Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 46

Sponsored Links

XLVI…
(46)

*Munayamaleek is Five hundred naira only via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, evidence of payment to 07082281566 ( don’t call me, only chat please)*

_zuciyata a hargitse take munaya, nayi dukkanin kokarina dan ganin cewa mun mallaki juna amma hakan bai yu ba, na kasa rarrashin zuciya ta, it hurts me to say this, but we can’t continue anymore, Hajiya ta ta ki amince min na aure, ki yafe min Munaya, and you Will forever be loved in my heart_

Related Articles

Wanna shine takaitaccen sakon da Abbas ya iya turawa munaya, domin bai da karfin guiwar kiran ta, gani yake kamar bazata fahimce shi ba, ya kashe Wayarsa jin ana sanarwa jirgin su zai tashi, ya jima bai kasance da kunci a zuciyar sa irin na yau ba.

Ya rufe idanun sa yana tuno yanda hirar su da yaya Sabuwa ta kasance.

“A’a Abbas, ba sai ka min dogon bayani, ita zainabun ta gaya min komai a waya kafin ka zo, toh nima ban goyi baya ba, idan har mun isa da kai ka hakura da ita waccan yarinyar ka samo wata, kana saurayi da kai zaka jajubowa kanka wata bazawara”

Yana jin ciwo idan suka kira Munaya da bazawara, da a ce zasu fahimce shi lallai zasu san cewa sam wanna sunan bai dace da Munaya,
Daga kuma lokacin da yaya sabuwa ta katse mishi maganar sa da kuma sanar masa da cewa Hajiya ta riga ta gaya mata komai ya sare, guiwar sa tayi sanyi, dama itace hope ɗin sa ta karshe Kuma bata goyi Baya ba ita ma, yanxu Yana ji yana gani ya rasa Munayar sa? waya isa ya mai haka idan ba uwa ba.

Da misalin ƙarfe uku da mintuna na rana Munaya na shirye-shiryen tashi, kasancewar karfe hudu ne closing time ɗin ta, ta ji karar shigowar massage a wayar ta, sai data kamalla dukkanin abubuwan daya kamata sannan ta zauna hadi da dauko wayar ta, ta shiga massage ɗin, ganin *my one* dinta ne ya saka murmushi subuce mata, ta danna kan sunan na sa domin karanta sakon.

Sai dai wani Irin lugudan bugu kirjinta yayi, wanda hakan ya saka ta daura hannun ta kan kirjin ta, tuni hawaye suka wanke fuskar ta, anya zata samu farin ciki a Rayuwar ta, kila bata da rabon samun farin cikin a duniya, ta rufe idanun ta, ta saki kuka Mai matukar taɓa zuciya, kukan da sautin sa ke fita da wani irin daci da ciwo daga kasan zuciyar ta, har bayan la’asar sannan ta tsagaita saboda wani irin ciwo da zuciyar ta hadi da kanta ya fara, ta lallaba ta mike saboda ruwan hawaye daya cika idanun ta ya sanya take ganin komai dishi-dishi, alwala ta dauro kana ta fito, ta shimfida sallaya ta kabbara sallar, a sujjadar ƙarshe ta jima tana kai kukan ta ga Ubangiji, sannan ta mike ta dauki jakarta, ta dauki bakin glass data zo da shi dake kan table din office ɗinta ta saka domin ya boye ja hadi da kumburin da idanun ta suka yi, sai dai kallo daya mutum zai mata ya fahimci cewa ta sha kuka musamman yanda hanci da kumatun ta suka yi ja kamar nunannan tumatir, ba wanda ta iya yiwa sallama a abokan aikin ta, ta fita daga asibitin ta tari napep ta shiga, cikin adaidaita tsaho ma hawaye ke kara zuba a fuskar ta amma sai tayi dabarar share wa ganin hankalin ababen hawa dake wucewa na kallon ta.

Tana shiga falon barrister Abrar ta kalle ta tace “munaya lafiya Meya same ki?”
Wanna tambayar ya kara raunata zuciyar ta ta fashe da kuka, kana ta tafi da gudu ta fada jikin barrister, hankalin barrister Abrar ya tashi matuka, ta rungume tana lallashinta tsawon lokaci kana ta iya yin shiru.

