Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 29

Sponsored Links

Uncle Isma’il ya goge zufar data yanko masa, duk da juriya irin ta shi da jarumtar shi a kullum a koda yaushe, bai hana shi sunkuyar da kai ba sbd hawayen daya taro cikin idanunsa ya ce “Alhj Abdul’aziz ka taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo? Bayan matarka daka bunne da hannayenka wacce matar kake nufi eh?” Abbu ya girgiza kai, yana damƙe photon hannunsa idanunsa ƙurr akan Gimbiya wacce ko kallo bai isheta ba, daman ba komai ke jan hankalinta ba, masifaffiyar jinkima ce da ita ga taurin kai da zafin zuciya, Abbu ya kalli wan nashi ya ce “Isma’il karka ce mini na haukace ce don Allah, bayan gaskiyar da Idanuna suka shaida mini gashi nan gata nan tana motsi, tana magana my wife is still alive Isma’il” Uncle Isma’il ya girgiza kai cike da damuwa ya ce “Idanunka sun yi mika ƙarya, ko baka haukace ba babu shakka ka fara zaucewa, zatonka ya saɓa lissafin da zuciyarka ke maka, Fulani bata duniya ka sani mun sani, she’s no more” Abbu ya yi shiru sbd komai ya tsaya masa daga aiki cak, jijiyoyin dake sarrafa ƙwaƙwalwar zuwa wanzar da tunani mai kyau ta ɗan ta kata masa da aiki na zuwa Shuɗewar daƙiƙo, Uncle Isma’il ya kama shi ya zaunar,kowa ka gani a parlon ya girgiza. Calmly Mai martaba ya ce “I can see the picture?” Uncle Isma’il ya miƙawa Mai martaba Ajlaal Sultaan, ya amsa tare da ɗora dara-daran idanunsa akai, wat kyakkyawar bugawa zuciyarsa tayi da ƙarfi a zaune yake amma sai daya nemi miƙewa tsaye Gimbiya tayi saurin damƙe hannunsa, domin duk wani abu na zubar da ƙima bata haɗa hanya da shi ba, duk girman abu tana iya haɗiye ta gwammace ya illata zuciyarta da a fahimci rauninta, a fili cikin ƙasa da murya ya furta “Samra” ambatar sunan Samra ya sanya Zaytoon zaro idanu waje cike da tsoro da fargaba, Rohaan ya yi saurin jingina da kujerar dake kare da gangar jikinsa, yana jin kamar duniyar ke juyawa masa, Gimbiya ko motsi ba tayi ba sai zufar dake tsastsafowa ta saman hancinta wanda ke bayyana asalin tashin hankalin da take ciki, Mai martaba ya kalli Uncle Isma’il ya ce “Ita ce ya rasu?” Uncle Isma’il ya jinjina kai, Mai martaba ya yi shiru yana kiran sunan Allah gabaɗaya zuwa Nigeria da suka yi ƙaddara ce, rashin sani ne, salwantar da RUHI BIYU ya ƙaddara zuwan nasu, ya kuma wargatsa farin cikin zuciyoyin su. A hankali ya ce “Samra da Hawwa’u biyuni ne, tagwaye ne ciki ɗaya ne ya kawo su duniya, rana ɗaya, wata ɗaya, shekara ɗaya, irin biyunin da ake cewa Identical twins, gane kamar su zai maka masifar wahala, Mahaifinmu Sultaan ya auri mahaifiyarmu Balarabiya ce, amma bata Saudiya ba Larabawan Diffa,wanda aka fi sani da larabawan Mahamid” Ya yi jima na wani lokaci kafin ya ce “Larabawan Diffa suna magana da larabci ne, kuma suna Balarabiya, amma ba su da alaƙa da Larabawa na yankin Maghreb na Afirka ko Larabawan Gabas ta Tsakiya, asalin su ƴan Sudan ne dalilin farin da ka yi a 1974 na Sahelian, hakan yasa suka nufi Diffa,sannan wasu da ke gujewa yaƙin basasa a cikin ƴan Sudan ɗin da rikicin Chadian da Libya a cikin shekarun 1980, suka zauna kusa da Diffa . Shugaban Ƙasar Nijar na farko wanda ɗan asalin Diffa Arab ne Mohamed Bazoum, bisa wannan dalilin da kakanmu mahaifin Takawa yaje Nijar yankin Diffa sai Babana Takawa kenan Sultaan ya haɗu da mahaifiyarmu har sukai aure, a haka kakanmu ya rasu aka bawa Mahaifinmu Sultaan sarautar Saudiyya, nine wanda ya fara haifa sai kuma Twins Samra da Hawwa’u, haɗuwar jinsu biyu kuma duka Arab sai Ubangiji ya bamu wani irin sahihin kyau musamman biyuni, wanda kuma kyan nasu ya jawo musu matsala da yawa, bayan haihuwar su aka haifi Rohaan autanmu kenan, iya mu kenan, kuma mahaifiyarmu ta rasu a haihuwar shi ne, Yayan ƙanin Mahaifinmu wanda ya kasance uba ga matata Ƙhulud ya raini Rohaan, wani babban uzuri ya kawo mu Nigeria wanda kuma a nan ne muka rasa biyuni lokaci mun shiga tashin hankali wanda baki ba zai iya faɗuwa ba, zuciya ba zata iya ɗauka ba, rauni ya mamaye zuƙanmu ruɗewarmu ta bayyana a sarari sai Mulki ya samu tawaya Takawa ya fara rashin lafiya rashin” Mai martaba Ajlaal ya yi shiru cike da damuwa yana jin kamar a lokacin ne komai yake faruwa, dal yake ganin hakan a cikin idanunsa.

