Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 17

Sponsored Links

Yadda Inna ta sunkuyar da kanta kaɗai ya alamtawa Latifa Omar maganar haka take, cikin yanayi na kiɗima ta shiga girgiza kai ta ce “Kada ki ce mini haka maganar take, kada ki ce ni Shegiya ce bani da uba, kada ki furta hakan a gareni na ruƙeƙi Mama” Girgiza kai ta ci-gaba da yi while hawaye na zuba a Idanunta ta ce “wallahi faɗar shegiya ce ni bani da toshe daidai yake da bugawar zuciyata Mama, ki ƙaryata Dr ki ce He’s lied to me, ki ce ba haka bane, bani Latifa yake nufi ba, bana son samuwar wata hujja ko tubalin da zai sanya na tsani sunana na Latifa Omar, You are my real parents, I have no one better than you in my world” Ta kalli mahaifinta dake kwance yana numfashi da ƙyar, ta juya ta kalli Inna wacce hawaye ya gama wanke mata fuska taƙi cewa komai, Dr na tsaye yana kallon Ikon Allah Latifa ta zube saman qiwwoyinta ta ce “I know that I am not an adopted child, I am not Shegiya and I was born wedlock,ku duniya ta sani matsayin iyayena Mama meke faruwa mene gaskiyar al’amarin? Shin ne Adopted child ce ko ƳAR-AMANA (Nimcy upcoming book)?” Inna ta ɗago kanta zuriyarta na bugawa da ƙarfi, ranar da take ta gudun zuwanta gashi ya zo, ranar da bakinta ba zai ƙarya ba ta kalli Latifa ta ce “Gaskiya kike son sani Latifa domin zuciyarki ta daina kokwanto, ko kuma salama da sanyi kike buƙata na kwanciyar tashin hankalin naki a yanzu ta hanyar rufe miki ainahinki da asalin wace ke?” Latifa ta ce “Gaskiyar nake son sani Mama, ina fatan kalaman da zasu sanya fuskata cikin walwala ya fito daga cikin bakin ki” Inna ta ce “Ke ba ƴar Malam ba ce, ba kuma ƴata ba ce” With shocked Latifa ta saki baki tana kallon Inna, kukan ya tsaya mata cak, gata dai a raye tana numfashi, ƙirjinta na harbawa alamar zuciyarta a daidai take aikinta, amma zufar dake yanko mata ya kure dukkan wata nutsuwar data samu wanda kai tsaye mai Kallonta zai samu tubalin gina tunaninsa wacce sarrafa ƙwaƙwalwarsa ga cewa ta samu matsala, tana raye amma jinta take tamkar matacciyya a rufe a cikin rami sbd tsananin gigita da tarin kiɗima wanda ya haɗe mata da tu’ajjujin jin al’amarin dake neman ruguza gobenta. Inna ta ce “Wannan shi ne gaskiya al’amarin, ke ƳAR-AMANA ce, rana tsaka kina jaririyar Malam ya shigo mini dake matsayin TSINTACCIYA, har yau har kwanan gobe bani da masaniyar daga inda ya samoki, balle na bincika asalinki ku da asirrin ce ne” Latifa Omar ta kasa cewa komai tana ƙoƙarin saita numfashinta dake ƙoƙarin yi mata gaddama. Dr ya ce “That means he is the only one who knows the truth about who Latifa is, and who is her real father?” Inna ta ce “That’s what I mean” Dr ya jinjina kai. Kafin su motsa na’urar jikin Malam ta fara ƙara da sauri Dr ya yi kansa yana duba gudun oxygen ɗin dake aiki a jikinsa, ya ƙara ɗaga kai ya kalli na’urar yaga numfashinsa ne ke tafiya yana yin ƙasa baya dawowa, Inna ta miƙe ta ce “Malam kada ka tafi ka barmu cikin wannan juyayyen al’amarin mai wahala fahimta ko gane asalin shi, kai ne kaɗai shaidar da zata fitar daga Latifa daga cikin halin da take ciki, tun ba yanzu ba nake jan kunnenka daka faɗa mata gaskiya amma kayi burus, ni ma kace nayi ta aurena idan na faɗa haka muke zaune tsayin shekaru, mai yasa kake ƙoƙarin tafiya bayan kasan zaka bar baya da ƙura? Eh Malam Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” A daidai lokacin numfashin Malam ya gama