Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 43

Sponsored Links

Ban yi Edited ba.. bear with meDa hannun bibbiyu Abuturab ya riƙe kansa yana kallon ƙyakƙyawar jaririyar da matarsa ta mutu ta bari. Mama dake Kallonsa tayi jigum ta ce “Ka yi haƙuri, ko wanne mai rai mamaci ne, damuwata har yanzu ban san mene ya samu Maysoon har ya yi sanadin Ajalinta ba” Abuturab ya yi shiru yana jin wani iri a ransa. Kallonsa kawai Mama take kafin ta ce “Na yarda da kai na aura maka ƴar mutane ta zauna dakai a yadda ta sameka, Ali wallahi muddin ka saɓawa yardar da na yi maka Ubangiji ba zai barka ba, zaka samu jarrabawa ta yadda baka yi tsammani ba, gwara tun wuri idan akwai wani abu ka faɗa mini” A hankali Abuturab ya ce “Are you accusing me, Mom?” Ta girgiza kai ta ce “Ba zarginka nake ba, kawai dai tunatarwa na yi maka” Ya jinjina kai ta ce “A sakawa jaririyar sunan uwarta Maysoon” Da sauri ya ce “No Mama” Ta ce “Why? I don’t think it’s a crime to inherit her mother’s name, no matter what, we’ll always remember her” Cikin rauni da siga ta tausayi ya ce “Mama zan dinga jin kamar zata dawo gareni ne, ni kaɗai na san abinda ke damuna, ko a saka sunanta ko ba a saka ba, she’s always be on my mind, she’s a kind and nice person da ban taɓa ganin irinta ba, so Please Mama ki yi haƙuri kada a saka sunan Please” Mama ta tsora masa idanu kafin ta ce “To wanne sunan kake so?” A hankali ya ce “Hawwa’u, we can call her Jidderh” Mama ta ce “Hawwa’u?” Ta tambaya da mmki ganin ka kaf Familynta babu mai irin sunan ya yi shiru. Ta ce “Ubangiji ya rataya, ya bata haƙuri irin na mahaifiyarta” Miƙewa ya yi zuwa part ɗinsa sbd jin muryar ƴan gaisuwa duk da ya hana zaman makoki for no reason. Kwanciya ya yi yana lumshe idanunsa tun auren su da Maysoon bai samu nutsuwa ba, gani yake kamar ya ci amanar wacce zuciyarsa take so da ƙauna da muradin kasancewa da ita, yanzu kuma wani irin sauƙi yake ji da nutsuwa ko babu komai she’s pass away frm his life,She was out of his life, He will live without constraints, he will live from him only what his heart wants. Ajjiye babyn ya yi yana jin son yarinyar har ransa musamman idan ya tuna sunan data mallaka. Wayarsa ce ta fara ringing a hankali ya duba ganin mai kiran ya sanya ɗauka. A nutse ya ce “Barka” Daga cikin wayar aka ce “Ka duba news kaga meke faruwa?” Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce “Bana ce ba, kasan am not in the mood” Mutumin ya ce “Motar ƴan boarding school dake tafiya zuwa wani abu na makaranta aka cinnawa wuta, ɗalibai sama da 500 sun ƙune ƙurmus ga kabari mutane wajan goma da aka tune aka kwashe gawarwakin an rasa waye, Hon ina jin tsoro baka tunanin jam’iyyar hamayya ta aikata wannan abun sbd kawai taci mulki? Ko wani asiri suke ki tsubbu?” Miƙewa Abuturab ya yi zufa na yanko masa ya ce “Yanzu Sir al’amarin har ya kai sbd son mulki a sanwaltar da rayukan al’umma wanda basu ji ba basu gani ba? Me ake son zama ne?” Mutumin ya ce “Calm down Hon, ina tunanin we can do something about that” Ya ce “Kamar m” Ta cikin wayar aka ce “Mu je makarantar mu jajanta lamarin mu bawa iyayen ko wanne yaro haƙuri da kuma ɗan wani abu, tare da al’ƙawarin yin bincike idan jam’iyyarmu ta samu mulki” Tattaunawa sukai kana suka sauka akan layi.
