Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 41

Sponsored Links

Have a nice weekend👑Rawa jikin Jee ya fara da wani irin ɓari naman jikinta na wani irin ƙyarma, tsoro da fargaba ya wanzu a zuciyarta, tana jin ƙirjinta na wani kalar ɗagawa da ƙarfi, sosai hankalinta ya tashi jin an sanya hannu tare da rufe mata baki, duk da kasancewar duhu bai hanata fahimtar waye ba, domin ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious ya riga daya fallasa waye. Majeederh na ƙoƙarin zame hannunsa ta ji ya cire nasa da sauri yana ɗan ja baya, cikin sauri ta miƙe jikinta na rawa ta nufi wajan socket ta kunna hasken bedroom ɗin, riƙe kanta tayi da kyau tana kai dubanta zuwa direction ɗin inda yake ta ganshi durƙoshe a kusa da kujera ya kifa kansa a armchair hannunsa duk biyun tsakanin cinyoyinsa, rawar da jikinsa yake da karkarwa ya sanya gabanta ya faɗi tare da tunanin ko bashi da lafiya ne? Me yasa mesa? Me ya kawo shi gidansu, har cikin bedroom ɗinta? Ko yau ɗin ma ta katanga ya shigo? Sake ware idanunta ta yi a kansa taga har lokacin jikinsa rawa yake ga jijiyoyin kansa da suka fito sosai. Da sauri ta ƙarasa kusa da shi ta ce “Khalil” Shiru bai bata amsa ba, duk da yana jin muryarta a tsakiyar kansa, Majeederh ta rikice domin daman tun yana ƙarami bata jure ciwonsa balle yanzu da take ganin ya yi ɗan wayo idan ya yi ciwo zai iya mutuwa, a yanzu kuma Abraham ya mutu zata iya zaucewa Ubangiji ne shaidar irin son da take masa, tuna hakan yasa ta ƙara yin ƙasa da murya ta ce “Khalil are you okay?” Ya yi mata shiru, ganin rawar jikinsa ka ƙaruwa fiye da kima har wata miƙa yake faffaɗan ƙirjinsa na buɗewa yana matse ƙafa ya sanya a ruɗe cikin tashin hankali Majeederh ta kai hannu zata taɓa kafaɗarta cikin sauri muryarsa bata fita sosai ya ce “Don’t torch me” Ya faɗa a rarrabe murya can ƙasa abubuwan da suke masa yawo a jiki ya sanya baya fahimtar taƙa maimai abinda gangara jikinsa ke buƙata. Majeederh ta cire hannunta a hankali kuma ta juya idanunta ya sauka akan wayarsa dake yashe har ta fashe ma, cikin sauri ta ɗauki wayar da mamakinta tana shafa saman screen ɗin iphone din idanunta ya sauka akan photonta wanda take zaune a office ɗin ta na B.u.k idanunta lumshe a photon kamar mai bacci sai ɗan murmushi da ta yi wanda ya sanya dimples ɗinta lomawa ta yi wani irin kyau sosai. A hankali ta lumshe idanunta tana wani irin son Abraham na ƙara yawa a zuciyarta, hasken da wayar ya kawo da sunan Taj a saman screen ya sanya Majeederh kallon wayar tana mamakin me ya sa ake kiran shi by this time? Kiran ya katse wani ya ƙara shigowa a sanyaye ta saka hannu ta ɗaga kiran tana mannawa a kunnenta tare da yin shiru tana son ji Who’s on the line? Daga cikin wayar Taj ya yi dariya ya ce “Bad boy gani a hanya ina following naka, amma banga motarka ba, ka nutsu wallahi ba zaka iya driving a halin da kake ciki ba, kuma duk masifar taurin kan ka yau ƙaryar alawa ƙasa dole sai ka nemi mace ka kwanta da ita kamar yadda na yi maka al’ƙawari, idan kowa ba haka ba You won’t sleep a wannan daren, shi ya nace Joshua ya zuba maka ƙwayar kaɗan a cikin Cork ɗin amma ya juye” Taj ya ƙara fashewa da dariya sosai ya ce “Zan yi dropping Debeka a gidanka sai ku kwanta tare kasan yadda take mahaukacin sonka, yarinyar classic beb ce yanzu zata gigitaka ka faɗa mini inda kake idan na yi dropping ɗinta a gidanka sai na zo na ɗauke ka, ni zan koma club ne Now the party has started, the classic babies are coming into the club, wallah ka yi missing Bad boy…..,” Cikin tsawa Majeederh ta katse Taj idanunta har wani rufewa yake a karo na farko na rayuwarta ta ce “Uwar Debeka da uban Debeka, wato kune kuke bashi kayan Shaye-shaye ko? Ko ke son haɗa shi da wata figaggiyar yarinya mara tsafta wacce take fama da Datti a jiki” Takaici ya sanya Majeederh yin shiru. Taj ya ce “Au wai wajanki ya zo?” Ya faɗa yana zare idanu, yana kuma danne dariyar dake ransa. Majeederh ta ce “Meye Sunanka?” Ya ce
“Taj” Ta jinjina kai ta ce “Baka da hankali ko? Kana forcing na shi ya aikata abinda Muslunci ya hana?” Taj ya ce
“A’a Mami, Debeka fa budurwar shi ce, kuma a gidansa take zaune, bayan itama akwai wasu ƴan matan da suke zuwa wajansa,kuma duk mu’amala yake da su kenan dai a lalace yake, kuma mene haramcin daga kwanciya da mace Mami?” Wani irin rikitaccen tashin hankali ne ya rufarwa Majeederh ta runtse Idanunta da kyau, tana son hana kansa gasgata abinda Taj yake ƙoƙarin faɗa mata. Ta cikin wayar Taj ya ce “Good night Mami, ki lura dashi please cikin dare yana yawon firgita” Yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da kifawa a jikin kujera ya dinga wata mahaukaciyar dariya kamar zautacce. John ya ce “Taj why?” Taj ya ɗaga kafaɗa hannunsa riƙe da pen Shisha ya ce “What?”
