Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 7

Sponsored Links

*WARNING❌*
_Only matured ahead🔞 idan kika zageni ban yafe ba domin banyi littafina don ƴammata ba idan kinga zaki iya go ahead._

 

Buɗe ƙofar gdan nasu tayi ta tsaya jikin ƙofar tana nazarin gurin iyakar hangenta wata mota ce kawai a gurin ƙirar Benz baƙa sai sheƙi takeyi, zuba idanunta tayi akan motar tanason ganin abinda ke ciki tunaninta na bata to waye baƙon Yaya Hasinan da bataganshi ba?
Juyawa tayi zata koma Cikin gidan taji ance ““Am babe bakiji ba” tsayawa tayi tare da juyowa ta zubawa me mgnr ido a ranta tace “Itakam Yaya da kwashe² take wannan kuma ina ta ɗeboshi? A zahiri kuma saita rusuna tace “Sannu ina yini? Murmushi matashin Saurayin Wankan tarwaɗa me ƙirar ƙarfi yayi daya fito da kyawawan haƙoransa masu ɗauke da siririyar wushirya yace “Miƙe mana Ƴammata ai bakya tsugunna ba” miƙewa tayi ya jingina jikin motarsa yace “Dama ba kece Hasina ba?” Kaɗa kai tayi tace “Eh sunana Hanisa” lumshe lumsassun idanunsa yayi yace “da kyau Aneey Ni inama tunanin kece Hasina dake sunan yayi tambari so duba da yanayinki sai nace duk yanda akayi kece am karna cikaki da zance nidai sunana Ibrahim ana kirana da Mu’azzam na jima ina huccewa ina ganinki inajin wani yanayi game dake saidai ina fargabar yi miki mgn sai yau dai na daure na tunkareki ina fatan bazaki ƙi amsa tayina ba?”

Related Articles

 

Kanta tayi ƙasa dashi gabanta na faɗuwa tace “buƙata kuma? Wacce irin buƙata?” Murmushi yayi ya matsota sosai har suna jin numfashin juna yakai hannu zai kamo hannunta ta janye yace “Kinga Aneey ki saki jikinki ni nan da kike ganina idan inason mace babu abinda banayi mata nidai burina ki bani damar nuna miki ƙauna zakiji daɗina kinsan kamar yanda mace me wushirya take da ruwa da garɗi wajen rayuwa haka namiji ma me wushirya yake da ɗanɗanon gamsarwa”
Wani baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshi ta dubeshi hawaye ya zubo mata me haɗe da murmushin ciwo tace “Wai meye yasa fuskarmu take bada damar kowanne shirme azo mana dashi ne Mu’azzam kake ko wa? To kamar yanda kake tunani ba haka nake ba banjin zaka samubiyan buƙatarka Indai irin wannan buƙatar ne…..” Juyawa tayi ta shige gda tabarshi tsaye shanye da baki cike da mugun mamaki yace “kayy dama akwai irin waɗannan yaran ƴar talla ce fah kayy aa saidai ko idan nine banyi mata ba amma bari na gwada wata dabara” yaro ya kira yace ya shiga gdan yace da Mama za’a shigo a gaisheta” yaron ya shiga ya isar da saƙon nandanan Mama da Ramma suka hau tsumar gyara shimfiɗa aikace da yaron yaje yace ya shigo.

 

Shigowa yayi ya zauna a tsakar gdan suka gaisa da Mama ya gabatar da kansa ya zaro kuɗi masu yawa ya aje mata ya miƙe zai tafi tanata kwarara masa gdy Hanisa na jinsu tana daga ɗaki tayi ƙwafa taci gaba da ninkin kayansu tana jerawa a jakarsu bayan ta gama ta shafa mai ta zura kayanta tana kiciniyar zuge zip Hasina ta shigo ta ƙarasa ta zuge mata tana cewa “Meyesa bakida sabo da sakin jikine Hanisa mutumin da zai cutar dakai ai daga yanayi zakaga alama yanzun ke zuciyarki ta karɓi abinda kikayima Abdu mutumin da yaketa ɓarnatar da Dukiyarsa da Lkcnsa duk saboda ke idan Abdu yanada nufin cutarwa gareki da bai taimakeki ba haba don Allah Hanisa meyesa kike haka daraja ta rinƙa cin arziƙin daraja mana yanzu saiki tashi muje yana ƙofar gda”
Gabanta ne ya faɗi ta dubi Hasina da sauri tace “biyoki yayi?” Murmushi tayi tace “Eh cewa yayi sai yazo ya baki hƙr” girgiza kai tayi tace “bawan Allah Ni baimin komai ba kawai dai naji tsoro ne” murmushi tayi tace “shima tsoron da yaga kinji ne yasa yakeson ya baki hƙr”

 

Sunkuyar dakai tayi kamar me nazarin wani abu Hasina ta taɓa ta tace “kije kinsan maza basu fiye son jira ba” tama manta da yana jiranta badon Hasina tayi mgn ba ta ɗauki mayafinta ta yafa tayi kyau sosai cikin gown ɗin ta shadda ruwan toka abinka da Chocolate saita haskata sosai gashin gaban goshinta ya kwanto har kusan girarta sajen nan kamar na maza da suke gyarawa ya kwanta luf me laushe fuskarta kullum cikin murmushi koda yanzu ma da take cikin damuwa smaling face nata bai canza ba.
Tsayawa tayi a kusa dashi ta dubeshi tayi murmushi tace “Yanzun Abdul-Ahad saboda Ni ka sake fitowa” ɗago idanunsa yayi da suka kaɗa sukayi jawur ya ɗan taune lips ɗinsa yaja numfashi ya sauke yace “Abin da tausayi da gigita zuciya lamarin yakan faɗarmin da gaba yana sani cikin zullumi da firgici shin ya al’amarin zai kasance idan har abinda yake faruwa ya tabbata gaske wanne kallo duniya zatayiwa abin?” Da rashin fahimta ta dubesa tace “Me kenan?” Murmushin takaici yayi yace “Manta kawai Aneey amma don Allah kiyimin Alfarma ɗaya” jingina tayi da motarsa tace “wacce irin alfarma Abdu?” Ƙasa yayi da gwiwarsa yace “ki daina guduna don Allah wlh bazan cutar dake ba Al’ada ce kowa da irin tasa Aneey addini ne ɗaya Ni banga kuskure cikin abinda nakeyi miki ba tunda har yanzu ban nemi wani abu saɓanin Shari’a a gurinki ba” dariya kalmarsa ta bata ta durƙusa ta riƙe tausasan hannayensa zuciyarsu ta buga da ƙarfi tace “bayan wannan saime?” Murmushi yayi ya ɗagota suka miƙe yace “ki mayar dani kamar Hasina kada ki rinƙa ɓoyemin komanki farin cikinki damuwarki dariyarki kukanki nima zanyi miki haka”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button