Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 51

Sponsored Links

Da kyar ta iya ta zauna akasa ta daura kanta akan kujera tana wani irin numfarfashi da baki tana cije baki tana jujjuya kafa sabida yanda taji kaman ana jajjage acikin nata, wasa wasa abu sai gaba yakeyi wani irin barje dataji cikin nata nayi yasa tawani irin buga kai akasa tana mukurkusu ahankali tace “wayyo Allah na, cikina na shiga uku” kokarin kamo kujera take ta tashi tsaye hala cikin yadena, da kyar ta iya janyo filo daga kan kujeran ta tusa akarkashin cikin nata ta, ji tayi kaman takara azaban datake jine, nukurkushewa ta dinga yi a wurin tana jujjuya kai tana dukan kasa da awahale tace “Ya Khaleel” tafara kokarin jan jiki dantai wajen kofa amma takasa ta kife kanta anan kasa tana dukan tiles din wajen da hannu, kofa taji anbude an shigo tsabagen azaban datake ji tama kasa dago kai ahankali ya tsugunna yana shafa kitson kanta daya mugun mai kyau yace “mekike yi akasa haka” yakarashe maganan yana murmushi wani karfi ne taji yadan zomata da kyar ta tashi tsaye tahau kan jikinshi ta yaye rigarta sama tana wani irin lankwashewa tanuna mai cikin ta dan tamakasa magana, adan rude ya kalli cikin ganin yanda yake wani motsi up and down da kyar tace “cikina Ya…” kasa karasa maganan tayi tawani shige jikinshi tana bangarewa, fashewa tayi da kuka sosai ta kankameshi tana wani irin mika, adan rude ya wawwaigawa baiga kowaba da sauri yaciro fuskarta daga jikinshi yace “ina Farida?” kasa magana tayi saima wani kanannade shi data sakeyi tana wani irin lankwashewa kaman macijiya tana kuka, hanunshi ya daura akan cikin wani irin motsi da kara yaji ba karamin faduwa gabanshi yayiba ciro kanta yayi daga jikin nashi ya kwantar da ita anan kasa ahankali da idanunshi dasukai jajir yace “am coming” tashi yay yay bedroom yana kwallama Farida kira “Farida Farida” har bayi saida ya bude bata, hakan yasa yafito ya shiga kitchen da sauri nanma bata harzai fito saiya hango farin leda dakuma farin marfi akasa kusa da bin, hakanan yaji zuciyar shi bata kwantaba shiga kitchen din yayi yana kallon ko’ina dan wari warin magani yakeji, digon wani abu daya gani akan fridge kaman mai yasa yasaka yatsa ya dangwala yakai hanci ya shinshina warin magani yaji kaman kalanzir da sauri yakoma wurin bola inda yaga farin marfi akasa ya daga yakai hanci same wari yaji tashi yayi yana kalle kalle bolan ya leka ganin Goran sniper a kwance cikin bolan yasa yaciro yana kallon goran dan yasan babu irin goran nan agidan, harda dan gudunshi yakoma falon plate din Indomie daya gani yaje yadaga yanama abincin wani irin kallo, shinshina abincin yayi da sauri ya ijiye yadau juice din ya tsiyaya a cup abu kaman maimai dayagani a kwance kan saman juice din cikin cup din yasa ya dafa kirjinshi jin yanda ya buga da karfi yace “innalillahi wa innailaihi raji’un” harda dan gudunshi yazo inda take kwance tana wani irin numfarfashi tana kuka yace “waya baki abincin chan shikikaci?” kasa magana tayi saima wani irin kukkule ido datake yi tana bubbuga kanta akasa danji take kaman ana tsitsinke hanjin cikinta, kama fuskarta yayi yay tapping kumatun ta da karfi yace “wayabaki abincin chan” kara fashewa tai da kuka tana nunamai cikinta da kyar ta iya cewa “Fa.. Far” wani irin ihu tayi ta buga kanta akasa sabida yanda cikinta yay wani irin kara dahar shi saida yaji da gudu yay gaban tv danhar yana huge kafa da center table, key mota yadauka ya dauke ta yafita tsakar gida da gudu yana kwalama gateman kira “budemin gate” kwantar da ita yay abayan mota yarufe da gudu ya shiga gaba yatada suka fita agidan, yanda take juyejuye sabida azaba har saida tafado kasa daga kan kujeran juyowa yay da idanunshi dasukai jajir yakira sunan ta “Islam, Islam” kasa amsawa tayi saima bubbuga kai datake yi a jikin kujeran. Allah ne kawai ya kaisu asibitin lafiya dan yana tuki yana kallon bayane yanda take nukurkusu akasa.
Idan kaga Khaleel zaka zaci ya haukace ne sabida yanda yake ihu a asibitin, da gudu aka karbeta Dr yace “maiya sameta” da kyar ya iya cewa “I think sniper aka bata” ganin yanda tawani bankare zata Fado daga kan gadon da aka daurata yasa ya riketa yace “Islam Islam am here babu abinda zai sameki kinji” cikin wani daki akai da ita ya bisu amma akace yafita.

