Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 52

Sponsored Links

Farida tafi minti 10 tsaye a wurin sanan ta daddafe bango tafito tana ganin jiri ta shiga napep din tareda cemai muje, tafiya kawai suke dan gabaki dayanta bata hankalin ta da kyar tace “kaini asibiti” “wani asibiti hajiya” Ahankali tace “kowanne” tafiya suka dingayi yay parking agaban general hospital yace “kije wanan sunfi kwararrun likitoci Allah sawake” duka kudin purse dinta taciro tabashi kaman wata tababba take tafiya har taje reception tana waige waige Allah sa nan suke, hijabin Anty Hindu ta hango ta cikin emergency ward hakan yasa ta daga kafa da kyar ta shiga ward din, tsayawa tayi daga ta wurin kofa tafashe da kuka sosai tana kallon su yanda suka tsattsaya gaban ICU.
Dago kai Khaleel yayi karap suka hada ido da ita, mikewa tsaye yayi kaman namijin zaki yana kallonta hakan yasa Abba suka jujjuya suna kallon inda yake kallo, hannu ya daura akan belt dinshi na jikin wando yana kwancewa batare daya dena kallonta ba, wani irin Fizgo belt din yayi azuciye koni bantaba ganin Khaleel ahakaba wanan zuciya hmmm! Ko kallon fuskar su Abba da mutanen dake ward din baiyiba yay inda take tsaye yana tafiya kaman wani mayunwacin zaki jikake fui fui fui dukan Farida yake da belt Kota ina…

Ahankali Islam ta rike hanun Dr yake daddane cikinta tana amayar da ruwan dasuka duramata ta baki, wani irin hawaye ne ya gangaro daga gefen idanunta da kyar ta iya magana tace “please stop abinan dakekemin yamafi min azaba kan komi, please I want to see my husband” yanda tai maganan yasa jikin Dr yay sanyi sosai, wani irin tari tayi hakan yasa ruwa yakara fitowa daga bakinta tace “please I want to see him” ahankali Dr yajuya yafita daga dakin hango Khaleel dayayi yana chasa Farida ga mutane duk antaru ana kallo su Abba dai na tsaye danko yunkurin kwatota basuyiba Mum ce ke kuka sosai, da gudu Dr yay wurin yana “subhanallahi” rike belt din yayi yana kallon yanda Farida ke kuka kaman zata mutu, dawani irin ido Khaleel da kallai, girgiza mai kai Dr yayi tareda janshi yace “kayakuri, Matar ka nason ganinka” bin bayan Dr yayi aka budemai dakin ya shiga kadan tabude idonta tana kallonshi da sauri yay kanta yana shafa kanta hawayen daya gangaromai ya share yama forehead dinta kiss yama kasa magana hanunshi yaji tarike gam hakan yasa ya dago kai yana kallon fuskarta, twisting jikinta tayi tareda fito da ruwa sosai daga bakinta tashi yayi zaije yakira Dr yaji takara kamkame hanunshi da sauri ya kalleta, dan murmushi tamai sanan ta bude bakinta da hakoran ta dasuka dan hade tafara magana, da sauri yakai kunen shi saitin bakinta yaji tace “Yaya Khaleel inaso Kamin alkawari” tadanyi shiru tana numfashi sama sama tace “inasonka sosai, I love you so much Muhammad Khaleel” daura fuskarshi yay akanta ahankali ya lumshe ido wani irin zazzafan hawaye ne suka zubo daga idonshi suka sauka agoshin n
ta da kyar yace “and I love you more than anything Islam, please stop talking, kidena magana kinji u will be fine lemme go and call d Dr” yajuya zai tafi hanunshi takara kankamewa tana kallonshi da idanunta dasuka kankance tafara magana, kai kunenshi yayi saitin bakinta ahankali yaji tace “Kamin alkawari, promise me zaka auri Farida idan namutu, Farida na sonka so na gaskiya, promise me” Ahankali ya dago kanshi dudda bata da lafiya bai hana ya mata wani irin mugun kalloba ya fizge hanunshi daga nata yana goge wasu hawayen bakin ciki dasuka zubo, da kyar ta iya daga hannu ta mikamai idanunta na fitar da hawaye ta gefe, ahankali ya tako zuwa gabanta yarike hanun gam zatai magana yadaura yatsan shi akan lips dinta ya girgiza mata kai idanunshi sunyi jajir, idanunta yaga sunsoma jujjuyawa wani irin nishi tayi tafara wani irin nannade kanta tana bankarewa sabida yanda cikin nata yafara wani iri kaman ana kakkatse duk wani hanji naciki, ihu Khaleel yay yace “Doctor”.
[6/23, 11:35 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button