Da turanci John ya ce
“Me ya sa zaka sakawa Bad boy ƙwaya a Cork? Muma da muka saba harka idan muka sha kusan haukacewa muke, balle shi da ko sakin fuska bayayi ko Debeka da yake ɗagawa ƙafa ta baro ƙasar su ta biyo su bai taɓa maganar 5 minutes da ita ba, even small hug bai taɓa yi mata ba, ka manta sanda tayi masa allurar bacci sbd buƙatarta kusan kasheta ya yi fa, amma all this ka ɗauki abu ka bashi yanzu kasan ba zai iya riƙe kansa ba idan ya aikatawa Mamin tasa wani abu fa? Jesus mummunar labari zai faru” Taj ya haɗe fuska irin ko a jininsa ɗin nan ya ce “Ni fa Am happy for him, ita Mamin tasa zata gane shi ba yaro bane”
Sai a lokacin wani da zuwansa country ɗin kenan kuma sun fi good time shi da Bad boy tsare girar su ɗaya ya ce
“This is not fair, how can you imagine yaje wajan Maminsa a haka? Kasan mugun son da yake mata? Ko fa president baya so kamar…..” Sai kuma ya yi shiru da bakinsa. Taj ya ce “C’mon ka ƙarasa faɗar maganarka, wanne president? Meye haɗin President da Abraham?” Salamon bai ce komai ba ya ɗauki kwalbar giyarsa ya ratsa ta cikin mata ya shiga rawa hankali kwance. Taj, John, Joshua suka kalli juna John ya ce “Who’s Abraham?” Taj ya ce “President’s son” Joshua ya ce “Dream, idan shi ɗan gidan shugaban ƙasa ne meyasa yake zaune shi ɗaya tal sai Grandpa yana rayuwa kamar mara gata, sai kuɗi da yake da shi kamar hauka, wallahi idan shi ɗan President ne bamu isa ya shigo cikinmu ba, kawai Salamon yana raina mana hankali ne” Taj ya ce “Something is fishy, Farkon haɗuwata da Abraham a University of Oxford, a lokacin na duba card ɗinsa naga alrdy ya yi nisa a karatu, naga tambarin Germany da kuma National I.d card na germany bai bari na gama gani ba ya karɓe ya ce, asali Grandpa University of Munich dake Germany ya sashi shi kuma bai so yama tsani ƙasar bakiɗaya, muna level ɗin ƙarshe a University of Oxford wasu manyan mutane suka zo tafiya dashi ya kafe babu inda za shi nayi mamakin yadda suka kasa kama shi sbd at the end ma ɗaya ya harba shi ne muka tattara mukabar ƙasar, daga ƙarshe dai ban ina yaje ba domin ya barmu for good 1yr” John ya ce “Baka tunanin laifi ya yi wa mutanen?” Taj ya ce “Maybe, he’s smart and stubborn boy to be honest ban taɓa ganin mutum bai iliminsa ba, baya taɓa zama lectures amma bugu ɗaya ya kewa exam, tun yana secondary haka record ɗin yake shi yasa aka dinga yi masa promotion da wur wuri ya gama secondary school sanda ya fara University zaka raina shi sosai, amma dake yana da jiki sosai ba a ganin shekarun nasa, kuma Grandpa ɗin nan nasa kuɗi ne dashi kamar su kashe shi wallahi, waye zai ce Bad boy ya karanci Likitanci? Kusan me ya sa?” Suka girgizawa Taj kai ya ce “Cos he’s not his dream, Abraham’s doesn’t like it, Business kawai yake so bayan nan sai ɓangaren tsaro yana son sama sojan ƙasa, yanzu haka idan ya yi zanen gida miliyoyi yake samu, gabaɗaya shi ke siya mana suttura sometimes” Gang team ɗin sukai shiru kenan dole akwai abinda Abraham yake ɓoye musu na daga rayuwarsa. Taj ya ce
“Excuse me” Wayarsa ya ɗauka ya ƙara danna number Abraham yana ji tana ringing ba a ɗauka ba, ya miƙe ya ce “Bari nayi dropping Debeka”

Majeederh ta ɗauke kanta daga kan wayar Abraham da taga still Taj ke kira, maybe ya yi dropping Debeka ɗin can gidan kamar yadda ya ce, so he’s waiting for Abraham to go back his home and… Ta yi saurin runtse Idanunta, fitar numfashinsa da ta ji ne ya sanya ta juya da sauri tana kallon at this time a kwance ta gansa yama kasa zama tsugunawa ta miƙe a hankali zuciyarta babu daɗi, ɗan ƙaramin yaronta wai har ya san mace? Mata ke bibiyar mata yaro? Yana Shaye-shaye shi ya sa ya zama criminal kenan bashi da tsoro? Banda haka ko zance Abraham bai isa ya tsaya yi ba, gabaɗaya nawa yake? He just 16 fa. “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Majeederh