Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 6

Sponsored Links

Dawani irin mugun gudu ya tsallako titin bai damu da babban trailer dayama fadi ba, tsayawa yayi a akan dakalin tsakiyan titin ganin motoci kusan uku su bubbuge juna, waigawa yayi sanan yasake waigawa again dan baiga Eesha ba, ahankali yace “kodai taji tsoro ne ta koma gida?” hanunshi yaji anrike da sauri ya daga kai Yusuf yagani ya rikemai hannu gam, gasu Ibrahim tela da abokanayen shi yan wajen aiki da suka daura hannu aka suna kallon titin ganin yanda mutane harsun cika wajen suna ku matsa aciro ta tana numfashi, wani irin fuzge hanunshi yayi daga Yusuf ya shiga titin, mutane kawai yake turewa kaman zararre yana kutsawa cikin crowd din, Yusuf da abokanansu ne suka bishi da sauri ture mutanen yayi duka harsaida yakai dadai saitin wata bakar jeep, kasa yabi da kallo kaman zararre ganin jini nabin wajen, da sauri ya tsugunna ya leka kasan motar, hango Eesha yayi hakan yasa ya tashi da sauri kaman zararre yace “ku matsar da motar da sauri masu motocin suka shiga, ahankali aka mammatsar da motocin, tsugunna nawa yayi ya jawota ya daura kanta akan kirjinshi yana kallon fuskarta yama kasa magana, murmushi tamai jini nafito wa daga bakinta, kokarin yimai magana take amma takasa da sauri Yusuf ya tsugunna ya dafa kafadar Khaleel ahankali yace “Aisha kice La’ilaha illallah Muhammadur rasulullah” bakinta ne ke rawa haka Yusuf ya dinga maimaita mata harta karba, da kyar ta daga dayan hannunta da ledan agogon ta ke ciki ta daura akan hanun Khaleel, sanan hanunta yay lagwal.

“Abba Abba” kanin Eesha ne Ibrahim yazo da gudu da farin shaddan anko dinshi ajiki, Abba dake tare da abokanan aikin shi yace “lafiya Ibrahim” yana haki yace “Abba anyi hatsari sosai akan titi wlh” subhanallah Abba yafadi shida abokanan shine suka tashi dan zuwa dubawa, Karo sukaci da Babban Khaleel da wanshi suma zasu dubawa hakan yasa dukan su suka dunguma zuwa titin.

Salati gabaki dayan crowd din wajen suka dauka, kowa ya kasa motsi barinma mutumin daya bigeta wanda yake arne yaci suit jikin shi yay mugun sanyi, ahankali Yusuf yakai hannu ya rufemata idanu, Khaleel ya kalla dayaga kallonta yake kaman zai cinyeta yace “Khaleel Khaleel” ko kallon shi Khaleel baiyiba har lokacin yana tsugunne da ita akirjinshi. Tashi tsaye yayi idanunshi sun xhanza launi, hango su Abba yayi kana ganinsu kaga tashin hankali karara akan fuskokin su, ahankali suka tako zuwa wajen tsugunnawa baban Eesha yayi ya kalleta shiru yayi yana addu’a sanan ya kalli Khaleel yace “Khaleel” ko dago kai Khaleel baiyi ba har lokacin fuskar ta yake kallo yay shiru da sauri Ibrahim tela ya koma shago ya dauko wata katuwar tabarman shi dayake yanka dinki akai, karaso wa yayi yamika ma Baban Khaleel ya karba, zuwa wajen yayi ya warware, ahankali baban Eesha ya mika hannu zai karbe ta wani irin ihu yayi yasake riketa yace “karku tabamin matata, bacci take” dariya yayi ya kalli fuskar ta yace “My Eesha sleep kinji idan kin tashi saimutafi, kitashi kafin karfe daya fa dan lokacin zaa daura mana aure” Ahankali baban Khaleel yake furta “innillahi wa innailaihi raji’un” ahankali yace “Son saketa zamu kaita gida amata sutura” ko kallon mahaifin nashi baiyi ba, hakama Baffan shi Abba babu wanda ya kalla cikin su, Yusuf ne da abokanansu su kusan takwas suka rirrike shi da kyar aka dauketa akai gida da ita, Khaleel kam ahaka abokan shi da Yusuf suka rirrike shi yana maganganu dako gane meyake fadi basayi suka taho kofar gidan su Eeshan dashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button