Ya numfasa bayan ya ɗan kurɓi ruwan da aka bashi mai sanyi sbd jikinsa dake rawa bayyane. Ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce “Ba zan iya cewa ɓatan su plan ne ba, garkuwa ko akasin haka, nasan dai akwai dalili wanda _Only God knows!_, Hakan ya sanya mini tsanar Nijeriya bakiɗaya, tun bayan barinmu ban taɓa zuwa ba sai dalilin Majeederh, mun rasa biyuni tun suna shekaru 6 a duniya lokacin Rohaan shekarar shi 4, daga nan ban san mene ya faru ba, sai bayan shekaru wajan 30 Ubangiji ya bayyana mana Gimbiya, ba baki ba ƙafa, bata cikin hayyacinta haka muka sameta a ƙofar masarauta, bamu da masaniyar aurenta banda yanzu, nasan tunda ta fara dawowa daidai take iya buɗe idanu ta zauna saman wheelchair bata da walwala kullum cikin kuka take, ciwon yau dab na gobe daban, tana yawan zane wanda ban san yadda akai ta zama ƙwararriyya a harkar zanen ba, ta zana baby boy, ta saka _I love u_ wani lokaci ta zana babban kuskure ta saka masa wuƙa a ƙirjin ban taɓa tsayawa na yi noticed me hakan ke nufi ba sai yanzu da gaban ku ta kira sunan Mr President da inda yaronta yake, kila bayan Khalil yana da wani ɗan maybe kuma dai Khalil ɗin ne wanda take nufi” Ya yi shiru yana mai da numfashi, tunda uwarsa ta haife shi bai taɓa magana mai tsayin hakan ba, har wani yaji-yaji ƙirjinsa yake na azaba. Mijin Malama baya fahimta sbd malam da shocked, ya kuma kasa gasgata abinda ke faruwa. A hankali Abbu dake jingine jikin kujera ya ce. “Kafin rasuwar Fulani ta bar mini WASIYYA ga yaranta, ta shaida mini yadda na yi zaton ita Bafullatana ce to ba haka bane, bata da mantuwa ba kuma zata taɓa mancewa ba, sace su akayi lokaci guda bata san su waye ba, amma taga mata da yawa, babu mamaki masu safarar mata ne a tunanin Abbu; sun shiga cikin jeji sosai sai motar su ta tsaya a nan kuma, they have been attack in the middle of the forest, ta ce; bata san mene ya faru ba sai farkawa tayi ta ganta cikin Fulani na garin Gombe, tayi rayuwa dasu ba tare da sun san wacace ita ma, haka ta zauna har tsayin shekaru goma sha biyar daidai lokacin dana aureta kenan, bata haihuwa ba sai da tayi shekara 25 domin tayi ƙanƙanta da haihuwa, har sannan bamu san asalinta ba” Abbu ya yi shiru a hankali kuma ya ce “Hatta ni ɗin nan, kawai tazo da gwala-gwale a jikinta wanda bani da tabbacin Fulanin sun san muhimmancin su gaskiya, sanda Ubangiji zai amshi rayuwata sannan ne take faɗa mini cewa idan Allah ya ƙaddara zuwana Saudiyya naje Palace na basa photon zan samu cikakken bayani, ta faɗa mini hakan ne domin bata san yaranta su tashi da kaɗaici na rashin dangin uwa, kamar yadda ta tashi ba danginta ba kuma wanda ta sani” Idanun Abbu ya cika da hawaye sosai ya ce “I was ashamed, I didn’t become a good man, I couldn’t fulfill my wife’s will” Hawaye masu zafi suka saukar masa ya yi saurin ɗauke kai muryarsa na rawa ya ce,I failed as a father; I was not a good father, I humiliated my daughter and turned her into my investment” Ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!I ruined Majeederh’s life” Kowa na wajan sai da ya ji tausayin Abbu ya ƙara cewa “I failed as a father!” Uncle Isma’il ya ce “U won’t, duk abinda ya faru ƙaddara ce