Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 28

Sponsored Links

XVIII….

*Munayamaleek is 500, pay to 3200689860 Haruna Rukayya first bank, then evidence of payment to 07082281566 (Dan Allah idan baki shirya siya ba, don’t chat NoorEmaan)*

 

Related Articles

Ashe fada kawai yake daya ce zasu yi magana da Shakur ɗin. Domin a lokacin ɗaya haɗu da Shakur sai ya kasa furta masa abinda ke ransa, ga son jinjirar nan ta mamaye zuciyar shi ta hana shi sakat.

Shakur kuwa tsaf Ya gane yanayin sa amma yayi kamar bai fahimci bakomi ba, hakan kuma ke kara saka Maleek jin haushin Shakur ɗin.

Shakur ya riga yayi alƙawarin cewa ba zai ƙara yi wa Maleek fada kan kula da munaya ba, wanna jaririyar itace maganin taurin kansa da alama.

Yayi wani murmushin da shi kadai ya san ma’anar sa kana ya fiddo wayarsa, lambar
Barr. Abrar ya kira, domin da safe ya kira ta munayan ba’a daga ba, da alama har yanzu wayar na gida.

“Assalamu alaikum, ina wuni barrister” Shakur ya fada.

“Wa alaikumu Salam, Shakur an wuni lafiya?”

“Lfy Lou, ya baby da munaya, ina fatan suna lafiya?”

“Munaya na bacci, jiya yar taka rigima tayi cikin dare”

“Ayyah! Allah ya kara mata lafiya, ina babyn?” Ya fada yana dan satar kallon Maleek daya mayar da dukkanin kunnen sa ga wayar da yake, a daidai lokacin ya dago suka hada ido, Shakur yayi masa murmushi, Maleek ya ɗauke kansa a ƙoƙarin sa na son basarwa.

Shakur ya ƙara da cewa ” barin kira video call in ga fuskar baby dita” ya fada yana katse kiran, cikin abinda bai kai mintuna biyar ba fuskar baby ta bayyana a screen din wayar sa.
Yace “hello cutie, shhhhhhhhhh” ya karasa da sigar da ake yiwa yara wasa, Maleek ya mike tsaye ya fara dube-dube kamar mai neman wani abu, ya dan dinga mika wuya ko zai gan babyn ta Wayar amma bai hango ta ba, hakan ya saka ya mike ya zagaya ta baya yana fadin “where did I misplaced this paper, ina na ajiye wanna takardan ne?” Ya tambayi kansa yana dube-dube, daidai lokacin daya karasa bayan Shakur ɗin domin ya more kallon sa, a lokacin kuma Shakur ya mike ya fice daga office ɗin yana cigaba da fadin “cutie, zan zo na gan ki kinji, be a good girl karki damu mummy, ki barta ta warke kinji?”

MALEEK ya dafe kugun sa daya da hannunsa, yana bin Shakur da kallo ta kofar glass din, kamar ya buge shi ɗan takaici, ya koma ya zauna, yana dafa kansa, tunanin mafita kawai yake.

A hankali munaya ke fitowa daga toilet, idanun ta sun yi ja, wankan jego tayi amma na towel tare da taimakon Barr. Abrar…
Ta samu gefen gadon asibitin ta zauna da kyar, ta juya ga yarta dake bacci ta zuba mata idanun ta.
Barrister Abrar dake tsaye a kanta tace “Munaya kina ji kamar ki hadiye ta ɗan so ko?”
Cikin sauri Munaya tayi kasa da kanta Cikin jin kunya.

Barrister tayi murmushi ta kara da cewa “soyayyar uwa kenan, tashi ki saka kaya kafin baki su fara zuwa”

Ba musu Munaya ta mike, ta shafa mai, da taimakon barrister Abrar ta shirya cikin doguwar rigar ta material peach color mai laushi, barrister ta zuba mata lafiyayyen kunun madara da kosai mai zafi.
Bayan ta gama yin breakfast, barrister Abrar tace “Yakamata a saka wa yarinyar nan suna, pure heart ma ya min maganar, amma nace zan tutunbe ki First, shin akwai suna da kike sha’awar a saka a mata?”