ta furta a ranta, ta durƙoshe gabansa zuciyarta na wani Irin harbawa bakinta na rawa ta ce “Khalil” Ya yi shiru Ta miƙa hannu zata taɓa shi cikin sauri ya ja baya yana mirginawa kamar zai shige ƙarƙashin gado muryarsa na shaking laɓɓansa na wani irin ɓari ya ce “Don’t torch me” Kamar za ta yi kuka ta ce “But My son taya zan iya barinka haka? Faɗa mini me suka baka? Meke maka ciwo? Headache? Fever? Bari na ji ki da zazzaɓi sorry” Ya tsoro mata narkakkun idanunsa wanda sukai mahaukacin jaa sosai da ƙyar yake iya ɗan buɗe su, bai taɓa jin abu makamancin abinda yake ji ba in whole his life shi ko ciwo baya yi sosai, Ya ja idanunsa ya rufe yana curewa waje guda yana magana ƙasa ya ce “Don’t torch me Maa.. Don’t” Itama Majeederh ta marairaice fuska ta ce “Please Baby son, bari na taɓa wuyanka ko robe na shafa maka” A hankali cikin muryar marasa lafiya ya ce “Ohk”
Ta sauke ajjiyar zuciya ganin har lokacin idanunsa a rufe yasa ta ƙarasa dab da shi tare da miƙa hannu zuwa neck ɗinsa ya yi saurin buɗe idanu tare damƙar hannunta kafin ta yi magana ya fizgota zuwa jikinsa daga kwance da yake. Gabaɗaya ta faɗa kansa tana zare idanu, Abraham ya zaga hannunsa tare da ƙanƙameta sosai a ƙirjinta yana wani irin mimmiƙa tare da jijjiga, yana jin kamar wani abu na jansa mararsa na wani irin azababben ciwo. Majeederh ta ce “Sakeni Khalil na baka magani” Slowly ya girgiza mata kai a hankali kuma ya ƙara manneta da jikinsa ƙamshin CLINIQUE Deep Comfort Body Lotion shower gel ɗin da ta yi using da shi wajan wanka ya ƙara rusawa Abraham sabuwar zuciyar tashi na daga abinda ya ke ji. A hankali ya tura kansa tsakiyar wuyanta hannunsa ɗaya a waist ɗinta ya riƙe ta gam yana wani irin fitar da wahalallan numfashi, Majeederh ta ruɗe tare da zaucewa a rikice ta ce “Khalil let go of me, ka bari na baka paracetamol” Ta faɗa muryarta na rawa tana jin tsigar jikinta na tashi, bakinsa dake wani irin ɓari alamar yana buƙatar wani abu ya manna a kunnenta ta wani kalar zabura ta ji ya sake riƙe waist ɗinta gam ya manna da nashi yana wani irin saukar mata breathing a kunne lips ɗinsa na gogar fatar kunnenta a hankali cikin raunatacciyar muryar ya ce “Allow me to kiss u Jee.. ƴar madara…Saboda Shocked kasa motsi Majeederh tayi, take kuma jikinta ya fara rawa na rashin sanin abin yi da kuma gingimemen tashin hankalin dake neman zautar mata da nutsuwarta. Fahimtar Majeederh bata da bakin magana ya sanya Abraham janye gajiyayyun idanunsa wanda ya laushi ya ƙanƙance sbd Baƙon lamarin dake son tafiya da ruhinsa, yadda jikinsa ke rawa naman wajan na zillo da harabawa ya sanya ya fahimci akwai abinda yake buƙata urgently. Fuskarsa dake manne a wuyanta ya zame yana sake manna mata kwantaccen beard ɗinsa wanda ya sha Jack Black Beard Oil sai sheƙi yake. Shortly can ƙasa Abraham ya ce “Plxxxx” Sai kuma jikinsa ya fara jijjiga gab gab gab kamar wanda ake zarewa rai a kiɗime Majeederh wacce ta kasa koda motsi ta yunƙura zata miƙe daga jikinsa ya yi sauri kama fuskarta tare da jawota dab da nashi fuskar, Majeederh baki sake take kallon ikon yadda take zare idanu kaɗai zai sanya kasan shocked ne ya hanata ɗaukan action akan abinda ke faruwa, tsinin hancinsa ya ɗora akan nata ya ware idanu a hankali cikin saa itama shi take kallo da sauri ta janye nata jin tsigar jikinta na tashi tana zubewa kame kanta tayi da kyau tana faɗin “Asstagafirullah, Subuhanallahi, Allahu Akbar!” A zuciyarta Abraham ya buɗe baki da ƙyar ƙamshin Colgate Vedshakti Mouth protect spray na fita daga bakinsa, lips ɗinsa na gogar nata ya yi attention to kiss her lips. Sai kuma ya zame kansa tare da yin ƙasa da zuwa neck ɗinta. Lokacin da lips ɗinsa ya sauka a skin ɗin wajan wani irin zabura Majeederh tayi sbd harabar da zuciyarta tayi wani abu ya fara