Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 45

Sponsored Links

Majeederh bata san lokacin data hantsilo daga kan gadon ba, tana ture kan Khalil, jikinta na rawa sai a lokacin ne take jin duk wata soyayyar shi matsayin ɗan uwa yana ratsa jinin jiki da tsokarta. Ta kasa magana sai kallon Maman Alpha take da wani firgitaccen tashin hankali, wanda ya kasa ɓoyuwa daga zuciyarta, gabaɗaya zuciyar buɗewa take a hankali ta shiga aikinta a gaggauce. Ƙirjinta tana jin kamar an ɗora mata dutsen dala da Gwauron Dutse saboda yadda take fusgar numfashi da ƙyar, ƙwaƙwalwarta na buɗe a gaggauce tana amsar saƙon, cikin yanayi na firgici da hali na gigita da manta kai. Khalil ya zura farar tattausar Muslimi thobe jallabiya ɗinsa, ta bi jikinsa ta kwanta kasancewar jikinsa ya buɗe ya ƙara cikar da zati da haibar shi ya ƙara bayyana a fili yadda maɗaukakan jama’a zasu gani su fasalta yanda kamalar ta kwanta a fuskarsa. Gashin kansa duk a barbaje baya son ya yi cutting ɗinsa gashi bai je saloon ba, ya ɗan juya sai yaga wani ƙaramin white ribbon siriri ya ɗauka ya tattare gashin ya ɗaure ya sauka a wuyansa, duk ya cuccure kamar Indomie, ya ɗauki p.cap ya ɗora a saman kan shi, babu abinda kake iya gani sai jajayen laɓɓansa masu kauri da taushi, sun ɗan jiƙe da damshin yawun Jee, sai fararen Idanunsa da suke jiƙaƙƙu kamar wanda hawaye ya kwanta a cikinsu, sun yi wani laushi a lumshe irin yanayinnan na kasala, asalin blue eyes ɗinsa da ba kowa ke lura dasu ba ya fiddo saboda yadda ya ɗan buɗe idanun yana gyara zaman agogon Rolex akan wrist ɗin shi, yanayin suffar Khalil ta cikakkun baƙaƙen ƴan America ɗin nan ne, a fusge kuma laushin fatarsa da ɗan duhunta kamar ta ƴan Etopia ko Mali, Khalil
baƙi ne sosai irin dark-skinned ɗin nan wacce har Shinning take, amma kana kallonsa kasan cewa hutu da jin daɗi sun zauna masa, saboda yadda dark-skinn ɗinsa tai fresh gwanin sha’awa _His elegant black skin_ sai sheƙi take cikin light blue ɗin hasken da yake ɗakin six-packs ɗinsa a bayyane ya bubbuɗe ta cikin jallabiya ɗin, ga Round face wacce saje da gemu suka yi covering ɗinsa,sexy eyes masu fitinannan ɗaukan hankali, ko namiji shakkar idanun yake balle mace, ba ruwansa da kowa amma wanda ya shiga inuwar shi a nan yake sanin asalin haukan Khalil, yana da rauni akan mata,baya son cin amana, ƙarya, da munafurci.

“Mu..mu..mutuwa?” Ya furta a rarrabe kamar bagware, yana fiddo idanunsa waje cike da razani, yama rasa cikakke kuma ainahin kalaman da zai amfani dasu wajen yiwa Maman Alpha magana ɗin. Majeederh ta kama hannun Maman Alpha ta ce “Ya..yaya..? Daman bai dawo ba gida ba? Karki ce mini ya mutu” Maman Alpha ta kama hannun Majeederh ta riƙe cikin nata idanunta na zubar da wasu azababbun hawaye wanda yake da cin zuciya ta ce “Ko wanne bawa mai rai a nan duniya, al’amarinsa na wanzuwa ne bisa tsarin Ubangiji, Alpha ya rayu a cikin uwa mai kyakkyawar zuciya na tsayin wata tara da kwanaki, tun kafin zuwan shi duniya Ubangiji maɗaukakin sarki ya zartar da ikon shi akan yadda rayuwarsa zata kasance a duniya” Ta sauke ajiyar zuciya tana ƙasa da kanta, Khalil duk baya fahimtar wannan farsafar zancan, mai wahalar fahimta azancin maganar na kalaman da akai amfani dasu sun dunƙule a kansa ne. A hankali Maman Alpha ta sake cewa.