tsayawa cak! Alamar ran shi ya tafi zuwa kushewa tasa ta ƙare ciwo bana tashi bane, Latifa Omar ta ƙurawa gawar Malam idanu kamar shasha kuma ta saki murmushi while hawaye na zuba daga cikin idanunta ta ce “This is something that will never be possible, there must be someone involved in all these things, it is necessary to find out who it is” Wannan abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, dole ne a samu wanda ke da hannu a cikin dukkan wadannan abubuwa, wajibi ne a gano ko wane ne. Inna dake kuka kamar ranta zai fita ta ce “Kul na kuma ji, ahir ɗinki Allah ne kawai mai yin yadda yaso da rayuwar bawa, ki yarda Ubangiji ya ƙaddara miki taki rayuwar haka nan, ya aminiyarki Majeederh tayi da nata rayuwar? Ba gashi komai ya zama tarihi ba, kalli wanda take aure ashe ɗan shugaban ƙasa ne, Kiyi haƙuri mu yi addu’a sai komai ya zo da sauƙi” Kamar zautacciyya Latifa ta ce “Majeederh” Mai yasa ba zata barta haka bane, ta ƙwace mata komai ba, a hankali ta ce “Now Majeederh will take revenge on me? Amma tasan abubuwan dana mata ba” Ita a dole yadda ta cutar da Majeederh bata yarda sakayya Ubangiji ya fara nuna mata ba, ta jingina hakan da alaƙanta shi da wani ke mata asiri. Ta riƙe kanta da hannu bibbiyu ta kurma ihu cikin I.C.U ɗin ta ce “Wai meke shirin faruwa dani ne, Ubangiji me na aikata da zafi har haka”… Uncle Isma’il na zaune a parlour shi, waya yake yi a hankali har Anti ta fito fuskarta ɗauke da murmushi yana ganinta ya kashe wayar yana haɗe fuska ta ce “Ashe ka shigo tun jiya, ina ta zullumin ina ka kwana” Uncle Isma’il ya ce “Kin san ai ba zan bar Kano ba tunda ba kurciya aka yi mini ba, aka rabani da Jawaad da Sona” Zuciyarta ya bada sauti gabanta ya faɗi, ta daure da ƙyar ta ce “Ayya wanne irin kurciya ba daɗin ji, yanzu dai bari na kawo maka breakfast” Ya ɗago idanunsu ya zuba mata su ya ce “Lubna” Ta ce “Na’am” Ya ce “Stop pretending plx” Ta ce “Kamar yaya kenan Abban Jawaad?” Ya ce “Kamar yadda dai kika ji na furta, ki daina nuna you’re smart, wlh tllhi I’m smarter than yanzu, i am smarter, kuma ko da ban gano gaskiyar labarin ba; babu mamaki garƙame tunanina ki kai da bakina kika yarda da ɗan maƙulik a tekun maliya” Baki ta buɗe za tayi magana ya ɗaga mata hannu ya ce “Baki da wani harafi da zaki harhaɗa wajan fahimtar dani abin da na jima da fahimta, da kuma wanda na gane a yanzu, ki buɗe kunne da kyau kiji! Ba zan tambayi hujjarki tayin hakan ba, yiwa Alpha kurciya da raba Abbu da majeederh tun tana shekaru goma, sam ba zan yi hakan ba Lubna abu ɗaya zan faɗa miki, wlh wlh Allah ba zan barki ba, ki shirya amsar hisabin duniya domin zaki amshi kasonki tun kafin zuwanki kushewa” Uncle Isma’il da idanunsa sukai jajur ya ce “Wlh wlh ina jin ni ba alkairi bane a cikin ƴan uwana, na zama silar baƙanta zuciyar su, ki shafa mini baƙin fentin da ba zai taɓa gogewa daga fuskata ba dani da yarana, kin raba Alpha da iyayen shi, da mahaifar shi cibiyar shi, kin raba shi da ƙasar shi bakiɗaya, a cikin hankalinsu yake ko yana cikin gushewar tunani ke kaɗai kika san hakan, kin raba soyayyar fari, Since Majeederh was a little girl, he has been taking care of her, he loves her so much, he has nothing to ask or care for except her, na jima da sanin zallar so yake mata, ba so na ƴan uwa ba so ne irin na aure, He is an arrogant and deep inside that is why his situation is not understood, wlh wlh bana ko jin ɗar baƙin cikin