mata yawo saman fata. Gam! Abraham ya riƙeta da hannu ɗaya idanunsa rufe ruf jikinsa na karkarwa kamar mazari duk wasu ƙofofi na jikinsa wanda suke buƙatar abinda gangar jikinsa ke so sun gama buɗewa cikin fitar hayyaci da zaucewar tunani a hankali ya ce “I am sorry Mami” Yana faɗin haka ya sauke mata wani irin zazzafan light kisses a neck skin ɗinta tare da murza hannunsa dake bayanta a hankali kuma ya damƙe hannunta ya yi kamar zai saketa. Da sauri Majeederh ta miƙe zata tashi ta ji ya saki wata kalar sounds idanunsa na yin fari jikinsa na ƙyarma yana ƙanƙame hannunsa kamar zai suma, a haukace Majeederh ta tsuguna wajansa ta ɗora hannunta a ƙirjinsa tana jijjiga shi muryarta na rawa ta ce “Little, Baby my son what happening to you?” Yadda take jijjiga shi ya ƙara sanya shi cikin wani irin azababben yanayi numfashinsa ya fara fisga a rikice ta saka hannu ta ɗago shi tana yin kuka tana cewa “Plxxxx Khalil open ur eyes” Da ƙyar ya buɗe idanunsa yana jin kamar ba a duniya yake ba, zuciyarsa ta gama tsinkewa, ya kafe Majeederh da kallo data kamo hannunsa tana cewa “Khalil my son mene? Me kake so? Ina ke maka ciwo?” A hankali ya kai hannunta saman mararsa da yake jin kamar ya tsinke. “Here”
Ya furta shi kansa bashi da tabbacin ta ji, hannunta ta miƙa da niyyar danna masa ai da wani irin sauri ta sake shi tare da miƙewa tsaye idanunta na rufe yana yarfe hannu tana jin kamar ta riƙe ƙaton katako. Miƙewa ya yi kamar ɗan maye kana kallonsa zaka san ba’a hayyacinsa yake ba yayi muguwar faɗawa sbd azabar da yake ji a jikinsa wajanta ya nufa yana zuwa ya ɗauke shi da wani irin gigitaccen mari, Without letting him come back to his senses ta sake sauke masa wani irin zazzafan mari idanunta rufe murya ƙasa gudun kada a jisu ta ce “Out, out Khalil” Kallonta kawai yana yin baya kamar zai faɗi idanunsa sunyi jajur ga wani zafin zazzaɓi da jikinsa ya ɗauka ta ƙara nuna masa ƙofa ta ce “Zoka fita” Shi dai yasan ko kashe shi za ta yi ba zai taɓa iya fita ba, to inama yaga energy ɗin fita balle driving? Ganin bashi da niyyar fita ya sanya ta shige ciki ta ɗauki wayarsa ta damƙa masa kana ta saka hannu ta kama nashi ta shiga jansa har zuwa bakin part ɗinta ta ƙofar baya, ta tura shi kaɗan har lokacin da idanu kawai yake binta yana kallo ta garƙame ƙofar ta murɗe key. A hankali ya ja gajiyayyun idanunsa ya rufe tare da sulalewa ya zauna zaman dirsham a ƙasa ya rufe idanunsa hannunsa riƙe da mararsa sai numfashi yake saukewa a wahale tuni zazzafan zazzaɓi ya rufe shi wanda bai taɓa yin irinsa ba. Majeederh ta sulale ta zauna saman gado tare da haɗe ƙafafuwanta waje guda tana girgizawa, zuciyarta a cunkushe Asstagafirullah kawai take a ranta, Abraham ɗan ta yana buƙatar taimako tasan cikin maye yake da ba zai taɓa aikata abinda ya yi ba, dole kuma ta nuna masa nasa kuskuren na yin Shaye-shaye. Almost 10 minutes ta ɗauka kafin ta miƙe ta leƙa ta ƙofar window ɗinta ta hango shi durƙoshe ya riƙe kansa da hannu bibbiyu, ta yi matsawa tana hana kanta jin tausayin ɗan nata, har kiran sallar farko na Subhi bata runtsa ba, ta miƙe da ƙyar ta nufi bathroom tayi wanka da kyau, ta fito ta tsafta ce jikinta ta zauna zaman azkar tunda ba sallah take ba. Wajejen 10:10 ta gama haɗa breakfast da taimakon Aaliyyah suka jera komai a dining area a hankali kowa na gidan ya hallara, sai a lokacin Majeederh ta san Raihana da Ruma a nan suka kwana suna zaune Mami ta fito cikin wata dakakkiyar atamfa Valisco ruwan huda da feshin blue a jiki ta murza ɗauri ana tafiya a hankali taja kujera ta zauna, Aaliyyah ta ce “Ina kwana Mami?” Ta ce “Lafiya lou” Majeederh tana juya tea da spoon a hankali ta ce “Mrng Mami?” Ta ce “How are you?” Ta ce “Good” Raihana ta ce “Nikam Majeederh da zaki zo gidana ko sati biyu ki yi mini, kina ɗan tayani aiki tunda ba