aka ɗauka Akeeth ya ce “Come with him”
Ya kashe kiran yana kallon Majeederh yadda take kallonsa yasa ya fahimci me take nufi ya ce “She’s goode, but she’s trouble Maker very stubborn boy” “….Am very sorry for that”
Majeederh said. Tana haɗe hannu waje guda alamar ban haƙuri.
Akeeth ya watsa hannu baya ya ce “Is there nothing serious, kawai har yanzu bai sauya ba”
Ya gyara zama sosai cikin fahimta ya ce “Baya jin magana, ya yi ƙanƙanta da irin trouble ɗin da yake haɗa mana, he just Five years amma fitar shi ne sai shi, baya ɗaukan karatu da muhimmaci” Majeederh tayi shiru kawai domin bata san me zata ce ba, bawai don ta rasa ba, sai don bakinta ya yi mata nauyi harshenta ya harɗe bakiɗaya. Tun kafin ya shigo jikinta ya bata yana tsaye a ƙofa ta juya da ɗan sauri ganinsa tayi tsaye daga shi sai gajeren wando na Adidas sai wata ƴar shirt mai photon lion a gaba wacce ka yaga masa ita ta baya, jikinsa futu-futu.
Kan nan na shi gabaɗaya a cure fatar shi haƙa ƙarin, ta dube shi suka haɗa idanu da gudu ya ƙarasa wajanta cikin farin ciki da murn ya faɗa jikinta yana cewa
“Mamina, ƴar madara”
Faɗa zata yi masa amma jin yadda yake sauke ajjiyar zuciya a jikinta ya yi lamo tare da ƙanƙameta ya sa rauni ya bayyana a tare da ita, rauni irin na uwa da ɗanta ta lumshe idanu tana shafa sumar kan shi “Little” “Ƴar Madara”
Ya ce yana rufe Idanu tasan tunda ya ce Ƴar madara bai ce Mamina ba to fushi yake da ita.
Akeeth ya ce “Majeederh ni banga cancantar riƙe shi a wajanki ba, duba da cewa ke ba aure gareki ba, kuma idan kika duba yanayin society ɗinmu akwai wasu abubuwan da idan mutum mara aure ya yi shi musamman ɗiya mace za a fara yi mata wani irin kallo nada ban, tunda mutane basa buƙatar bincike kafin making decisions zuwa zatar da shi, kawai the only thing da suka iya yaɗa jita-jita da ƙanzon kurege, You have to be very careful”
“I’ll, but” ta yi shiru daga maganar. “But what? Open your heart Mrs Khan” Majeederh ta ce
“About his family?” Akeeth ya ce “Oh Yes! Babu wata amsa gamshasshiya wacce bincikenmu ya nuna, na faɗa miki a bakin masallaci aka tsince shi a shekaru uku da suka gabata,zan ci-gaba da bincike komai ake ciki I’ll let you know” ta jinjina kai Akeeth yana ta son ko sau ɗaya ne yaga fuskar Majeederh amma ina. Ta miƙe tsaye tana riƙe da hannun Little.
“Thank you!”
“Always Wlcm” fita su ka yi har bakin gate tana kallon yadda Little yaƙi ce mata komai, alamun ya yi fushi sosai ta duba hamsin ɗin da tayi saura a hannunta sai kawai ta bawa mai ice-cream na kan hanya ya bata na hamsin ɗin ta kalli kyakkyawar fuskar shi wacce ta kasa bayyanar da asalin yare ko ƙabilar daya fito ta ce “Take Little, Mami ce am sorry muje gida na baka chocolate” ya buɗe idanunsa ya ce “Ƴar madara” ta dungure masa kai, ganin daga gidan marayun zuwa gidansu akwai tafiya ya sa ta durƙosa tare da cewa “Hau baya, sweetheart” da sauri ya haye bayanta ya maƙale hannunsa a ƙasan ƙirjinta….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button