Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 54

Sponsored Links

54…

Ahankali yake bude idanunshi dasuka mai mugun nauyi ga kanshi dake mugun sarawa, da kyar ya iya bude idanun duka ya sauke su akan wani Dr dayaga ya rikemai hannu yana shafa tafin hanunshi yana bubbugawa, sama sama yakejin doctor nacemai “can u here me, I need you to tell me your name” kadan kadan idanunshi ke kukkulewa ganin gabaki dayan dakin na juyamai in a circle, kara bubbuga tafin hanun nashi Dr yayi yana rubbing tsakiyar yana kallon fuskar shi da kyar yasake bude idon yadan kallai kadan yace “can you hear me? Me sunanka?” da kyar ya iya bude bakinshi sabida wani irin nauyi dayamai sosai yace “Islaaam, I want to see her” yana maganan yana kukkule ido har suka rufu tass, murmushi Dr yayi ya juyo ya kalli su Ammi harda Goggo dasuka tsattsaya kowannen su hankali tashe yay murmushi yace “Alhamdulillah ya farka, anytime from now zai farfado full.. ” “Islam” da Khaleel yakira yasa dukansu harda Dr sukai kanshi wanan karan yabude idon duka saidai kanshi dayaji yana mugun ciwo, Ammi ne tai maza ta rike hanunshi tana share hawayen dataji yazo mata, ahankali ya kalleta yace “Ammi ina Islam?” shafa goshin shi Ammi tayi tana girgiza mai kai tace “kafara hutawa tukunna Son, kasan yau kwanan ka Uku unconscious ko” ta kalli Dr dake checking pulse dinshi tace “Dr yayake yanzu?” murmushi Dr yay yace “Alhamdulillah he’s pulse is stable, blood pressure din kuma yadawo normal, ku taimaka mai yay wanka da lukewarm water it will really help him” kokarin tashi yake amma yakasa sabida yanda kanshi yaji kaman zai fadi ahankali ya kalli Abban shi da Umma da Yusuf da Goggo dake wajen dakuma Anty Hindu da idanunta sukai jajir sabida tausayi hanunshi ya daga da kyar yay pointing Anty Hindu ahankali yace “ina Islam dina?” bude kofar dakin akayi hakan yasa dukansu sukabi kofar da aka bude da kallo wheelchair din asibiti yafara gani, dan dago kanshi kadan yayi da taimakon Mum yana kara kallon kofar, Abban Islam yagani ya gunguro Islam dake zaune akan wheelchair ta duke kai sosai dan bata iya dagowa complete sabida cikinta, lips dinta sun kumbura sosai sunyi jajajir bakinta nata dilallar da miyau, kasa dauke kanshi yay daga kanta har Abba yakawota jikin gadon dayake ya tsaya, kokarin tashi yake Yusuf yayo kanshi zai taimakamai ya tashi dagamai hannu, alamun yabari, rike kanshi yay ya sakko daga kan gadon da kyar kaman zai fadi, da kyar ya iya ya tsugunna agabanta ya mika hannayen shi ya daura akan fuskarta ya dago kanta yana wani irin kallonta idanunta alumshe, ahankali dawata irin murya mai taba zuciya yace “Islam” shiru tayi batare data bude idonta ba batare datace mai komiba, ahankali Abba yace “Muhammad Khaleel Ummi tasamu nakasu guda biyu, na farko dai tana fama da wanan uncontrollable zuban miyau wato drooling, nabiyu kuma tunda ta farfado ko uppan batace ba, Dr yace yana tsammani Sniper yamata dameji a wuya ne amma basuyi concluding ba, sanan bata iya mikewa tsaye sabida intestine dinta wai basu warkeba tukun, and kaga bakinta yanda yakoma” Abba yadanyi shiru sanan ahankali yace “banason na daurama dawainiya aka, after all yar uwarta ce ta maida ita haka, to Khaleel idan baka sonta, idan bazaka iya zama da itaba wlh bazan taba ganin munin kaba, bazan ji haushi ba, zaka iya sauwake mata” tunda Abba yake maganan yakasa dauke ido daga kanshi gawasu jijiyo yi dasuka fiffito a forehead dinshi, da kyar ya iya janye idanunshi daga kan Abba sanan ya kalli Islam dahar lokacin taki bude idonta, ahankali yasake matasawa kusa da ita yadade yana kallon fuskarta da bakinta dake dulalar da miyau ya daura kanshi akan cinyar ta ya fashe da kuka sosai, Yusuf ne yafara fita daga dakin jin idanunshi sun kawo ruwa, hakama sauran iyayen da Dr suka fita daga dakin yarage daga shi sai ita, yafi 5min yana kuka sanan ya dago kanshi ya share idanunshi da kyar dan muryanshi ma ta dishe yace “Wife” ahankali ta bude ido ta sauke su akan nashi, ganin yanda yake kallonta yasa ta daga hanunta ta rufe fuskar ta tana wani irin kuka mara sauti dan kunyan fuskarta take sosai, hannu yasa yakamo hanun ya saukar dasu yana girgiza mata kai, hanunta ya daura akan kirjinshi daidai wajen zuciyar shi ya goge kwallar data zubomai yace “kinga wanan zuciyar, only beat for u” ahankali yace “koma yakike, koma yakika koma, koma menene you will always be my Islam, my one and only wife, wacce nakeso wholeheartedly” sosai yaga take kuka ahankali ya kai hannu ya share mata hawayen dake zubowa yace “am sorry, am sorry Islam is all my fault” hannu tasa ta kara kare lebenta tana kawad dakai dan ba karamin kunya takeji ba idan yana kallonta, wani hawayen yasake gogewa ya juyo da fuskar nata tareda saukar da hanun nata yana girgiza mata kai ganin yanda take kuka mai cin rai, ahankali yakai bakinshi ya daura akan katon lips dinta dake fitar da miyau.

Guys yau weekend am a little busy ne so manage this I love you all.
[6/25, 2:17 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Related Articles

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button