Munaya ta jinjina kai, kana cikin rawar murya tace “Amnah ta zan yi takwara, sunan ta nakeso a saka”

“Masha Allah, hakan ma yayi, amma menene asalin sunan Amnah din?”

“Nabeelah, Nabeelah sunan ta”
,,
“Masha Allah, Allah ya raya ta, ita kuma Allah jikin ta”

Rufe bakin barrister ke da wuya aka kwankwaso kofar, taje bakin kofa ta bude, Shakur ne ya shigo yau ma hannun sa dauke da leda.

“Shakur kaine da safen nan?”

“Eh wallahi, ina da class anjima, nace barin fara zuwa nan”

“Toh sannu da zuwa, shigo” barrister tace cikin fara’a tana matsa masa, ya shigo dakin sosai, ya ajiye ledar hannunsa, kana ya dauke jaririyar bakinsa kamar gonar auduga domin farin ciki, wani kyau yaga yarinyar na ke karawa a kullum.

“Ya Shakur ina kwana?” Muryar munaya ta katse masa kallon sa.

“Oops my bad, ki min uzuri bana ganin kowa yanzu sai baby na” ya fada yana dafe kansa, murmushi mai sauti munaya tayi a kullum kimar Shakur ke daduwa a ranta.

Ya kara cewa “kin tashi lafiya ya jikin ki?”

“Da sauki, ya Shakur baka gajiya da dawainiya?” Munaya ta tambaya tana kallon ledar dake kasa.

“Kin taba ganin inda uba ya gaji da yiwa yarsa hidima?”

Munaya ta girgiza kai, tana jan yatsun hannunta, yayi murmushi yace “kina da sunan da kike so a sanya wa babyn?”

“Eh maganar da muka gama yi kenan ka shigo”
Barrister ta sanya musu baki.

“Toh Masha Allah. Wani suna ta zaba” yace yana kallon barrister Abrar ɗin.

“Nabeelah, islamic pet name Kuma Amnah”

“Masha Allah, sunan yayi sosai” ya fada yana murmushi kana a hankali ya dora bakin sa a kunnen jaririyar ya rada mata sunan.

“Allah ya raya mana little Amnah”

“Ameen” barrister ta amsa, a ranta tana mamakin anya dan’uwan Shakur ɗin nan Maleek na da hankali kuwa, ace har yanzu bai zo ba, ko dan yarsa?

Kwana Munaya biyar a asibiti aka sallamo su bayan an tabbatar da lafiyar su kalau, bayan Munaya ta shiga dakin ta nan ta ga an sauya mata gado da katifa zuwa mai girma, haka ma wardrobe dinta, ga kayan little Amnah da aka cike shi a wardrobe daya, komai na dakin ya sanja ya kara kyau, har home decor aka kara wa dakin.

Ta juya ta rungume barrister Abrar ta fashe da kuka, “Mami ngd, Allah ya saka muku da alkhairi”

Barrister ta shiga bubbuga bayan ta alamun tayi shiru, kana tace “ya isa haka, barin je a daura ruwan wankan ku, zauna ki bata ta sha kafin na dawo”

“Toh”Munaya ta amsa a hankali tana zama a bakin gadon, ta ɗauki babyn dake witsil-witsil da kafafu zuwa cinyar ta.

Zuwa yanzu ta fara sabawa da tsotso irin wanda little Amnah ke yi, zata kula da yarta da dukkanin karfin ta, girman daya hau kanta a wandanan kananun shekarun ta karba.
A hankali ta fito da mamar ta ta sanya wa little Amnah a baki, ta karba ta fara sha, Munaya ta shiga shafa fuskar ta “kanwataaa” ta fadi kalmar a sanyaye cikin jan fasali, taji hawaye ya ciko idanun ta tunani mabanbanta ne suka ziyarci ƙwaƙwalwar ta cikin abinda bai fi dakika goma ba, kifta idanun ta da ta yi ne shi yayi sanadiyyar zubar kwallar daya cika idanun ta.
Ta share hawayen cikin sauri, little Amnah ta bude idanunta da sak irin na Maleek ne, hanci kadai ta dauko irin na munaya.
Ta saka ƙaramin yatsan ta cikin hannun little Amnah, karaf yarinyar ta rike gam, munaya ta saki murmushi tana lumshe idanun ta, ina ma abubuwan nan basu faru ta wanna hanyar ba? Ina ma komai ya tafi kan turban addinin Musulunci daga samun little Amnah, ina ma Amnah dinta na raye, ta haifi takwarar ta, ta san data yi farin ciki sosai, sai dai all this are just a dream and her imagination. Taso ko da ta rasa dukkanin abubuwan nan amma ta tsira da budurcin ta, amma bata isa tsallake ƙaddarar ta ba, wanda ta sanadiyyar wanna ƙaddarar ta samu wanna innocent baby dake hannun ta, wanda take jin son ta har ruhin ta.