“To me zamu ce da Ubangiji banda godiya ga ni’imar shi? Daman wanda bai godewa ni’imar Allah ba to zai godewa azabar shi, Alpha ya jawa kansa, tun a haihuwar Bilal yaci ace jirkitacciyyar ƙwaƙwalwar shi mai wassafa masa muggan abubuwa wanda zasu gurɓata goben shi, fahimtar shi Zuleehart kyauta daga Allah ce, kuma ita ce ni’ima a gare shi, ni, ke, Khalil, Alpha kowa na duniya yana rayuwa a cikinta bisa yardar Allah, kowa na rayuwa da kalar tashi ƙaddarar, wacce Ubangiji ya samar da ita tun kafin zuwanmu duniya, hakan rubutacce ne, kuma halataccen rubutu ne akan allon da ba zaiyi ƙarya ba, hannun da ba zai rubutu ba daidai ba, zuciyar da bazata cutar ba, kyakkyawan rubutu ne kamar rubutun tawada a jikin dutse wanda baya goguwa balle ya zama shuɗaɗɗe, barin Alpha garin nan, aurenki da Khalil, dawowar Alpha, mutuwar khalil, aurenki da Alpha, dawowar Khalil a matsayin rayayye gabaɗaya yana zane jikin Lauhul Mahfouz, wata ƙaddarar mune muke janta, wasu siya musu akayi, i believed cewa General ba alheri bane ga duniyarki shi yasa abinda ya faru, bai wakana ba sai ana ranar aurenku” A kiɗime Majeederh na damƙe hannun Maman Alpha muryarta na sarƙewa da ƙyar da iya cewa.
“Fahimtar dani meke faruwa? Ina jin kamar na yi ba daidai ba!” Maman Alpha ta ce “Majeederh alfarma nake nema, amma kafin nan kizo muje hospital ɗin” Majeederh ta juya ta kalli Khalil bai kalleta ba, ya ɗauki key d’in motarsa wanda alama ne ya kewa majeederh ta shirya, doguwar riga ta saka ta ɗauki mayafi tayi rolling, wani fitinannen kallo Khalil ya yi mata ba tare da ya ce komai ba yana ɗaukan Alhassan, wajan wardrobe ta nufa ta ɗauki hijab har ƙasa ta saka, ta nufi wajan Al’hussain a ɗan hankali ya ce “Madam, ur niƙab” Tayi jim domin bai taɓa nuna sha’awa akan niƙab ba, ta ɗan hargitsa kayanta ta ɗauka ta saka, ya dinga kallonta from head to toe kafin ya nufi waje ta ɗauki Al’hussain dake kusan lokaci ɗaya yaran suke bacci, suka jero gwanin sha’awa suka samu Maman Alpha a motarta, gabaɗaya suka kwantar da yaran a baya da wani irin gudu Khalil ke jan motar har tsoro ta ji, ta manta komai nasa a gaggauce yake yinsa, kuma ya saba da tseren mota tun sanda suke kasawa da ƴan sanda. Lokaci kaɗan suka ƙarasa shiga cikin hospital ɗin kai tsaye kuma Emergency, a reception suka samu Yaya Bilkisu dasu Widad da Du’a su nata kuka, jikin Majeederh ya yi sanyi zuciyarta ta karaya, Uncle Bello ya kalli matarsa ya ce “And who gave you the permission? Me kike ƙoƙarin yi?”
“Ni uwa ce, zuciyata ba zata ɗauki halin da ɗana yake ciki ba, zan nema masa abinda kai ka kasa nema masa bayan kana da ikon yin haka” Uncle Bello ya ce “Idan taƙamar shi ɗan uwanta ne kin manta ya suke da mijin nata? Ko kema son zuciyarki zaki gwada ne?” Maman Alpha ta cillawa Uncle Bello dairy ta ce “Ka duba, General shi ne ya sakawa Majeederh suna tun ranar da aka haifeta, babarta Fulani tayi Supporting nasa, ya nemi ta bashi Majeederh zai kula da ita, a nan Fulani ke cewa ba kulawar Majeederh ta bashi ba, har duniya ta naɗe ta mallaka masa Majeederh, ta bashi ita matsayin matar aure ya yi mata wannan alfamar, ya amshi batunta wanda ita ta kasa gane ribar tasa ce, sai dai ashe kashin dankali ne, General yana jin zai sadaukar da komai wajen ganin ya auri Majeederh ya cika mafarkin Fulani, da al’ƙawari na muradin zuciyarsa” Ta goge hawayen fuskarta ta ce “Kun kasa fahimta, nima a bincike na gano hakan gabaɗaya bedroom ɗin shi pictures d’inta ne tana ƙarama har zuwa girma, ba wanda ya taɓa faɗawa hakan wanda dalilin hakan akai masa asiri, after all these things he did, didn’t he deserve to be Majeederh’s husband?”