auren su kike shi ya sa ki ka aikata hakan” Uncle Isma’il ya goge hawayen daya sakko masa ya ce “Ki kwantar da hankali bashi ki kaiwa ba, Jawaad da Sona su kika jawa, faɗar Ubangiji ce duk abin da kayi za ai maka, ƙaiƙayi koma kan ɗan masheƙiyya, zaki saka wutar gaba tsakanin Mijin Malama Khalil da ɗan uwan Malama Alpha” Ya miƙe tsaye yana kaiwa da dawowa ya ce “Me tayi miki da zafi har haka ne don Allah? Me kuma ɗan uwana ya yi miki?” Za tayi magana ya ƙara ɗaga mata hannu ya ce “Ya isa, enough is enough bana son ƙara ganinki Lubna ki tattara komai naki ki shige Gombe ki koma cikin Fulani wajan Ruga a ci-gaba da tatsar nono, ashe da nake cewa Fulanin Gombe ba dai asiri ba gaskiya ni ma ba haka kika barni ba, Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Lubna kin cuceni kin cuci kan ki, kuma kin cuci yaranmu, maza ki fita daga gidan nan, na sake ki saki ɗaya, na sakeki saki biyu, na sakeki saki uku” Dim! Anti ta yanke jiki ta faɗi babu inda yake motsi a jininta, Uncle Isma’il ko a jikinsa ya sanya kai ya fice, yaci karo da Jawaad a entrance zai shigo ya ce “Jawaad” Ya ce “Abba” Ya bashi key ya ce “Muje gidan Uncle ɗin ka, i can’t drive myself” Jawaad ya amshi key suka nufi gidan Abbu…. Kasancewar weekend ne yasa kowa yana gidan, Abbu na zaune a parlourn shi dake part ɗinsa, baya cewa komai sbd abubuwan da suka taru sukai masa yawa a zuciya, lokaci yake sawa a kira masa Majeederh sai ya yi ta Kallonta can yaje ta je kawai, yanzu ma yana zaune sanye da Khasmir fari tas ya ɗora ƙafarsa akan table idanunsa rufe ya jingina da jikin kujera, hannunsa riƙe da black tea yana ɗan juyawa,a hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar Parlourn ta shigo bakinta ɗauke da sallama ta shigo, tana sanye da hijabi har ƙasa ta ƙara haske tayi ƙima ta ƙarasa zata zauna ƙasan carpet ya nuna mata saman kujera ta zauna ta ce “Gani Abbu” Ya zuba mata idanunsa ya yi ta kallonta ta sunkuyar da kanta ƙasa, ya jima yana binta da kallo kafin ya ce “So da gaske kece dai Hawwa’u” Tayi murmushi ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ce “Kina son Mijin naki?” Tayi shiru clamly ya ce “Open your heart dear” A hankali ta ce “Even though I did, is a different thought that flashes through my mind” Ya shiru abubuwa da yawa suna masa yawo aka silently ya ce “Come here” Ta miƙe ta ƙarasa kusa da shi saman kujera ya kama hannunta ya ce “Meke faruwa? Do you like him?” Ta kasa cewa komai ya saka hannunsa tare da ɗago fuskarta ya kalleta tayi saurin ɗauke nata idanun kamar wanda akai forcing nashi na yi mata magana ya ce “Ya akai?” Ya furta yana ɗan riƙe ƙansa da son daidaita nasa nutsuwar ta kasa cewa komai sai ta fashe da kuka tana ɗora kansa akan ƙafafuwansa, kuka take da dukkan ƙarfinta wanda yake tasuwa tun daga ƙasan zuciyarta, kuka ne wanda ta jima bata samu zarafin yinsa ba, Abbu ya runtse idanunsa a hankali cikin sanyi kukan nata yake shiga yana ratsa ko’ina na zuciyarsa, gabaɗaya ƙofofin gargasar jikinsa suka bubbuɗe yana amsar kukan nata cikin yanayin da ba zai iya fahimtar shi ko gane shi ba, muryarta na rawa ta ce “He is the one who destroyed my life, without my consent or approval, ba tare da yarda ko amincewata ba su Uncle suka ɗaura mini aure da shi, Abbu Khalil baya ji zuciya gare shi baya iya bakinsa da sarrafa kansa, na girme shi ba zan iya zama da shi ba, ba zan iya yi masa biyayya ba” Abbu was speechless, shi kansa zuciyarsa