After 1weeks
Majeederh na zaune tana duba wasu files da aka turo mata na Human rights akan wani cases da ake son ta taimaka kamar daga sama taga Abbu ya shigo cikin sauri ta ɗago kanta ta dube shi jikinta duk rawa yake ta kasa cewa komai Abbu ya ce “Hawwa’u me ya kai ki Bristol Palace Hotel?” Wani irin bugawa ƙirjinta ya yi ta ce “Hotel Abbu?” Hannu ya ɗaga ya zabga mata mari ya ce “Are answering my questions with a question? How dare you?” Yatsunsa ya fito sosai akan fuskarta sosai idanunta ya shiga fitar da hawaye ta ce “Abbu ban taɓa zuwa Hotel ba, don Allah…” Wani marin ya kuma sauke mata idanunsa sukai jajur kamar zasu fito waje yama kasa magana sai pointing ɗinta da hannu da yake “Ban haifi yarinyar da zata ɓata mini sunan family da nawa ba, kin yi kadan zaki san cewa ni na haifeki ba kece kika haifan ba wallahi lokaci kawai nake jira” Kuka take sosai kamar ranta zai fita ta ce “Why should i do that Abbu? Wallahi ban taɓa zuwa Hotel ba mene ribata bayan nasan illar hakan don Allah Abbu…,” Hannu ya ɗaga ya ƙara sauke mata wani marin kafin ya ce “Idan ba ki ki Hotel ba to wace wannan? 1week ago wacce ta je gidan ƙartin maza? Past week’s waye ya dinga hauro mini gida yana shiga ɗakin ki? Ko shi ma bake bace baki san anyi ba? Shekaran jiya kin ce mini zaki wani meeting a Abuja daga nan mene ya kai ki Lagos?” Wani irin kuka take sosai bakinta na rawa ta ce “Abbu zan maka bayani wlh ba abinda kake tunani bane” Jin hayaniya ya saka Mami fitowa Main parlour, Raihana ta fito itama da sauri Mami ta ce “Meke faruwa ne?” Da hannu Abbu ya ce
“Hawwa’u zata saka mini ciwon zuciya, tana sane ta ƙi yin aure take yawo tarbiyyar dana baki kenan? Na yarda dake na amince miki shi ne zaki aikata mini haka? Kin san bana iya bacci sbd damuwarki, burina kawai na ganki a ɗakin mijinki kamar sauran ƴan uwanki amma abin ya ci tura, ashe haka zurfin ilimi ke jawowa?” Mami ta ce “Take ur heart please Alhji baka da lafiya ka dinga bin komai a sannu Please, kada ka yanke hukunci ba tare da bincike ba” Abbu ya ce “Wanne irin bincike bayan wanda na yi? Komai nake idanuna yana kan Majeederh bani da cikakkiyar nutsuwa private Investigators nawa na saka akanta?” Da wani irin tashin hankali Majeederh ta ce “Zargina kake Abbu? Innalillahi wa’inna ilahir raji’un na shiga uku, wallahi Abbu ban taɓa aikata sabon Ubangiji ba, ba zan taɓa cutar da tarbiyyarka ba da nayi haka gwara mutuwata, taimakon al’umma musulmi kawai nake” Wata zabgegiyar bulala ya ɗakko ya nufi Majeederh zai daka da sauri Mami ta shiga tsakani idanunta na zubar da hawaye ta ce “Haba Alhaji idan rai ya ɓaci nutsuwa ake samu, hankali ke nemo shi, idan ka yarda da Majeederh tun farko bai kamata ka zargeta ba yanzu, zargi haramun ne a musulunce wlh” Yana huci sosai ya ce “Leave, Asabe ki matsa daga nan ko na haɗa dake” Mami na kuka sosai ta ce “Wlh sai dai ka dake mu tare, na fara gajiya wanne irin mutum ne wai kai? So kake a zageni ace sbd bani na haifeta ba? Ka sassautawa zuciyarka, kabi komai a sannu faɗa baya magani idan ba kangarar da yaro ba, ko ƙaddara ce fa ta faɗa mata dole ka zauna da ita ƴarka ce jininka ce hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar” A wannan karan hatta Raihana sai da ta ji tausayin Majeederh, babbar mace mai shekaru ilimin addini dana boko kuɗi hankali nutsuwa amma ita ake doka kamar Ƴar shekara biyar. Zubewa Abbu ya yi dafe da kansa dake juya masa yana jin kamar zuciyarsa zata fashe, shigowar Abraham cikin main parlour ya sanya Abbu miƙewa da sauri ya ce “Ban hanaka shigo mini cikin gida ba? Ban hana mara tsafta me yawo da datti ya dinga shigo mini cikin gida ba? Ban hana mara gata da ƴanci wanda bashi da mara da almajirin kan titi shigo mini gida ba?” Abraham kallon Majeederh dake durƙoshe yake wacce gefen bakinta ya fashe, ta kasa ɗago kanta ta kalli Abraham sbd gujewa ganinsa da take rabon data ganshi ma ta mance ta rufe duk wata hanya da zata haɗata da shi ba da son ranta ba. Abbu ya ce “Da kai nake magana?” Abraham ya zame idanunsa ya kalli Abbu, sauyin idanun Abraham ya kaɗa hantar cikin