Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 23

Sponsored Links

23*

Likitocine suka rufu akanta dan gano meke damunta,
Awanni biyu suka kwashe kamun bincikensu yazama ready,

Kamun lokacin Hammad mummy ya kira a waya ya sanar da ita suna asibiti zahra ba lafiya.

Related Articles

Daddy na gida lokacin daya yo wayar dan haka ɗunguma sukayi zuwa asibitin dan hankalinsu ya tashi.

Sun iso ba jimawa,likita ya buƙaci ganinsu,bayan sun zaunane,likitan ya zare glass ɗin idonshi sannan yaja dogon numfashi yace.

“munyi bincike zahra na fama ne da ciwon hawan jini,sannan zuciyarta ta kumbura,single mistake ze iya janyowa ta rasa rayuwarta,dole ne akaucewa duk wani abu daze ɓata mata rai,ayi mata kuma abinda takeso,insha Allahu zuwa nan gaba zaa iya nasarar warkewarta gaba ɗaya”

Hammad hannu yasa ya dafe kansa,hawaye na bin idanunsa,yaushe ne zahra zata tsira daga baƙin cikinsa?yaushe ne zahra zata mori rayuwarta kamar kowa?wannan sune tambayoyin dake yawo a kansa.

Magunguna likitan yabasu,jiki asanyaye suka fito daga office ɗin daga mummy har daddy kallon tuhuma sukewa hammad ɗin.
Hakanne yasa ya kasa zama cikinsu ya koma can gefe ya takure,yana adduar Allah yaba zahransa lafiya.

Baa basu damar ganinta ba se bayan kwana biyu.har rige rige suke gurin shiga ɗakin da take,hammad daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta,sosai tausayinta ke nuƙurƙusar zuciyarsa,ta rame lokaci guda tayi fari sekace wacce ta shekara tana ciwon.

Har lokacin bacci take, sede bana daɗi bane,dan oxygen ne a bakinta.ga sauran naurori da suka kewayeta.

Hammad sosai lamarim ya firgitasa kuka sosai yakeyi da ƙyar daddy ya rarrasheshi.

Wata guda Zahra ta kwashe a asibitin sannan ta samu sauƙi,koda aka sallameta fafur tace ita gun mummy zata koma,dole hakan akayi dan gudun ɓacin ranta.

A iya zamanta a asibitin magana bata taɓa haɗata da hammad ba,dan ko ganinsa batason yi,yana shigowa take lumshe idonta,

Duk abinda ke faruwa iyayensu na lura dasu sede basu sa kansu aciki ba tunda basu sako su ba.

Hammad ji yake kamar zeyi hauka gudun gidansa da zahra tayi daurewa kawai yakeyi,kallo ɗaya zakai masa ka ɗauka ya shekara yana ciwo sabida tsabar ramar da yayi.

Ɗaki guda mummy ta ware mata,sannan taci gaba da kulawa da ita.

Hammad rashin zahra kusa dashi ba ƙaramar illatashi hakan yayi ba,shiyasa kullum yana gidansu shima ko ze samu sauƙi,gashi fafur taƙi bari su haɗu.

Bayan wata biyu da dawowarta gidan,tasamu mummy a ɗakinta,bayan sun gaisa tace”mummy inaso ne inci gaba da karatuna tunda nasamu sauƙi”ta faɗi a shagwaɓe.

Shuru mummy tayi tana nazarin ta,zuwa can ta ce,”to ay kinga bamu da iko akan hakan,kije ku yi maganar da mijinki,abinda ya yanke se ki sanar damu mu kuma mu aywatar”mummy ta faɗi fuskarta cike da walwala.

Ran Zahra in yayi dubu ya ɓaci,ita fa bason ganinshi take ba,bare har suyi magana,miƙewa tayi bakinta a gaba alamar jin haushi ta fice daga ɗakin zuwa nata.

Girgiza kai mummy tayi sannan tace aranta”kwayi kwa gama shashancin naku ku koma gidanku”.

Zahra kwanciya tayi tana nazarin ta inda zata ɓullowa lamarin,dan da gaske karatunta takeso taci gaba dayi,ganin bata samu mafita bane yasa ta miƙe jiki ba ƙwari ta nufi ɗakin Hammad ɗin.

Tura ƙofar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama,baya cikin ɗakin,jiyo sautin ruwa tayi a toilet,hakan ne yasa ta fahimci wanka yake.

Ɗakin ta shiga ƙarewa kallo,sosai yayi datti,ga kayan da yake cirewa duk a ƙasa baa kwasheba,inba hancinta ne ba ɗakin har ɗan wari wari taji yakeyi.

fitowa yayi ɗaure da tawul aƙugunsa,yana riƙe da wani ƙarami a hannunsa yana goge ruwan kanshi,sam be kula da ita dake zaune a gefen kujera ba,kamshinta yaji ya daki hancinshi. ɗauka yayi gizon da take masa kullum ne zama yayi gefen gadon ya dafe kanshi hawaye na bin idanunsa yace”haba zahra ta,nace miki na tuba,kiyafemin,nasha wahala sosai arayuwata arashinki,koda na sameki bansan ke bace ƴarfillon danake nema,na rayu cikin so da kaunarki tun bayan faruwar lamarin nan,zahra ki daure kisoni koda rabin wanda nike miki ne”ya ƙarasa maganar hawaye na bin idonsa.
Sosai zahra maganganunsa suka shigeta,sede batajin akwai yafiya tsakaninta dashi.

Gyaran murya tayi,a firgice yakai dubansa gareta,mamakine ya cikashi ta yadda ta shigo ɗakin besani ba.

Jikinshi har rawa yakeyi yataso yazo gareta,tsugunawa yayi ya kama ƙafafunta,ya ɗora kanshi akan cinyarta,ya fashe mata da kuka kamar wani ƙaramin yaro,yana faɗin”ki gafarceni zahra,sharri shaiɗanne yasa na aykata hakan kiyi hakuri zahra kibani damar gyara kuskurena don Allah kimin afuwa zahra na gaza jure raahinki kusa dani”kukan dayaci ƙarfinshi ne yasa yayi shuru.

Zahra lumshe ido tayi hawaye na biyo idonta,sosai take ƙaunar Hammad so ba na wasa ba,haka zalika sosai take ƙin soja me ulcer ƙi bana wasa ba,yazatayi da wannan rayiwa tsakanin so da ƙiyayya.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button