Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 34

Sponsored Links

Aika Mum yayi takirasu zama sukayi su biyun afalon Abba yay gyaran murya yace “burin kowani uban ne yaga yarshi ta sami miji dan mutunci yaro mai hankali da addini da hikima, to Alhamdulillahi Ummi nariga namiki miji wanda kika sanshi sosai Muhammad Khaleel” ba karamin bugawa kirjinta yayi ba har saida ta dago kai ta kalleshi ya cigaba yace “mun riga mun gama magana da iyayen shi, an saka rana sati hudu, bayan biki zankudan yi kwana biyu anan yola sanan ku wuce Abuja sabida ya koma aiki, idan kinada any abu dakike so ki fadama Mummy ku sai asiyo miki” Ya gyara zama ya kalli Farida akunyace ta labe abayan Islam tace “Abba nima kwanan nan zan fito da nawa” murmushi kawai Abba yayi yace “Faridan Abba kenan to Masha Allah, Allah nuna mana ku tashi kutafi” atare suka fito daga dakin Farida ta kalleta tadan zaro ido tace “ke waye kuma Muhammad Khaleel nazaci Fahad ne ya turo?” kasa magana tayi sabida wasu hawayen bakin ciki da suka zubomata da gudu ta bude kofar dakinsu ta shiga ta zauna akan gado, Farida ta zauna akusa da ita tace “waye Muhammad Khaleel din?” kwallan daya dan zubomata ta share tace “wani ne fa datunda muka hadu duk inda naje saiya bini kaman maye, yace yana sona ni banason shifa Fahad dina nakeso” Farida tace “to mesa baki fadama Abba baki sonshi ba?” turo baki tayi ahankali tace “kasawa nayi wlh kaman antushe min baki” murmushi kawai Farida tayi tace “lemme not waste my saliver akanki dan ga sonshi nan kuri aidonki, nidai duk randa yazo I will love to meet him o” tashi tayi fuuuu ta dau wayarta ta shiga bayi ta rufe tai dailing number shi harya gama ringing bai dagaba saida ya katse ya kirata back cikeda tsiwa tace “nace ina sonka ne dazaka tura gidanmu?” murmushi yayi sanan yay magana ahankali yace “ai basai kince kina sonaba wife, gangar jikin ki, rohin ki, murmushin ki, kwayar idanunki sun riga suncemin suna sona so mezan jira? Yau dayake fada kikeji shine harda kirana bayan idan nakira ki u don’t pick” rasa abinyi tayi hakan yasa ta fashe mai da kuka dan dariya yayi kafin ya sassauta murya yace “please don’t cry, how about gobe nazo na lallasheki da kaina” tsayar da kukan tayi tace “Allah inkazo gidanmu saina cirema kafafu” wanan Karan dariya yayi sosai, shiru tadanyi tana sauraron yanda sautin dariyar nashi ke fita kaman Karya dena, dan shiru yayi kaman yasan meke zuciyar ta yace “you like how I laugh, na cigaba?” da sauri ta kashe wayar tana dan murmushi bude kofar tayi tafito daga bayin Farida ta harareta tace “kai Islam keko, kina so kina iskanci hegiya pretender” dauke kai Islam tayi kaman bataji taba tazo zata zauna akan gado filo Farida ta naka mata hakan yasa ta fada gado tana dariya ita kanta mamakin kanta take to Mesa tama kasa fushi.
