Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 56

Sponsored Links

Washegari wuraren 10 suka shigo airport din, bangaren private jet terminals suka tafi, sukai parking mota suka fiffito, yana sanye cikin kananan kaya Jean da t-shirt fara, yafito da Islam dake wheelchair Anty Hindu ta shiryata cikin light kayan kanti pink skirt da riga, an samata hula, tsugunnawa yay agaban ta yamata peck a kumatu tareda share mata wuya da soft towel sabida yanda miyau yabata mata jiki yay murmushi yace “you will be fine kinji wife” tashi tsaye yay ganin su Abba da kowa sun fiffito, Yusuf kuma ya gunguro akwatinan guda biyu, tafiya duk suka fara shikuma yana turata har suka kai gaban jirgin da sauri nurses din cikin jirgin suka sauko daukar ta sukayi awani gado suka shiga da ita ciki Ihsan ta rungume Ammi tana daga musu hannu ta shiga, murmushi Abban Islam yay yace “Allah maka Albarka Muhammad, kaje Allah ya kiyaye hanya Allah kaiku lpy” ahankali yace “Ameen” Ya rungume Ammin shi sosai fuskar shi ta shafa sanan tace “take care of my two daughters kanajina ko” gyada mata kai yayi sanan ya daddaga musu hannu yajuya ya shiga cikin jirgin sukuma su Abba sukabar filin jirgin, ahankali jirgin ke tafiya harya daga.
Kan kujeran dake kusa da ita ya zauna hanunta yarike yakai kirjinshi ya rungume yana kallon fuskarta, dayar hanun kuma yana shahshafa goshin ta dashi, kadan kadan take bude ido tana kallonshi har bacci yay gaba da ita.

Karfe 6 na yamma suka sauka jirginsu ya sauka a UK saukowa sukayi aka shigar dasu motar ambulance din datazo daukan su aka tafi dasu asibitin, har lokacin hanunta na sakale cikin nashi yana kallon fuskarta dan bacci takeyi har yanzu, suna kaiwa hospital din doctors suka karbeta akai ciki da ita sanan suka zauna, wayarshi ya ciro ya chanza line zuwa old Sim dinshi na UK yana chanza wa ya kunna wayar yay dailing wani number bayan sunyi magana ya kashe ko 10min ba’ayi ba wani bature dan yaro dabazai wuce 20 ba yazo jakunkunan su ya amsa sanan yacemai ta harshe turenci yakaimai gida sanan ya bashi kudi yaron yatafi, Ihsan ta kallai tace “Ya waye shi” murmushi yamata yace “wani yarone tun Ina school na sanshi, errand boy ne, yanada kirki” tashi yayi yace “lemme get something for you” restaurant yaje coffee kadai ya siyoma kanshi ita kuma yasaimata snacks sanan yadawo yabata ya zauna, Dr Omprakash ne yafito yakirashi hakan yasa ya bishi office, murmushi Om yamai ya mikamai hannu suka kashe sanan ya nunamai kujera yace “ka zauna” zama yayi sanan Om yace “I have good news” dan murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya ya gyara zama Om yace “zata warke, yanzu dai for now step by step zamu dinga daukan treatment dinta, target dinmu na farko bakinne which for sure zata warke, we will be able to stop d drooling and kumburin komi zai dawo daidai sabida tasamu ta dinga shan maganin dazai warkar da intestine nata tasamu tana mikewa, den daganan ne zamu fara duba abinda ke hanata magana inma any damage ne za’ayi surgery komi ya dawo daidai in sha Allah” ajiyar zuciya ya sauke tareda mikamai hannu yace “thank you so much Dr” murmushi yayi yace “zaka iya zuwa ka ganta kasan 7 ake koran visitors and kasan hospital dinan ba’a bari kowa ya kwana da patient, so jeka ganta kafin 7 tayi” murmushi yay yatashi yafita daga dakin. Ahankali ya bude dakin datake ciki, wata nurse yagani tana saka mata safa akafa an chanza mata kaya zuwa kayan asibitin gaishe dashi nurse din tayi sanan tafita, karasowa jikin gadon yayi yaja kujera ya zauna ya daura kanshi akan cinyarta yana kallon fuskar ta.
[6/26, 4:58 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button