Mami. “What brought you into my house?” Gently Abraham ya taka har gaban Abbu ido cikin ido ya ce “Ƴar ka nake so” Hatta Mami ta jijjiga da wannan maganar ta Abraham, Abbu kuma ji ya yi zuciyarsa ta tsaya na wani lokaci cikin rashin fahimta ya ce “Me ka ce?” A takaice Abraham ya ce “Zan auri Mamina” Abbu ya ce “A sbd kai Mahaukaci ne?” Shortly ya ce “Akan ta, ni Mahaukaci ne Grandpa ya turo ni wajanka just to ask ur permission na aurenta” Abbu ya juya ya kalli Majeederh wacce kanta ke sunkuye sai numfashi take da ƙyar ya dawo kan Abraham ya ce “Ka zo gidana, a gabana ka kalli cikin Idanuna ka ce kazo auren ƴata?” Abraham ya ɗan watsa kafaɗa tare da fito da Teller ya ce “Daga 1m zuwa ko nawa ka faɗi kuɗin da kke buƙata yanzu ka bani ita mu tafi” Mami ta ce “Son ta kake?” Ba tare daya kalleta ba ya ce “I don’t know, kawai ina son auren ta” Abbu ya ce “Mara addini kamar ka shine zan bawa auren ƴarta? Wanda bashi da gata, Ahhali mai yawo da ƴan iska suke fashi da bindigogi zan bawa auren ƴata? Mai Shaye-shaye da yawo da mata wanda yake gidan kansa maimakon na iyayensa shi zan bawa auren ƴata?” Abraham kallo Abbu kawai yake ba tare daya damu ba ya ce “Yanzu ma kuɗin auren nata ai fashin su na yi” Majeederh dai ta kasa motsi zaka iya ɗauka bata cikin hayyacinta ne Abbu ya ce “Ban yi mamakin hakan ba, bari na faɗa maka abinda baka sani ba, wallahi tallahi dana aura maka ƴata gwara naga gawarta, dana aura maka ƴata gwara ni na mutu, dana aura maka ƴata gwara duk me zai sameta ya sameta, dana aura maka ƴata gwara naga ta zube mini shego gwara ko wacce ƙaddara ta faɗa mata” Da wani irin tashin hankali Majeederh ke kallon Abbu sbd jin furucinsa wanda ya gigita ta ya sauya mata lissafi tunaninta ya tsaya, kalmar shego ta nemi tarwatsa mata zuciya da sanya wa ta jita kamar matacciyya. Mami ta ce “Alhaji kasan me kake cewa kowa? Kada ka jawa Majeederh masifa da bakinka” Abbu ya ɗagawa Mami hannu ya ce “Ki daina saka mini baki cikin maganata Asabe” Mami ta zaune tana rushewa da kuka. Abraham jijiyoyin kansa suka fito tare da yin raɗa raɗa saman goshinsa silently ya ce “Ohk, ka shirya ganin babies” Yana faɗin hakan ya juya tare da ficewa daga cikin gidan a hanya suka haɗu da Latifa dake shigowa Murmushi tayi masa ta ce “Our son kana ta girma abinka wajan Mamin taka ka je?” Ko inuwarta bai kalla ba balle ya bata amsa shi duk duniya da Majeederh kawai yake duguwar magana. Yana zuwa mota Taj ya buɗe masa ya shiga gidan baya, Salamon na gaba shi kuma Taj ya nufi mazaunin driver bayan sun fice daga cikin gidan Taj ya ce “Bad boy ya amince?” Abraham ya yi shiru Salamon dake danna waya ya ce “What did i miss?” Taj ya ce “Bad boy ya je neman auren Mami” Da wani irin sauri Salamon ya juya ya kalli Abraham dake bayan mota idanunsa rufe ya dunƙule hannayensa ya birkita sumar kansa ya dawo da ganinsa kan Taj ya ce “Shawarar wace wannan?”Taj ya ce “I, to me zai zauna jira kawai ya aureta” Salamon da wani irin yanayi yake kallon Taj kafin ya ce “Wai mene ruwanka da rayuwar Abraham ne? Me yasa kake sawa ya aikata abinda bashi kenan ba? Daman haka ake neman aure a musulunci? Kawai ya tunkari mahaifin Mami ya ce he wants to marry his daughter ko me?” Taj ya ɗaga shoulder ya ce “Is just a suggestion, kawai na duba yanayinsa baya bacci cikin kwanakin nan kullum kiran sunan Mami ni kuma i can’t take it anymore” Salamon ya ce “U can’t take it a matsayinka na ubansa ko uwarsa ko kuma me?” Taj ya ce “A’a kada ka zageni bafa fini son Bad boy kayi ba, ina yin komai sbd farin cikinsa da kwanciyar hankalin sa ai shi ya sani idan kai baka sani ba” Tuni zuciyar Salamon ta fara kaiwa ƙarshe ya ce “Farin cikinsa ko kuma ɓata shi? Ka bashi ƙwaya ya sha ka saka masa maganin felling da burin ya yi wa Maminsa Fyaɗe Allah ya taƙaita, ka kirata har gidansa ta da burin ta ganshi kwance da Debeka, ka haɗa plan da Engagement, yanzu ka sanya ya je wajan mahaifinta wai ya bashi aurenta are you mad….,” Da ƙarfi suka ji Abraham ya ce “Stop the car” Taj ya tsaya bakin titi cikin ƙara ji Abraham ya ce “Salamon get out of the car, bana