Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 37-38

Sponsored Links

Bonus 37-38*

 

Kinkimar Aneey yayi ya fita da ita da mugun gudu yana jijjigata cikin tashin hankali yana cewa “na shiga uku Aneesah kada ki mutu wlh Ni dake na kwanta bansan ya akayi kika zama Hasina ba wlh tallahi tunda kika nunamin ɓacin ranki ban ƙara sha’awar zina ba Aneey ki taimakeni kada ki mutu ki tsaya kiji abinda zan faɗa miki gashi ki bari mu raini Mutallab tare Please…..”
Jefata yayi a mota Jimba ta shiga ita da Mother suka fice daga gdan suka nufi Royal hospital ɗin dake jikin gdan sarautar yanda ya taka birki ne yasa dukkan likitawan fitowa ganin Little Prince ne da kansa yasasu rugowa a guje suka cacumi Aneey cikinsu babu wanda ya damu da jinin da take zubarwa suka shige da ita ICU saboda tafi gaban emergency ɗakinta guda ita kaɗai suna shiga suka jorner mata na’urori a ƙoƙarinsu nason ganin sun daidaita bugun zuciyarta amma abin ya faskara har saida Prince Abdulmunaf yazo yasa hannu sannan suka samu bugawar zuciyar ya fara hawa me makon ƙasan da yayi.
Jini suka jorner mata sannan sukayi mata allurai suka fita dukkansu suna sharce gumi Abdu dake zaune ya tashi ya tari Prince Munaf yace “Bro ya jikin Wyf?” Wata gwauruwar ajiyar zuciya Munaf ya sauke yace “Meye yasa zuciyarta wannan bugawar ta rashin shiri ko kasan ikon Allah ne kawai ya kawota yanzu kuma har yanzun ma bamuda tabbacin zata tashi domin ta shiga yanayi na doguwar suma waima Abdu ya akayi ta haihu a gida bayan kasan cewa tun farkon cikin nan an faɗa muku zuciyarta tana ɗan kumbura meye ya kawo me kakeyima yarinyar nan…..”

Related Articles

 

Kunya ce ta sanyashi shafa kansa ya ɗago idanunsa suka haɗa idanu Munaf yace “Tun kafin wannan lkcn nasan yarinyar nan hƙr takeyi dakai Abdu nasamu lbrn duk abinda yake faruwa a gdanka ka mayar da neman matan banza ɗabi’arka ka kora matarka sashin Mother ka kawo WATA KARUWA ka ajiye a gdan Ahad da ka kashe ƴar mutane da wannan baƙin cikin ina ganin gara kabarta ta koma ga iyayenta zaifi sauƙi”
Jikinsa ne yayi sanyi tsoro ya kamashi wato duk abinda yakeyi ashe ansani kallonsa kawai akeyi lallai yana cikin matsala Mother ce ta zuba masa ranƙwashi tace “mugu dashi Allah dai saiya biwa yarinyar nan haƙƙinta kasan cewa bazata isheka ba meye yasa ka aureta Abdu yarinyar nan batason auren nan kayi ƙarfa² ka aureta maimakon ta samu kulawa da tattali na musamman a gurinka sai akasin haka to gakanan ga duniya nan ga Allah nan kaci gaba idan zakakai labari kaima dai yanzu ubane ga Mutallab nan yazo duniya bamusan adadin nawa ne zasu biyo bayansa ba”
Tana mgnr tana gyarawa yaron rufar da tayi masa da wani towel me laushi, tuɓus jikin Abdu ya mutu wata kunya da tausayin Aneey ya shige shi ya tambayi kansa ashe dama tasan yana neman mata amma bata taɓa nuna masa ba? To wai shima meye yasashi bin matane bayan duk abinda yake nema gurin mace matarsa tana dashi?”

 

A kasalce ya fice daga asibitin shima ƙa’idar asibitin ce ba’a zaman jinya hakan yasa kowa ya tattara ya koma gda sai ita kaɗai a asibitin, abu kamar wasa saiga Aneey tayi wata guda a asibitin satinta biyu ta farko amma bata iya mgn sai hawaye kawai Mother da kanta ke jinyarta abinda Mother ta lura dashi ko idonta biyu Indai Abdul-Ahad ya shigo to zata rintse idonta bazata buɗe ba har sai yabar asibitin tausayin kanta da Mutallab na damunta ƙasan zuciyarta na tambayarta meye ribarta a nuna Abdu tace uban ɗanta ne babban tashin hankalinta kullum idanunta gizon yanayin da taje ta tarar da mijinta da yayarta yakeyi mata da ta tuna sai zuciyarta ta kama zafi hawaye ya ƙwace mata wannan rana tayi muni a rayuwarta batason tunawa da ita.
Ranar data cika kwanaki talatin aka sallameta a asibiti suka koma gda wani abun tashin hankali daya damu ruhinta Mamansu taji haihuwarta amma bata iya zuwa tayi mata sannu ba Baba da yake fama da jikinsa shine ya hawo mota yazo har asibitin ya dubata saida yayi kwana shidda ya tafi, Hassy kuwa tun ranar da abin ya faru da daren ta sace jiki ta fice daga gdan wannan karon taci alwashin ko zata tafi baibai saita watsa auren na ƴar’uwarta.

