Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 59

Sponsored Links

Taxi yatare ya shiga motar suka fara tafiya wani shago ya hango da ake saida teddies masu kyau cema mai taxi din yayi ya tsaya ya shiga shagon wani jan teddy yasai mata mai kyau da taushi yabiya kudin yadawo mota ya shiga ya zauna yana kallon teddy din yanda yarike flower.

Ahankali yatura kofar ya shiga dakin bata kangadon ma hakan yasa ya ijiye teddy akan gado, maganar nurse dayaji tana cewa gently raise your head yasa yaja kujera ya zauna yana kallon kofar bayin, wajen 3 min da zaman shi sanan nurse din tabude kofa ta gunguro ta akeke an chanza mata rigar asibiti zuwa pink amma desame design ne fuskar ta dadan ruwa ga nurse din rike da karamin farin towel a hanunta saida takawo ta bakin gadon sanan nurse din ta gaida Khaleel daya kasa cire idonshi akan Islam dan gani yay bakin yadan sabe jan dayayi ya ragu sosai, tsugunnawa nurse din tayi zata share mata ruwan fuska da towel din hanunta ya tashi tsaye yana tattare hanun doguwar rigar dayasa yace “may i” yay maganar tareda mika ma nurse din hannu murmushi tai tace “sure” tabashi towel din tsugunnawa yayi yana kallon fuskar ta yakai towel din kan fuskar yana share mata ruwan ahankali, lumshe ido tayi tadan saukar da ajiyar zuciya wuyarta ya share sanan ya dauketa ahankali daga kan kujeran sabida karya fama mata ciwo ya mike tsaye yana kallon fuskarta, ahankali tadan bude ido takallai kara gyara kanta tayi akan kirjinshi tasake sauke ajiyar zuciya, kwantar da ita yay akan gado ya rankwafo yamata runfa batare daya dagoba yace “good morning wife” hanunshi dayaji ta rike yasa yadan dago ya kalli hanun, murmushi yamata sanan ya zauna yakai hanunshi kan filon ya budemata yana kallonta, ahankali tasake matso da fuskarta tadaura kan hanun sanan ta lumshe ido tareda sakin ajiyan zuciya takara kankame dayan hanunshi data rike within 1min bacci yay gaba da ita, batare datamaga teddy ba.
Murmushi Nurse din dake tsaye tana kallonsu tayi cikin turenci tace “her mind is at ease anytime u are around, inhar tana ganinka haka kullum zaiyi helping recovery nata” murmushi yamata batare daya dena kallon fuskarta ba hakan yasa nurse taje ta bude wardrobe din dakin ta ciro wani ruwa dake cikin farin gora ta ijiye akan table din gefen gadon tace “wanan ruwan zata sha dazaran ta tashi, bari naje inta tashi ka danna mana alerm” tana fadin haka tajuya tafita daga dakin, yadade yana kallonta kafin ya daura kanshi agefen gadon shima bacci yay gaba dashi dan jiya kasa bacci yayi sabida tunanin ta.

Yau kwana su sha bakwai a asibitin, sosai condition din Islam ke improving dan bakin tass ya warke babu kumburin babu zubar yawu tana iya hadeye magani yanzu, cikin ne yanzu ake kai, kullum Khaleel na tareda ita abinda ke dagashi daga dakin salla ne kokuma idan zaije siyo magani a pharmacy hospital, shima idan zaije to Ihsan na wurin, Ihsan taita karanta mata novel tana murmushi kadan kadan, idan kaga yaci abinci to coffee ne yadan sha, baya iyacin wani abinci ko Ihsan ta girka saidai yay wasa da abincin kawai yatashi yabarshi, jiyake kaman ciwon yadawo jikinshi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button