son ganin fuskarka har abada” Murmushi kawai Salamon ya yi yana kallon Taj ya ce “Wannan shi ne abinda kake buƙata?” Taj bai ce komai ba, Salamon ya buɗe ƙofa ya fita tare da matsawa can gefe da gudu kuma Taj ya ja motar sai Club. Wine yake tsiyayawa Abraham yana zubawa cikinsa sai da ya sha ya yi tatul kafin Taj ya ce “Bad boy ni zan tsaya maka ko kowa zai gujeka ka mini halacci a rayuwa, Salamon son Maminka yake” Sai a lokacin Abraham ya buɗe rinannun idanunsa ya kalli Taj wani irin kallo yake masa kafin can ƙasa ya ce “I’ll kill you Salamon” Taj ya ce “Ganin yana son ta shi ya sa nace bari kawai mu fara da neman auren amma tunda Abbu yaƙi kawai ka tafi gidan Uncle Isma’il yanzu kafin Abbu ya bata auren wani a daren nan” Cak yaga Abraham ya miƙe yana tangaɗi daga shi da three quarter ya zari key ya nufi hanyar fita daga cikin Clun ɗin da ƙyar, murmushi Taj ya yi ya ce “Well-done Abraham Daniel David”
Uncle Isma’il da Uncle Bello sai Abbu na zaune a compound na gidan Uncle Isma’il su kaga an buɗe gate wata dalleliyar mota ta shigo, gabaɗaya suka kalli motar banda Abbu da kansa ke ƙasa, Abraham ya buɗe murfin motar da ƙyar ya fito yana layi da tangaɗi ko idanunsa baya iya buɗewa sbd wine ɗin da Taj ya bashi mai ƙarfi ce, bibbiyu haka yake ganin su Uncle Isma’il, Uncle B ya gyara zama ya dinga bin Abraham da kallo har ya ƙarasu ya zube akan qiwwoyinsa ya lumshe idanunsa. Uncle Isma’il ya ce “Khalil lafiya?” Abraham ya yi shiru, Abbu ya miƙe zai bar wajan Uncle Bello ya ce “Ka zauna plx” Ya koma ya zauna daman alrdy ya shaida musu everything daya faru. Dafa shoulder ɗin Abraham ya yi ya ce “Khalil me kake so?” Kansa a ƙasa a hankali ya ce “Mami” girgiza kai kawai Uncle Isma’il ya yi ya ce “Mamin take kake so yanzu kuma?” A hankali ya ce “Yes, ina so Mami” Ya ce “Khalil bana jin ko ka kasance Musulmi Majeederh zata amince ka aureta, ta raineka da hannunta ta kula da kai da ace tayi aure babu mamaki ta samu ɗa kamarka, addininmu da naku ba ɗaya bane, babu yadda za a yi ka auri Majeederh, yau da ace kai Musulmi ne ita Christa to da sauƙi, amma kana Christa tana Musulma kuma Malama? Ba zai taɓa yiyuwa ba, ka yi haƙuri Ibrahim” Abraham baya fahimta bai kuma san haƙuri ba ya ce “Uncle Mami, ina son zama da ita” Ganin kamar zai basu matsala ya sanya Uncle Bello cewa “Ohk, ka turo iyayenka sai a saka muku date na bikin” Da ƙyar suka lallaɓa shi ya shiga mota yabar gidan. Uncle Bello ya kalli Abbu ya ce “Wai lamarin Majeederh ke damunka ne Alhji Abdul’aziz?” Abbu ya ce “Me ya sa ba zai daman ba?” Uncle Bello ya ce “Gaskiya bai kamata ya dameka ba, sbd komai ya faru kai ka siya da hannunka, akwai ƙaddara amma tana zuwa da sanadi, tun Majeederh na da 20yrs a duniya ta nuna aure take so, amma kayi burus ka nuna kamar baka sani ba, kamar baka san meke damun ƴarka ba, Imran ya fito aurenta ta kure shi sbd kawai cikar burinka, bata san karatu amma haka ta daure ta maida kanta kamar namiji ta tafi wata ƙasar tsayin shekaru Takwas, ta dawo ka tilasta mata fara aiki, yanzu kuma ka samu abinda kake so shi ne zaka damu sbd ba tayi aure ba? Allah zaka ma wayo ko ka nuna masa dabara kenan? Muna rayuwa da ƙaddararmu wacce Ubangiji ya tsara mana, ƙaddarar jinkirin aure ta samu Majeederh sai ka tayata amsa kayi mata addu’a, kuma ka bar ƙaddara ta yi aikinta” Abbu kallon Uncle Bello kawai yake, Uncle B ya ɗora da faɗin “Yanzu da kake zargin Majeederh a matsayinki na mahaifinta mu kuma da jama’ar gari mu ce me? Da Majeederh zata lalace to da tun a Misira hakan zai faru, ka gode Allah ka masa mubaya’a akan yadda ya tsara lamuransa, komai ya sameta a rayuwa kai ne sila, sannan daza ka yi wannan lalataccen furucin akan Abraham shi me ya yi masa zafi? Mutumin da yake da zuciya na ci, da taurin kai ka zafin rai, baka tunanin kalamanka su haifar da wani abu? Kai fa uba ne komai ka faɗa akan ƴarka Immediately Mala’iku za su amsa su rubuta, idan Allah ya ƙaddara Abraham mijinta sai kaga ya musulunta kuma ya aure ta” Abbu ya ce “Har abada ba zan taɓa bawa lalataccen yaron can auren yarinyata ba” Uncle Isma’il ya ce “Idan da rabo mai zafi sai kaga ya kashe ka, rashinka a duniya babu abinda zai hana, ka karɓi ƙaddara a yadda tazo domin allon lauhil mahfuz baya rubuta abin da ba daidai ba, komai ta faru da sanin Ubangiji, zanen ƙaddararta kenan”
