Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 15

Sponsored Links

ATM gallery din yakoma yaciro cash sanan yawuce gida.
Wuraren 4 suka shigo gidan, dawani irin gudu Farida taje ta fada jikin Mum tace “oyoyo Mummy na mundawo” murmushi Mum tayi tace “wanan murnan na lafiya ne” ta kalli Islam dake kokarin bude bottle water tasha dan kishi takeji tace “Ya school din Islam hope kunbama Olayinka credentials dinku danace” gyada mata kai Islam tayi sanan takafa goran abaki, tashi daga jikin Mum Farida tayi tace “Mum yunwa nakeji sosai” tai hanyar kitchen taji andaka mata tsawa “my friend will you leave there! wuce sama kije kafara wanka ki canza kayan jikin ki kafin kinemi abinci, yara duk anbi anbata su” takarashe maganan tana huhhura hanci tana kallon Mum dako daga kai batayi ba, saima marking scripts din dake gabanta da takeyi, turo baki Farida tayi ta juyo tai stairs hakama Islam tabi bayan ta sum sum sukazo suka wuce ta sukai dakinsu.
Dakinsu suka shiga duk ransu abace, suka zauna akan gado, murmushi Farida tayi tafada jikin Islam tace “no Anty Hindun nan bazan bari tai running mood dina yauba am so so happy” baki a sake Islam ke kallonta irin lafiyan ki lau, dariya tayi sosai sanan tasa hannu ta Fizgo Islam suka fada kan gadon a kwance tace “Islam yau I met my superman, wlh Islam yanada mugun kirki, kinsan nasauka daga mota a bakin ATM ba ke Bala ya wuce dake school ba, shine fa bayan naciro kudi wani barawo ya fizge jakana ya gudu, haba saiga giant huge gallant superman dina ya kwatomin jakan, and ko, baima barawon komiba saima kyauta dayamai ya bashi card wai yazo address din zai bashi aiki” ajiyar zuciya ta sauke tace “Sis kingan shi wlh kyakkyawane sosai, black arab, gashida kirki, he is so cute” ba karamin mamaki abin yabama Islam ba tace “Auwal dinki fa Faree?” tsaki taja tace “please karki karamin maganan shi nidai” murmushi tasake yi sanan ta bude ido ta kalli Islam daketa kallonta cike da mamaki tace “gist me jor dazu ina hall Fahad yakirani wai yanaso yazo gida kin hanashi, mesa kika hanashi yazo yaga Dad?” kaman zatai kuka ta tashi tana zage zip din sket din dake jikinta na material tace “kinga Anty Hindu tazo banason anything dazaisa tasani agaba wlh banason masifar ta” da sauri Farida tace “to shikenan saiki hanashi zuwa?” turo baki tayi batace komiba ta zame sket din ta ninke, tashi Farida tayi tace “shikenan karki gayamin gaskiya zurfin ciki saiya miki illa wataran” tai hanyar bayi da sauri ta rike hanunta hawayen datake kokarin boyewa ne yadan zubo da sauri ta share cike da damuwa Farida tace “talk to me Islam” ahankali ta zauna abakin gado tissue ta dauko ta share fuskar ta sanan tace “yasami wani job offer ne a Dubai kuma in two months time akace yay resuming yafara aiki, shine yake damuna yanaso yazo gida ya gaida su Dad, shiwai so yake muyi aure yatafi dani chan, so yake ai auren nan da 2 months, and because nace karyazo shine yaketa fushi jiya ko kirana baiyiba text kawai yamin jiya wai yatafi Abuja yin some papers zai dawo ran monday” “and all this while baki fadamin ba kikai shiru tun jiya nake lura dake kaman abu nadamin ki nadaiyi shiru, wai mesa kike hakane why are you my sister idan nima zaki dingamin zurfin cikine” girgiza kai tayi ahankali tace “am sorry Faree bansan tayaya zan fara fadan miki bane” hugging dinta Farida tayi ta shafa kanta tace “stop crying” share fuskan tayi sanan ta saketa ahankali tace “tun muna SS3 kuke soyayya da Fahad, baki taba bari yazo gidaba kibarshi yazo yaga Dad koma mezai faru ya faru” girgiza kai tayi tace “yanzu fa muka fara University sai kawai nai maganan aure, Anty Hindu da Dad zasuce dama aure nakeso maisa nabari ya kashe min kudi a school, am scared” tureta Farida tayi tace “banza kekika sani sabida tsoro zakije kiyi asaran love dinki, bari naje I will tell mum” tai hanyar kofa da sauri Islam tarike mata hannu tace “dan Allah karki fadama Mum, we will sort it out ran monday idan ya dawo, zance yafara aikin tukunna nan gaba sai muyi auren” sosai ta mugun bama Farida tausayi hakan yasa tace “okay shikenan amma karki bari abin yaja muku matsala” gyada mata kai tayi tadanyi murmushi sanan ta wuce bathroom da gudu jin Anty Hindu ta kwalla musu kira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button