 

Ita kuwa Aneey ƙoƙarin danne abinda ya faru takeyi tunda suka dawo gda amma abin ya faskara kullum abin ƙara cin zuciyarta yakeyi inda shikuma Abdu kunyarta yakeji idan ya zauna yanason fahimtar da ita abinda ya faru a daren sai kawai yaji zuciyarsa ta karye tunba idan yaga ta lumshe idonnan ta rungume Mutallab tana hawaye ba.
Juriya ya aro ya azawa ransa yau dai yayi niyyar ko Aneey bazata saurareshi ba saiya zayyane mata komai musamman ma da yaga tabarshi ta zubansa idanu babu uhm babu uhm-uhm saidai kallo gashi iya bala’insa ta haramta masa ɗaukar ɗanta saidai ya hangeshi da taga zai ɗauke shi zata ɗauke abinta ta shige ɗaki ta kulle wannan horo nata yayi masa tsauri a ganinsa Gara ta zazzageshi ta huce zaifi masa sauƙi. Ko kaɗan bayason yaren shiru gashi Aneey dashi take azabtar dashi.

 

Tun yamma yake fakonta har dare yayi Sa’a ranar data cika kwana sittin da haihuwa taci kwalliyarta ta goye ɗanta a baya ɗan da rabonsa da taɓashi tun kafin ta samu hayyaci yanason yaji ɗuminta dana gudan jininsa ya kasa yayi mata kawaicin har ya gaji.
Fitowa tayi daga ɗakinta ta nufi kitchen saboda yunwa da taji tanaji ta zuba abinci jallop ɗin Shinkafa ce da taji hanta da kifi sai ƙsmshi takeyi ta ɗauko lemo ta fito tana jijjiga Mutallab wanda suke kira da King little ta nufi ɗakinta batare data duba ba ta mayar da ƙofar ta danna mata key tabar key ɗin a jiki ta nufi gadon ta aje abincin saman wani ɗan ƙaramin table ta kwanto little King ta cillashi sama ta cafe tace “Baban kowa ka cika rigima ka daina kuka kaji bani na zaɓa maka ba ƙaddararmu ce a hak…..”

 

Numfashinta ne ya ɗauke ta ɗauke wuta gabaɗaya saboda ɗumin hannunsa da taji a bakinta ta saki wani numfashi me ƙarfi daidai lkcn da yaja hannunta ta fuzge tare da ƙanƙame ɗanta ta buɗe baki zatayi mgn kawai sai hawaye ya zubo mata sharrr tayi saurin juyawa zatabar ɗakin ya maza ya zare keyy ɗin ya tsaya jikin ƙofar jikinta yana rawa tayi ƙasa tace “na roƙeka da girman Allah ka barni na fice maka daga ɗakin nan inma gdan kakeson nabar maka zanbar maka”
Buɗe ƙananun idanunsa yayi akanta yace “Duk abinda kika zaɓawa rayuwarmu kiyi Aneey amma kafin nan kiyimin Alfarma ɗaya ki saurari me zance miki na rantse da Ubangijin da yake nufina da numfashi ina azabtuwa da matakinnan da kika ɗauka a kaina Aneey wlh tallahi bansan ya akayi na kwanta da Hasina a wannan daren ba nidai kawai muna kwance dake naji kaina yana ciwo zuciyata ta ƙuntata sai na tashi na fito na shiga ɗakina nayi tagumi daga haka bacci ya ɗaukeni a zaune kawai sai nayi mafarkin mun tafi kilisa daji na nemeki na rasa na rinƙa nemanki lungu da saƙo banganki ba shine fa na zabura na tashi ina salati ina ta ƙwala miki kira sai naga kin turo ƙofa kin shigo kika zauna kusa dani na zamo ina kallonki kinamin murmushi kina shafa kaina daganan muka kwanta Allah shine shaidata ban bambance badake nake tare ba sai lkcn da naji ƙarar ki da kukan Mutallab daganan na dawo hayyacina Aneey inasonki wlh bansan meye yasa nake kasa faranta miki ba kiji tausayina addu’a nake buƙata bansan meye yake karakaina da rayuwata ba……”

 

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

*OUM HAIRAN*
[12/24, 10:21 AM] Oum Hairan&Affan:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button