wani abun kike ba” Majeederh ta yi shiru, Ruma ta ce “Wlh idan ta gama miki ki sending ɗinta gidana, ma rage mata zaman kaɗaici” Daga Aaliyyah har Majeederh ba wanda ya kula su, Raihana ta ajjiye spoon ɗin hannunta ta kalli Mami ta ce “Yawwa gwara da ban manta ba, ni shawara ce dani idan tayi muku” Mami ta ce “All ears” Ƙamshin turaren Hugo boss da suka ji ya sanya sukai shiru, Majeederh jikinta ya ɗauki rawa amma ta dake Mami ta kalli Abbu da yake shigowa kamar sabon ango, wani tattausan voyel ne a jikinsa nevy blue ya murza jaddara akan shi ya nemi waje ya zauna. Mami ta ce “Barka da fitowa Alhji” Abbu ya jinjina kai, Raihana da Ruma suka haɗa baki wajan cewa “Sannu da shigowa Abbu” Aaliyyah ta ce “Abbu ina kwana?” A hankali ya ce “Lfy” Sanin ba a magana idan yana wajan duk sukai shiru. Gently Majeederh muryarta na rawa sosai ta ce “Mrng Abbu” Slowly ya ɗaga kansa tare da zuba mata idanu can kuma ya ɗauke ganinsa ba tare daya amsata ba, Duk motsin Majeederh yana gani juyawa spoon kawai take tana cakalkala dankali, few minutes ya sake ɗago kansa ya zuba mata Idanu “Hawwa’u” Ta ji saukar muryarsa ji tayi kamar tayi fitsari a wando ta ce “Na’am Abbu” Shortly ya ce “Leave” Miƙewa tayi tabar wajan da sauri tana jinta kamar ware a cikinsu. Mami ta ajjiya cup ɗin hannunta ta ce “Me ya sa kake yi wa yarinyar nan haka ne Alhji? Me ya sa kake son nuna fifiko a cikin yaranka, bana son haka a gaskiya ni” Bai ce mata komai ba, Aaliyyah ya tsame hannunta zata miƙe Abbu ya ce “Sit” Ta zauna tasan me yake nufi. “Raihana me kike cewa?” Raihana na rarraba idanu ta ce “Daman wani ne ke mini aike yana da hankali sosai daga ƙauyen Rurum yake naga da ƴar sana’arsa daidai gwargwado domin har ɗan dako yake, na ce ko shi za a haɗa da Majeederh tunda Kinga al’amarin nata shiru babu mashin shi ni, sunansa Tasi’u” Ruma ta ce “Lallai da kin yi aikin lada sosai Raihana” Mami ta ce “Shi ɗan dakon kenan?” Raihana na kallon Abbu ta ce “Wlh ai irinsu babu ruwansu, musamman ga Majeederh fara tas wlh haukacewa zai ya samu mata ta keta raini bama zai duba taimakon da ya yi ba, nan nan zai dinga yi da ita kamar ya lashe” Cak Abbu ya ajjiye cup ɗin hannunsa da yake ƙoƙarin kawai baki zai sha ruwa, ya mayar ya ajjiye tare da miƙewa ya fice daga parlourn. Compound ya nufa Driver na ganinsa ya miƙe tsaye, Abbu ya nufi wajan mai gadi ya ce “Waya shigo cikin gidan nan jiya?” Mai gadi ya kama kame kame Abbu ya ce “Ohk haɗa baki ake da kai ana shigo mini gida? Ka tattara kayanka na sallameka kuɗinka zan tura maka ta acct” Mai gadin ya rikice sosai ya zube yana bawa Abbu haƙuri amma ina tuni ya shiga mota… Zuwanta gidan Maman Alpha kenan ta nufi part Innati tabar Latifa tare da Maman Alpha, bayan sun gaisa Innati ta ce
“Ina Kululu?” Majeed ta ce “Gani kusa” Innati ta ce “A to bana ganki ba kuma, ƙara tabbatarwa zan yi” Ta ƙara zama ta ce “Shikenan ku dangin mahaifiyarku basa ƙaunarku ne?” A sanyaye Majeederh ta ce “Me kika gani?” Innati ta yi mitsi mitsi da idanu ta ce “Ji wata wulaƙantacciyar tambaya?? To ke yanzu dan Allah wa kika sani a dangin Fulani?” Majeederh ta ce “I don’t know anyone, I’ve never seen anyone from my mother’s family” Innati ta saki baki ta ce “To banda kin so wulaƙanta ni a idanun jama’a meye zaki sauya raye, ni zakiwa turanci?” Ita dai Majeederh bata ce komai ba, domin jikinta duk ya mutu tana son yi wa Abbu maganar Mother’s family ɗin su tana jin tsoro. Innati ta ce “Kawai ki rutsa mahaifinki shi ne nunafukin ki ce ya fito miki da dangin mahaifiyarki, ki ɗaga masa hankali sosai idan ma kidnaping ɗin su ya yi sai mu ji labari, tunda ba wani yarda nayi da zuciyar Audil azizu ba, sama taka mu kaga yayi arziƙi fa? Shi yasa yake ta wani fankama yana ɗaga kai, to ai mu munga ƙaruna ma” Majeederh ta yi shiru Innati ta ce.