“Gayamin menene?” Barrister Abrar ta kara tambayar ta a dame.

“Mami ya….” Sai ta kasa cigaba da maganar domin wani kukan ke kokarin kufce mata, kawai ta mikawa barrister wayar ta.

Kasancewar bata fita daga massage ɗin ba ya sanya barrister na buɗe wayar ta ci karo da sakon doctor Abbas din.

Bayan ta gama karantawa ta ajiye wayar a sanyaye tana kallon Munayan cikin matukar tausayin ta, tabbas rabuwa da masoyi da daci, dacin da baya mistaltuwa.

Ta riko hannayen Munaya duka biyun tace “munaya! Na fahimci yanda kike ji a zuciyar ki, i understand, amma kiyi hakuri, duk abinda kike ga bawa ya rasa lallai ba rabon sa bane, kila Allah yayi miki wani tanadi na musamman a gaba, kiyi hakuri, nasan ke din yarinya ce mai juriya, You re very strong munaya More than you can imagine, sau tari zaki ga wani abu ba alkhairi bane a rayuwar mutum amma yana so, wanda kuma yake alkhairi zaki ga yana kin sa, wanna gaskiya ce mai daci but it need to be told, kiyi hakuri dan Allah kinji, ki barwa Allah zabin ki, idan kuma Allah ya nufa akwai aure tsakanin ki da Abbas din sai ki ga Allah ya sanyaya zuciyar mahaifiyar ta Sa ta amince”.

Jinjina mata kai kawai munaya ta iya yi, sannan ta mike kamar zata fadi, barrister ta riƙe hannunta har daki ta raka ta, tace “kwanta and have some rest kinji?”

Ta kara jinjina wa barrister Abrar kan ta.

Haka ta yi lamo a kwance kamar mai yin Bacci, sai dai hawaye dake bin gefe da gefen kunnen ta zai tabbatar wa mutum da cewa lallai idanun ta biyu.

Har shida tana kwance ta ji an buɗe kofar dakin ta, little Amnah tace “salamaaa alaikummm mummy na dawo” munaya ta kara runtse idanun ta kamar bata ji ba.

A shagwabe little ta kara cewa “mummy! Bacci kike?”

Jin ba amsa ya saka ta ficewa daga dakin domin zuwa wajen barrister Abrar.

Munaya ta sauke wani irin numfashi mai karye zuciya kamar Marayan da ya yi kukan neman mahaifiyar sa ya gaji.

 

Cikin takun sa dake nuni da cewa shi din cikakken namiji ne ya shigo falon na su, sai dai bai ga mahaifin na sa ba, hakan ya saka ya nufi dakin Alhaji Dawood bakin sa dauke da sallama.

Alhaji Dawood dake hada wasu takardu ya dago hadi da amsa sallamar sannan yace “yauwa Maleek ka dawo, I’m even trying to reach you on phone, ga su nan” yace mika wa Maleek ɗin takardun ya dora da cewa “komai na tafiyar ya kamalla, ka ce can travelling Agency ɗin ko?”

“Eh daga can nake yanzu haka”

Alhaji Dawood yace toh madallah, Allah ya kaimu goben, what time jirgin ku zai daga?”

“Karfe takwas”
Ya amsa wa Alhaji Dawood din.

Bayan Maleek ya yi sallar isha, daga masallaci mota kawai ya fito da ita kasancewar da key a aljihun sa.

A tsakiyar haraban gidan doctor Aaban yayi parking, ya fito da wayar sa ya danna kira wa munaya sai dai a kashe wayar ta, ya kalli mai gadi dake zaune a gate sai kuma ya nufi Kofar da zai sada mutum da falon ya kwankwasa.

Babu jimawa aka zo aka bude kofar, ya ga mimi ce, ya sakar mata murmushi, ita ma ta mayar sa cikin jindadin yau ta ga yayi mata fara’a.