Har sunkai layinsu itada me napep din daya dauketa sai kuma taji jikinta yay wani irin mugun sanyi yanzu sabida namiji zata iya kashe Islam? Wata zuciyar tacemata amma ai idan ta mutu zai aureki, dafe kanta tayi tana girgizawa da sauri tace “no no, I can’t do dis, Islam jini tace ” da sauri ta kalli driver tace “malam komar dani GRA dan Allah kayi sauri” juyawa sukayi addu’a kawai take ido arufe Allah yasa bataciba jikinta har wani bari yake, har suka kai sauka tayi tacemai yajirata da gudun ta ta shiga gida mai gadi namata magana amma Kota kanshi batabi ba, a bakin kofa ta tsaya ganin plate din Indomie andan ci kadan sanan ga dan kwalin material dinta akasa maganan mai gadi taji tabayan ta yace “Hajiya basanan yanzun nan alaji yafita da ita kaman hajiyar ba lpy ne” wani irin bugawa kirjinta yayi tai wani irin suman tsaye, da kyar ta iya cemai to ganinan fitowa, wani luuu tayi zata fadi da kyar ta iya dafa bango tana kwalalo idanu tareda dafe kirjinta kaman wata mahaukaciya tafara lalubar jakarta watsar da komi tayi na jakan kasa ta ciro wayarta hanunta har wani barbar yake number Abba tai dailing ringing daya Abba ya daga kafin yay magana tace “Abba, Abba, Abba na kasheta, Abba nakashe yar uwata, wlh wlh bansan meyakai ni bata sniper ba, Abba na shiga uku shairin shaidan ne” maganganu kawai take zaroma Abba kaman zarrara hakan yasa Abba hankalin shi yatashi kodai Farida ta zarene ahankali yace “Farida mekike fadine haka wakika kashe?” “Islam, Abba kanwata, yar uwata jinina nakashe yau, Abba…” katse wayar Abba yay jin yanda take xazzaro maganganu kaman mara lpy number Khaleel dayaji kotaje gidan sune dan yasan batasan gidan bama, yay dailing number saida ya kusa katsewa yay picking ahankali yace “Abba” tashi tsaye Abba yay daga kan kujera dan yanda yaji muryan Khaleel yasa kirjinshi yawani irin mugun bugawa “Khaleel meke faruwa yanzun nan Farida takirani” da kyar Khaleel ya iya cewa “muna general hospital Abb…”wayarce tafadi kasa ta tarwatse sabida yanda jikinshi ke wani irin rawa, ganin ankara gunguro Islam daga dakin datake, wani irin abu kaman babban straw abakinta wata nurse kuma ta rike jakan ruwa da ake dura mata ta bakinta dan yay washing cikinta sunyi ICU da ita, da gudu yabisu amma har an shige da ita anrufe kofar bubbuga kofar yake kaman zai fasa yana kiranta, ahankali ya sulale ya cusa kanshi acikin kafafu tareda sanya hannu akan wuyarshi yafi 15mins ahaka a wurin, bayanshi yaji andafa hakan yasa ya dago jajayen idonshi Abba yagani da Anty Hindu dakuma Mum kana ganinsu kaga tashin hankali karara akan fuskokin su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button