“Allahu Akbar, ai ba zaki san ƙaruna ba, munga ikon rabbi a wajan bawan Allan nan, gashi dai ƙarshen shi bai wani kyau ba, ai wallahi wannan kyan na fuskarki da farar fatar nan kamar sadaka yalla to haka uwarki take, har ta ɗaraki a kyau mace mai sanyin hali da haƙuri, ta sha fama da talaucin Audil azizu sana’a kala-kala tayi fa? Ko Attajirin uban naku bai baku labari ba? Babu mamaki gadonku ya tattara ya siyar kwasha kwasha, domin har gwala-gwalai ne da ita” Majeederh idanunta ya cicciko da hawaye ta kasa cewa komai. Innati ta zabga sallati ta ce “Yanzu kamata Kululu ni zakiwa turanci? Ni zaki sauya harshe, yanzu fa muke Shira dake rumi rumi kawai sai kika sauyan raye ni ki kaiwa turanci” Majeederh ta miƙe ta ce “Kyaci kanki ke kaɗai” Ta yi waje abinta, Innati tayi ƙasa da murya ta ce “Tab, kaɗan ya rage ban saki fitsari ba yarinya kamar Aljana, zaki Albarka,zaki Albarka mijinki daban yake sananne ne shi tauraro ne, wanda duniya ta gama saninsa” Haka take something kamar wacce ake buɗewa idanu. Maman Alpha da kalli Majeederh ta ce “Majeederh Kinga ɗan uwanki har yanzu shiru? Ko yana raye ko ya jima da mutuwa? Ko a hankalinsa yake ko ciwon hauka ya same shi Allah kaɗai ya sani” Gently Majeederh ta kalli Maman Alpha ta ce “Ki yi haƙuri, addu’a za a yi” Murmushi kawai ta yi kafin ta ce “Ya maganarki kowa? An samu tsayayyen?” Kafin Majeederh ta yi magana Latifa Omar ta ce “Aliyu ya ce zai aureta, amma taƙi” Maman Alpha ta ce “Mijin naki?” Latifa ta ce “Eh” Da mamaki Ta ce “Son ta yake?” Latifa ta ce “Sosai, sbd ya ce na yi conversing ɗinta to marry him take gaba dani” Maman Alpha ta yi shiru for a second kana ta ce “Eh to gaskiya conversing Majeederh to marry ur husband Aliyu, kamar ki yi forcing nata ta cakawa kanta wuƙa a ciki ne, How do you think she can marry her Aminyya’s husband? It is a difficult thing that the mind cannot handle. Honestly, even I do not support this useless thought, Majeederh tana buƙatar taimakonki,She needs your help, but not this way, think of something else besides this” Latifa ta marairaice ta ce “Ni wlh tallahi na amincewa Aliyu, ba zan taɓa kishi da Majeederh ba, zamu ci-gaba da zama kamar yadda muka sabaSocially there is sacrifice, I sacrifice my husband’s love for Majeederh” Maman Alpha ta ce “Sacrifice?”