“How are you doing? please call me Munaya”

“I’m fine, Ok” ta amsa tana rufe kofar, yayinda shima ya koma bakin motar sa.

“Waye ne mimi?”

“Mami Daddyn little ne, wai na kira masa anty Munaya”

“Okay, jeki gaya mata”

Babu jimawa ta dawo tace “Mami na gaya Mata girgiza min kai kawai tayi”

“Zauna ina zuwa” barrister ta fada tana mikewa.

Tana shiga ta tarar da Munaya zaune, little Amnah dake bacci ta ɗora kanta kan cinyar munayan.

“Munaya baki ji magana ta ba kenan?”

“Allah Mami na ji” ta ce cikin sanyin murya.

“Kin san yanayin zuciyar ki bata bukatar damuwa ko, toh taso”

“Mamiii toh me zan masa?” Munaya ta fada kamar zata saki kuka.

“Kije ki ji, kila sakon yarsa zai baki”

“Toh na tashe ta taje ta karbo”

“A’a allow her to sleep, ke kije tunda ki yace a kira”

Bata son yiwa Mami musu hakan ya saka ta kwantar da kan little a gado sannan ta mike, ta buɗe wardrobe ta zaro hijab baby pink color ta zura, ta bar dakin yayinda barrister ke rufawa little bargo.

Maleek ya saki ajiyar zuciya ba tare da sanin cewa yayi hakan ba, a da gani yake kamar kauyanci ne saka hijab, ya kuma ga mata sun dawo wata kala idan suka saka, amma yanzu babu shiga daya fi so ya ga mace ta yi kamar hijab, musamman Munaya da yake mata wani mahaukacin kyau.

A hankali take nufar sa, iskar dake kadawa ya saka wani sanyi ke shiga jikin ta sakamakon zazzaɓin da take, ta tsaya dan nesa da shi ba tare da tace komai ba, fuskar ta a cure.

“Matso” ya ce mata, tayi masa shiru, duk da ya ji ba dadi amma sai ya matso kusa da ita yace “bakya sallama”

Nan ma shiru, yace “toh Ni barin yi Miki, Assalamu alaikum”

Labban ta kawai ya kalla ya fahimci ta amsa sallamar ba dan sautin ya fito ba.

“What’s wrong with you?” Ya tambaye ta da kulawa karon farko a rayuwar sa.

Sam Munaya bata ji ya burge ta ba, sai ma haushin sa data ji, ta bude bakin ta da kyar da tace “gani”

Ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace “Ina angel?”

Kawai sai munaya ta yi gaba ganin yana bata mata lokaci, taku biyu kacal yayi Ya cimmata duk saurin da take, ya mika hannunsa ya riko hijab din ta, ta dakata hadi da waiwayowa tace “sakar min hijab”

“Toh waya ce ki tafi, na baki izinin tafiya ne?”

“Baka da wanna matsayin” munaya tace tana watsa masa wani kallo mai cike da haushi da tsana da idanun ta da suka tara ruwan hawaye.

Yayi kamar bai ji kuma bai ga abinda ta masa ba, yace “ki tsaya Toh na gama sai ki tafi, ko kuma mu tafi cikin tare” yace in a serious tune.

Tilas ta tsaya domin ta san zai aikata, a hankali Maleek yace “where’s my angel”

“Tayi bacci” ta amsa a takaice tana kauda kanta.

Ya duba tsadadden agogon hannun sa yace “yau ta kwanta da wuri, Ko dukan min ita kika yi?”

“Eh!” Tace tana murda bakin ta.

And that drives him crazy, ya saki Wani murmushin gefen baki, yace “cigaba zan rama mata ne”
Ta masa Banza tana ƙara tsuke labban ta.

Ya mika mata key din mota yace “gobe in Sha Allah zan yi tafiya zuwa Mexico, wani zai zo yana driving Angel zuwa school mun gama magana da shi tare zaku na tafiya, ki kula min da yarinya ta”

Ya kuma zura hannun sa cikin aljihu ya fiddo bandir din dubu daya yace “wanna ki ajiye idan tana buƙatar wani abu sai ki siya mata”

Duka cikin abubuwan da yake mika mata munaya bata karba ba yace “ki karba mana”

“A’a ajiye kayan ka, zan kula da yata, ina aiki ai”

Cikin murya kasa kasa yace “ai nima ban ce bakya aiki ba, amma hakki na ne yin haka, saboda haka ki karba”

Bata kara sauraran sa ba ta yi gaba abin ta, ya bita da kallon.