wacce ta riga fata, Ubangiji ya riga ƙaddara hakan baka da laifi, duk abinda ka yi baka cikin hayyacinka an sanya tunaninka da ƙwalƙwarka a kwalba rufe, idan da wanda ya yi asara ni ne wanda auri mace mai tsanani son zuciya kowa yasan yadda kake so da ƙaunar Majeederh” Abbu ya girgiza kai kawai, daman ba sosai yake magana ba idan ya tuna wai da bakinsa ya tsinewa Majeederh sai ya ji duniyar ta masa zafi. Zaytoon ya kalli Gimbiya ta ce “Ur turn, bamu labari” Gimbiya tayi shiru tafi ƙarfin seconds arba’in ba tayi ko motsi ba, babu alamar zata tanka can ta ce “Ya faɗa muku, ya fini sanin komai” Ta faɗa Idanunta a gefe tana kallon Khalil da ya yi lamo jikin matarsa kuma ƴar ruwarsa ta jini, Mr President ya san da shi take ya yi kamar bai ji ba, jinkima da taurin kai ya haɗu waje guda wanda Khalil ya yi gadon ko wanne daga wajan uwa da kuma uba. Uncle Bello kallon kowa yake yana son ganin waye zai fara sauke izza ɗin shi, Innati ta ce “Tur ƙasshi; gobara a gefe, kawai ku kaiwa juna hari, to wlh tallahi iblis ne kawai mai wannan izza ɗin da girman kan ai kuna ganin dai yadda ƙarshen shi bai kyau ba” Innati ta ce “Kai shugaban ƙasa ka fara bamu labari ai sarauta ba wasa ba ta take komai billahi” Yadda Gimbiya bata motsa ba haka Mr President ba wanda ya kalli ɗan uwan shi, can ya miƙe tsaye ya ce “Bani da lokacin ɓatawa a nan, kamar yadda ta faɗa haka ne Khalil ɗanta ne, ita ce babarsa kuma ni ne ubansa” Gimbiya tayi wani miskilin murmushi tana girgiza ƙafa ta ce “What are you afraid of? Ko kuma….” Da sauri Dad ya kalli Gimbiya ya ce “Jidda” Ta miƙe tsaye itama tana murmushi idanunta tar a kansa ya ce “Karki manta you are still my wife” Ta kalle shi sosai clamly ta ce “Zan sauke maka girman kan ka” Ya ce “Baki da zarra, ba a haifi mai iya sauke mini girman kai da jinkimata ba babu shi” Khalil kallonsu kawai yake ganin kamar zasu daku kuma wai sune iyayen shi, what kind of parents they’re? Ya miƙe tare da miƙawa Majeederh hannu ta kalle shi ta kasa cewa komai, idanunsa jajur kamar gauta naman jikinsa na wani rawa ya ce “Zo” Ta miƙe tsaye ya damƙe hannunta tare da nufar waje Uncle Isma’il ya ce “Khalil ina zaka?” ba tare daya juyawa ba, ya sake damƙe hannun Majeederh kamar zai ɓalla biyu rai ɓace ya ce “Idan duka su biyun suka sauke girman kansu, suka faɗa muku yadda suka haɗu, da aure suka haifeni ko babu sai mu dawo, muna son juna; i love my wife zan ci-gaba da amsa sunan Mijin Maluma, suna iya kashe junansu idan sun so” Yana faɗin hakan ya nufi waje Gimbiya ta ce “Criminal” Dad ya ce “Da wasa kika faɗi waye ni zan kashe yarinyarki dake wajena, Abraham has a sister, su tagwaye ne kamar yadda kuke da ƴar uwarki, rana ɗaya kika haife su ni na ɗauketa tun a labour room, sbd wannan ranar na yi miki al’ƙawari daman ni ne wanda zai fara sauke girman kan ki, kin san waye ni sarai tun kafin na aureki, idan ki ka yi kuskuren faɗawa kowa asalina na rantse da Jesus sai na yanka wuyan ƴarki” Da sauri Khalil ya juyawa ya kalli Dad ya ce “Before you kill my sister, let me kill you first” Yan faɗin hakan ya saki hannun Majeederh tare da nufar inda Dad ɗin yake….

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button