“Eh” Cewar Latifa Omar
Maman Alpha ta ce “Let me tell you something you don’t know, ko da ƙanwarki da kuke ciki ɗaya aka haɗaki waje gudu wlh sai kin yi kishinta, balle Majeederh? Sanda zaki shige ɗaki kina ihu idan suka keɓe Allah kaɗai ya sani,We are dedicated to Love, it does not mean that we have stopped loving, in love there is jealousy, Think about that Latifa Omar” Kafin kowa ya yi magana Innati ta shigo tana kuka wiwi hannunta riƙe da sanda. Maman Alpha ta ce “Subuhanallah lafiya Innati?” Innati ta ce “Fatima wai ni Kululu zata juyawa yare ta yi mini turanci?” Maman Alpha ta ce “Allah gasky bata kyauta ba, turanci ana zaune lafiya?” Lafita ta dinga dariya sosai sun jima a gidan kafin su ta fi. A hanya Lafita ta nufi Tahir Quest Palace Majeederh ta dai kalleta ganin hakan ya sa ta ce “Abu zan karɓo kin san mu ƴan jarida, muna amfani da Opportunity da zarar ya samu”
5 days left. Tun ranar Majeederh bata ƙara jin motsin Abraham ba even on the phone, har numbersa ta kira ta ji a kashe. A hankali ta rufe Idanunta da sauri ta buɗe kuma tama rasa wanne kalar tunani za ta yi, tana zaune wayarta ya fara ringing dubawa ta yi taga new number sharewa ta yi, kuma ba a fasa kiran ba, tunaninta ya bata masu neman taimako ne ko wani abu ne ya tashi a Ngo ɗinta. Ta ɗaga kiran tare da cewa “Assalamu alaika/ki” Taj ya yi wa Salamon alama da ya yi shiru a ladabce ya ce “Good day Mami” Sosai Majeederh ta ɗauki muryar ta yi shiru, Taj ya ce “Sorry na kira without ur permission, am very sorry about that” Bata ce komai ba, a ransa yana mamakin girman kanta ya ce “Abraham, baya da lafiya kwana biyar kenan, baya ci baya sha sunanki kawai yake kira gashi Grandpa baya gari” Majeederh ta yi shiru a hankali ta ce “Bashi wayar” Taj ya ce “Dr ya duba shi yanzu bacci ya ɗauke shi, amma yana da kyau idan ya buɗe idanu ya ganki” Shortly and silently ta ce “Address” Ya ce “Ohk check ur Dm” Kashe kiran ya yi ba jimawa ya tura mata da Address ɗin gidan. Sosai ta dinga duba location ɗin tana mamakin unguwar. Shiryawa ta yi cikin mik ɗin Abaya mai kyau ta ɗauki hijab ta saka tare da liƙab, waya da key kawai ta ɗauka ta nufi waje. Mami na zaune Main parlour watching TV ta ce “Mami zan ɗan je dubiya” Mami ta ce “Subuhanallah wani ne bashi da lafiya?” Majeederh ta ce “Eh” Ta jinjina kai ta ce “Kada ki jima” Fita tayi ta nufi wajan baƙar motarta tare da buɗewa ta shiga bismillah ta yi tare da yin key tai reverse gatekeeper ya buɗe mata, tana fita motar Abbu na shigowa, Aliyu dake tsaye a bakin gate ya ji he need to follow her, ya ga where she’s going to?….
Babban gida ne wanda kafin kaga irinsa sai an tona, tsayawa faɗin yadda gidan yake ɓata baki ne, ga wasu mahaukatan securities birjik, gidan ta ciki part part ne. Gang team ne zaune a wani haɗaɗɗan parlourn gidan wanda ya kasance mallakin Abraham shi ya zana gidan da kansa. John ya ce “Taj me ya sa ka yi mata ƙarya?” Taj ya ce “Kawai ta zo ta gansa” Salamon ya girgiza kai ya ce “Baka da kirki wlh” Dry ya yi sosai duk sun cika parlourn da hayaƙin Shisha ya ce “Na kusa barin country ɗin nan” kafin su yi magana sun ji ƙarar doorbell. Taj ya miƙe ya ce “Ta ƙarasu, ku ɓoye kayan drugs ɗin nan” Da sauri suka kwashe komai, ya buɗe mata ƙofa ya ce “Wlcm Mami” Bata kula su ba sai parlourn data shiga ƙarewa kallo ya ninnka na gidansu a komai, ta yatsuna fuska. Gabaɗaya suka miƙe kamar marasa gsky sbd kwarjini ta yi musu duk da fuskarta a rufe yake. Salamon dake ya fi kowa bin diddigi ya shiga ƙarewa yatsun ƙafar Majeederh har wani yellow suke don fari. Waya Taj ya ɗauka kira Abraham dake can cikin wani narkakken part. Majeederh ta kasa zama har wajan minti biyar kafin ta ji John ya ce “Gashi nan ma” Bata ɗago kai ba haka nan Moment ɗin su ya faɗo mata, da tunanin wanda aka ce bashi da lafiya me ya fito da shi?