Kwanan sa biyar kacal ya dawo, wanda ranar dawowar tasa ta kasance juma’a, Alhaji Dawood yayi farin ciki da dawowar tasa, musamman daya yi aikin daya tura shi perfectly.

 

Washegari da yamma ya tarar da Alhaji Dawood a farfajiyar gidan, yana zaune a gefen da aka tanada domin hutawa, ya gaida shi hadi da mika masa katin gayyata, Alhaji Dawood ya karba yana kallon katin, zai tambayi Maleek din kenan karin bayani kan invitation card ɗin, sai ya hango AbdulMaleek Dawood a lamba ta biyu cikin jerin sunayen mutane arba’in da zasu yi saukar qur’ani, yayi matukar ƙaduwa da ganin haka.

Maleek yace “gobe ne Dad, zan yi farin ciki idan ka kasance tare da ni a wajen”

“In sha Allah” kawai bakin Alhaji Dawood ya iya furta wa, yana bin bayan Maleek da kallo mamaki na kara Ka masa, dama Maleek bai yi saukan qur’ani tare da maragayi kanin sa Tun a kananun shekaru ba? tausayin Maleek ɗin ya kama shi, shin tsawon wani lokaci Sa’adah ta dauka tana cutar masa da yaro, lallai akwai abubuwa masu yawa da bai sani ba har yanxu gami da irin rayuwar data ɗora Maleek, yana son sani, amma idan ya sani ɗin zuciyar sa ce zata kasance cikin kunci, rashin bincike kan wasu abubuwan yafi alkhairi akan idan suka bayyana.

MALEEK ya riga Alhaji Dawood isa wajen saukan, domin har an fara bikin saukar ya karaso had’add’en hall ɗin, ya samu waje daga baya ya zauna kasancewar gaban ya cika, zaman sa babu jimawa aka kira AbdulMaleek Dawood ya fito, zuciyar Alhaji Dawood ya shiga bugawa yana kallon dan sa dake tafiya kan tsage, Maleek ya saka mic din saitin bakin sa ya yi Bismillah kana ya fara karanta suratul Maryam cikin wani mugun kwarewa yana bawa kowacce harafi hakkin ta husky voice dinsa ya yi wani mugun dadi, yayinda yanda yake rera qur’anin ke shiga zuciya da bargon jama’ar wajen wanda hakan ya sanya sigar jikin su zuba, Alhaji Dawood ya saka babbar rigar sa ya share hawayen da ya zubo masa, yana mai alfahari da dansa.

 

_dan Allah masu min magana kan ina ja musu rai a book din Munayamaleek su yi hakuri su daina, maganar da ake min a conversations groups ma sun ishe Ni, fisabillahi taya mutum zai biya kudin sa na ja masa rai, ko a free book bana jan rai sai wanda mutum ya saka kudin sa ya isa? Wallahi yanxu haka ban da lafiya kusan kwana hudu kenan amma idan na ce bazan Yi typing ba ba lallai a yarda da Ni ba, shiyasa ma na daure ina yi, wadanda suka san ina kokari sun sani, dama duniya bazaka taba yiwa kowa yanda yake so ba, kullum nake typing, idan aka ga ban yi ba toh lallai baban uzuri ne ya rike Ni, Wasu writes din ma suna ɗaukan kwana biyu, uku, hudu a matsayin ranakun hutun su, Ni na taɓa dauka? Saboda nima ina son sauke nauyin jama’a dake kaina, a part from social media kowa Yana da personal life din sa, dan Allah kuyi hakuri, in sha Allah babu jimawa daga ni har ku Zamu huta idan book ɗin ya ƙare, ba shikenan ba ?_
NoorEemaan ✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button