Munaya bata san anyi wa little Amnah yanka ba sai Bayan an yanka din.
Hakika little Amnah ta samu dukkanin wani gata da ake yiwa jarirai, A wanna rana tayi godiya sosai ga barrister Abrar, ta kuma ce ta taya ta yiwa doctor Aaban din godiya domin ba kasafai suka haduwa ba.

A wanna daren munaya tayi mafarki da Amnah, ta ga Amnah ta kara tsayi, tana tsaye cikin wani kyakkyawan garden, yayinda ita kuma munaya ke cikin tafiya.
A mafarkin Amnah tace “munaaaaaa” ta kira ta da irin salon da takan yi amfani dashi a lokacin da suke duniya daya tare.

Munaya ta juyo ta ga Amnah ce tsaye cikin fararen kaya tana daga mata hannu alamun bye bye fuskar ta ɗauke da murmushi.
Munaya ta shigo tahowa domin cimma Amnah, farin cikin ganin kanwar ta bayyane a fuskar ta, sai dai tana daf da karasa wajen ta, taga Amnah ta bacewa idanun ta, ta durkusa a wajen tana kuka sosai har ta farka daga bacci, hawayen da take yi a mafarki shi ta gani cabe-cabe a fuskar ta, ta shiga kallon dakin, ta san dai a mafarkin tayi kuka amma Meyasa ta ga hawayen ta a zahiri, kanta ya kulle, yayinda kewar tilon kanwar ta ya dawo mata sabo a ranta, she wish zata kara ganin ta a rayuwa ko da sau daya tak ne, ta goge idanun ta, daidai lokacin da ake kokarin turo dakin, ta san barrister Abrar ce, domin a kullum sai ta shigo Kusan sau biyar duba su Kafin gari ya waye.

“Munaya! Lafiya?” Ta karasa maganar tana dafa ta.

Ta dago kanta tana kirkiran murmushin dole kana tace “bakomi Mami”

“Okay, little bata yi kuka ba ko?”

“Eh, tun sha biyun nan bata farka ba”

“Aah ta fara wayo kenan, dama wasu yaran na rigima farko farkon zuwan su duniya amma suna daina wa idan an kwana biyu, ki koma ki kwanta, zan dawo anjima” barrister Abrar ta fada tana kokarin barin dakin.

“Mami!”

“Na’am” barrister Abrar ta fada tana juyowa.

“Dan Allah Mami ki kwanta ki huta kema”

Barrister Abrar tayi murmushi tana fadin ” koda na kwanta bazan iya bacciin ba, Allah ke tsarewa, amma a matsayina na babba ya kamata in dan dinga duba ku”
Munaya tayi shiru ta kasa magana.

Shakur da Maleek na zaune a garden da misalin karfe shida na yamma suna hutawa, wayar Maleek tayi kara alamun shigowar sako, wayar tayi haske hakan ya saka Shakur ganin hoton little Amnah daya mamaye screen din wayar sa, ya cika da mamakin zurfin ciki irin na Maleek, ace kana son abu ka gagara furta wa Bayan gashi baroro rubuce a fuskar sa.

MALEEK kuwa ko duba sakon bai yi ba duk da yaji karar, domin abinda ya damu zuciyar sa daban, har wani xuru-xuru yayi saboda tunanin little Amnah. Amma nukunfurci da girman kai sun hana shi furta abinda ke cin sa a zuciya, ya Kuma ga da gaske Shakur yake bai da alamu ɓalle niyyar sanar da shi ko yi masa maganar jaririyar sa.

