Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 11

Sponsored Links

*11*

Muhammad tsawon sati guda ya kwashe ba inda yake zuwa sabida firgicin da yake ciki,sosai zancan auransa yasakashi,a damuwa,

Zahra sanda mummy ta sanar mata auranta da muhammad sosai taji daɗi,sabida taga ɗan uwanta ne,ze rufa mata asiri,dan haka bata da damuwar komai aranta.burinta Allah ya nuna mata lokacin.dan ita tun haɗa idonta dashi na farko taji ya kwanta aranta.

Related Articles

Sosai walwalarta da jin daɗinta ya ƙaru agidan ba mummy ba har daddy ya fahimci hakan,wani sanyi yakeji aransa sabida ya mata abinda takeso.

Mummy gyara zahra take da duk wani abu data san baze cutar da lafiyarta ba,,cikin ƙanƙanin lokaci zahra tayi wani kyau na musamman fatarta ta murje tayi fari har wani sheƙi take,gashi yanzu ba wata rama ajikinta,sema wata ƙiba data mulka,zahran inna kenan matashiya ƴar kimanin shekaru goma sha shida.kyakkyawa ajin farko,

Saura kwana biyu ɗaurin aure,muhammad na zaune a lambun gidansu zahra ta ƙaraso gurin,yana ganinta ya ɗauke kai kamar be ganta ba,murmushi tayi dan tasan baya sonta,ita ko sonshi take dan haka zatai haƙuri da duk wani halinsa har shima ya sota,gefenshi taje ta zauna,kamshin da take ne yasashi ɗago kai ya dubeta,sannan ya maida kansa gefe.

“yaya dama inaso in baka haƙuri ne akan auran dolen da zaay maka”
Ɗagowa yayi ya dubeta rai aɓace yace”au auran dolen ni kaɗai zaayiwa kenan ke banda ke?”

Murmushi tayi kumatunta suka lotsa tace”banda ni gaskiya,kai de za’a yiwa,ni auran nagani inaso za’a min,”ta faɗi a kunyace.

Tsayawa yayi,yana ƙare mata kallo,tattaro hankalinshi yayi gaba ɗaya kanta,hannunta ya kamo ya dibeta a tsanake yace”zahra ni kikeso?”yayi tambayar a tsanake.
Murmushinta me sanyi tayi sannan tace “Tunda naganka,naga kuma irin taimakon daka ba rayuwata da lafiyata,yaya muhammad naji ina sonka,wallahi da gaske nake har raina”ta ƙarasa maganar kamar zatai kuka.

Yatsun hannunta yake kallo,sannan ya ɗago ya dubeta yace”zahra to ya zakiyi in kika fahimci ba matsuguninki a zuciyata?”

“addua zanyi,wataran zaka soni”ta bashi amsa batare da damuwar komai ba.

Murmushin takaici yayi sannan yace”to in kuma ba kya cikin kalar matan da nake so fa?”

“Zanyi ƙoƙarin maida kaina kalarsu insha Allahu”tabashi amsa.

“to ay ni zahra gaba ɗaya kin min ƙanƙanta a aure,taya zan iya zaman aure dake?”

“wataran zan girma yaya,in zama babba,sede ko kace sauran wanine baka so,inaga shine kawai dalilin daze hanaka aurena”ta ƙarasa maganar tana kuka,

Runtse ido yayi maganar na masa ciwo a zuciyarsa,a hankali ya dubeta yace”to naji zahra tashi kije kar mummy ta nemeki,”

Miƙewa tayi a hankali,tabar gurin tana waigenshi.

Shima miƙewa yayi yaja motarsa zuwa Hammad hospital dan ya sanar da amininsa halin da yake ciki,dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button