gudu take, ya saka hannu ya ɗagota bakiɗaya fuskarta cikin hannunsa ya ce “Ba wannan nake son ji ba” Ya lumshe idanunsa ya buɗe shortly ya ce “Do you love him?” Majeederh tayi shiru a hankali kuma ta girgiza kanta alamar “A’a” Abbu ya ɗora kanta a shoulder ɗinsa yana sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya mai ƙarfi wacce take daga ƙasan zuciyarsa ta kuma jima shekara da shekaru. A hankali ya ce “I am sorry, I’m sorry Hawwa’u”…… Parlourn ya yi shiru bayan zuwan President Denial David, Dad ya kalli Majeederh dake gabansa ya ce “Ba zan raba muku aure ba, idan ya amince da auren ƴar uwar ta shi” Ya yi shiru can ya ce “Idan kuma yaƙi shi ma zai ɗan-ɗana zafin rashin masoyi, don sai raba auren” A hankali Majeederh ta ce “I am sorry Dad, na amince ya auri Debeka ni kuma ya sakeni” Chancellor dake zaune ya ce “For what reason?” Kanta a ƙasa ta ce “I don’t love him anymore” Gabaɗaya Mutanen wajan suka kalli Majeederh da mamaki cikin sauri Yaya Bilkisu ta ce “You’re Liar, ƙarya kike kina son mijinki” Majeederh ta girgiza kai ta ce “Tun farko kun san bana son shi” Zata sake magana Dad ya ɗaga mata hannu ya kalli Khalil da Majeederh kawai yake kallo without blinking his eyes ya ce “Yanzu zaka rubuta sakin ko ya?” Khalil ya miƙe tsaye ya ce “Burinka ya cika? Wannan shi ne Abin da kake so ko?” Dad ce “Her divorce paper, write it immediately” Khalil ya girgiza kai yana kallon Majeederh domin tafi bashi mamaki ya ce “To bari kiji na faɗa miki sai dai mu mutu haka nan, amma ba zan taɓa rubutu tsinanniyar abar da kike muradi ba” Dad ya miƙe tsaye ya zabgawa Khalil mari ya ce “Her divorce papers, ka rubuta do so immediately” Khalil ya kalli Dad ɗin nasa ya ce “I can’t write it, Dad please tell me are you real father?” Abbu dai na zaune watching all of them tunaninsa ya bambanta da nasu, zuciyarsa ta kaɗai ta da wajan gabaɗaya, Uncle Isma’il ya ce “Mr President sir ina tunanin wannan ba hanya bace ta nemi mafita, Ibrahim zai auri Debeka, kuma zai zauna da matarsa Majeederh” Dad ya numfasa ya ce “Baka ji ba da bakinta bata son shi, daman yake kukewa yaranku Forced married?” Ya girgiza kai cike da takaicin zuciyar Khalil ya ce “Yarinyar ku mai kyau, hankali ilimi, sam ba tayi deserving auren yaro irinsa ba na faɗa muku” Uncle Isma’il ya ce “Karka damu da hakan, mun san halinsa mun zauna da shi kuma ko zaiwa kowa banda ita” Dad ya miƙe tsaye Chancellor ma haka kana ya kalli Majeederh ya ce “Daughter jeki waje wajan Zizi ki jirani” Majeederh ta miƙe tsaye ta juya ta kalli Abbu taga ita yake kallo ta nufi waje da sauri hannunta riƙe da waya da hand bag, Khalil ya bi bayanta hakan yasa Dad gyara zaman bluetooth na kunnen shi ya yi magana, ya kalli Uncle Isma’il ya ce “A bani a ron daughter in-law, gobe idan an ɗaura auren su a church ina nufin shi da Debeka ita kuma zata dawo ku shiryata zuwa Germany” Yana faɗin hakan ya fice daga ciki, tun a entrance ya hango yadda ake zuba dambe da Khalil sun riƙe shi da ƙarfi, shi kuma yana ƙoƙarin kwancewa ya ƙarasa wajan Majeederh, Gabaɗaya ya yi wa Escorts ɗin duka ya karya hannun wasu wani ya fasa masa baki, Dad ya ce Majeederh ta shiga mota akan idanunsa suka fice daga gidan kana Escorts ɗin suka sake shi ya bi motar da kallo, zuciyarsa a sunkushe bai taɓa jin zafin Majeederh ba irin na yau, tana son dawo masa da halin daya manta da dainawa, idanunsa har wani ruwa ke kwanciya a cikin su, burinsa a yanzu ya yi Idanu biyu da barasa…. Har dare ya yi Majeederh ta kasa samun sukuni a ranta, haka kurum ta tsani harafin D ta dinga juyi akan gado, ita kanta a wannan lokacin burinta ta samu maganin da His Excellency Abu-turab yake mata take yin bacci, ta kuma kasa gano wani magani ne, ta kasa rabuwa da shi yana nan zaune a ranta, a hankali ta jawo jakarta da nufin kiran Latifa sai ga Envelope ya faɗo, gabaɗaya ta mance da ita cikin sauri ta ɗauka tare da buɗewa abinda ta fara gani shi ne….