Suna a haka wayar Shakur ɗin tayi ringing ya dauka, doctor Abbas ne cikin sakkakiyar murya Yace “Barka da yamma doctor”
“Yawwa Barkan mu dai Shakur, kwana biyu? Haɗuwa tayi wuya”

“Wallahi, Bama haduwa a wajen munaya. Ya kira sunan Munayan da biyu

“Eh wallahi, na dan tafi karo wani course ne, amma jiya na samu na duba su, naga little Amnah sai kara girma da wayo take, nan gaba zata fi mamanta girma da alama”

Shakur yayi dariyar jin dadi yace “wallahi, ai little Amnah na girma sosai alhamdulillah”
Daga lokacin da Shakur yace Little Amnah Maleek ya Daina fahimtar komai, nazari ya shiga, wacece little Amnah din? Ba dai yarsa ba?

“Toh nagode sosai doctor sai anjima” abinda Shakur ya fada kenan yana katse wayar.

Ya kalli Maleek yana sakin murmushi, kana ya tabo shi yace “Are you okay?”

“wace Amnah?”

“Baka san ta ba?” Shakur ya fada.

“Ba dai baby na kake nufi ba?” Maleek ya kara tambaya.

“Baby? Dama kana da baby bansani ba?” Abinda ya tsana kenan a raina masa hankali kuma shi Shakur ke masa.

Cikin ƙarƙashi mai cukurkurde da ɓacin rai yace “eh ina da y’a”

“Wow, and you never told me, where’s she now?”

“Shakur!” Maleek ya kira shi cikin kakkausar murya yana kokarin danne zuciyar sa domin yana daf da fusata.

“Maleek meya faru haka? Tambaya mai sauki na maka nace ina yar taka?”

Ya murza hannun sa, har zai ce wacce ya gani a status ɗin shi sai ya ga hakan ai dolanci ne, it doesn’t make any sense ace wai yaga yarsa a status, ya cije labbansa yace “wacce kaje wajen ta shekaran jiya”

“Oh I thought baka da alaka da ita”

“Shakur Please stop all this, you know i hate it, waye ya rada mata suna bayan ko shawara ta ba’a nema ba.

“Okay, akwai sunan da kake son saka Mata ne” Maleek ya fada hankalin sa a kwance cikin rainawa Maleek din hankali.

“Yeah” ya amsa.

“Okay wani suna kake so?”.

“Bilkeesu sunan mahaifiyata nake son a saka Mata, sannan islamic pet name din ta kuma Fadwa”

Jikin Shakur ɗin yayi dan sanyi jin ya ambaci sunan Mahaifiyarsa data rasu, lallai ba karamin abu bane ya saka Maleek din tuna ta har yaso a saka Mata sunan ta, domin ya san shi kan shi Maleek yana manta cewa ba Hajiya Sa’adah bace real mother din sa ba. Babu abinda zai iya yi,
baƙin alkalami ya bushe, ba zai dinga tauye munaya ba, saboda farin cikin gudan jinin sa ba, ita ma tana da hakki akan jaririyar, domin tafi kowa sanin wahalar ta.

Ya sauke boyayyar ajiyar zuciya, so yake Maleek ya gane kuskuren sa amma ta ruwan sa, “ai Allah ya raya mana Nabeelah, inkiya Amnah kawai, it has been done and dusted”

Cikin fusata MALEEK yace “ban gane ba, da izinin wa aka bata wanna sunan?”

“Da izinin Munaya, mahaifiyar ta, wacce tasha wahala da ita tun tana ciki har tayi wata goma Kafin ta haifo ta, kuma karka manta, sunan wacce a silar ta aka samar da babyn nan aka saka”

Da alama maganar Shakur ta ƙarshe ta shige shi, yayi shiru na mintuna biyu kana yace
“Ni a bani yata, zan kula da ita, zan kuma samo nannies da zasu kular min da ita. Ya fada kamar wanda ya zare.

Shakur ya mike, Cikin jin haushin halin Maleek din yace.

 

 

_Mu haɗe Monday, Dan Jin yanda zata kaya, zan sha Panadol domin Maleek ya bani headache, mutumin ku Maleek fa bai dai rashin m ba, ga ba kunya, ko da yake ya sha a maman Hajiya Sa’adah ne_🙌🤭😂

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button