“Hold on. Who is that girl standing next to him….??” Jin an ambaci yarinya ya sanya Majeederh ɗago da kanta da sauri, idanunta ya sauka akan wata siririyar yarinya chocolate colour tana da kyau daidai da ita, daga ita sai half vest da wando iya laps ɗinta, ga wani gashin doki sai mannewa Abraham take, Wanda ya haɗe rai kamar ya ce ya shigo uku, tun faruwar abun babu wanda ya sake kulawa sbd ransa ya ɓaci da abinda Taj ya yi masa, Kallonsa Majeederh ta dinga yi ganin ya rame sosai idanunsa ya faɗa, a hankali ta juya ta kalli budurwar sunan Debeka ya faɗo mata wato ita ce Shegiyar dake lalata mata yaro? Salamon ya ce “Ur mother is here” Da wani irin sauri Abraham ya kalli Doorway idanunsa ya sauka cikin nasa, ya miƙe tsaye tare da ƙare mata kallo yaga tana kallon Debeka wacce ta yi tsaye tana kallon Majeederh, Shi kuma ya juya ya kalli Taj irin me ya sa? Ganin Abraham ya kasa cewa komai ta juya zata bar parlourn murya ƙasa ya ce “Ma….mi.. Mami” Cak ta tsaya ba tare data juyowa ba, Abraham ya nufi inda take yana zuwa ya rungumeta ta baya yana sauke ajjiyar zuciya a hankali dadai kunnenta ya ce “Am sorry Mami” Ta juya ta kallesa ta kasa ce masa komai ya riƙe hannunta har zuwa tsakiyar Parlour ya ce “Wlcm come to my house Mami” flowers ta ji suna zubu mata aka daga ita har Abraham ɗin, Kafin ta yi magana ta ji Gang team ɗin sun saki ihu tare da yin tafi sun ce “It’s ur day bad boy, happy Engagement” Mami ta kalli Debaka bandai da ita ya yi Engagement ɗin ba? Debaka kowa suman tsaye ta yi numfashinta ya shiga ɗaukewa, Abraham ya ɗan yi cute smile da jajeyen laɓɓansa ya ɗauki wata ƴar ƙaramar box ya buɗe wani ɗan ƙaramin Gold ring ya bayyana sai sheƙi yake, a hankali ya durƙoshe akan ƙafafuwanta ya kama hannun Majeederh cikin low voice da wani irin sound ya ce “Ƴar Madara Mamina, Will you marry me?” Bugawar da zuciyarta tayi ya sanya ta yi baya kamar zata faɗi sai kuma ta tsaya da kanta jikinta ya shiga rawar da bai taɓa yi ba. Abraham na durƙoshe ya ce “Zaka auren Mami? Ɗan ki zai zama mijinki” Taj ya ce “Wip wip Wip hureee, baka faɗa mata how much u love her ba, tell her” Ya ɗan langwaɓar da kai shi fa bai wani iya ɓata lokaci da wani i love you ba, a aikace yake komai ya kwaɓe fuska ya ce “I don’t need all this, ta san ina sonta ai ko Mami?” Majeederh kamar wacce ƙwaƙwalwarta ta tsaya ta kasa magana tana ji ya zura mata ring ɗin a yatsarta, ya sumbaci wajan ya ce “You’re Mine” Wani kalar Ihu Gang team sukai tare da cewa “Happy Engagement Bad boy, the leader team the richer young boy” Ya miƙe tsaye yana lumshe idanunsa wanda suka azabtu da rashin ganinta sosai, John ya ce “Remain kiss, First kiss” Shi kansa Abraham mmkin yadda Majeederh batai masa komai ba yake, ta yi accepting nasa as her husband? Bai san cewa brain ɗinta ce ta tsaya cak ba. Slowly ya nufi inda take da niyyar kissing nata, Debeka dake tsaye tunaninta ya gama bata Majeederh ita ce wacce Taj ya faɗa mata Abraham ya je wajanta jiya ya kwana, Gadan-gadan ta nufi kanta da plate zata kwaɗa mata Abraham ya yi saurin tare Majeederh ta hanyar rungumeta ya ce “Mami…” Plate ɗin ya sauka a kansa nan take jini ya shiga fita ƙarar plate ɗin ya sanya Majeederh sakin ajjiyar zuciya ya haddasa dawowarta cikin tunaninta, Abraham ya juya da saurin still holding onto her ya ce “Debeka stop” Hawaye kwance akan fuskar Debaka ta ce “Stop? Na bar iyayena, karatuna ina level na ƙarshe na zama cikakkiyar low na bar ƙasata na biyoka sbd kawai ina sonka? Shi ne zaka kawo wata tsohuwa wacce ta haifeka ka ce zaka aura? To bari naga ta yadda za a yi auren” Ta ƙara nufar su Abraham ya ɗauka Majeederh zata daka babu zato balle tsammani yaji saukar hannunta a mararsa ta damƙa tare da murɗewa ya fisga, wani masifaffan zafi ya ratsa kwanyar kansa numfashinsa ya tsaya cak domin inda ransa yake ta taɓa, a hargitse Majeederh ta ce “No!!!!!! Zaki nasaka shi” Debaka ta ƙara murɗewa da ƙarfi ta ce “Sai ayi auren muga” Baya Abraham ya yi Majeederh ta tare shi suka zube a ƙasa ya faɗa kanta babu numfashi……..

 

Related Articles

Har yanzu a labari muke,sai mun koma asalin labari za kuga muhimmancin baku wannan labarin….. The story is going to be different In sha Allah🫰🏽💔 muna zuwa page 50 zamu gama labari a nan book 1 ya ƙare.*_Sai Mace ta turo wata yaƙunanniyyar ƴar dubu ɗayanta tana son MIJIN MALAMA, kuma sai ta dinga sharing gari gari har Aljanu duk su karanta akan guntuwar 1k? To Sannunku ku ta nadi kuɗinku idan mun dawo labari a book2 zan muku Discount kowa ya karanta Allah ne ya taɓa zuciyata wlh…….. MIJIN MALAMA 08119237616_*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button