Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 48

Sponsored Links

Bari muleka Faridan mu.
Idan kunga Farida saikun tausayamata ta rame sosai, da kyar Mum kesata taci abinci, bata da aiki sai daukar waya taita dailing number superman da baya shiga ko kadan, Abba kullum wa’azi yake mata da fada, Mum dai duniya yay mata zafi hakan yasa wani zubin idan Farida tafara kuka itama jonata takeyi suyi tayi tare, ba irin Allah ya isan da basuma Islam ba sabida bakin ciki.

Hakanan yau Wednesday taji tanajin fita kotadan ga rana, doguwar riga baka tasaka ta yana gyalen ko hoda bata shafaba tafito daga gidan danko Mum bata fadimawa ba, keke napep ta tare tace “yakaita Infinity gym” ta shiga ciki yaja har wajen yana ijiyeta ta ciro kudi ta bashi, sucurity ya bude mata ta shiga ciki, wani kukane yazo mata ganin treadmill din data taba ganin superman dinta akai, da kyar ta hadiye hawayen ta karasa wajen eatry din, order strawberry smoothie tayi ana kawomata ta karba tareda bada kudin tanata kallon smoothie din tana tuna ranan da superman dinta yasaimata yabata ahankali tace “menama Islam haka datamin irin wanan abu? Mesa nakasa cire sonshi araina why, please God inaso na manta dashi please” share da kwallan daya zubomata tayi tadau smoothie zatakai baki da sauri ta ijiye ta kife kanta akan table din tana wani irin kuka mai cinrai, “hey is everything okay” dago kai tayi suka hada ido da Yusuf dake sanye cikin sport wears hanunshi rike da cold bottle water, share ido tayi ta juya da sauri ta duba ko suna tareda superman dinta ne taga shikadai ne, juyoda kai tayi ta harari Yusuf tace “wat are you doing here?” kujera Yusuf yaja ya zauna yana kallon fuskarta yace “nothing banmasan kebace” tashi tsaye tayi tajuya zata bar wajen dan wani irin haushin Yusuf takeji da sauri yabita juyowa tai cike da masifa tace “kadena bina harda kai aka hadu aka yaudaran, Islam Islam” takira sunanta saikuma tajuya tafita daga wajen da sauri jin wani kukan ke zuwan mata suna fita Yusuf yasha gabanta yace “hear me out, kidena blaming sister ki wlh batada laifi, Allah kuwa trust me” bakin gyalen ta tasa akan fuskar ta tafashe dawani kukan, jitake kaman zuciyata zai fashe, ba karamin tausayin ta Yusuf yaji tabashi ba ya tsaya kawai yana kallonta da kyar tai shiru ta kalli Yusuf da rinannu idonta tace “koma menene at least for d sake of ni yar uwartace, tasan yanda nake sonshi saitaki auren shiko” ta dago kai ta kalli Yusuf tace “kataba son wata?” girgiza mata kai yayi alamun a’a hakan yasa tadanyi murmushi tace “bazaka taba iya gane wat am going through ba, Islam” tasake kiran sunan Islam tana wani irin dafa kirjinta da sauri tajuya tabar wajen akan bakin titi ta tare napep ta shiga tana goggoge ido da bakin gyale. Sosai Yusuf yaji jikinshi yay sanyi wanan wani irin sone, yanda take haukan son Khaleel dinan shikuma haka yake haukan son Islam, oh Allah kayaye ma wanan baiwar naka wanan son maso wanin, ahankali ya juya ya shiga ciki.
Islam dai sai gyaran jiki ake mata in and out, Goggo yanzu kulle kofa take idan baka kwankwasa ka fadi sunanka ba bazata taba budewa ba duk dan kar Khaleel ya ganta take wanan.

Dayake yau asabar yasa anata shirye shirye kowa na hada kayanshi dan gobe zasu tafi, Wuraren 11 Khaleel yafito daga part dinsu yana sanye da jeans black da blue t-shirt mai gajeren hannu, fuskar nan tashi adaure har wata yar raman dole yayi sabida rashin ganin Islam, dakin Ammi yayi yasameta zaune kusa da Dad datake hadama tea gaishe su yayi suka amsa, Dady ne yace “mekake so son” kallon fuskar Ammi yayi hakan yasa ta dauke kai ahankali yace “dama Dady inaso Ammi tasa Islam muje ta tayani hada kayan mune nachan gidan tunda gobe zamu tafi” Dady ya Kalli Ammi yace “kiramai matarshi tazo sutafi ta tayashi mana” Mum zatai magana Daddy yace “ki kirata nace banson jin komi” murmushi Khaleel yayi hakan yasa Ammi ta watsamai harara sanan ta wuce tafita tai dakin Goggo saida tai magana sanan Goggo tabude ta shigo Islam dake sanye da riga da sket nawani soft material mint green dake zaune rike da wayar Ihsan tana karanta wani novel tace “dauko Hijab dinki kizo Islam” ajiye wayar tayi tadau hijab Goggo tace “ina zata?” “Kiranta Alaji yake” black hijab tadaura akan kayan tabi bayan Ammi har falo, tunda ta shigo yake kallonta ganin yanda fatarta har wani kyalli take takara haske, dudda tasaka hijabi bai hanashi ganin yanda tawani kara cikowa ba tai fresh like honey wine, gaida Abba tayi cikeda girmamawa tana kallon Khaleel ta gefen ido dudda tadanyi kewanshi amma taki Koda kallonshi balle ta gaidashi, Abba ya nuna mata Khaleel yace “kuje kuhado kayanku na dayan gidan dan gobe da safe zamu tafi” ahankali tace “to daddy” fita Khaleel yayi batare daya kalleta ba hakan yasa tabi bayanshi kirjinta nadan bugawa, mota ya shiga hakan yasa ta bude gaban motar ta shiga ta zauna tarufe, kunna motar yayi suka fita daga gidan su aranta tace “nan da nanne bazai iya zuwa da kafaba, lazy fellow” horn yay mai gadinsu yabude yay parking yafito ya shiga ciki saida tai kusan 2min a motan sanan tafito jiki duk asake, ahankali ta bude kofar ta shiga falon, da kyar ta iya daga kafa takai tsakiyar falon ta tsaya ganin bata ganshi ba, tabaya taji anrungumeta hakan yasa saida tai yar kara sabida tsoro, tsamtsam ya rungumeta yakawo kanshi ta wurin kunnenta yace “I miss you” juyo da ita yay yakai hanunshi yay cupping fuskarta ya kalli cikin idonta yace “did you miss me” dan murmushi tai sabida yanda yay maganan ta dauke kai, zama yay ya daurata akan cinya yana kallon fuskarta yace “waye lazy fellow?” adan rude ta kallai ta dafe kirji, ganin yanda yake kallonta yasa ta tashi da guda tana dariya tai hanyar bedroom tace “bafa dakai nakeba” harta zauna akan gado taji yabude dakin da gudu ta tashi zata shiga bayi ya rikota tabaya tareda cire hijabin jikinta ya matseta yana kallon idonta yace “Wana kama?”.
[6/22, 7:53 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button