Wuraren biyar na yamma yazo yana sanye da shadda mai ruwan toka sai kamshi yake, Anty Hindu tasa aka shigo dashi saida suka gaisa sanan tabar falon sama taje tasami Farida da Islam zaune tace “ke tashi ki xhanza kayan jikin nan naki Khaleel yazo” ganin Anty Hindu ta tsaya masu akai yasa ta tashi shiryawa tayi cikin simple brown material da akai mata doguwar riga ta daura milk color hijab din gida daya tsaya mata acinya tadan shafa hoda tasa lipgloss tadan fesa turaren Posess sanan ta kalli Farida tace “zomuje ki ganshi fa” girgiza kai tayi tace “ke haka akeyi jeku fara gaisawa tukun anjima zanzo” fita Islam tai daga dakin. Shigowa falon tayi batare data kalleshi ba ta wuce kujeran 2 sitter dake kusa da kujeran daya zauna ta zauna tana gyaggyara hijabin jikinta. Ahankali yataso yazo ya zauna akan kujeran datake ya fuskanceta yana kallon fuskar ta batare dayace komiba, dan dago kai tayi ta kallai, hararan shi tayi sanan ta turo baki tace “katashi kabarmana gidan mu” make mata kafada yayi hakan yasa ta dauke kai da sauri dan wani iri taji, ahankali kaman mai rada yace “I miss you ummina” dan dago kai tayi suka hada ido hakan yasa tasake dauke kai, tagumi yay ya cigaba da kallon ta kaman yau yafara ganin ta, batare data juyoba tace “stop looking at me” girgiza kai yayi yace “I can’t” juyowa tayi tace “kabar mana gidanmu kuma” girgiza kai yasake yi yace “I can’t” juyowa tayi cike da masifa tace “ninace ina sonka ne dazaka tura aje wurin Abban mu” Ahankali yace “but I love u” yay maganar murmushi kwance kan fuskarshi, ahankali yace “Are you angry with me?” hararan shi tayi ganin yamaida ita wawiya, hannu yasa a aljihun rigar shi yaciro chocolate bude chocolate din yayi yadan matso kusa da ita ya Kalli fuskar ta yace “kinsan ance chocolate na mantar da mutum fushin dayake yi ko” yay maganar yana kallon kwayar idonta…
Ahankali Farida ke sakkowa daga stairs sanye da hijab harta shigo falon, numfashin ta taji yana neman barin kirjinta ganin Superman dinta da Islam suna wani irin kallon juna…
Cikinsu babu wanda ya lura da Farida, kallonshi Islam tayi sanan ta kalli chocolate din daya bude yana miko mata make kafada tayi tace “I don’t want” dan matsowa yay kadan ya sassauta murya kaman me lallaba yaro yace “plzzzzzzz” yanda yaja plz din haka tajishi har cikin ranta ahankali ta mika hannu zata karba girgiza kai yayi batare dayay magana ba ya nuna mata bakinta da yatsa yace “haaa” wai mutumin nan magic yake minne dudda yanda taso tahana kanta kasawa tayi ahankali ta bude bakinta kadan, murmushi yayi yakai chocolate din bakinta yana kallon fuskarta Islam! Farida takira sunanta dawani irin murya da tunda suke bata tabajinta dashi ba, adan rude ta juyo dan yanda Farida takira sunanta saida ta firgita shima ita ya kalla, gyara zama yay sanan yace “Hi how u?” dan wlh yamanta sunan ta, da kyar ta iya kakalo murmushi tace “fine” murmushi yamata sanan yace “don’t tell me u two are sisters” Ya kalli Islam sanan ya kalleta ya nuna Islam yace “itace dama Islam din dakike ta bani labari” gyada mai kai tayi tana kokarin danne hawayen dake barazanar zubomata, yay murmushi yana wani irin kallon Islam kaman ya cinye ta yace “I see” dan murmushi tamai sanan tace “bye” tajuya tafara tafara hawa stairs, tashi Islam tayi zata bita dawani irin murya yace “ina zaki My Ummi, we are not done yet baki karbi Chocolate dinba” wani irin hawaye ne mai zafi ya zuboma Farida da sauri sauri tai tawuce dakinsu jin yanda Superman kema Islam muryar dabata sanshi da ita ba, dama yanama magana haka?.
Zama Islam tai ahankali ta kallai dauke kai tayi sanan tace “dama ka San Farida ne?” gyada kai yayi yace “yea I helped her once haka dawani thief ya kwace mata jaka and daga nan I think mun sake haduwa twice ko I think, ashema sisters neku, Kinga ko Allah ma wants me to marry u tunda har yasa nasan yar uwarki” tashi tayi tsaye tace “bye” da sauri shima ya tashi yace “but I don’t wanna go now” hawaye ne yacika idonta tadan kalleshi sanan ta dauke kai, ahankali yace “okay I will go, Plz don’t cry” dan matsowa yayi ya tsaya a gabanta ya mika mata chocolate din yay murmushi yace “u have to eat it before i go” bakinta yakai hakan yasa ta kawad dakai, tsayawa yay yana nazarin fuskarta kaman something is wrong ahankali yace “Are you okay?” murmushi tayi tadan bude baki hakan yasa yay wani murmushi daya bayyana fararen teeth dinshi yasaka mata chocolate din abaki ta gutsiri kadan sanan ya cire yana murmushi, dadan sauri tabar wajen murmushi yayi saida yaga tai sama sanan yafita daga dakin tareda kai sauran chocolate din bakinshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button