After 2 yrs. Lokacin Majeederh nada 33yrs a duniya Abraham kuma 18 Abubuwan sun faru, tashin hankali fiye dana baya, Majeederh ta gujewa Abraham ya haukace baya iya ci baya iya sha duk wani abu da ta hana shi baya yi amma ya fita daga hayyacinsa, ganin hakan yasa Abbu barinta tafiya aikin Hajji bayan an kammala Azumin Ramadan. Fitowarta kenan daga bathroom ɗaure da towel duk ta rame tana daga tsaye taga kamar gilmawar shadow da sauri ta ɗauki hijabi ta saka tana juya idanunta ya sauka cikin na Abraham wanda ya sauya mata ya ƙara yin wani girma na ban mamaki kamar ana ƙara shi kyansa na baƙin ɗan America ya sake fitowa a fili. A kallo ɗaya da tayi masa ta fahimci bashi da cikakken nutsuwa walking slowly ya nufeta da sauri ta ce “Karka zo nan” Ya yi mata banza kamar ana jansa haka ya nufeta kafin ya ƙarasa ta ɗauke shi da mari ta ce “Mahaukaci, to addinina ba irin naku bane, ɗabi’ata tasha bambam da taku kada ka sake mafarkin taɓa jikina, ni ba Maminka bace ok fine ni ma ban haifeka ba, ba zan taɓa haifarka ba ka fice mini daga….,” Caraf ta ji ya cafke lip’s ɗinsa da bakinsa tare da manneta da jikin bango ya shiga….Zare idanu tayi alamar ya haka? Banda bugawa kuma babu abinda zuciyarta take. He was kissing her passionately, the kiss coming from the land of his heart with all love and affection. Takaici ya sanya Majeederh runtse Idanunta wani irin hawaye mai zafi ya shiga gangaro mata ta gefen idanunta, jikinta ya saki ta kasa koda motsa hannunta, tunda ta zo duniya bata taɓa jin wani abu mai kama da wannan ba, ji tayi jikinta ya shiga rawa da ɓari kamar ana kaɗa mata gangi, wani abu ke tsarga mata tun daga kan babban yatsar ƙafarta har tsakiyar kanta. Tsigar jikinta ya shiga tashi yana zubewa ganin yadda jikinta ya ɗauki rawa da ɓari numfashinta na neman ɗaukewa sbd kawai yana kissing ɗinta ya sanya Abraham buɗe idanunsa da sukai jajur yana jin kansa na masifaffen sara masa sbd baƙon lamarin daya ziyarce shi ba tare daya shirya zuwansa ba.
This is the first time in his life that he kissed a woman and the woman he looked upon as his mother. A hankali ya zame bakinsa ganin tayi baya zata faɗi ƙasa ya yi saurin saka hannu ya dawo da ita saman chest ɗinsa hannunsa ɗaya a waist ɗinta, idanunsa ya ware sosai cikin mutuwar jiki ya kasa cewa komai yadda take sauke numfashi haka shi ma yake ganin babu mai ƙauri a cikinsu ya sanya ya ƙara riƙeta sosai a jikinsa yana riƙe kansa da ƙoƙarin ganin ya dawo cikin nutsuwarsa. A hankali ya zame daga inda take yana matsawa ta yi baya zata kifa sbd ta gama tunanin tana jikinsa ta gama sakin jiki bakiɗaya, cikin sauri ta riƙe kanta da kyau tana jan breathing ɗinta da saukewa a hankali, har lokacin jikinta kuma bai gama daidaituwa ba rawa yake still. Idanunta ta buɗe da son nuna masa ko a jikinta ta ce “Ka fita daga cikin bedroom ɗina” Ta faɗa ba tare daya kalli direction ɗinsa ba, shi kuma ya zubawa yatsun ƙafarta idanu yana karantar yanayin da kike ciki, a hargitse ta ƙara cewa “Khalil get out of my room,i Said” gently ya ɗaga kai ya kalleta da rikitattun idanunsa wanda sukai laushi calmly ya ce “Bayan kasancewata Christa mene hujjarki?” Wani irin murmushi ta yi ta ce “Waya faɗa maka sbd kai ba musulmi bane ya sa naƙi amincewa? Da ace ina sonka da na ja ra’ayinka kan musuluncin ai” Ta gyara tsaiwa ta ce
“Ba zan taɓa son ka, ba zan taɓa son yaron cikina ba, ba zan taɓa auren under age irinka ba, kayi mini ƙanƙantar da ba zan iya cewa kai mijina bane, infact i don’t love you, wani gwanini da kai a gabana” Tunda ta fara maganar yake kallonta da wani irin yanayi wanda ba zaka iya tantance shi akan fuskarsa ba, ya nufeta da niyyar riƙe hannunta ta yi saurin matsawa ta ce
