Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 31

Sponsored Links

Ahankali yake daga kafa haryakai bakin gadon ya tsaya yay folding hanunshi a kirji cikin sanyin murya yace “is it paining you?” gyada kai tayi tana yarfe hannu tana hurawa batare data dago kaiba dan gabaki dayan hankalin ta nakan ciwon, dago kai tayi da sauri ta kalleshi da katon bandejin dake goshinta da sauri ta saukar da rigarta ta rufe kafafun ta, dan murmushi yayi sanan ya zauna abakin gadon yana fuskan ta hararan shi tayi tace “waikai duk inda nake sekazo, tracker kake amfani dashi ne? Wlh ko kafita daga dakin nan kona kirama Abbana nahadaka dashi komame zai faru ya faru” murmushi yasake yi sanan yace “how are you feeling now?” dauke kai tayi ta turo baki, sosai yake kallonta sake juyo dakai tayi ta kalleshi tace “wai bazaka fitaba sai su Abbana sunzo, okay bari na kirasu” bude baki tayi zatai ihu yadaura hannu akan lips dinshi alamun tai shiru, kasa magana tayi kaman wacce yama magic saima dauke kai datayi daga kallon dayake mata jitake kaman ta makeshi, hanunshi yasa a aljihun wandon shi yaciro wayarta ya mika mata juyowa tayi tana ganin wayarta ta karba da sauri akuma dan rude tace “a ina kasamo wayata?” baice komiba yatashi tsaye yana kallonta yace “waye My heartbeat” da sauri ta kallai sanan ta harareshi tareda murguda mai baki tace “meruwan ka and kafita daga nan” kallon cikin idonta yayi yace “well I told him karya sake kiranki because am ur husband to be” kwalalo ido tai ta kalleshi da so much pain a idanunta tace “Fahad din nawa ka fadanma haka?” gyada mata kai yayi yace “yes” azuciye ta juya tana waige waige pillow dake bayanta ta raruma ta jefamai da duka karfin ta ya chafe yana murmushi har saida hakoranshi suka bayyana daidai lokacin Anty Hindu da Abba suka shigo, Abba yace “Ummi Khaleel din kike bugama pillo mutumin daya taimakeki dabadan shiba da Allah kadai yasan mezai sameki” da sauri ta kalli fuskarshi, dan murmushi yamata sanan ya tako yadan duka ya ijiye filon abayanta ahankali yace “I will come and check you tomorrow, I love you” yay maganar ta yanda ita kadai zata iyaji ya juyo ya Kalli Abba da Anty Hindu yace “Abba saida safen ku” addu’a sosai da godiya Abba da Anty Hindu sukamai sanan ya juya zai fita daga dakin dan waigowa yay ya kalleta daidai lokacin itama tadan dago kai suka hada ido hannu yadaga mata alamun bye, kawad dakai tai da sauri murmushi kwance kan fuskarta.
[6/17, 6:38 PM] Maman Jedda: Novels
*JARABTA*
Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button