_“No words to explain, no words to describe; no words to ask your forgiveness, Wait for me I’ll be back sooner or later! Please Jee”_
Sune rubutun da idanunta ya fara cin karo da shi, ta juya bayan paper ɗin taga an saka BAD MAN, _THE STUBBORN BOY, CRIMINAL, GANG BOY, THE LEADER_ Cikin sauri ta shiga karantawa, kafin ta ƙarasa kuka take kamar ranta hadda majina jikinta rawa yake da ɓari yana wata iriyar ƙyarma,wani irin zazzafan zazzaɓi ya nemi rufeta bata iya ƙarasawa ba ta ɗauki hijabi ta saka, a hankali ta fita daga cikin bedroom ɗin gidan da suke tana fita waje wani soja ya sara mata cikin dauriya ta ce “Key car Plx?” Ya ce “Madam zaki fita ne?” Ta zuba masa Idanu ya ce “I’ll drive you” ta ce “No Thank you” Ya bata key ta amsa tana shiga motar ta jata da wani irin sauri tana tafe tana kiran number Khalil but a kashe, kuka take cikin damuwa ta ce “I am sorry, i know nothing about that” Har gidansa taje amma ba alamar mutane, wannan gidan kawai ta sani, tana da tabbacin ba zai je gidan Uncle’s ba, sbd ya yi zuciya daman bai damu da zama gidan Abbu ba “Lebanon Club” Shi ne ya faɗo mata a rai, tabbas ta taɓa jin Taj ya faɗa, daga inda take a yanzu 22ms 10km ne zai kaita Fagge due to the traffic conditions duk da dare ne, magana ake ta wajan 12 na dare, gudu kawai take akan titi without knowing yama take driving ɗin a haka ta shige Bampai Rd, ta shige Zaria Ave ta zo Miller Rd daidai by pass na firstmonie agent on the left ta samu traffic, ji take kamar ta tashi sama deep down na zuciyarta kuma addu’a take Allah yasa yana wajan, don tasan baƙar zuciyarsa yanzu sai ya bar ƙasar idan har ya samu jirgi, motar ta ƙarawa gudu har ta iso fagge dake daga Miller Rd zuwa nan tafiyar 600m, ta dinga kallon Lebanon Club ɗin ganin kamar rana manyan motoci birjik a hankali tayi parking ta fito, har lokacin hannunta riƙe da envelope ɗin, ta shiga ciki wani ta gani sukai ɗan magana ya ce “I am sorry Maa, he’s not around” jikinta ya yi sanyi ta juya zata bar wajan ta hango shi tsaye ya juyawa ruwan da yake gudana a wajan baya, hannunsa ɗaya riƙe da rigarsa ɗaya kuma ya riƙe wata ƙatuwar kwalba wacce ya kasa buɗeta, ya fashe gabaɗaya Glasses cup ɗin da aka kawo masa, gabanta ya faɗi badai giya ya sha ba? Jin tsaiwa a bayansa ya sanya ya juya a hankali sukai idanu biyu, taga idanuna kamar gauta don jaa yadda yake Kallonta a makake yana lumshe idanunsa ta ɗauka a cikin maye yake ta ɗaga masa envelope ɗin ta ce “Why?” Ya kalleta ya kalli envelope ɗin sai kawai ya sake juya baya, cikin sauri Majeederh ta ƙarasa inda yake tare da tsayawa a bayansa, a hankali ta zura hannayenta ta ƙasan nasa hannunsa ta ɗora tafin hannunta a ƙirjinsa dake a buɗe babu riga hannun ya sauka a kwantaccen sumar wajan, ta ɗora kanta a wuyansa cikin wani irin yanayi dake fisgarta yana shigarta ta bashi da ƙyakƙyawar runguma ta baya ta fashe da wani irin raunataccen kuka ta ce “I… I… Love You