“Ya zama last time da zaka ƙara gigin riƙe wani sashi na jikina, addina da naka akwai tazara mai yawan gaske” Rai ɓace kamar Mahaukaci! ya ce “Wanne irin addini ne wannan for God sake? Komai ba kyau” ta fizge hannunta, kau! Ta ɗauke shi da mari ta ce “Mahaukaci, addinina ya fi ƙarfin cin mutuncinka sai a yanka wuyan wanda duk zai aibata Musulunci” idanun Abraham sukai jawur ya ce “Shi addinin ya haramta auren macen data girmeka kenan? Shekaruna 18 mene abun yarinta a jikina? Me ya sa ki ka raina ni? Kawai saboda ni yaro ne, saboda kin girmeni da shekaru goma sha biyar?” “Kai yaro ne”
“Zan wadataki da komai JEE, don kin rai ne ni a lokacin dana rasa iyayena bashi ke nuna ba zan iya zaman aure dake ba, ina soyayyar da kika nuna mini ina yaro? Okay fine, i have a solution! Your father doesn’t like me kawai muyi auren Choci ko kuma wallahi mu haifi ƴa ƴan banza kuma shegu, ko kuma na wulaƙanta addinin Musuluncin naku” Yana faɗin hakan ya fice daga cikin bedroom ɗin. Zubewa tayi saman gado tana riƙe kanta wanda yake juyawa mata, tama rasa wanne irin tunani za ta yi da matakin da zata ɗauka, Abraham na neman zame mata ƙarfe ƙafa. A hankali ta lumshe idanunta da sauri ta buɗe jin tsigar jikinta na tashi har yanzu while bakinta na mata wani iri, Abraham ya bar mata wani irin moment da memory mai wahalar mantawa a zuciya, ya yi abinda babu wani namiji daya isa ya yi shi ya kafa tarihi a rayuwar Majeederh. Shuɗaɗɗan abinda ke damunta shekara da shekaru wanda tayi maganinsa ya dawo mata sabo fil. Gabaɗaya ta hargitse tare da yin luf saman gado ta rungume pillow addu’a take Allah ya kawo mata ko tsoho ne wanda ya girmi Abbu ta aura ku ta samu sauƙin maganganun jama’a ta kaucewa rashin kunyar ɗan cikin nata.. Uncle Isma’il ne zaune a parlourn baƙinsa ya dubi Pasto David kana ganinsa kaka cikakken Christa gaba da baya. Uncle Isma’il ya yi murmushi ya ce “Sir Please ga ruwa nan” Grandpa ya yi murmushi ya ce “My pleasure sir”
Uncle Isma’il ya gyara zama cikin nutsuwa da harshen turanci ya ce “Kafin na ce komai zan su nasan waye kai, kuma na yi maka some of questions akan Abraham” Grandpa ya jinjina kai yana yaba nutsuwar Uncle Isma’il kafin ya ce “David sunana, shugaban church, business man with experience, sai wani secret aikina, kuma Abraham’s Grandfather” Uncle Isma’il ya watsa hannu ya ce “That’s good and i like it, amma Sir daman can Abraham Christa ne?” Kallo Uncle Isma’il kawai Grandpa ke yi kafin ya ce “Maybe, Abraham gaba da baya Christa ne kamar yadda ka ganni ɗin nan, muna ganin kima da matar tabar addininmu kamar yadda kuke ganin naku, muna ƙarfafa al’adunmu mun san muhimmancin hakan sosai, sai dai Abraham rayuwarsa ta samu bambanci da tamu kasancewar a nan Naija aka haife shi tun yana da 3yrs baya ƙaunar zama cikin gidan iyayensa, akwai wasu Neighbor ɗin su da suke Musulmi kullum yana gidan, yana da masifar wayo na ci da taurin kai, idan su kai alwala haka shi ma zai yi, ko sallah sukai haka shi ma zai. Bayan mahaifinsa ya fahimci hakan ya fara dukansa san bai gwadawa Abraham tausayi ba, ya tashi cikin mugunta yau zai dake shi ya fasa masa jiki haka zai wayi gari babu shi ya koma gidan Musulman nan, daga bisa ni ya kulle shi a wani ɗakin duhu babu abinci ya gana masa azaba sbd kawai ya daina zuwan gidan mutanen, kai har farcen ƙafa dana hannu Denial ya cire Abraham yana ɗan ƙaraminsa, shi yasa zuciyarsa ta ƙeƙa shi bashi da tsoro ko kaɗan, watarana kawai aka wayi gari babu shi neman duniya, shi kuma Denial ya yi tafiyarsa tunda daman ba a ƙasar yake ba, bai damu da ɗan ba ya ce watarana dole zai dawo gare shi idan har yana raye shi kuma daya haifi musulmi gwara ya kashe ɗan da hannunsa ya wuta” Wani irin tashin hankali ya bayyana akan fuskar Uncle Isma’il, da wani irin Expression yake bin Grandpa da kallo kafin ya ce “To mahaifiyarsa fa?” Ya ce “Ta mutu tun yana ƙarami ai, amma bai san da hakan bai kuma taɓa tambayar wani abu daya danganci mahaifiyarsa, Abraham bai taɓa zama da mace na minti ɗaya da sunan kulawa da bashi tarbiyya ba, mace ɗaya ta fara ƙoƙarin saita shi da ganin ya dawo hanya ita ce wacce yake kira da Mami, ur daughter Malamar nan” Uncle Isma’il ya ce “To ya akai ya dawo gare ku bayan ya ɓata? Tunda