Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 75

Sponsored Links

Tadade tsugunne a wurin tana raira kuka kafin ta mike tsaye da kyar ta share fuskarta da kyau tabar wajen tana tafiya kaman zata fadi sabida rashin karfi, ahankali ta tura kofar dakin da sallama ta shiga Mummy ce kadai zaune tana waya kaman ma da Abbane sai kuma Farida dake rungume da gwangwanin pringles din dayabata tana bacci, karasa shigowa dakin tayi ta maida kofar ta rufe, katse wayar Mumy tayi ta kalleta tace “me kuma kikeyi anan bakibi mijin naki bane?” girgiza kai tayi ta karaso gaban Mumy ta tsugunna ta daura hanunta akan cinyarta ahankali tace “Mummy dan Allah kidena fushi dani kiyakuri kinji” wani irin murmushi mai ciwo Mum tayi ta ture hanunta daga jikinta tace “Islam kenan inda kin kirani da sunana ai dayama fi dan kin dade da nunamin cewa nibani na haifeki ba, hakurin me kika bani iye? Mekika mini?” share kwallan daya zubomata tayi da bayan hanun muryar ta har rawa take tace “Mumy wlh bani bane kawai naga Abba yakaini gidanshi ne, ni bansan ya akayi ba dan Allah mumy am sorry” “are you?” Mum ta tambaye ta tana mata wani irin kallo, gyada mata kai tayi, dan shiru Mum tayi sanan tace “ai ga Faridan nan kinsa mata ciwon zuciya inta mutu ai duk a dadin ki saikiyita rayuwan ki da Khaleel tunda miji yafi miki yar uwa, Islam ni kikama abunan, ni Islam” ta nuna kanta da yatsa, “ni dana raineki uwarki nafama da sikila, oh duniya kenan, yata ke wahala haka sabida ke Islam” girgiza kai tayi tafashe da kuka sosai, tsawa mum ta daka mata tace “wuce, fita daga dakin nan, karki kara shigowa, nidai ba Mummy ki bace daga yanzu, ki nisanta kanki daga yata tariga ta hakura da mijin ki, kuyita shagalin ku, itama Allah zai bata wanda yafishi, yinan” ta nuna mata kofa, kasa fita tayi saima wani sabon kukan datake tana shashare fuska da hijabi, hakan yasa mum ta nunata da yatsa tace “wlh idan kika tadar min ya daga bacci bazan barki ba zan mugun sabamiki, ki wuce ki fita kafin na kaimiki hannu munafuka, nafada miki nidai ban tsaneki ba, bakimin komiba, kuma bazan taba cutar dakeba dan nima banason acutar min da ya, amma kawai dai bani bake ne, kuma ki rabu dani da yata, dama baban kune yahada mu to acigaba a hakan, wuce kawai kifita” sum sum sum tawuce tafita daga dakin ta zauna anan kujerun da aka jera a gaban record inda patient ke jiran folder tana kuka tana shashare fuska. Haka ta zauna awurin o har azahar tawuce tafita taje massallaci tai alwala tai salla ta dawo takara zama a wajen saiduk taji tagaji gawani irin yunwa datake ji, bini bini mum na fitowa saidai ta watsa mata harara takoma ciki, gashi babu wani dan gidan su dayazo balle tadanji dadi, itane azaune awurin har la’asar, duwawun ta har zafi yake sabida zaman kujera, ta tashi ta wuce massallaci tai salla, kwanciya tayi awurin har dan gajeren bacci yay gaba da ita wuraren biyar ta tashi tafito ta wanko fuska tadawo cikin hospital din ta zauna a wurin tanata kallon dakin jin hanayina, ganin Mum tafito ta wuce ta kara zuba mata harara yasa ta mike tsaye tana waigen Mum ganin tai nisa yasa tayi dakin, Khaleel tagani wanan Karan ya chanza kaya zuwa Jean da riga ya zauna akan kujera yana kokarin bude takeaway daya yoma Farida da idonta biyu sai kallonshi yake, dan karasa shigowa dakin tayi tana satan kallanshi, Farida ne ta kalleta dayar muryar ta dabata fita da kyau tace “tun dazu natashi inata tambayan ki ina kikaje?” murmushi ta kakalo tazo kan gadon ta zauna ta wurin kafar Farida tace “ina mosque ne nai salla sai bacci ya kawasheni” tai maganan tana satan kallonshi, dan murmushi yayi ya kalli Farida yace “Mac and cheese ne nakawo zakici ko? Lemme feed u” gyadamai kai tayi tana soft murmushi, fork yasa aciki zai debo yabata da sauri ta tashi ta karbi take away daga hanunshi bakinta har rawa yake tace “un zan.. Zan.. Ni zan bata” ita kanta batasan yaushe tai hakan ba, dago kai yayi ya zuba mata ido itama shi take kallo da kyar ta janye idonta daga nashi jin kwalla yataru ta juya ta kalli Farida dake kallon su tace “is being long bari nizanyi feeding dinki” debo wa tayi takai bakin Faree ahankali ta bude ta karba tana murmushi, shima murmushi yay aranshi sanan yaciro wayarshi daga aljihu yana dannawa bini bini yana satan kallonta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button