 

Bear with the errors👐🏼zaku samu tun daga 67 har 70 a arewabooks kuma zan rage yawan readmore, idan ba a daina fitar mini da littafi ba wlh zan tafi ya ji aikin book 2 #500 ne ba tsada 08119237616

Related Articles

 

Idan menstrual period dinki is too DARK yay baƙi ko green kuma yana wari sosai KO KINA FAMA DA KAIKAYIN GABA DA VAGINAL DISCHAGE DIN DA BAKISAN KANSU BA.

KO PERIOD baya zuwa kwata kwata ko baya xuwa da yawa ko yana zuwa over dose koma fallobian tubes naki ya toshe baki daukar ciki ta dadi, KO kina FAMA DA shegun toilet INFECTION DA SUKA GURBATA MIKI HAR CIKN JININKI *MAGANIN MATA BAIYA MIKI AIKI,KINYI AURE AMMA BAKI SAN JIN ƊADIN JIMA’I BA KUMA BAKISAN MATSALAR BA* PELVIC OR SEXUAL TRANSMITED DISEASES NE MASU *TOSHE BAKIN MAHAIFA*, I MEAN KO WANI IRIN CIWON INFECTION NE JUST NAME IT.

HAIHUWA NE BAKIYI SABODA👇🏿

PID, STDs DA FIBROID?

CIKIN BAYAN HAIFA?

YAWAN ƁARI?

LOWS cervical fluid
COUNT..?

CYSTIC INFECTIONS?

KINASON KWAN HAIHUWAR KI YAY KARFI DA QUALITY

LOW LIBIDO NE?
KO KUWA SEXUAL WEAKNESS?

💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾SAUƘE KAYAN KI ANAN

*Our 7 DAYS EXTENSIVE INFECTION CLASS ZAI SANAR DAKE KOMI GAME DA FEMINE HEALTH DINKI*
Sann kuma zasu tsakuro lecture akan matsalolin *FAMILY PLANNING*
HAKAXALIKA SUNA DA FANNIN TATTAUNAWAR SIRRI WATO *PRIVATE CONSULTATION GA DUK MAI BUKATA KAN LAMARIN LAFIYARSA KO AURENSA*

CLASS DINMU XAI SHARE MAKI HAWAYEN KI YAR UWA, ZAMU FARASHI NE A WATA MAI KAMAWA.(SPTEMBER)

DOMIN SHIGA WANN
CLASS MAI RAHUSA KA BIYA *1K* TA WANN ACCT LAMBA👇🏿

*0472624453 Musa Maryam Aminu,Gtbank*
Shedar biya 08060712446.
REGISTAN PRIVATE CONSULTATION A TUNTUBE MU 08060712446(CHATS ONLY)
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *The messenger*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button