mun zauna da shi shekaru 2” Grandpa ya ƙara yin murmushi ya ce “His father, shi zuba private Investigators everywhere domin hankalinsa ya dawo kan shi, cikin sa a kuma aka same shi daga nan ya ɗauke shi zuwa wata ƙasar” Mamaki fal ya cika Uncle Isma’il sbd yasan cikin dare aka nemi Abraham aka rasa. “Waye mahaifin nasa? Yanzu yana ina? Me yasa kuma basa tare” Grandpa ya ce “You can ask him by yourself” Uncle Isma’il ya jinjina kansa kana ya yi murmushi ya ce “Yanzu ga abinda jikan naka yake ƙoƙarin rikituwa, kana ganin zai iya musulunta” Grandpa ya jima yana kallon Uncle Isma’il kafin ya ce “Har abada, ku gaggauta yiwa yarinyarku aure, idan kuma zaku bashi aurenta haka to, kai ko zaku bashi mahaifinsa ba zai taɓa yarda y auri musulma ba kuma ba wacce ta girme masa ai tayi tsofa da yawa gsky” Ran Uncle Isma’il ya fara ɓaci sosai kafin ya ce “Kai kake ganin tsofanta, bamu zamu gaggauta mata aure ba ku ne zaku jawa naku ɗan kunne akan ya fita harkar yarinyarmu ko kuma duk abinda ya same shi shikenan, ko hukuma ta rabamu da shi” Miƙewa Grandpa ya yi da sanda a hannu irin tsofaffin attajiran nan masu arziƙin gaske ba muna kuɗi ba ya ce “Hukuma? Waya faɗa maka Abraham na tsoran hukuma bayan shi ne hukumar kansa? Abraham babu wanda ya taɓa zama ya ce masa wannan abinda kake ba daidai bane ga wanda ya kamata ka yi, Abraham ko yini guda ya yi bai kai abinci bakinsa ba babu wanda zai ce masa ɗauki abinci kaci, irin wannan wanda bai san bambancin fari da baƙi be kake tunanin zai fahimci wani ya daina kula muku ƴa?” Grandpa ya girgiza kai kawai kafin ya ce “Sbd karamcinta ya sa nace kuyi nesa da ita daga idanunsa, Abraham ne yaro ne mai naci da taurin kai, tun yana ƙarami idan yana son abu kansa yake bugawa a ƙasa ba zau taɓa bari ba sai an bashi, Have a good day!” Yana faɗin haka ya fice daga cikin Parlourn ya nufi compound da sauri driver ya buɗe masa bayan mota ya shiga.
Anti dake shirya Lunch ta kalli Uncle Isma’il ta ce
“Ya akai kai jarumin namiji?” Ya nemi waje ya zauna tare da rufe idanu ya yi shiru. Ganin yanayinsa ya sa ta nemi ruwa mai sanyi a cup ta miƙa masa tana zama kusa da shi, bai musa ba ya amshi ruwa ya sha sosai yana sauke numfashi. Ganin bai ce komai ba itama Anti ta yi shiru da bakinta, har ya je sallar Asr ya dawo ya zauna cikin iyalansa idanunsa akan Jawaad ya kasa cewa komai, tunani fal ya sa yana sanya Jawaad matsayin Abraham taya zan iya sanwaltar da rayuwar ɗan shi ya bawa duniya ajjiyar shi? Ba dole ya kan gare ba. “Abba” Jawaad ya kira sunan Uncle Isma’il ganin kallon da yake masa kafin ya ce “Abba ruwa zan baka?” Ya girgiza kai kawai ya ce “Allah ya yi maka albarka Jawaad” Ya ce “Amin Abba” Sona ta ce
“Jawaad kaɗai Abba?” Ya haɗe rai ya ce “Sona dake da Jawaad waye babba?” A hankali ta ce “Shi ne” Ya ce “To ya zama last day da zan ji bakin ki ya ce Jawaad ki bi bakin Majaufiarki na Fulanin Gombe ki ce Hamma, ko ki ce Brother da turanci ko Yaya da Hausa” A hankali ta ce “Am sorry Abba” Ya ce “Bashi haƙuri” Ta kalli Jawaad ta ce “Am sorry Yaya” Jawaad ya yi murmushi ya ce “No bad my dear” Bayan sun kammala cin abinci Uncle Isma’il ya zayyane wa Anti yadda sukai da Grandpa. Anti ta yi shiru zuciyarta fal tausayin rayuwar Abraham ta ce “No wonder sweetheart, ka duba Abraham sosai wallahi kallo ɗaya nayi masa nasan babu kulawar uwa a tare da shi ita kuma ya yi missing, duk lalacewar yaro idan har a gaban mahaifiyarsa yake wlh zai samu nutsuwa da sauƙi wani abu, shi yasa a kullum muke addu’a Ubangiji ya bamu tsayin rai mai amfani mu rayu tare da yaranmu” Ta girgiza kai ta ce “I felt sorry for the boy, his life is full of challenges, wallahi ya bani tausayi yanzu da babarsa na duniya taya zai dinga garari? Ba sai dai su shiga duniyar tare ba?” Uncle Isma’il ya ce “Ƙaddara” Wani irin kuka Anti ta rushe da shi ta ce “Wallahi tallahi na ji gwara ɗana ya mutu ya barni da ace na mutum na barshi ban san wacce kalar rayuwa zai yi ba, ban san waye zai kula da shi ba, Innalillahi wa’inna ilahir raji’un Ubangiji kayi mana tsayin rai mu rayuwa da yaranmu cikin kulawa da