“Idan mutuwa gaskiya ce, hisabi wajibi ne, haka nan Soyayya ma gaskiya ce Ubangiji ke samar da ita a zuƙanta bayinsa, ba tare da sani ko tambayar su ba” Khalil dai kallonta kawai yake a hankali ya ɗauki wayarsa dake ringing shiru ya yi a hankali yana ƙasa da murya ya ce “Ko Latifa ne, arrest her directly ku kai ta prison” Yana faɗin hakan ya kashe wayar ganin Maman Alpha ta ja hannun Majeederh zuwa room ɗin da Alpha ke ciki ya miƙe tsaye walking slowly ya bi bayansu, rashin sanin abinda zai iya faruwa ya saka Uncle Isma’il da Uncle Bello da Yaya Bilkisu suka rufa musu baya. Cak Majeederh ta tsaya ganin gabaɗaya jikin General maƙale da na’ura musamman ƙirjinsa, cikin bakinsa ga oxygen ta hancinsa, sai wani green ɗin yadi da aka ja masa zuwa wajan cibiyar shi babu inda yake motsi a jikinsa kamar matacce, Maman Alpha ta juya ta kalli Majeederh sai kuma ta zube akan ƙafafuwanta tana riƙe ƙafar Majeederh ta ce “Alfarma nake nema a wajanki Majeederh, ba don na taɓa taimakonku a rayuwa ba, ba dan na wahalta miki ba, ba don na kasance cikin zuciyarku ba, yadda Ubangiji ya bayyana miki gaskiya akan Latifa da Hajiya Luba, yadda Ubangiji ya dawo da hankalin mahaifinki, yadda Ubangiji ya sadaki da dangin mahaifiyarki, kiji tausayina,kiji tausayin halin da ɗan uwanki yake ciki, ki duba girman Allah, kaɗaitar shi da buyawarsa ki sadaukar da soyayyar Ibrahim wa Alpha…” A gigice Khalil ya kalli Maman Alpha sai kuma ya cire p.cap ɗin kansa, tare da zare ribbon ɗin ya girgiza kansa gabaɗaya sumar ta wargatse ta rufe fuskarsa, a hankali ya yi kneeling down a gaban Maman Alpha shi ma ya dafa ƙafarta ya ce “I love you Maa, and i also respect you, ke uwa ce kina fahimta, ni i don’t know how to explain yadda Ƴar madara take a raina, ki yi tunani idan na rasata ya Ummie na zata shiga? I love my wife ku barni da ita nayi rayuwar farin ciki don Allah…,” Kafin ya sauke Maman Alpha ta damƙe hannun Khalil tana kuka kamar ranta zai fita ta ce “Don Allah don Annabi Ibrahim, ba danni ba saboda girman da Soyayyar da kake ma Ummie ka barwa ɗana Majeederh bari na har abada….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button