amincinka ya Rahamanu ya Rahimu” Uncle Isma’il ya ce “Ke fa daman haka kike babu dama ki ji abu sai kuka haba” Ta girgiza kai kawai wani kukan na kwace mata ta ce “Yallaɓai baza ka gane ba, don Allah ka jawo Abraham jikinka plx” Ya yi shiru for good 3 minutes kafin ya ce “I’ll think about that dear” Abraham na kwance saman 3 sitter a haɗaɗɗan parlourn shi kwana uku kenan cif babu inda yaje, duk ya fita daga cikin hayyacinsa. Taj ya kalle shi ya ce “Wani ya yi mini maganar zanen gida da kukai da shi, gashi har time ya shige” Abraham ya yi shiru idanunsa buɗe yana kallon sama alama ya lula duniyar tunani. Taj ya ce “Ina ta magana?” Sai a lokacin ya ce “Ka tura masa kuɗin shi ba zan ba” Taj ya ce “Nawa ne kuɗin?” Shortly ya ce “3M” Joshua ya girgiza kai ya ce “A’a ba za a mayar ba, a bashi haƙuri zuwa wani week ɗin kafin nan sai ka yi” Taj ya ce “Ya ce a mayar kuma daman shi zai aiki tunda ba zai ba bashi kenan ba?” John ya ce “Taj kada a mayar plx mu yi tunanin wani abun” Duk sukai shiru. John ya ce “Kunga news guy’s?” Taj ya ce “What news? What’s happening in the world?” A hankali ya ce “Wai President ɗin Germany aka kaiwa hari za a kashe shi” Da wani irin Mamaki Taj ya ce “Kashe kuma? President ɗin guda? Kuma a hospital?” Join ya ce “Daman wai jinya yake fa bashi da cikakkiyar lafiya, to a hospital ɗin akai attempting kashe shi amma ya kuɓuta, irin haka dole akwai haɗin bakin wani na kusa shi” Taj ya saci kallon Abraham da idanunsa ke lumshe yana jin duk abubuwan da suke cewa ya ce “Ayya! Shi bashi da ɗa ne wai?” A hankali Abraham ya miƙe ba tare daya kalli kowa ba ya nufi cikin part ɗinsa ya kwanta saman bed, haka kawai ya ji bashi da nutsuwa gabansa sai faɗuwa yake, ya runtse idanunsa sosai a hankali ya ce “Daddy”
Majeederh ta kalli Latifa a sanyaye ta ce “Yanzu Latifa ya zan yi? Wanne irin baƙin jini ne irin wannan? Kamar wata mujiya” Latifa ta girgiza kai ta ce “Ki daina cewa haka komai lokaci ne, ƙaddara ce kuma tana da nata lokacin” Ta goge hawayenta tare da yin shiru a hankali ta ce “Surutun jama’a ya fara damuna ana son mini sharri” Cike da tausayawa Latifa ta ce “Duk yadda kake kare kanka ba zaka taɓa hana jama’a faɗar abinda su kai niyya ba, wani ma bai san waye kai ba labari kawai zai ji yaje ya ɗorar ba zaki taɓa yiwa kowa daidai ba rayuwa kawai ki tsarkake zuciyarki” Latifa ta ce “To yanzu da Uncle ya kira Abraham gidan nan parlourn Abbu me zai masa?” Ta girgiza ta kasa cewa komai. Uncle Isma’il ya kalli Abraham ya ce “Khalil me ya kawo ka bedroom ɗin Mamin take few days ago?” A hankali ya ce “Matata dai not Mami” Uncle Isma’il ya jinjina kai ya ce “Ohk me ya kawo ka?” Ba tare da damuwar komai ba ya ce “Just to see her, sai kissing ɗinta da na yi” Uncle Isma’il ya saki baki dan ya san da gaske anyi hakan tunda har ya faɗa don baya ƙarya. Abbu ya runtse idanunsa sosai yana jin kamar zuciyarsa ta fita. Uncle Isma’il ya ce “kiss fa kace Ibrahim?” Abraham ya ɗan kalli Uncle I sai kuma ya kwaɓe fuska ya ce “A small kiss, kaɗan na yi fa” Uncle Isma’il ya ce “Tab ɗin” Uncle Bello shi abin dry ya bashi yana kallon Abraham cike da birgewa ganin baya ƙarya ko kaɗan kuma hakan alamar mutum mai nagarta ce wanda zai iya riƙe amana ta komai. Uncle Isma’il ya ce “Khalil ka san me kake cewa?” Ya ɗan watsa kafaɗa cikin turanci ya ce “Exlty, kwana biyu bata kulani Uncle I ka barni naje ko ɗan hugging nata na yi da kiss ɗin sai nayi ta ganinta a baccina” Kallonsa kawai suke, Abbu kuma ji yake kamar ya shaƙe Abraham Uncle Isma’il ya lura magana ce sosai a bakin Abraham wacce ya jima bai ba dan haka ya ce “Ya akai to yanzu?” Abraham ya gyara zama idanunsa sun yi jajur yana riƙe hannun Uncle Isma’il ya ce “Uncle I Mamina muguwa ce, bata so na ta hana ni sakat a bacci sai na dinga jin kamar gani kwance da ita” Wani irin hawaye ya zubu masa a cikin idanunsa masu zafi wanda rabon da ya yi kuka har ya manta ya ce “Uncle ka aura mini Mami idan na mata ciki zai sanya sunanka ka barni naje wajanta yanzu na yi mata small kiss…….

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button